BARRISTER SUHAIL

86

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️—86

Suhail ya daɗe zaune a falon gidan Aunty Zarah

Ko motsi bai yi ba

Kalaman da ta gaya masa suna ta maimaituwa a cikin kunnuwansa

“Na ga wani mutum da ya bari tsoro ya rinjayi adalcinsa…”

Ya lumshe idanunsa

Hawayen da ya yi ƙoƙarin dannewa suka sake gangarowa.

A hankali ya ɗauki Khalil

Ya sumbaci goshinsa

“Ka yi haƙuri ɗana…”

“Ni kaina ban san inda rayuwata ta dosa ba"

Ya miƙe tsaye.

Cikin sanyin jiki ya nufi mota


Hajiya rabi mahaifiyar zeeenah tun ajiya ta kira Alhaji ibrahim ta faɗa masa Abinda ke faruwa

Alhaji ibrahim ya ce "gashi nan zuwa gobe in sha Allah"

Da misalin ƙarfe goma na safe

Motar Alhaji Bashir ta tsaya a harabar gidan

dakin sa ya nufa koda ya shiga ya dauki wayar sa ya kira suhail

ya tambaye sa mike faruwa tsakanin sa da zeenah 

Suhail ya ce"gashi nan zuwa yana dap da zuwa gidan"

Alhaji ibrahim ya ce"Allah ya kawo ka lafiya"

ba'ayi mintuna talatin da gama wayar ba Suhail ya ƙaraso gidan

Alhaji ibrahim da kanshi ya fita ya taro sa suka shigo cikin dakin

amsar khalil yayi daga hannun sa 

ya gaishe dashi cikin ladabi

Abba ya amsa 

ya lura da yanayin fuskar sa gaba daya baya cikin hayyacin sa 

Suhail ya chanza fiye da yadda ya sanshi a baya 

wayar sa ya dauka ya kira hajiya rabi ta turo masa zeenah  yanzu

Ba tare da ta tambayi dalili ba ta fita zuwa dakin zeenah ta fada mata mahaifin na san ganin ta

Bayan minti kaɗan

Zeenah ta shigo

ganin Suhail zaune a ƙasa yasa ta hade fuskar ta 

ta sami waje gefe guda ta zauna 

Alhaji ibrahim ya gyara zaman sa ya dubi Suhail ya ce

"Jiya zeenah ta dawo gida a yadda ta fada ma mahaifiyarta ta ce kai ne ka kore ta amman naga ya dace na haɗa ku waje guda dan jin abinda ke faruwa"

ya dubi zeenah ya ce"ke ce zaki fara magana"

“Me ya faru tsakaninki da mijinki?”

Zeenah ta ɗan yi shiru

Sai ta ce

“Daddy Tun bayan tafiyar matarsa… ya daina ba ni haƙƙina na aure"

"Ko ɗakina baya zuwa"

“Na yi ta haƙuri"

“Ranar da na iske shi mace masa ma gaji haƙƙina nake buƙata a matsayina na matar sa shi ne ya koreni"

ta kai Maganar kenan Hajiya rabi na shigowa dakin 

mutuwar tsaye tayi jin abinda zeenah take faɗa a gaban mahaifin ta da kuma mijin ta 

Suhail ya zaro ido mamaki ya kashe shi a zaune

Bai taɓa tunanin Zeenah za ta iya faɗar irin wannan magana a gaban iyayenta  ba

Kunya ta rufe shi

Ya sunkuyar da kansa

Kafin kowa yayi magana

Alhaji Ibrahim ya ɗauki remote ɗin da ke gabansa

da bugi bakin zeenah

kan kace mi bakin ya kumbura yayi suntum 

tsawa ya daka mata 

"zeenah ke wata irin marar hankalin yarinya ce"

"baki da kunya ne"

"a gaba na kike fadar wannan maganar"

“Idan akwai matsala tsakanin mata da miji… haka ake fito da ita?”

Zeenah ta fashe da kuka"

“Daddy"

"kimin shiru zeenah bana son ji wani abu daga bakin ki"

nuni yayi mata da ƙofa 
"fita ki ban waje"

Da sauri ta fita tana kuka.

Alhaji Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya

Ya juya ya dubi Suhail

“Suhail,nasan ba iya wannan ke damunku kaba,fada min miya chanza haka kar ka ɗauke ni a Matsayin siriki ka dauke ni tamkar mahaifinka"

"ka fadamin miya rabaka da matarka"

Suhail ya yi shiru

Na wasu daƙiƙu

Sai hawaye suka cika masa ido

A hankali

Ya fara ba shi labarin komai

yadda mami ta tilasta mata masa akan sai ya saki iman 

har i zuwa furucin da tayi masa 

koda ya gama

Alhaji Ibrahim ya daɗe yana kallonsa

Sai kuma ya girgiza kai


“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.”

“Allah Ya jarabce ka da babbar fitina Suhail"

Ya matsa kusa da Shi

Ya ɗora masa hannu a kafaɗa

“Amma ka sani…”


“Uwa tana da matsayi"

“Amma ita ma Allah ne Ya ba ta wannan matsayi"

“Ba a amfani da wannan matsayi wajen zaluntar wani "

Ya ci gaba da cewa

“Yanzu abin da ya rage maka shi ne ka yawaita tuba zuwa ga Allah dan al'amarin saki babban ne"

“Ka roƙi Allah Ya buɗe maka hanyar da zaka gyara abinda ka ɓata"

“Idan har akwai damar dawo da aurenku cikin shari’a… kada ka yi wasa ka dawo da ita ko zaka samu natsuwa"

Abba duk wasu kalmomi daya san zasu kwantar Suhail da hankali yayi masa 

shine mutun na farko daya bashi goyon baya ya kuma fahimce sa tun bayan faruwar al'amarin

Aunty Zarah ma daya ke gani kamar zai sami kwanciyar hankali a wajen ta 

itama daga karshe korarsa yayi

duk sanda ya tuno Wannan abun a zuciyar yanajin ƙiyayyar mami a ransa

Abba yasa a kawo masu Abinci 

cikin Sa'a Suhail yaci abincin sossai rabon dacin abinci irin haka har ya manta 

bayan sun gama Abba ya shiga cikin gidan 

a falo ya iske zeenah har lokacin kuka take 

“Zeenah!”

Ta shigo kanta a sunkuye

Bai ko kalle ta ba

Ya ce

“Ki shirya"

“Ki bi mijinki  ku koma gida"

“Ki je ki gyara abin da kika ɓata"

“Kuma ki sani"

“Gidan aure ba gidan wasa ba ne da rashin hankali"

“Na haife ki ne domin ki zama mace ta gari… ba mai ƙara hura wutar rikici tsakanin da miji ba"

a halin da Suhail ya ke ciki "kula yake buƙata da janyo sa a ciki Har zuwa lokaci da Allah zai yaye masa damuwar sa"

Zeenah ta share hawayenta

ta jinjina kai 

"tashi maza ki hado kayan kizo ku tafi ga Khalil nan ma yayi Bacci"

har baƙin mota hajiya rabi ta raƙo Diyar Tata

nasiha take yi mata akan tabi mijinta kuma ta rage ƙorafi 

Abba ya basu driver ya kaisu har kaduna a motar da Zeenah tazo da ita

like 
share 
comment