87
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️—87
Bayan Suhail ya bar gidan Aunty Zarah
Tun daga lokacin da ya fita Aunty Zarah ta kasa samun nutsuwa
Ta zauna a falo tana kuka
Kalaman Suhail da halin da ta gan shi suna ta dawo mata a rai
Cikin ƙanƙanin lokaci, Sadeeq ya dawo daga kai Amatullah da Junaid makaranta
ko da ya shiga falon ya ga idanunta sun kumbura saboda kuka da take
Ya ƙarasa kusa da ita cikin damuwa
“Zarah… lafiya?”
Ta share hawaye
“Lafiya lau"
Ya girgiza kai
“Ba zan yarda ba Me ya faru? haka kawai bazaki zauna kina kukan da bashi da dalili ba"
Nan ta ba shi labarin komai
tun da yadda Suhail yazo
yadda ya rame…
Har yadda ya furta cewa ya saki Iman saboda matsin lambar Mami
da kuma yadda ta koreshi daga gidan a fusace
Sadeeq ya daɗe yana shiru
Daga ƙarshe ya sauke ajiyar zuciya
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un"
“Babu shakka an yi babban kuskure"
"kuma kema kinyi kuskuren korar sa daki kayi"
Ya dubeta
Me kike son yi?”
Ta ce
“Ina son zuwa Kaduna.”
“In ga Iman"
“In tabbatar da halin da take ciki"
Sadeeq ya jinjina kai
“Ki je"
“Amma ki kwantar da hankalinki"
“Kar fushinki ya sa ki faɗi abin da zai ƙara dagula al’amura”
Ta ce
“Na yi maka alkawari.”
Sai dai a zuciyarta
Ta san ba za ta iya yin shiru ba idan ta ga an zalunci yarinyar da bata san hawa ba bare sauka
Nan take ta kira driver
Ba tare da ɓata lokaci ba ta shirya suka kama hanyar Kaduna
Bayan doguwar tafiya
tana bin kwantacen da suhail yayi mata kwanaki na gidan su iman
lokacin bikin Mubarak
duk da bata samu damar zuwa ba
amman ta riƙe
ko da suka shiga cikin layin da tambaya har suka karasa kofar gidan Malan
Aunty Zarah ta fito
duk da faduwar gaban da take ji a haka ta daure ta shiga
dauke da sallama a bakin ta
iman da Hafsat na zaune ƙarƙashin inuwar suna cin dambun shinkafar da Ammi tayi
Da jin motsin ƙafa
Iman ta ɗago
Idanunsu suka haɗu
Nan take Iman ta miƙe tsaye cikin mamaki
“Aunty Zarah kece a gidan mu"
Zarah kuwa
Ta tsaya cak
Idanunta suka sauka kan cikin Iman
Cikin da ya riga ya fara bayyana
Jakar hannunta ta zame ta faɗi ƙasa
Bakinta ya kasa furta komai
Iman ma ta kasa matsowa gare ta
A wannan lokacin Ammi ta fito daga ɗaki
Da murmushi ta ce,
“sannu da zuwa"
iman ta bata Labarin yadda tayi Rayuwaa gidan Suhail da kuma yadda mami da Naima suka takura mata
da yadda aunty Fauziya da aunty Zarah ke jiɓantar lamarin ta
hakan yasa koda Ammi taji sunan ta tare ta cikin mutunci
Amma Zarah ko kallonta ba ta yi ba
ta Duka ta dauki jakar ta ta fita
koda ta fito
drivern ya ce"hajiya ko ba gidan bane"
cikin tsananin fushin ta ce"nan ne zamu tafi dutse"
cikin mamaki ya ce"Hajiya dutse kuma"
ta ce"eh,ko bazaka je bane"
kai ya Girgiza ya shiga motar suka kama hanya
Bayan sun isa Dutse…
Kai tsaye Zarah ta ba driver kwatancen gidan Na’ima
Motar tana tsayawa a harabar gidan
Tun kafin driver ya buɗe mata ƙofa
Ta fito cikin hanzari
Security suka yi saurin tare ta
suna tambayar inda zata je dan gaba daya an sauya securities da suka san Matsayin ta a gidan
Ba ta saurare su ba
ta shige ciki
cikin Sa'a kofar falon a buɗe take ta shiga
dakin yayi shiru
Sai wata mai aiki ce kaɗai tana goge babban TV
Da ta ga Zarah sai ta yi saurin miƙewa
"Aunty sannu da zuwa"
Zarah ba ta tsaya ba
Ta ce
“Ina Na’ima"
“tana sama bari na kira ta"
ba bata lokaci suka dawo tare da Naima
Cikin mamaki Na’ima ke saukowa daga saman bene
ganin Zarah ya sa ta tsaya cak
“Aunty Zarah kece a gida na"
Ta yi saurin saukowa
“Lafiya? Rabonki da gidan nan tun suna Ayla"
Zarah ta ce cikin fushi,
“Eh…
"Yau ba zumunci ya kawo ni ba"
Ta kalleta
“Ina Mami?”
Na’ima ta ɗan yi shiru kafin ta ce
“Tana guest room"
Zarah ta yi mamaki
“Guest room?”
A zuciyarta ta ce
“Ashe yanzu har ta kai matsayin zama a guest room a gidan yar lelen tata"
“Allah baya barin zalunci"
Ba ta ƙara cewa komai ba
Na’ima ta yi gaba
Suka nufi ɗakin
…
Mami na zaune kan kujera
Kafar roba ce a ƙafarta
Fuskarta ta rame
Idanunta sun nuna gajiya
koda Zarah ta shiga
ta yi murmushin da bai kai zuciya ba
“Sai yau kika tuna da uwarki?”
