BARRISTER SUHAIL

80

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----80


Bayan tafiyarsu…

Gidan ya sake komawa cikin shiru kamar yadda aka saba

A ranar da Ibrahim Khalil ya cika kwana bakwai da haihuwa, aka yi masa taron suna

Ba a gayyaci mutane da yawa ba

’Yan uwa na kusa da wasu abokan arziki kaɗan ne suka halarta

A ɓangaren Iman kuwa

Babu wanda ya samu damar zuwa

Ko Hafsat da ta yi matuƙar son zuwa, daga ƙarshe ta kira ta ce

“Ki yi haƙuri Iman, ba zan samu zuwa ba"

Murmushi kawai Iman ta yi

“Ba damuwa Hafsat, Allah Ya sa haka yafi alkhairi"

Ta kashe wayar

A ranar suna gaba ɗaya

A ɗakinta ta yini

Sai dai tana jin motsin baƙi da dariyarsu daga nesa

Fa’iza kuwa…

Tun da safe ba ta bar Iman ta hutu ba

Duk lokacin da ta shigo ɗakin, sai ta jefa mata wata magana mai zafi

“Wasu dai Allah yana ba su haihuwa ban su huta ai Yara ni’ima ce, da Allah yake ba wanda Ya so wasu luma yayi su a juya haka zasu ta zama a gida suna cika masai"

Iman ba ta ce komai ba

Sai dai ta amsa da murmushi tana ci gaba da abin da ke gabanta

Ba ta nuna damuwa ba

Domin ta riga ta san cewa

Wasu yaƙe-yaƙe ba da baki ake cin su ba

Da haƙuri da addu’a ake cin su.

A wannan ranar ma

Bayan ta idar da sallolinta, ta ci gaba da karatun Alƙur’ani cikin nutsuwa.

Fuskarta cike take da kwanciyar hankali

Duk wanda ya gan ta…

Ba zai taɓa tsammanin irin abubuwan da take fuskanta ba

Amma a zuciyarta

Ta riga ta yanke hukunci

Za ta ci gaba da zama mutuniyar kirki 

Komai halin da mutane za su nuna mata komai maganganun da mutane zasu mata 

zata cigaba da haƙuri har zuwa yadda Allah ya tsara mata Rayuwar ta

40 days later

ranar da Zeenah tacika kwana arba'in da haihuwa tun safe ta shirya ta fita yawon arba'in

gidan yan uwa da kuma dangin su dake cikin garin Abuja 

tun dafe data fita ba ita ta dawo ba sai bayan Sallar isha'i

duk da Suhail yaso ta biya. gidan Aunty Zarah amman ta daƙa tsalle ta ce"wallahi bazata je ba zarar da har ko barka batayi mata ba zuwan mi zatayi gidan ta"

jin hakan yasa Suhail bai kara magana ba 

bayan kwana biyu ya faɗa masu su shirya zasu je kaduna su duba jikin Mami 

Suhail ya riga su fitowa 

hannunsa riƙe da Khalil yana masa wasa a mota

zeenah ta fito sanye take da wani haɗaɗɗen applique lace dinkin doguwar riga duk ya fitar da shape din jikin ta 

da kyar take tafiya ta kawo wani dan karamin mayafi ta saka a samar kanta 

hannunta riƙe da wata haddiyyar hand bag mai tsada wada tayi kala da hill din dake kafarta

idan ka ganta bata da maraba da irin ƴan matan nan masu rawar kai babu wanda zai ganta yayi tunanin ita ce ta haifi khalil Tafiyarta cike take da izza, kamshin turarenta ya mamaye harabar gidan

ta nufi wajen motar a front seat ta zauna 

ganin Suhail baida niyar tada motar su tafi zeenah ta ce"ba tafiya zamuyi ba"

duban ya kai kan agogon dake da daure a hannunsa ya ce"sai iman ta fito"

wani irin kallo tayi masa ta ce"dama har da ita zamu tafi"

kai ya Daga mata ya ce"sure"

bata ƙara magana ba ta mirror ta hango fitowar iman dakw sanye da atamfa anyi mata riga da siket 3 quarter ta yafa wani farin mayafi hannun ta riƙe da farar jaka kirar gucci tare da farin flate su

duk da ba wani make up tayi ba, natsuwa da kamala sun ƙara mara kwarjini fiye da tunanin mai karatu

har ta shigo cikin motar Suhail bai sauke idon sa daga kanta 

yau tayi masa wani irin kyau fiye da ko yaushe 

sai dai ta rame sosai

da sallama ta shiga cika motar 

Suhail ya amsa 

gyara zaman sa yayi ya dauki Khalil dake kan ciyar sa ya zai miƙa iman 

zeeenah tayi saurin karɓe sa

Suhail ya ce"bazaki bata ta taya ki riƙon saba"

tsaki taja tare da harara lokacin guda ta ce"ɗa na bazai zauna hannun bare ba"

ran Suhail ya baci ya dubi zeenah ya ce"Iman din ce bare"

"Eh,mana ai bata da alaƙa dashi may be da ta haihu ne za'ayi dan ganta yaran ta a matsayin uban su ɗaya"

Suhail bai ƙara Magana haja motar suka tafi 

tun kafin su fita daga Kaduna Khalil ya soma rigima kuka yake sosai zeenah ta rasa yadda zatayi dashi dan ba wai ta Saba renon sa bane kullum ya hannun jennifer

tayi masa rarrashin duniya amman yaƙi yayi shiru ko ta bashi nono ma baya amsa 

ta dubi Suhail da hankalin gaba daya yana wajen tuƙi tamkar baya jin kukan da Khalil ya ke 

ta ce"Wai Suhail mi kake nufi baza ka tayi mi rarrashin saba"

"tunda ba zaije hannun bare ba ai nima bai kamata yazo hannu na ba dan haka ki cigaba da lallashin har yayi shiru"

zeenah ta kule hakan yasa ta ajiye Khalil ya cigaba da kukan sai gab da zasu shiga Abuja bacci ya dauke sa



KUYI HAƘURI DA WANNAN WLH BIKI MUKE KO KADAN DIN MA DA KYAR NAKE SAMUN LOKACI NAYI SABODA KAR KUJI SHIRU BABU DADI 

BABU POSTING GOBE SAI JIBI IDAN ALLAH YA KAIMU