87
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️—88
Suhail ya daɗe riƙe da wayar a hannunsa
Har Mami ta gama kuka ta katse kiran
Shi kuwa bai motsa ba
Idanunsa suka cika da hawaye
A hankali ya sauke wayar kan gadon
Ya dafe kansa da hannayensa biyu
“Alhamdulillah…”
Ita ce kalma ta farko da ta fito daga bakinsa
Ya daɗe bai furta komai ba sai wannan
A karo na farko cikin watanni…
Ya ji kamar wani dutse mai nauyi ya sauka daga zuciyarsa
Sai kuma wata irin tsoro da fargaba suka mamaye shi
Ta yaya zai je ya fuskanci Iman?
Da wace fuska zai kalli iyayenta"
Me zai ce mata?
“Ki yafe min?”
Shin hakan zai isa?
amman kafin ya tun kare ta ya kamata ya fara zuwa ƙasa mai Tsarki
yayi addu'a yana mai yaƙinin Allah zai taimake sa
a daren ya kira Sameer
ya faɗa masa ya sama masa booking na zuwa umrah
Sameer ya amsa masa da "babu matsala zanyi hakan in sha Allah"
yana kwance akan gado ya tsurawa dakin ido
zeenah ta shigo
kayan Bacci ne a jikin ta riga da wando
bakin gado ta zauna
"Suhail"
ido kawai ya iya bin ta dashi
ta cigaba da magana
"na kusa yin twenty seven birthday dina"
"ina son ka bani kudi zanyi celebration"
Suhail ya girgiza kai
"zeenah i'm sorry for now dai banda kudi infact ma cikin satin nan zan tafi Umarah"
“Duk kuɗin da nake da shi akwai abin da zan yi da su"
Fuskar Zeenah ta sauya
"nasan da Iman ce ta tambaye ka kana rawar jiki zaka ɗauka"
murmushi yayi ya ce
"she will never come with such of this need"
zeenah ta ce"fine"
ta juya ta fita
koda mami ta ajiye wayar Zarah ta dube ta ta ce"ya kamata kuje kuma ku nemi yafiyar iman"
"ba iya Suhail bane kadai zai je"
mami ta ce"zan je"
na'ima ta ce"nima zanje amman wallahi inajin kunyar haɗa ido da aunty zarah"
anan ta ba mami labarin komai da ya faru da suka je yiwa zeenah barka
da yadda ta raina kayan da irin taɓar wulakanci datayi masu
daga karshe iman ce ta basu Abinci tare da wajen kwana
amman duk da hakan suka yi tafiyar su ba tare da koyi mata sallama ba
Zarah ta ce"yanzu ba lokacin kunya bane,ki sa a ranki zaki je gyara kuskure da kika ɓata ne"
Mami ta ce
“Amma dole ki raka mu.”
“Idan mu kaɗai muka je… ba za su saurare mu ba"
Zarah ta yi shiru
Daga ƙarshe ta ce"zan raƙa ku amman babu abinda zan ce"
take ta kira Sadeeq ta faɗa masa
"sai gobe zata dawo"
ya ce"bakomai"
washe gari
Motoci biyu suka kama hanyar Kaduna
A gaba
Motar security ce da mijin na'ima ya basu
A baya kuma,Mami,Na’ima da Aunty Zarah
basu tsaya ko ina ba sai kofar gidan Malan
ko da suka isa suka tarar da malam a kofar gida
mami da kyar take tafiya da kafar robar nan
Ya yi mamakin ganinsu
Ya amsa sallamarsu
Ya ce
“Ku shigo"
Iman da Hafsat suna zaune kan tabarma hafsat tana karanta mata wani littafin Hausa
ganin Mutane na shigo wa gidan malan na gaba suna biye dashi a baya
Iman Idanun ta ya sauka kan mami
cikin sauri ta tashi ta koma dakin ta ta rufe kofar hadda saka mata makullin
tamkar taga dodo
duk abinda ya faru babu wanda bai gani ba
Ammi ce ta fito
Ta tarbe su
Amma babu murmushi a fuskarta
tabarma ta shimfida masu
ta ce"sai dai kuyi haƙuri babu carpet din da zaku zauna sai tabarma"
"Abinda da gidan talakka"
kowa yasan magana ce Ammi ta faɗa
murmushi yaƙe mami ta yi ta ce"ai ba wani abu"
malan ya samu waje gefe ya zauna
Ammi ta koma kan tabarmar da Iman ta tashi
gaisuwa ta biyo baya
Hafsat ko ko daga kai batayi ba ta kalle su bare su saka ran zata gaishe su
Mami ta sunkuyar da kanta ta ce"munzo neman tafiya ne akan Abinda ya faru"
Ammi ta ce"ai baku yi kowa laifi ba hasalima mu muka maku laifi da muka ɗauki ɗiya muka baku"
Duk maganganun da take yanka musu malan bai hanata ko ya tsawatar mata ba
Aunty Zarah ta ce"haba Ammi ai ku aka wa laifi dan Allah tunda har mami ta gane kuskuren ta ku yafe mata"
Ammi ta ce
“Bani ta yi wa laifi ba"
“Iman kika zalunta"
“Idan ta yafe miki… alhamdulillah"
“Idan ba ta yafe ba… ba zan tilasta mata ba"
Mami ta share hawaye
"dan Allah ku kirata na nemi yafiyar ta"
Ammi ta girgiza kai ta ce"hajiya kiyi haƙuri Gaskiya kina ganin yadda ganin ku ya tsorata ta ,bazaki samu damar ganin taba"
mami ta juya kan Malan ta ce"dan Allah ka saka baki mana"
Nan take fuskar Ammi ta canza.
Ta ce
“Yanzu?”
