BARRISTER SUHAIL

99&91

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️—90&91

Da yamma, bayan Malam ya dawo daga masallaci,Ammi ta kaimasa Abincin ranar sa da bai samu damar ci ba 

waje ta samu kusa dashi ta zauna

ya ce

"Maryama"

Ta ɗago ta kalle shi

“Kin faɗawa Mubarak abin da ya faru da iman kuwa"

Ta girgiza kai

“A’a ban faɗa masa dan sai yama fi iman shiga damuwa ita da abinda ya shafa"

Malam ya sauke ajiyar zuciya

“Bai dace ya ci gaba da zama bai sani ya kamata a sanar dashi ba"

“Shi ma ɗan gidan nan ne"

“Ya kamata ya san halin da ƙanwarsa take ciki"

Ammi ta ɗan yi shiru

Daga ƙarshe ta ce

“To, idan ka ga hakan ba damuwa sai ka sanar dashi"

Kai ya jinjina

Nan take ya ɗauki waya ya kira Mubarak

Bayan sun gaisa, ya ce

“Mubarak"

“Ina so kazo Kaduna gobe idan ka sami dama"

“Akwai magana mai muhimmanci"

Mubarak ya lura da yadda muryar Malam ta canza

Bai yi wata tambaya ba
Ya ce

“In sha Allah, Malan Zan zo"

Washegari da safe

Mubarak da matarsa Raihan suka iso gidan

Da fara’a suka gaisa da Malam da Ammi

a falon Ammi suka sauka bayan ta kawo masu ruwa 

A hankali Ammi ta fara ba Mubarak Labarin duk a Abinda ke faruwa

duk da Mubarak baiso Ammi ta mishi maganar a gaban raihan ba 

amman a ganinta ai an zama ɗaya

kuma ta yaba da hankalin ta sossai da sosai 

duk inda ake neman mace ta Gari Mai hankali Raihana ta kai 


Bayan Ammi ta gama labarin

Ta miƙe ta shiga ɗaki domin ta ɗauko abin sha 

a falo ya rage Mubara, Raihana, iman da kuma Hafsat

Shiru ya ɗan ratsa wajen

Mubarak ya dubi Iman

Ya ce

“To ashe haka aka yi?”

“Mutumin da ya fi ni kyau…”

“Ya fi ni tsayi"

“Ya fi ni ɗaukar wanka"

“Shi ne ya sake ki?”

Nan take Iman ta tuna wata tsohuwar maganar da ta taɓa faɗa masa tana zolaya duk da tasan yaya Mubarak

baya da mantuwa musamman idan baiji dadin Magana ba

Ta sunkuyar da kai

Kunyarta ta bayyana ƙarara

Raihan ta harareshi

“Yaya Mubarak"

"ka barta mana"

Ya juya wajen Hafsat.

“Ke kuma"

“Har yanzu kina gidan na"

“Kin gama makaranta amman baki tsayar da mijin aure koda babu tsayyaye"

“a samo miki wani almajirin Malam?"

Hafsat ta zaro ido.

“Allah Ya sauwake!”

“Degree holder  da ni a Nursing"

“Kace wai almajiri?”

“Yaya, ai na fi ƙarfin wannan wallahi"

Dariya suka yi gaba ɗaya

Mubarak ya nuna ta da yatsa

"to tunda haka kika ce na baki sati biyu ki gabatar min da Wanda zaki aura"

“Shekara ashirin da biyu kina zaune gida"

“idan ma daga nan Kaduna"

“Ko daga Katsina"

“Duk inda yake, ki faɗa min zan dawo nan da sati biyu masu zuwa"

“Bana so ki kai ƙarshen shekara kina gidan nan"

Hafsat ta ɗaga gira.

“To Yaya"

“Ni zan je na ce masa ina son sa ne ya turo gidan mu"

“Wannan kuma aikinki ya rage naki ne "

Ya miƙe tsaye

“Ni bari na fita wajen Malan"

Ya bar su a falon

Raihan kuwa ta ci gaba da hira da Iman da Hafsat 

Tamkar dama chan sun jima a tare

Ko kaɗan ba ta nuna girman kai duk da ta ɗara su a shekaru

haka Ammi ta dawo ta iske su dauke da tray a hannun ta

fatan masara ne a ciki sai Kamshi take

Ta ajiye a gabansu

Raihan ta yi murmushi

“Ammi ai da kin kiramu sai mu taya ki aiki "

“Sannu da aiki"

Ammi ta yi dariya

“Ke kike zo yanzu"

“Ai bai kamat ki shiga  kitchen ba"

“Iman kuma yanzu ta yi nauyi"

"Ita kuma Hafsat"

“Idan kin ga aikinta"

