84
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️—84
Mami ta tattara kayanta ta bar gidan Suhail ba tare da sanin kowa ba
Tun daga wannan ranar
Gidan ya yi shiru
Shirun da ba ya ɗauke da kwanciyar hankali ga ko wanne mutun dake rayuwa a ciki
Sai dai shiru ne da ke cike da baƙin ciki
A gidan malan kuwa…
Rayuwa ta ci gaba da tafiya
Cikin iman na ƙara girma a hankali
Sai dai jikinta ba ya samun ƙarfi
Kusan kullum cikin laulayi take
Ba wani abinci take iya ci ba duk Abinda taci Sai ta amayar dashi
Ruwa kaɗai ke zama acikinta
Ammi da Malam sun dami sossai kan rashin lafiyar ta
Ammi kullum sai ta dafa mata abincin da take ganin wataƙila zai kwanta mata
Amma duk da haka Ba ta iya cin
ta rame fiye da ƙima
Sai dai abin mamaki
Fuskarta kullum cikin ƙara kyau take
Wani irin hasken ciki ya ƙawata fuskarta
Duk wanda ya ganta zai san tana dake da juna biyu
Iyayem ta suna kula da ita fiye da yadda suke kula da kansu hatta Hafsat bata barin ta ko tsinke ta kauda tare suke rainon cikin
Malam kullum bayan sallar Asuba sai ya mata rubuta wanda zai saukaka mata laulayin
A ɗaya ɓangaren kuma
Suhail
Tun bayan rabuwar tasu
Bai taɓa kiran Iman ba
Bai aika saƙo ba
Bai kuma je gidansu ba
Ba don ya manta da ita ba
Sai don yana tsoron kalaman mahaifiyarsa da tayi masa
“Idan ka bi bayanta ko ka dawo da ita gidan nan"
Allah Ya sa nonon da na shayar da kai haramun a gare ka
Waɗannan kalamai kullum suna yawo a cikin kansa.
Suna hana shi samun nutsuwa
Rayuwarsa ta sauya gaba ɗaya
Ya daina zuwa office ya daina fita ko ina baya magana da kowa
Sameer ya yi ta kiransa.
Amma bai ɗaga waya ba.
Wasu lokutan ma
Sai ya kashe wayarsa gaba ɗaya.
Kullum yana killace kansa a ɗaki
Ruwan tea kaɗai yake iya sha wanda yake hada ma kansa
Ko yunwa ba ya ji
Jennifer sau da yawa tana kai masa abinci
Sai dai idan ta dawo
Yadda ta kai shi haka take dawo da shi
baya ko kallon Abincin
Har jikinsa ya soma nuna wa wata irin rama yayi
Gemunsa ya fara fitowa har yana ƙoƙarin cika masa fuskar
Idanunsa sun yi zuru-zuru
Mutumin da kullum yake cikin shiri mai kyau da daukar wanka da ƙamshi
Ya zama tamkar wanda ya rasa Rayuwar sa
Hatta Zeenah
Ya daina ba ta haƙƙinta
Tun bayan rabuwar Iman
Bai sake kwana a ɗakinta ba
Kullum idan dare ya yi
Sai ya killace kansa cikin ɗakinsa
Zeenah ta fara lura da canjin da Suhail yayi
Da farko ta yi tunanin komai zai wuce
Amma da kwanaki suka zama makonni
Sai tsoro ya fara shiga zuciyarta
A karo na farko
Ta fara fahimtar cewa
Ko da Iman ta fita daga gidan
bazata taɓa shiga zuciyar sa ba
Daren ranar
Suhail kuwa yana zaune a gefen gadonsa
Hoton iman daya yake daukar Lokaci zuwa lokaci ya tusa a gaba yana kallo
Idanunsa sun yi jajur saboda rashin barci da baya samu a ƴan kwanakin nan
Sai aka ji ana kwankwasa ƙofar ɗakin
Bai amsa ba
A karo na biyu aka sake bugawa
“Suhail ka buɗe"
Ya gane muryar Zeenah
A sanyaye ya ce
“a buɗe yake"
A hankali ta buɗe ƙofar
Kayan barci ne a jikinta iya gwiwa
Ta ƙaraso cikin ɗakin ta tsaya gabansa
“Suhail…”
Ya ɗaga kai ya kalleta
Ta sauke ajiyar zuciya
“Tun yaushe kake shiga haƙƙina haƙuri ya soma karewa akan hakan"
Ya haɗe gira.
“mi kike nufi"
“Tun bayan tafiyar Iman ka daina shigowa ɗakina"
“Ka daina kula da ni"
“Ni ma fa matarka ce"
“Ko saboda ta tafi sai ka ci gaba da hukunta ni akan laifin da bani na aikata ba"
Suhail ya yi shiru
Bai ce komai ba
Ta sake cewa
“Wallahi ba zan yarda da haka ba"
“Ko matarka ba ta nan… ai ni ina nan ni kake samu wajen iman din da Ni baka samu wajena"
Suhail ya ce"Abubuwa da yawa nake samu wanda ko rabin su bana samu a wajen ki kuma bari na faɗa maki iman ta tafida duk wani farin ciki na da walwala ta"
“Ka ba ni haƙƙina"
Suhail ya lumshe idanunsa
A hankali ya miƙe tsaye
Ya nuna mata ƙofar ɗakin
“Zeenah… ki fita.”
Ta zaro ido
“suhail ni ka ke kora"
“Na ce ki fita"
“Ba nason magaka da kowa"
“Don Allah ki bar ni ni kaɗai"
Ta ɗan yi dariyar takaici
“Saboda Iman?”
“Har yanzu ita ce ke cikin ranka ko to in sha Allah tayi tafiyar da babu dawowa"
Suhail ya ɗan ɗaga murya a karo na farko.
“Na ce ki fita.”
Ta tsaya tana kallonsa.
“basai ka kore ni ba zan fita ba a iya dakin ka ba gidan ka gaba daya zan bar maka"
“Ki bar ni da abin da ke cikin raina.”
Maganar ta tsaya mata a zuciya
Ta juya ta fita
ko da ta shiga ɗakinta
Fushi ya turnuƙe ta
“Saboda wata da aka riga aka sake?
Ta buɗe wardrobe
Ta fara jefa kayanta cikin trolley
Hawaye da fushi suka gauraya a fuskarta
har ta ɗauki Khalil
Sai kuma ta tsaya
Ta kalle sa
A hankali ta mayar da shi kan gadon
Ta ce
“Ka zauna tare da mahaifinka.”
“Shi ya fi buƙatarka fiye da ni"
Ta ja trolley ɗinta.
Ba tare da ta yi sallama da kowa ba
Ta fita daga gidan
Kai tsaye ta shiga motar ta ta nufi Kaduna
A daren nan
Suhail bai ma san cewa Zeenah ta bar gidan ba
Yana nan a zaune cikin ɗakinsa…
Yana kallon hoton Iman
Hawayen da ya daɗe yana ɓoyewa suka sake gangaro masa cikin sauri ya soma goge wa
like
share
and comment
idan kuma comment da liking nafi jin dadin yi maku posting