Zarah ta tsaya gabanta
Ta haɗe hannayenta
“Mami"
"ba wannan ya kawo ni ba"
Ta yi shiru na wasu daƙiƙu.
Sannan ta ce
“Na zo ne saboda Suhail"
Nan take murmushin Mami ya ɓace
“Me Suhail yayi kuma kuma?”
“yayi ko akayi masa"
Zarah ta fada
“Mami"
"kin sa ɗanki ya saki matarsa ba tare da wani laifi ba"
“Kin san halin da yake ciki yanzu"
“Kin san ko office baya zuwa?”
“Kin san baya cin abinci?”
“Kin san ya rame ya koma kamar mara lafiya?”
Mami ta yi ƙoƙarin magana
Amma Zarah ta dakatar da ita
"A’a Mami"
"ki bari na gama magana"
“Kullum kanki kika sani"
“Kullum abin da ranki yake so shine daidai"
“Ko da zai lalata rayuwar ‘ya’yanki"
Na’ima ta yi shiru
Tun farko ba ta taɓa ganin Zarah cikin irin wannan fushi ba
Zarah ta ci gaba
“Ki sani"
idan Suhail ya mutu saboda wannan damuwar
Wallahi alhakinsa yana wuyanki"
Nan take Mami ta girgiza kai
Ta matsa kusa da ita
“Mami"
idan ni ce ko Na’ima
"uwar mijinmu ta yi mana irin abin da kika yi wa Iman za ki ji daɗi?”
Mami ta yi shiru
Ba ta iya amsa ba
Zarah ta ci gaba
“Kin manta hadisin Manzon Allah ﷺ? Babu cikakken imani har sai mutum ya so wa ɗan’uwansa abin da yake so wa kansa"
“To…
me kika so wa Iman?”
“Wulakanci?”
“Kuka?”
“Saki?”
"gori"
Mami ta sunkuyar da kai
Karo na farko…
ta rasa abin faɗa
Sai Zarah ta sake cewa
“Kuma abin da baki sani ba…”
Ta ɗan dakata kafin ta ce
“Yarinyar nan da kike goranta saboda ba ta haihuwa"
“Allah Ya azurta da ciki kuma na danki"
Mami ta ɗago da sauri
Na’ima ma ta miƙe tsaye
“Me kika ce?”
Zarah ta ce
“Eh Iman na da ciki"
“Cikin Suhail"
Shiru kowa yayi
Wani irin shiru mai nauyi
Mami ta buɗe baki
Amma kalma ta ƙi fitowa
Na’ima kuwa
Hannunta ya rufe bakinta
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…”
Hawaye suka cika idanunta.
“Ashe…
duk wannan abin da aka yarinyar tana da ciki?”
Zarah ta ce
Mami ta fara rawa.
Numfashinta ya canza.'
Ta dafe ƙirji
“Na shiga uku…”
“Na lalace…”
Zarah ta ce
“Kuma ba nan abin ya tsaya ba"
“Daga nan zan wuce Kaduna"
“Na faɗawa Abba komai"
Nan take Mami ta fashe da kuka
“A’a Zarah"
“Don Allah"
“Kada ki gaya masa"
“Wallahi zai sake ni"
“Ba zan iya jurewa ba"
Na’ima ma ta durƙusa
Ta kama hannun Zarah
“Aunty don Allah"
“Ki yi haƙuri"
“Ni ma zan shiga matsala"
“Daddy ba zai bar wannan magana haka ba"
Zarah ta daɗe tana kallonsu.
Daga ƙarshe ta ce
“Zan yi haƙuri"
“Amma da sharadi"
Dukansu suka ɗago
“Mene?”
“Mami…”
“Za ki janye duk kalaman da kika yi wa Suhail"
“Za ki roƙe shi gafara"
“Kuma za ki umurce shi ya je ya dawo da matarsa"
Mami ta share hawayenta
Ba tare da wata gardama ba
Ta ce
“Na yarda"
“Wallahi na yarda"
“Na gane kuskurena"
“Allah Ya gafarta mini"
Nan take ta miƙa hannu
Na’ima ta kawo mata waya
Da hannunta na rawa
Ta kira Suhail
…
Suhaila na zaune a ɗakinsa
Wayar sa ta yi ringing.
Da ya ga sunan Mami
Sai ya yi niyyar ƙin ɗagawa
Amma daga ƙarshe
Ya amsa
“Assalamu alaikum"
Muryar Mami ta fito cike da kuka
“Suhail…”
Ya yi shiru
“Suhail ka gafarta min"
Numfashinsa ya tsaya
Bai taɓa jin Mami cikin irin wannan yanayin ba
Ta ci gaba da kuka
“Na zalunce ka"
“Na zalunci Iman"
“Na yi babban kuskure"
“Don Allah ka yafe min"
“Ka je…”
“Ka dawo da matarka"
“Ka dawo da ita gida"
“Ni na janye duk maganganun da na faɗa a kanka"
“Allah Ya gafarta mini"
“Na zalunci jikana ma ban sani ba…”
Suhail ya dafe wayar da ƙarfi duk tunanin sa mami ta zauce ne
Idanunsa suka cika da hawaye
Bai iya magana ba
Sai kuka da ya ƙwace masa
A ɗayan ɓangaren wayar…
Mami ma kuka take yi
Karo na farko cikin shekaru masu yawa
Uwa da ɗa
"Dukansu suna kuka saboda kuskuren da ya raba iyali"