BARRISTER SUHAIL

83

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️—83

hankali Ammi ya tashi matuƙa har ta kasa daure wa ta kira malan yazo asibiti

ta fada masa duk Abinda ke faruwa

cikin ƙanƙanin lokaci ya karaso asibitin ya dubi Ammi da Hafsat ya ce"suje waje yana so zaiyi magana da iman"

haka suka tashi sanyi qlau suka fita waje 

Malan ya yi shiru na wasu daƙiƙu

Ya kalli Iman cike da tausayi

Hawayen da ke idonta suka sa zuciyarsa ta yi nauyi

A hankali ya ce

“Iman… kin san me ya fi bani ciwo?”

Kai ta girgiza

“Ba sakin da aka yi miki ba"

Ta ɗago ta kalle shi

“Abin da ya fi bani ciwo shi ne yadda shaiɗan ya fara rinjayar tunaninki har kike ganin zubar da cikin da Allah Ya ba ki baki tunanin mafita ce"

Nan take Iman ta fashe da kuka

“Abba… na gaji da wannan rayuwar"

Ya ɗaga hannu ya dakatar da ita

“A’a ‘Khadija Ki ce kin gaji da jarabawa, ba rayuwa ba Domin rayuwa ni’ima ce, jarabawa ce kawai ta yi tsanani kuma Allah yana jarabbatar bayin sa na kwarai"

Ya ɗan gyara zama

“Ki saurare ni da kyau"

“Allah da Ya ba ki wannan ciki, bai taɓa yin kuskure ba"

“Wataƙila wannan yaron shi ne zai zama sanadin farin cikinki"

“Wataƙila shi ne zai zama wanda zai share miki hawayen da kika yi tsawon shekaru"

“Wataƙila saboda shi ne Allah Ya rubuta za ki shiga Aljanna"

Ya yi shiru kaɗan

“Kin san Annabi ﷺ ya ce, idan Allah Yana son alheri ga bawansa, sai Ya jarabce shi"

“Saboda haka jarabarki ba alamar Allah Ya ƙi ki ba ce"

“Alama ce cewa Allah Yana kallon haƙurinki"

Iman ta share hawayenta

“Abba  zuciyata tana ciwo"

Malan ya yi murmushi

“Na sani" saki babu dad'i dole zaki ji ciwo

“Ko Annabi Ya’qub ya yi kuka har idanunsa suka yi fari saboda rashin Yusuf"

Amma bai taɓa yanke ƙauna daga rahamar Allah ba

Ya ɗora hannu a kanta

“Iman… ki yi mini alƙawari"

Ta ɗago kai

“Ba za ki sake furta maganar zubar da cikin nan ba"

“Domin wannan ba laifin yaron ba ne"

“Shi bai san rikicin dake tsanin ki da mahaifin sa ba"

“Shi bai san rabuwar auren ku ba"

“Shi bai san wanda ya zalunce ki ba"

“Me ya sa zai zama shi ne zai biya kuɗin abin da bai aikata ba?”


Kalaman suka shiga zuciyar Iman kamar ruwan sanyi.

Ta fashe da kuka mai ƙarfi.

“Na yi nadama Malam kuma bazan sake maganar zubar da cikin ba"

Malan ya ce,

“Allah yana karɓar nadamar bayinsa"

“Ki tashi ki yi alwala"

“Ki yi raka’a biyu"

“Sannan ki ce wa Allah"

‘Ya Allah, idan na yi kuskure Ka gafarta mini Ka ba ni ƙarfin zuciya, Ka sa wannan jariri ya zama alheri a gare ni duniya da lahira"

Ya miƙe tsaye

“Kuma ki tuna wannan magana ta ƙarshe

“Namiji zai iya sake mace"

“Mutane za su iya juya mata baya"

“Amma Allah ba Ya taɓa watsar da bawan da ya dogara gare Shi"

Abba Nagode


“Ki gode wa Allah"

“Domin ina da yaƙinin cewa wata rana za ki tuna da wannan ranar ki ce ita ce ranar da rayuwarki ta sake farawa"

ya ce"ko Akwia Abinda kike buƙata kai ta Girgiza masa alamar babu"

a ranar aka sallamesu daga Asibiti suka koma gida bayan an rubuta mata magungunan da za tayi amfani dasu 

tun bayan farkawar Suhail ya tashi ya koma dakin sa 

tsawon wunin ranar nan ba bi takan kowa ba ya shiga dakin ya rufe kansa 

yana kwance akan gado ji yake tamkar dakin na juya masa 

tun jiya ya ga kiran Malan amman ya ƙasa dagawa yasan warhaka iman ta faɗa masa Abinda ke faruwa bazai iya dagawa ba baisan mi zai ce masu ba 

kunyar Abinda ya aikata masu

Zeenah bata san Abinda ke faruwa ba sai da jennifer ta faɗa mata 

ai Mami tasa Suhail ya saki iman tun jiya ma ta kwashe kayan ta tafi 

zeenah tayi shiru tana tunanin maganar da jennifer ke fada mata 

lallai mami butulu ce duk abinda wannan yarinyar take yi mata da Abinda zata saka mata kenan

