85
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️—85
a daren nan Zeenah ta isa gidan Mahaifin janye da trolley din ta
hajiya rabi na falo tana kallon wani series da mamaki
ta ga zeenah na shigo da jaka
tun kafin ta zauna
mummy ta ce"zeenah daga ina kike da kaya haka"
turo baƙi zeenah tayi ta ce"mummy Suhail ne ya ko reni"
mummy ta ce"ya koreki kamar yaya hala wani laifin kika yi masa ko"
"mummy ni ba Abinda na masa"
"ina kika baro shi khalil din"
zeenah ta kauda kai
"ba barshi wajen mahaifinsa"
tsawa mummy ta daƙa mata
"zeenah kina hauka ne yaro karami irin wannan zaki Bari a gida"
"zeenah anya kin san minene haihuwa,ke kuwa ce komai"
cikin fushi zeenah ta ce"mummy ba shine ya koreni ba, saboda mi zan taho da shi bayan ba dashi naje ba"
Mummy ta ce"kin tabbata marar imani zeenah,ke haka aka maki idan da haka na rene ki ai bazaki kai labari ba"
ƙasa tayi da kai
Mummy faɗa take mata ta ida take shiga ba ta nan take fita ba
daga karshe ta mummy ta tashi ta ce"gobe mahaifinki zai dawo sai ki shirya fada masa Abinda ya hadaki da Suhail har ya koro ki nasan ba ƙaramin abu kikayi masa har ya yanke Wannan hukunci a kanki"
a nan ta barta
Zeenah ta zauna tana kuka.
A karo na farko
Ta fara jin nauyin abin da ta aikata
na baro Khalil da tayi
a gidan Suhail babu wanda ya san da tafiyar zeenah
sai mai gadi dalilin buɗe mata kofa da yayi
jennifer ce zaune a falo tun shigowar take juyo sautin kukan khalil daya karaɗe ko ina
jin kukan ya soma yawa,ta tashi da sauri ra nufi cikin dakin
yana jikin gado ya sauko ƙafafuwan sa ƙasa kadan ya hana shi fadowa
cikin hanzari ta taro sa ta fara dube duben dakin bata ga zeenah ba ta daga bathroom nan ma babu kowa
ga dakin duk a hargize
hakan yasa ta duba parking space ta window
babu motar zeenah ,hakan ya tabbatar mata da bata gidan
ga Khalil sai kuka yake
ta nufi dakin Suhail
knocking take ba ƙyaukyautawa
jin haka yasa Suhail ya ƙasa daure wa sai da buɗe jennifer ce riƙe da Khalil
tsabar kukan da yake har ya soma fita daga hayyacin sa
da sauri ya karbe sa daga hannun ta
ya ce"ina zeenah din ta barshi yana kuka"
jennifer ta ce"sir bata nan"
Suhail ya ce"ina ta tafi"
nima ban sani ba ina zaune a falo na jiyo kukan Khalil ina shiga dakin naga yana dab da fado wa
koda na duba nata cikin dakin na duba parking space naga ba motan ta a wajen
Suhail ya sauke ajiyar zuciya
kenan zeenah data ce zata tafi sai da ta tafi kuma shine zata bar masa yaro
Suhail ya dubi jennifer ya ce"jeki hado masa madara ki kawo min na bashi"
ba tare da bata lokaci ta dawo masa da madarar ya amsa ya koma dakin ya fara bashi
sai da yasha Fiye da rabin feedar
kan kace mi ya dauke sa Suhail ya kwantar dashi a gefen gadon ya bishi da kallo
wanda baya wuce na tausayin da da yake ji,gaba daya Alhakin ya dan ƙawa mami
dan ita ce Ummul a basin duk wani abu daya faru a gidan
ya yanke shawarar gobe zaije ya dawo ta zeenah ta cigaba da kula sa khalil
a haka shima baccin ya dauke sa
bashi ya farka ba sai asuba cikin Sa'a ko Khalil bai masa rigima ba sai dai lokaci zuwa lokaci yakan tashi
data bashi ruwa sai ya koma ya kwanta
a gida yayi sallar Asuba bayan gari ya soma wayewa
ya dauki Khalil ya kaiwa jennifer tayi masa wanka ta shirya zasu fita
shima ya daw dakin sa wanka yayi ya shirya cikin wani black egypian yard mai kyau da tsada
ya fito daidai lokacin jennifer ta gama shirya khalil cikin wasu kayan riga da wando brown color ya cika su dan Khalil irin yaran nan ne masu girman jiki
duk da baifi wata tara da haihuwa ba idan ka gansa zakayi tunanin yafi shekara guda
Suhail ya amshe sa zasu fita
jennifer tace"sir na gama breakfast"
Suhail ya ce"thanks bana buƙata"
haka ta juya ta koma ciki
Suhail ya zaunar da khalil a front seat ya saka mashi seat bell
haka ya bashi hadin kai ya na kallon titi yana wasa abinda
Suhail bai tsaya ko ina ba sai kofar gidan aunty Zarah
horn yayi mai gadi ya buɗe masa
ya fito ya dauki Khalil suka shiga ciki
aunty Zarah na bakin dining tana tattara kayan da sukayi breakfast fa
Suhail ya shiga
Da sallama a bakin sa
Aunty Zarah ta amsa tana juyowa
Da farko idanunta suka sauka kan Khalil.