“To wajen cin abinci ne kawai"

Nan take falon ya kaure da dariya

Hafsat ta kwaɓe fuska

“Ammi kenan"

Raihan ta ce cikin murmushi

“Ni har ina tunanin tafiya da Hafsat Kano ta mana koda sati ma"

Ammi ta ce

“Aiko tana zaune"

“Sai dai ki girka ki kawo mata"

Hafsat ta yi saurin cewa

"to na fasa zuwa ma"

“Zan zauna nan"

“Na ci gaba da kula da Iman"

“Har sai ta haifi Baby Girl ko Baby Boy"

Duk suka sake fashewa da dariya

Har Iman

Ta yi murmushi a karo na farko bayan kwanaki masu yawa

Tun bayan ziyarar farko da Suhail ya kai gidan Malam

Bai daina zuwa ba

Kusan duk bayan kwana uku ko huɗu sai ya sake zuwa kaduna

Wani lokacin da kayan jarirai

Wani lokacin da abubuwan ci kala kala

Wani lokacin kuma ba ya zuwa da komai sai zuciyarsa mai cike da fatan ko zai hango iman

Amma…

Ko sau ɗaya bai sake ganin ta ba

Duk lokacin da ya isa

Malam ne kawai yake tararsa

Yakan karɓi kayan cikin mutunci

Su gaisa

Sai Suhail ya juya ya tafi

Babu tambayar ganin Iman

Saboda ya san ba shi da wannan haƙƙin yanzu

Sau da yawa yakan daɗe zaune cikin mota bayan ya fita daga gidan

Ba don komai ba

Sai don zuciyarsa ta ƙi barinsa ya tafi

Amma daga ƙarshe

Sai ya kunna mota ya kama hanyar komawa Abuja

A gidan Malam kuwa…

Lokacin da Hafsat ta shigo da kayan da Suhail ya kawo

ya tasamu iman zaune a kan gado

bayan ta ajiye kayan a gabata ta ce"yaya Suhail ne yau ma ya dawo"

Hafsat ta ƙara da cewa

“yaya Suhail na zuwa akai akai"

Amma ko sau ɗaya bai ce yana son ganinki ba"

Shiru Iman ta yi

Sai bayan wasu daƙiƙu ta ce cikin sanyin murya

“Ki kai kayan wajen Ammi"

“Ni ba na son jin wani labarinsa"

Hafsat ta kalli fuskarta.

Ta fahimci muryarta ta nuna ƙarfin hali

Amma zuciyarta har yanzu tana jin ciwo

Lokaci ya ci gaba da tafiya.

Cikin Iman ya shiga wata shida

Tun daga lokacin Ammi ta dage sai an kai ta antenatal akai-akai.

Ko da farko Iman ta ce

“Ammi  ni lafiya ta qlau"

Sai Ammi ta girgiza kai

“shi awo ba wai sai mutum baida lafiya ake yi masa ba"

"Amma kulawa wajibi ce"

A ranar da suka je asibiti

Likitar ta yi mata cikakken dubawa 

An auna jininta

An duba nauyin cikinta

An yi mata scan

Bayan komai ya kammala

Likitar ta zauna tana kallon sakamakon

Sai ta ɗago ta kalli Iman

“Alhamdulillah… jaririn yana cikin ƙoshin lafiya"

Murmushi ya bayyana a fuskar Ammi

Sai dai murmushin likitar ya ɗan sauya

Ta ce

“Akwai wani abu da ya kamata ku sani"

Nan take gaban Ammi ya faɗi.

“Lafiya kuwa Doctor?”

Likitar ta jinjina kai

“Lafiya lau"

Amma ƙashin ƙugunta ya yi ƙanƙanta

Ta nuna hoton scan

“Saboda haka idan cikin ya kai wata tara…

ba za mu bari ta yi ƙoƙarin haihuwa da kanta ba

fuskar iman ta sauya

Ammi ta ce 

“Me hakan yake nufi?”

Likitar ta ce cikin nutsuwa

“Za a yi mata Caesarean Section (CS)"

Shiru ya mamaye ɗakin.

Iman ta ji kamar an cire numfashinta.

“Doctor…

kenan ba zan iya haihuwa da kaina ba?”

Likitar ta yi murmushi.

“Ba wai ba za ki iya ba ne.

Amma muna son kare lafiyarki da ta jaririn.

CS ba abin tsoro ba ne

Dubban mata ana yi musu kowace rana kuma suna haihuwa lafiya"

Sai dai duk da kalaman likitar…

Zuciyar Iman ta kasa samun natsuwa

A Hanyar ta komawa

Tun daga asibiti har gida

Babu wanda ya yi magana

Da suka isa gida

Ammi ta lura har yanzu Iman tana cikin tunani

Ta zauna kusa da ita

Ta kamo hannunta

“Iman…”

Idanunta suka cika da hawaye

“Ammi"

ina jin tsoro.”

