82
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
💖 Dedicated To My Mom 💖
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️—82
Haka ta juya ta fice daga ɗakin ba tare da ta damu da halin da ya shiga ba
Mami ma ta firgita
Ko da yake zuciyarta cike take da fushi, ganin ɗanta kwance babu motsi ya sa gabanta ya faɗi
Hankalinta ya tashi matuƙa Da ƙyar ta iya rarrafe ta fito ta kira mai gadi
Tare suka dawo ɗakin, har yanzu Suhail na kwance ba ya motsi
Da sauri mai gadin ya ɗebo ruwa ya yayyafa masa Nan take ya sauke ajiyar zuciya, amma ya ji gaba ɗaya jikinsa ya yi nauyi Duk yadda ya yi ƙoƙarin tashi ya kasa.
Hawaye kuwa suka fara zuba ta gefen idanunsa yayin da yake tuna abin da ya faru
⸻
Iman kuwa, da ta bar ɗakin Mami, kai tsaye ɗakinta ta koma Ta janyo trolley ɗinta, ta fara zuba kaya babu tsari, ko ita kanta ba ta san abin da take sakawa ba
Da ta gama, ta ɗauki handbag ɗinta ta fito.
Ko da dare ya riga ya yi, hakan bai hana ta barin gidan ba
Tafiya take yi tana kuka har ba ta ganin gaban ta Da ƙyar ta samu Napep wanda ya kai ta tashar mota
Motar Kaduna ta shiga Babu wani fasinja, hakan ya sa direban ya tambaye ta,
“Hajiya, za ki iya ɗaukar shata ne mu tafi?”
Kai kawai ta ɗaga masa, domin bakin nata ya daɗe da mutuwa
Nan take suka kama hanya
Karfe tara na dare suka isa Kaduna
Da direban ya lura da yadda tashin hankali ya bayyana ƙarara a fuskarta, kuma ga ita mace ce ita kaɗai cikin dare, sai ya kai ta har ƙofar gidan.
Tana yi masa kwatance har suka iso.
Ya sauke mata trolley ɗin.
Ta buɗe handbag ɗinta, ta ciro kuɗi ba tare da ta ƙirga ba ta miƙa masa
Ya karɓa cikin godiya
Ita kuma ta ja trolley ɗinta ta shiga gidan
⸻
A lokacin, Ammi na zaune a ɗakin Malam tana dama masa fura suna hira
Tun bayan bikin Mubarak, kusan shekara guda kenan, babu ranar da ba su tuna Iman ba
Hafsat kuwa na zaune a tsakar gida tana cin tuwon da Ammi ta zuba mata
Iman ta shigo tsakar gidan
Ta saki trolley ɗinta a wurin, sannan ta ruga zuwa ɗakinta.
ta hau kan gado, ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, kukan da tun dazun take dannewa
Hafsat ta razana
Da farko ma sai da ta tabbatar da cewa Iman ce
Ta bi bayanta zuwa ɗakin, amma ganin yadda take kuka ya ƙara saka mata tsoro
Da gudu ta koma ɗakin Malam.
Ta yi sallama.
Ammi ta ce
“Shigo"
Tana haki ta ce
“Ammi… Iman ce ta shigo… tana kuka.”
Kafin ta ƙarasa maganar, Ammi ta miƙe tsaye.
“Wace Iman ɗin? Ina take?”
Hafsat ta nuna mata hanyar ɗakin
Da gudu Ammi ta nufi can, har zanin jikinta na neman kwacewa
Malam ma ya biyo bayanta
Suka tarar da Iman ta lulluɓe fuskarta cikin hijabi tana kuka mai tsuma zuciya
Duk ƙoƙarin da Ammi ta yi na janye hijabin daga fuskarta ya ci tura
Malam ya fara tambayarta cikin nutsuwa
“Khadija, lafiya? Me ya faru? Me ya kawo ki cikin wannan dare?”
Amma babu amsa
Kuka kawai take yi
Sama da awa guda suna tambayarta abin da ya faru, amma ta ƙi cewa komai
Daga ƙarshe Malam ya ce
“Ku ƙyaleta tukuna Bari na kira Suhail, na ji abin da ke faruwa.”
Ya koma ɗakinsa, ya ɗauki wayarsa.
Kira sama da biyar ya yi wa Suhail, amma bai ɗaga ba.
Ya dawo ya shaida wa Ammi.
Nan take Ammi ta fusata
“Malam, ai dama ba zai ɗaga ba Allah kaɗai ya san abin da suka yi wa yarinyar nan har suka kore ta cikin dare"
Malam ya ce,
“Haba Maryama Ki zama mai kyautata zato mana mu fara jin ta bakin Suhail tukuna Tunda Khadija ta ƙi magana.”
Ammi ta girgiza kai
“Malam, ba ka san halin wasu masu kuɗi ba. Ni ma fatana kawai Allah Ya sa ba cutar da ita suka yi ba.”