    
Ta fara jin tsoron cewa idan wata rana ita ma ta rasa tagomashin Mami, za a iya yi mata irin abin da aka yi wa Iman

haka gidan ya wuni kowa yayi ragam 

mami na zaune a daki yunwa duk tabi ta ishe ta rabon ta da abinci tun jiya da dare wanda iman ta kawo mata 

hakan yasa ta dauko sandar ta da kyar ta nufi cikin gidan

a zaune ta iske zeenah akan kujera tana ba khalil nono

ta shigo tana dogara sanda

a gefe guda ta zauna tama yashe baki"zeenah hala bakin san abinda ke faruwa a gidan ba"

wani kallo tayi mata ta ce"idan naji ma sai me"

Mami ta ce"ai nayi Saboda kene"

tsaki zeenah ta ja ta ce"banda dagula min rayuwa mi kikayi,dama ya muke rayuwa da Suhail a gidan yanzu shikenan kin koreta shi kuma ya kulle kansa a daki"

mami ta saki tana kallon ta "Zeenah ashe baki da mutunci duk Abinda nayi maki shine zaki butul cemin"


zeenah ta ce"ai duk wani butulu ya biyo bayan ki, duk yadda yarinyar nan ke kula dake amman ki rasa da Abinda zaki saka mata sai wannan"

"Allah ma bazai barki ba, wannan kafar ma in sha Allah sai an ida cire ta sai ki koma ki tsugun na 

mami ta fashe da kuka"zeenah Ashe yar iskar yarinya ce ke kuma in sha Allah kafar uwarki za'a cire ba tawa ba shegiya yar iskar marar mutunci”

Zeenah ta mike ta ce”ai uwata bata da hakkin kowa ke dai zaki cigaba da girbar abinda kika shuka"

Mami ta zube a kasa tana birgima har ta fama ciwon ta 

Jini ke zuba zeenah ta kalli Jennifer dake tsaye ta ce”kamata ki fitar mun da ita tun kan ta cika min daki da ƙarnin jini"

Jennifer ta tsaya cak

Ta kasa motsi

Idanunta suna kai komo tsakanin Mami da Zeenah

“hajiya… jini fa na fita"

Zeenah ta yi mata wani irin kallon raini

“Ba na gani ne? Na ce ki fitar da ita"

Mami kuwa tana riƙe da wajen da aka yanke ƙafarta

Zafin da take ji ya sa hawayenta suka gagare tsayawa

Ko kallonta Zeenah ba ta yi ba

Ta rungume Khalil tana girgiza shi

Jennifer ta rasa abin yi

A ƙarshe ta ajiye tsoro

Ta ƙarasa wajen Mami


Ta taimaka mata ta ɗaga jikinta

Sai dai Mami ta kasa tsayawa

Ciwon ya yi mata tsanani sosai

Jennifer ta fara kiran mai gadi

“Security!”

Mai gadi ya shigo da gudu

Da ya ga Mami cikin jini sai ya firgita

“Innalillahi… Hajiya me ya same ki?”

Jennifer ta ce

“taimaka mana mu kai ta ɗakinta"

Su biyu suka ɗaga ta a hankali

Yayin da suke fita

Mami ta waiwayo ta kalli Zeenah.

A karo na farko

Sai hawaye kawai da suka zubo mata.@

A hankali ta ce

“Allah Ya isa tsakanina da ke"

Zeenah ta yi murmushin 

Da wannan ta juya kai ta ci gaba da shayar da Khalil nono


A ɗakin Suhail kuwa

 yana kwance kamar gawa

Wayarsa ta yi ta ringing sau da yawa

Bai ɗaga ba

Ko motsi bai yi ba

Idanunsa sun kumbura saboda yawan kukan da ya yi

A zuciyarsa kuwa

Muryar Iman ce kawai ke yawo

“Yaya Suhail… ka sake ni na koma wajen talakkawan iyayena…”

Ya runtse idanunsa da ƙarfi

“Ya Allah… me na aikata?”

A wannan lokacin

Bai san cewa a cikin gidan sa 

Mami da Zeenah sun fara sabon yaƙi ba

Ya kuma kasa sanin cewa

Wannan yaƙin ne zai fito da gaskiyar da ta daɗe tana ɓoye

su jennifer na kaita daki suka yi fitowar suka barta da kafa 

mami ta dauko wayar ta tayi niyyar kiran zarah tazo ta dauke sai kuma ta fasa dan dole sai ta tambayi dalili ita kuma da kunya ta ce ga Abinda ya faru

hakan yasa ta ƙira naima cikin kuka take fada mata abinda ya faru

ga kuma kafarta dake ciwo dan Allah tazo ta dauke ta tun kafin su rasata 

naima ta ce"ita bata da lokacin zuwa Abuja yanzu"

Amman zata Turo yar aiki da driver su dauko ta

share 
like 
and comment