Sai kuma kan Suhail.
Nan take ta haɗe gira
Tare da furta “Subhanallah… Suhail”
A Wani irin yanayi ganin Suhail
Ta ci gaba da kallonsa
ya yi Baƙi
Ya rame
Gemunsa ya cika da gashi
Idanunsa sun kumbura tamkar wanda bai san barci ba tsawon kwanaki
ta matso kusa dashi
"suhail miya same ka"
kai ya girgiza mata babu komai aunty
kama shi tayi ta zaunar da shi kan kujera
ta amshi khalil daga hannun sa
“A’a Wannan ba fuskar mutumin da babu komai ba ce ka fada min miyasa same ka"
Suhail ya runtse idanunsa
"ina iman"
bai iya amsawa ba
ta sake tambaya
"bata gidan" shine abinda ya faɗa
aunty zarah ta ce"tana ina"
ya hadiye yawu da kyar
"mun rabu"
Aunty Zarah ta tsaya cak
Ta kafe shi da ido
Khalil ma da ke hannunta ta kusa zubewa saboda gigicewa
"innalillahi wa'inna illahir rajiu'un"*3
shi kadai ta iya furtawa
Ta zauna a kujera saboda tashin hankali
“Yaushe hakan ya faru Suhail"
“Kimanin wata ukku kenan"
Aunty Zarah ta ɗaga kai a hankali
Aunty Zarah ta ɗaga kai a hankali
“Wata ukku"
“Kana cikin wannan bala’in tsawon wata ukku… amma ka kasa sanar da ni?
“ko ka ga bai dace na sani ba?”
Suhail ya sunkuyar da kai
“Ki yi haƙuri Aunty…”
Ta katse shi
kaine abin ba haƙuri suhail ba ni ba
“Ka ci amanar Iyayen Iman"
“Ka ci amanar yarinyar da aka ba ka amana"
“Har ni ma ka ci amanata"
Idanun Suhail suka cika da hawaye
“Aunty…ki saurareni ba laifi na bane mami ce ta tilastamin sai na sake ta"
“Ka yi min shiru Suhail"
Ta nuna shi da yatsa
“Ku duka ku da Mami kun zama masu bin zuciya"
“ina tunanin za ka tsaya ka kare gaskiya"
“Ashe kai ma idan aka matsa ka, sai ka zubar da wanda bai ji bai gani ba"
Suhail ya girgiza kai
Wa ya riƙe hannunka?”
“Wa ya ce maka ka yi wa Allah tawaye saboda biyayya ga mutum?”
Ta matso gabansa
“Suhail… ina karatunka?”
“Ina iliminka?”
“Ina hujjojin da kake kare mutane da su a kotu?”
“Ko duka sun ƙare ne a ranar da aka zo kan rayuwarka?
Suhail ya kasa ɗaga kai
Hawaye suka gangaro masa
A hankali ya ce
“Mami ta ce idan na bi bayan Iman… ko na dawo da ita gida… Allah Ya sa nonon da ta shayar da ni haramun a gare ni"
Aunty Zarah ta ɗan yi shiru
Sai ta sauke ajiyar zuciya
Ta ce
“Wa ya gaya maka fushin iyaye yana tattare da saɓawa Allah?”
“Idan iyaye suka umurci ɗansu da zalunci… addini bai ce ya aikata zaluncin ba"
“Biyayya tana cikin abin da Allah Ya halatta"
“Ba cikin danniya da zalunci ba"
Ta share hawayenta
“Ka san me ya fi bani ciwo?”
Kai ya girgiza
“Yarinyar nan ta yi wa Mami hidima fiye da yadda wasu ‘ya’ya suke yi wa iyayensu"
“Amma sakamakonta shi ne saki?”
“Saboda ba ta haihu ba?”
“Ko kuma saboda ta yi haƙuri fiye da kima?”
Shiru ya mamaye falon
Suhail yana kuka kamar ƙaramin yaro
A ƙarshe Aunty Zarah ta miƙe tsaye
Ta kalli Khalil
Ta sake kallon Suhail
Cikin sanyin murya mai cike da ɓacin rai ta ce"
“Tun wuri ka je ka nemi matarka"
“Ka je ka nemi gafararta"
“Idan har ba ta gama iddarta ba… ka dawo da ita cikin mutunci"
“Domin wallahi idan ka ci gaba da wannan shiru… wata rana za ka yi nadamar da ba za ta amfani kowa ba"
Ta juya zata tafi
Sai kuma ta tsaya
Ba tare da ta waiwayo ba ta ce,
“Daga yau… kada ka sake zuwa gidana"
“Har sai ranar da ka maido Iman gidanka"
“Saboda yau… ban ga Suhail a gaba na ba"
“Na ga wani mutum da ya bari tsoro ya rinjayi adalcin sa"
Da waɗannan kalaman
Ta shiga ɗakinta
Ta rufe ƙofa
Ta bar Suhail tsaye a tsakiyar falo
Tamkar an cire masa numfashi