“Tsoron me?”

“bana so na mutu yanzu”

“Ban san yadda ake yi ba"

“Ban san ko zan fito da lafiya ba"

Ammi ta rungume ta

Ta shafa kanta

“Ki daina wannan tunanin.”

“Rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke"

“Likitoci sababbi ne kawai"

Allah Shi ne Mai warkarwa"

Hawaye suka gangaro daga idanun Iman

A hankali ta ce

“Ammi…

idan wani abu ya same ni fa?”

Nan take Ammi ta dafe bakinta

“Kada ki sake furta irin wannan magana"

“Da izinin Allah…

"za ki haihu lafiya"

“Za ki dawo gida kina rungume da jaririnki"

A lokacin ne Malam ya shigo daga masallaci

Da ya ganin yanayin fuskokinsu

Ya fahimci akwai abin da ya faru

Ammi ta ba shi labarin abin da likita ta ce

Malam ya yi shiru na wasu daƙiƙu

Sai ya ce

“Subhanallah"

Ya dubi Iman

“Khadiija duk yadda Allah Ya ƙaddara shi ne mafi alheri"

“Mu ƙara yawaita addu’a"

“Idan Allah Ya rubuta lafiya zaki haihu"

babu wanda zai hana.”

Ya ɗaga hannayensa sama

“Allahumma inni as’aluka salamatan fid-din wad-dunya wal-akhirah…”

Duk suka amsa da

“Ameen"

Sai dai

Ko da dare ya yi

Iman ta daɗe tana shafa cikinta

tare da addu'ar Allah ya sauke ta lafiya

Bayan wata ukku

tun da sassafe

Iman ta fara jin wani irin ciwo a ƙasan cikinta

Da farko ta ɗauka irin ciwon da take ji lokaci-lokaci ne

Ta ci gaba da aikinta cikin natsuwa

Sai dai duk bayan ɗan lokaci

Ciwon yana dawowa

Ammi ta lura da canjin yanayinta

Ta ce

“Iman lafiya kuwa?”

Ta yi murmushi mai yaƙe.

“Ba komai Ammi"

“Tun safe nake jin ɗan ciwo ne"

Ammi ta shafa bayanta

“Wataƙila alamar haihuwa ce"

“Ki kwantar da hankalinki"

Iman ta jinjina kai

Sai dai

ko Da la’asar ta yi

Ciwon ya sauya gaba ɗaya

Ya fara zuwa da ƙarfi

Har ya sa ta kasa tsayuwa

Ta dafe cikinta tana jan numfashi.

“Ammi"

Muryarta ta fito a raunane

Ammi ta yi saurin ƙarasowa kusa da ita 

Da ta ga yadda zufa ta jiƙa goshin Iman

Sai da gabanta ya faɗi

“Hafsat!" Ammi ke kira

Hafsat ta fito da gudu daga ɗaki

“Na’am Ammi.”

“Ki kawo hijabinta da takalmanta da sauri"

Ba tare da tambaya ba Hafsat ta shiga ɗaki

Ta fito da kayan

A wannan lokacin Malam ya shigo daga masallaci

Da ya ga halin da Iman take ciki…

Ya fahimci lokaci ya yi 

“Mu tafi asibiti"

Nan take suka fito da malan ya sama masu mota

A hankali suka taimaka wa Iman ta shiga

Duk lokacin da ciwon ya taso

Sai ta runtse idanunta

Ta kama hannun Ammi da ƙarfi

“Ammi"

“Ki yi mini addu’a"

Ammi ta riƙe hannunta

“Allah zai sauƙaƙa miki ’yata"

“Babu abin da zai same ki In Sha Allah"

Da suka isa asibitin…

An yi saurin karɓar Iman.

Likitoci suka shiga da ita ɗakin dubawa.

Bayan wasu mintuna…

Likitar da ke kula da ita ta fito

Ta dubi Malam.


Ta ce

“Mun duba ta.”

“Naƙuda ta fara sosai"

“Amma saboda irin yanayin ƙashin ƙugunta…”

Ta girgiza kai

“Ba za ta iya haihuwa da kanta ba"

“Emergency Caesarean Section za mu yi"

Ammi ta dafe ƙirjinta

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…”

Hafsat kuwa idanunta suka cika da hawaye

Ta kama hannun Ammi

Ammi ta share hawayenta.

