BARRISTER SUHAIL

89

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️—89

Bayan tafiyar su Mami da 

Gidan malan yayi shiru

tun da iman ta rufe kanta a daki har yanzu bata buɗe ba

Ammi ta nufi dakin tana bugawa

"iman ki buɗe sun tafi"

shiru 

ta sake bugawa

nan ma bata buɗe ba

"haba Iman dan Allah ki buɗe baki gudun wani abu ya same ki"

sai ammi ta kusa shafe mintuna goma 

kafin ima ta buɗe kofar

Da kyar

Da Ammi ta shiga

Ta tsaya chak

Idanun Iman sun kumbura sossai

Fuskarta duk hawaye ne

Da alama tun bayan shigarta ɗakin take kuka

Ammi ta ƙarasa ta rungume ta

“Ya isa haka”

Iman ta ƙara fashewa da kuka

Ta riƙe Ammi sosai

“Ammi"

“Sun sake dawo mini da ciwon da nake tunanin ya fara warkewa"

"miya kawo su gidan mu"

Ammi ta shafa bayanta

“Ki yi haƙuri, khadija"

Iman ta girgiza kai

“Na fara koyon rayuwa ba tare da Suhail ba"

Na fara yarda da ƙaddarar Allah"

“Yau da na sake ganinsu"

“komai ya dawo sabo"

Ta share hawaye

Ta ɗago tana kallon Ammi

“Don Allah"

“Kar ku taɓa tilasta ni in koma wajensa"

"Wallahi ni kaɗai na san wahalar da na sha"

“Na san yawan daren da nake kwana ina kuka.”

“ni kadai Na san yawan kalaman da suka karya zuciyata"

"Ammi banga amfanin zama da wanda dangin sa basa sona,na tabbatar cikin nan da aunty Zarah ta gani ta fada masu shiyasa suka zo"

Ammi ta kama hannunta

cikin taushin murya ta ce

“Iman…”

“Ki kwantar da hankalinki.”

“Babu wanda zai tilasta miki komai komawa"

“Ko ni…”

“Ba zan taɓa tilasta miki komawa inda ba kya so ba.”

“Abin da muke nema shi ne Allah Ya zaɓa miki mafi alheri"

Iman ta jingina kanta a kafaɗar Ammi

A karo na farko

Ta ji wani ɗan sauƙi a zuciyarta

tun da Suhail yaji batun cikin iman gaba daya ya maida hankalin sa kam siyyayar kayan jarirai

kullum yana kasuwa 

siyyaya yake hada ta ba gaira babu dalili

kwanan shi goma sha biyar ya juyo gida Nigeria

koda ya isa Dakin sa yana nan yadda ya barshi

sai dai ya lura da locker daya ajiye kudin sa kamar ba daidai ba

koda ya ƙarasa yaga an kwashe fiye da rabin kudin

koda bai tambaya yasan Zeenah ce

Ya lumshe idanunsa.

“Allah Ya shiryi Zeenah"

Bai tambayi Zeenah komai ba

Bai yi faɗa ba

Bai nuna fushi ba

Saboda a wannan lokacin

A gabansa akwai abin da ya fi kuɗi muhimmanci

Washegari

da wurii ya tashi Ya yi wanka

Ya saka wani farin  Egyptian yard mai tsananin kyau

Ya shafa turare

Ya ɗauki jakunkunan kayan da ya dawo da su daga Makkah

Ya shiga mota

Kai tsaye

Kaduna ya nufa

tunda ya tun kari unguwar su iman gaban sa ke faduwa

sai yayi niyyar kamar ya juya sai kuma ya tuna Abinda zai kaishi

haka ya daure ya isa

malan na kofar gida yana wazifa 

ya faka motar ya fito

Ya yi sallama

koda malam ya amsa ya cigaba da wazifar 

duk Suhail na zaune Abinda malan bai taɓa yi masa ba kenan

duk ƙaratun da yake yagan sa yakan katse su gaisa

koda yana tare da mutane yakan tashi ya bashi lokacin

amman Yanzu duk ya rasa wannan

sai da malan ya gama

ya dubi suhail 

suka Gaisa

Babu fara’a.

Babu murmushi.

Shiru kawai.

Suhail ya sunkuyar da kai

Ya miƙa masa jakunkunan.

“Malam…”

“Waɗannan…”

“A ba Iman.”

Malam ya kalli kayan

Sai ya sake kallon Suhail

Suhail ya buɗe baki

Yana son ya ce wani abu

Amma kalmomi suka ƙi fitowa

Daga ƙarshe

ya tashi ya tafi 

malan ya bisa da kallon

Da Suhail ya shiga motar sa 

Malam ya ɗauki jakunkunan ya shiga cikin gida

Ammi na zaune a falo tana linke Kayan da Hafsat ta wanke 

ganin malan na shigo da akwatuna ta hade rai 

Ta ce

“waɗannan daga ina kuma?”

Malam ya ajiye su a hankali

Ya ce

“Suhail ne ya kawo su"

Nan take Ammi ta miƙe tsaye

“wai!”

“Me mutanen nan suke nufi ne damu ne ko a tunanin wannan kayan zasu rude mu"

“Yanzu kullum sai su ta mana zirga-zirga a gida?”

“Bayan abin da suka yi wa yarinya?”

Malam ya kalli Ammi cikin nutsuwa

Ya ce

“Maryama”

“Kar ki manta Iman na ɗauke da cikin ɗansa.”

“Dole tana karkashin su har Yanzu"

Ammi ta girgiza kai.

“Ciki nan nata"

“Ta ɗauke shi ita kaɗai"

“Lokacin da aka kore ta daga gidansu ai ba wanda ya tuna wannan da ita"

“Yanzu da suka ji tana da ciki ne suka fara neman hanya?”

Malam ya sauke ajiyar zuciya

“Na san haka"

“Kuma ba na cewa wai abin da suka yi daidai ne bane "

“Amma kada mu rufe ƙofar sulhu tun kafin Allah Ya buɗe ta"

Ammi ta ɗan ɗaga murya

“Malam"

“Kana nufin ka goyi bayan abin da suka yi wa Iman kenan"

Malam ya girgiza kai

“A’a.”

“Ni ba na goyon bayan zalunci"

“Amma kuma ba na son fushi ya hana a yi adalci ga ɗayan ɓangaren"

“Allah Shi ne Mai juya zukata"

"idan Allah bai nufa zaman su ya mare ba fa?"

“Mu bar komai a hannunsa.”

Ya miƙe tsaye

“Ni zan shiga masallaci"

“Ku kuma ku kiyaye harshenku.”

Ya juya ya fita

Ammi ta bi shi da kallo

Ta girgiza kai kawa

Hafsat kuwa ta matsa kusa da jakunkunan.

Ta ce

“Ammi yaya Suhail ne ya aiko kayan"

Ammi ta ce cikin rashin damuwa,

“Ki kai su ɗakin Iman.”

“Idan ta ga dama ta karɓa"

“Idan ba ta so…”

“Za mu ba wa mabukata.”

Ba tare da ta ƙara magana ba…

Hafsat ta ɗauki jakunkunan

Ta nufi ɗakin Iman


like
share
comment