“Yanzu da kuka ji tana da ciki?”
“Watanni uku tana gidan nan"
“Ko sau ɗaya ba wanda ya zo"
“Yanzu ne kuka tuna tana matar ɗanku?”
Mami kuka take
Ammi ta ci gaba
“Wallahi…”
“Iman ta gama auren ɗanku"
“Ko da za ta mutu ba aure ba za ta koma gidan da aka wulaƙanta ta ba"
Ta juya
Ta shiga ciki
Ta barsu zaune
Malam ya daɗe yana kallonsu
Daga ƙarshe ya ce
"Hajiya kuyi haƙuri ku tafi kunga dai Yadda ran kowa yake a bace"
"kuje ku cigaba da addu'a Allah ya kawo saukin abin"
Shiru ya mamaye falon
Aunty Zarah ta sauke ajiyar zuciya
Ta ce a hankali
“Na san abin zai yi wuya…”
“Amma ban yi zaton zai yi wuya haka ba"
Haka suka fito daga gidan…
Kowa da nauyin da yake ɗauke da shi
a cikin satin Suhail ya tafi makkah
kwana daya da tafiyar sa
Zeenah na zaune a ɗaki abin duniya ya isheta
ga kudin da zatayi birthday nata bai samu ba
take wata shawara tazo mata ta shiga dakin Suhail ta duba
tasan bazai rasa ajiye kudi a ciki ba
da sauri ta nufi dakin take ta fara janyo lockers tana dubawa
cikin Sa'a kuwa ta na buɗe wata ta ga dollars shimfiɗe a ciki
hamdala tayi ta kwashi Fiye da rabin kudin ta fita
A ƙasa mai tsarki ta Makkah
Bayan Suhail ya idar da sallar Magariba a Masallacin Harami
Suhail ya daɗe zaune yana kallon Ka’aba
Idanunsa cike da hawaye
Kalaman addu’a kaɗai suke fita daga bakinsa
“Ya Allah…”
“Na zo gare Ka da zuciyar da ta karaya"
"Allah ka dubeni da idon rahama,ka sa Imam ta yafe min"
Wayarsa ta fara vibrating.
Da farko bai kula ba.
Sai da ta sake yin ringing
Ya zaro ta a hankali
Da ya ga sunan Aunty Zarah sai gabansa ya faɗi
Nan take ya amsa
“Assalamu alaikum Aunty…”
“Wa alaikumus salam Suhail.”
Muryarta ta yi sanyi
Ta lura da muryarsa ma cike take da kasala
ta ce"Suhail ya ibadah"
"Alhamdullilah"
Ta yi shiru na ɗan lokaci
Sai ta ce
"na kiraka Na fada maka munje gidan su iman tare da mami da kuma na'ima"
“Sun… sun karɓe ku?”
Aunty Zarah ta yi murmushin takaici
“Mun yi ƙoƙarin neman yafiya.”
“Amma ba wannan nake son ka damu da shi ba"
“Bana son ka bari hakan ya rage maka ƙwarin guiwa.”
“Ka ci gaba da addu’a.”
Suhail ya lumshe idanunsa
“Zan yi Aunty.”
“Akwai wani abu kuma…”
ji yayi bugun zuciyarsa ya karu
Ka saka Iman cikin addu’arka sosai.”
“Allah Ya sauke ta lafiya.”
“Domin tana ɗauke da juna biyu"
wuta ta dauke masa na wasu ɗakiku
Suhail bai iya cewa komai ba
Ya yi zaton kunnensa ne ya ruɗe shi
Da ƙyar ya furta
“Aunty…”
“Me kika ce?”
Ta maimaita cikin nutsuwa
“Iman tana da ciki”
“Allah Ya azurta ku"
Wayar ta kusa zamewa daga hannunsa
Idanunsa suka cika da hawaye cikin mintuna
Numfashinsa ya rikice
“Alhamdulillah…”
“Alhamdulillah…”
“Alhamdulillahi Rabbil Aalameen…”
Bai san lokacin da hawaye suka fara gangarowa ba
Kuka ya ƙwace masa
Kukan da ya daɗe yana dannewa tsawon watanni
Ya sauke wayar a hankali
Sai ya juya ya fuskanci Ka’aba
Nan take ya faɗi ƙasa cikin sujjadar godiya
“Ya Allah…”
“Na gode maka…”
“Na gode maka da wannan ni’ima"
“Na gode maka da ka ba Iman abin da ta daɗe tana buri"
Ya Allah ka sauke ta lafiya.”
Masu ibada da ke gefensa suka ɗan juyo suna kallonsa
Amma bai damu da komai ba.
Hawaye kawai yake
A zuciyarsa ya tuna daren da Iman take kuka tana tsoron ba za ta taɓa haihuwa ba
Ashe a lokacin da yake ganin komai ya ƙare… Allah yana rubuta musu ni’imar da ba su sani ba"
Yana sake-sake faɗin
“Alhamdulillah…”
“Alhamdulillah…”
A wannan lokacin…
Ya ji kamar Allah Ya buɗe masa wata ƙofa ta rahama
A karon farko cikin watanni…
Wani ɗan ƙaramin fata ya fara haskaka cikin zuciyarsa
Fatan cewa…
Wata rana…
Zai sake rungumar Iman
Zai kuma ɗauki ɗansa ko ’yarsa a hannunsa wanda iman ta haifa masa
“A karon farko tun bayan rabuwarsu bai sake ganin kansa a matsayin mutumin da ya rasa komai ba Ya ji kamar Allah Ya nuna masa cewa har yanzu ƙofofin rahama ba su rufe ba Sai dai ya san dole ne ya biya farashin kuskurensa kafin ya samu damar sake kiran Iman… matarsa"
likee
share
and comment