Ta ce

“In Sha Allah zata haihu lafiya"

Malam ya dubi likitar

Ya ce cikin nutsuwa

“Doctor"

“Ku yi duk abin da ya dace"

“Allah Ya bada sa'a"

Likitar ta jinjina kai

“In Sha Allah za ta kasance lafiya"


Aka fito da Iman a kan gadon asibiti

Za a shiga da ita theatre

Da ta ga ƙofar theatre

Tsoro ya mamaye zuciyarta.

Hawaye suka zubo daga idanunta

Ta fara karanta shahada cikin sanyin murya

“Ashhadu an la ilaha illallah… wa ashhadu anna Muhammadan Rasulullah…”

Ta juya ta kalli Ammi

“Ammi"

“Ki yafe min idan na taɓa yi miki laifi"

Nan take Ammi ta fashe da kuka

“na yafe maki Ke ma ki yafe min ’yata.”

“Allah ba zai raba ni da ke ba"

A hankali aka tura gadonta zuwa cikin theatre

Ƙofar ta rufe


A waje…

Ammi ta zauna tana share hawaye

Hafsat kuwa ta kasa zama

Sai ta riƙa karanta Ayatul Kursiyyu da Suratul Ikhlas tana tofawa

Malam ya zauna gefen corridor

Tasbihi kawai yake ja

Labbansa ba su daina motsi ba

“Astaghfirullah… Astaghfirullah… Astaghfirullah"


Shiru ya mamaye corridor ɗin asibitin

Ammi na zaune kan kujera tana jan tasbihi, amma hawaye na ci gaba da zuba daga idanunta

Lokaci-lokaci sai ta ɗaga hannu sama.

“Ya Allah"

“Ka sauƙaƙa wa Iman"

“Ka fito da ita lafiya"

Hafsat kuwa ta kasa zama wuri ɗaya

Sai kai-komo take yi a corridor

tana fadin Abinda ke bakin ta 

Lokaci ya yi kamar ya tsaya

Minti goma

Ashirin

Talatin

Ga Ammi kamar sa’o’i ne suke wucewa

Ba wanda ya sake cewa komai.

Sai ƙarar takun nurses da ke shige da fice

Can cikin theatre

Likitoci na ta aikin ceto Iman da jaririnta

Bayan kusan awa guda

Sai karar jariri ta cika wajen

Ammi ta ɗago da sauri

Hafsat ta tsaya cak

Malam ya lumshe idanunsa

“Alhamdulillah"

Shi kaɗai ya furta

Ƙofar theatre ta buɗe

Likitar da ta jagoranci aikin ta fito

Fuskarta ɗauke da murmushi

Ta cire safar hannunta

Ta dubi Malam

Ta ce

“Congratulations"

“Allah Ya azurta ku da kyakkyawar yarinya"

Hawaye suka cika idanun Ammi

Ta ɗaga hannayenta sama

“Alhamdulillahi Rabbil "Aalameen.”

Hafsat kuwa ta yi tsalle cikin farin ciki samun

“Baby Girl!

Ta rungume Ammi tana dariya da kuka lokaci guda.

Likitar ta ci gaba da cewa

“An yi aikin cikin nasara"

“Mother and baby are both fine"

“Amma za ta yi wasu sa’o’i kafin ta farka gaba ɗaya saboda maganin barci"

Numfashin da kowa ya riƙe ya fita lokaci guda

Malam ya sunkuya ya yi sujjadar godiya a wajen corridor

“Alhamdulillah…”

“Ya Allah, godiya ta tabbata gare Ka"

Bayan wasu mintuna

Nurse ta fito riƙe da jaririyar

An naɗe ta cikin farin blanket mai kyau Wanda yana daya daga cikin siyyayar haihuwa da Mubarak da Raihan suka yi

Fuskarta fara ce fes

Ƙaramin hancinta ya yi daidai da na Iman

Idanunta a rufe suke cikin barci

Nurse ta miƙa ta hannun Ammi.

Da Ammi ta karɓe ta

Hawayen farin ciki suka sake zubo mata

Ta sumbaci goshin jaririyar

Ta ce cikin rawar murya

“Maraba da zuwa duniya, ’yar albarka"

“Allah Ya raya ki"

“Hannu ne ya kawo ki, ba ƙafa ba"

Hafsat ta matsa kusa

Ta shafa ƙaramin hannunta

“Masha Allah"

“Kamarta da Ima"

Malam ya tsaya yana kallon jaririyar

Fuskarsa cike da godiya

A hankali ya ce

“Allah Ya sanya ta daga cikin bayi na ƙwarai"

“Amin"

Duk suka amsa

A wannan lokacin

Ba wanda ya san cewa

Suhail na zaune cikin dakin ɗinsa…

Ba tare da sanin cewa Allah Ya azurta shi da kyakkyawar ’ya mace ba

like share and comment