Malam ya ce
“ki kiyi kuma"
Ya juya ya fita
⸻
Haka aka kwana cikin tashin hankali
Iman ta ƙi magana da kowa
Idan aka tambaye ta, kallo kawai take binsu da shi
Ga kuma wani zazzaɓi da ya rufe ta
Jikinta ya yi zafi matuka
Har Ammi ta riƙa jika zani tana shafa mata a jiki, amma duk da haka zafin bai sauka ba
Washegari da sassafe, zazzaɓin Iman ya ƙara tsananta
Har yanzu ba ta ce uffan ba
Idanunta sun kumbura saboda yawan kukan da ta yi cikin dare
Ammi kuwa ta rasa abin yi Duk lokacin da ta kalli fuskar Iman, zuciyarta sai ta ƙara cika da tausayinta
Malan ya gama shirin fita masallaci, amma kafin ya tafi ya ce,
“Maryama, idan har zuwa ƙarfe goma ba ta samu sauƙi ba, ku kai ta asibiti"
Ammi ta gyada kai
“To, Allah Ya ba ta lafiya"
A can gidan Suhail kuwa…
Tun bayan fitar Iman, gidan ya koma tamkar ba a ciki
Mami na zaune a falo cikin damuwa
Ko da yake har yanzu zuciyarta ba ta sauko daga fushin da take yi ba, amma ganin Suhail cikin wannan hali ya fara sa ta jin nadama
Likita ya zo ya duba Suhail
Bayan ya gama dubawa ya ce,
“Babu wata matsala ta jiki mai tsanani Shock ne ya same shi Ya samu matsananciyar damuwa Amma ku tabbatar ya huta sosai.”
Da likitan ya tafi, Mami ta zauna gefen gadon.
“Suhail…”
A hankali ya buɗe idanunsa
Ya juya ya kalli Mami, amma bai ce komai ba
Ta ce
“Ka yi haƙuri Ka tashi ka ci wani abu.”
Ya girgiza kai
“Bana so.”
“Suhail…”
Ya lumshe idanunsa
“Mami… ina Iman?”
Tambayar tasa ta sa zuciyar Mami ta buga
Ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce
“Ta tafi.”
Ya buɗe idanunsa da sauri
“Ina ta tafi?”
“Ban sani ba"
Nan take ya yi ƙoƙarin tashi.
Amma zafin jikinsa ya hana shi
Ya koma ya kwanta
Hawaye suka sake cika masa idanu
“Mami… me ya sa kika yi mata haka?”
Muryarsa cike take da ciwo.
Wallahi Mami, ban taɓa cutar da Iman ba ,Da wane ido zan kalli iyayenta idan wani abu ya same ta?”
Mami ta sunkuyar da kai.
A karon farko tun abin ya faru, ta kasa kallon idon ɗanta
a chan kaduna kuwa
Da ƙarfe goma na safe, Ammi da Hafsat suka kai Iman asibiti
Likita ya duba ta
An auna mata zafin jiki
An saka mata drip saboda jikinta ya bushe
Likitan ya ce
“Ba zazzaɓi kaɗai take yi ba. Tana cikin matsananciyar damuwaKu tabbatar ba ku matsa mata ba"
Ammi ta share hawayen da suka cika idanunta
BP ɗinta ya sauka saboda tashin hankali da rashin cin abinci Ku tabbatar ta samu hutu sosai"
likita ya ce“Allah Ya ba ta lafiya, sannan kafin Ruwan ya kare a sama mata Abinda zata ci"
Ammi ta ce"to likita mun gode"
yana fita Ammi ta dubi iman tace"mi zaki ci ,in samo maki"
"kunu" ta faɗa Ammi kadai ke iya jin maganar ta ko hafsat dake gefe bata ji Abinda ta ce ba
Ammi ta dubi Hafsat ta ce"ki kula da ita zanje gida na dawo yanzu"
kai kawai Hafsat ta daga
ammi na fita bacci yayi awon gaba da iman
a hankali take sauke ajiyar zuciya
hafsat ta na kallon ta wani irin tausayin ta ke ratsa zuciyar ta
wanda batayi aune ba hawaye suka fara zubo mata ta saka bayan hannun ta ta goge
Ammi na komawa gida ta fara hada kunun bayan ta gama ta juye a flask
malan ne ya shigo
hannunsa riƙe da charbi
"Maryama ya jikin Khadijar"
"da sauki malan, yanzu ma kunu take son sha shine na dawo na hada mata"
Malan ya ce"Allah ya sauwake ya bata lafiya"
Ammi ta ce"malan har yanzu baka samu mijin nata a waya ba "
"ban samee shi ba,dazu dana kira ma wayar a kashe"
"Allah yasa dai lafiya,ba wani anu ya same shi ba "
Malan ya ce"Amin"
Ammi ta hado komai ta fito
Malan ne ya taro mata mai keke ya ce"zuwa anjima zaizo dan kar ya tafi Suhail yazo"
har Ammi ta koma asibitin iman bata farka ba sai gab da Sallar Azahar ta farka
koda Ruwan ya kare hafsat ce ta cire mata
bayan ta farka ta dubi Ammi ta ce"zatayi sallah"
Ammi ta kamata ta kaita bandakin ta yi mata Alwala da bazata iya ba jikin ta yayi weak
ta saka mata hijabi ta shimfida mata abin Sallah
a zaune ta gabatar da sallar bayan ta gama Ammi ta dauko flask ta zuba mata kunun
ta miƙa mata
"hafsat ke bazaki sha kunun ba"
kai ta Girgiza "na koshi Ammi"
iman ta sha fiye da rabin kofin
a hankali ta soma tashin zuciya batayi aune gaba daya ta dawo da kunun data sha
Ammi sai faman sannu take yi mata
hafsat ta cire mata hijabin da amman ya zuba akan ta ta maidata kan gado ya gyara wajen
Ammi ta koma office din likitan dan faɗa masa Abinda ke faruwa
tare suka dawo dakin
iman na kwance akan gado
ya karaso kusa da ita "sannu khadija"
kai kawai ta daga masa
Likita ya kare mata kallo sosai ya dubi Ammi ya ce"zan turo nurse zata dauki jinin ta Akwai awon da za'ayi mata"
Ammo ta dube sa a raunane ta ce"likita wani abu ne ya same ta"
murmushi yayi ya ce"ba wani abu bane ki kwantar da hankali ki everthing will be fine in sha Allah"
likitan na fita ba dadewa nurse ta shigo ta dauki jinin iman da kyar ta bari aka dauka
suna nan zaune kusan awa guda likita ya dawo hannun sa rike da wata farar takarda
fuskar dauke da murmushi
ya kalli Ammi da taki daina kallon sa ya ce"mama congratulation Diyar ki na dauke da juna biyu na tsawon sati ukku"
Maganar likitan ta sauka a kunnen Ammi kamar walkiya
Ta zaro idanu tana kallonsa
“Likita… me ka ce?”
Likitan ya sake murmushi.
“Na ce, mama, diyarki na ɗauke da juna biyu Kimanin sati uku kenan"
Hafsat ta saki baki
“Subhanallah!”
Ita kuwa Iman…
Da jin kalmar juna biyu, sai ta dafe cikinta da hannu biyu
Hawayen da ta yi ta dannewa suka sake kwaranya
Kai ta girgiza a hankali
“A’a…”
Ta faɗa cikin muryar da kyar ake ji
“A’a… ba na so.”
Ammi ta matso kusa da ita.
“Khadija…”
Iman ta fashe da kuka
“Ammi… ba na son cikin nan"
Kalmar ta gigita kowa
“Likita…”
Ta juya tana kallonsa da idanunta cike da hawaye
“Don Allah… a cire min shi"
Ammi ta zaro ido
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Khadija! Me kike cewa?”
Iman ta ƙara rushewa da kuka
“Don Allah Ammi… bana son wannan cikin. A cire min shi"
Ammi ta kama hannunta
“Saboda me? Wannan ai ni’ima ce daga Allah da Kin daɗe kina fatan samun zuri’a, yanzu kuma kina cewa a cire?”
Iman ta girgiza kai.
“Ba zan iya ba…”
“Me ya faru?”
Ta yi shir
“Khadija, ki gaya mana"
Likitan ya kalli Ammi
“Zan ba ku ɗan lokaci Idan kun gama sai a kira ni.”
Ya fita tare da nurse
Shiru ya mamaye ɗakin
Sai ƙarar kukan Iman kawai ake ji.
Ammi ta zauna gefenta
Ta kamo hannunta cikin taushin murya
“Yata… ki gaya min abin da ke damunki"
Iman ta share hawayenta.
Ta kalli Ammi
Sannan ta ce cikin rawar murya,
“Ammi…”
“Na’am, Khadija.”
“Na dawo gida saboda"
Ammi ta daure fuska
Hafsat ta matsa kusa
“Ki yi magana mana"
Iman ta lumshe idanu
Wasu sababbin hawaye suka zubo
A hankali ta ce
“Saboda… Suhail…”
Ta yi shiru na ɗan lokaci
"ya sake ni.”
Duk ɗakin ya yi tsit
Ammi ta tsaya cak
Hafsat ma ta rasa abin cewa.
Da ƙyar Ammi ta furta,
“saki”
Iman ta fashe da kuka.
“Maman sa ce tasa ya sake ni"
Ta dafe fuskarta.
Ammi ta dafe ƙirji.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel…”
Hafsat kuwa ta fara kuka
Iman ta cigaba da magana cikin kuka.
“Shi ya sa bana son cikin nan"
“Idan na haifi wannan yaron…”
“Zai tashi ba tare da mahaifi ba"
“Ba na son ya rayu irin rayuwar da zan ba shi"
Ammi ta rungume ta da ƙarfi."
“A’a Khadija.”
“Ko me ya faru tsakanin ki da Suhail…”
“Ba za mu taɓa kashe rai saboda wannan ba"
“Yaron nan ba shi da laifi."
“Allah ne Ya ba ki amanarsa"
Iman ta ƙara fashewa da kuka
Ammi kuwa ta ci gaba da shafa bayanta
Amma a zuciyarta
Tambaya ɗaya ce kawai ke yawo
shin iman ta sauku kuwa
like
share and comment