92
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️—92
Bayan wasu sa’o’i
A hankali Iman ta fara buɗe idanunta
Har yanzu jikinta a sanyaye yake
Ta ji kamar ba nata ba ne
Cikinta na mata zafi mai tsanani saboda aikin tiyatar da aka yi mata
Da ƙyar ta juya kanta
Sai ta hango Ammi zaune gefen gadonta
Idanunsu suka haɗu
Ammi ta yi murmushi mai cike da hawaye
“Alhamdulillah… kin farka, Khadija"
Iman ta yi ƙoƙarin magana
Sai dai muryarta ta fito a raunane ta kira
“Ammi"
Ammi ta kamo hannunta
“Komai ya wuce ko"
“Allah Ya baki lafiya Ke da jaririyarki"
Da jin kalmar jaririya, Iman ta lumshe idanunta
Hawaye suka cika mata ido
Ba ta san lokacin da murmushi ya bayyana a fuskarta ba
A hankali ta ce
“Baby tana lafiya?”
Ammi ta fada
“Kyakkyawa ce sosai"
A wannan lokacin Hafsat ta shigo ɗauke da jaririyar
An naɗe ta cikin farin blanket mai laushi
Fuskarta ƙarama ce
Fatarta fara sol kamar madara
Ƙaramin bakinta ja ne tamkar an shafa masa jan baki
Hancinta ƙarami ne irin na Suhail
Dogayen gashin idanunta sun kwanta bisa kumatunta
Ƙananun yatsunta kuwa suna buɗewa suna rufewa cikin natsuwa
Hafsat ta miƙa jaririyar kusa da Iman
Da Iman ta kalleta
Sabbin hawaye suka zubo mata
Ta shafa kumatunta da yatsa
“Alhamdulillah…”
“Allah Nagode maka"
Ammi ta ce
“Ki huta tukuna"
“Da zarar kin sami ƙarfi za ki riƙe ta sosai"
Hafsat kuwa ta kasa daina kallon jaririyar
“Wallahi Baby Girl nan kamar doll take"
Ta zaro wayarta
“Ammi bari na ɗauke ta hoto"
Ammi ta yi murmushi
“Ki ɗauka"
Ta ɗaga wayar ta ɗauki hotuna masu kyau na jaririyar
Bayan ta gama
Sai wata dabara ta faɗo mata
Ta buɗe WhatsApp
Ta shiga chat ɗin Suhail
Ta tura masa hoton jaririyar
Sai ta rubuta
“It’s a baby girl for Iman amma don Allah kar ka ce ni na turo maka"
Ta danna Send
A wannan lokacin
Suhail yana kwance a ɗakin sa.
Wayarsa ta yi ƙarar saƙo
Bai damu ba da farko
Sai da ya ga sunan Hafsat
Nan take ya miƙe zaune
Da sauri ya buɗe saƙon
Hoton jaririyar ya bayyana a screen ɗin wayarsa
Ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu
Tamkar numfashinsa ya tsaya
“Subhanallah"
Ya furta a hankali
Idanunsa suka cika da hawaye
Ya ƙara matsowa da hotan kusa"
Yana kallon ƙaramin fuskarta
Yana kallon ƙananun hannayenta
Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa
A hankali ya shafa screen ɗin wayar da yatsansa
Tamkar yana shafar fuskar jaririyar ne
Hawayen farin ciki suka gangaro masa
"my Daugther"
Ya faɗa cikin rawar murya
“Alhamdulillah"
“Allah Ya raya ki"
“Allah Ya sa ki zama abin alfahari ga iyayenki"
wayar daga ya sumbaci screen ɗin hoton
A karo na farko
Ya ji ainihin ma’anar zama uba
Sai dai farin cikin nasa yana tare da wani raɗaɗi mai ciwo
Domin ya san
Ba ya tare da matar da ta haifa masa kyakkyawar diyar sa
Ba ya kusa da jaririyarsa
Ba shi ne ya fara ɗaukarta a hannu ba
Kawai hoton yake kallo
Yana share hawaye cikin shiru
Kwana biyu Iman ta yi a asibiti
A hankali jikinta ya fara samun sauƙi
Ko da yake ciwon wajen aikin tiyata bai gama raguwa ba, amma tana ƙara samun ƙarfi a kullum
Jaririyar kuwa lafiya ƙalau
kullum bacci take
Ammi da Hafsat ne suke kula da komai
Ba sa barin Iman ta wahala
A rana ta uku
Likita ya sake duba Iman
Ya yi murmushi ya ce
“Alhamdulillah.”
“Komai yana tafiya"
“Za ku iya komawa gida"
Ammi ta yi godiya
Hafsat kuwa ta yi saurin haɗa kayan jaririyar
An saka ta cikin wani ƙaramin baby dress ruwan hoda mai laushi
Da ƙaramin hula da safa masu launin iri ɗaya
Ta yi matuƙar kyau
Kowa da ya ganta sai ya yi mata addu’a dan yarinyar Allah ya azurtata da kyau
A wannan lokacin
Suhail yana Abuja
Tun bayan da Hafsat ta turo masa hoton jaririyar
Kullum yana ɗaukar wayarsa na hannun sa yana kallon hoton
Yana ta jiran a kira shi a ce masa Iman ta haihu
Amma babu wanda ya kira
Sau da dama ya kan ɗauki mukullin motarsa
Ya yi tafiya zuwa Kaduna
Sai kuma ya tuna kalaman Hafsat
“Don Allah kar ka ce ni na turo maka"
Nan take sai ya ajiye mukullin
“Ba zan so na jefa ta cikin wata matsala ba"
Ya faɗa a hankali
Saboda haka
Ya ci gaba da haƙuri
Yana addu’a kawai
A ranar da aka sallamo Iman daga asibiti
Malam ya ɗauko wayarsa
Ya kira Suhail
Da sauri Suhail ya ɗaga
“Assalamu alaikum Malam"
“Wa alaikumus salam"
Malam ya ce cikin nutsuwa
“Khadija ta sauka an samu ɗiya mace”
“Sun dawo gida lafiya"
Suhail ya lumshe idanunsa
“Alhamdulillah…”
Ya sauke ajiyar zuciya
Sai ya ce
“Nagode malan Allah raya"
ko da ya katse
Bai tsaya ɓata lokaci ba
Kai tsaye kasuwa ya nufa
Ya shiga shagunan kayan yara
Ya sayi kaya masu yawa
tunda kam Baby dresses,Blankets,Towels,Diapers
Har da wasu kayan wasa masu masu kyau wanda ma lalle suyi amfani dashi yanzu ba
Ya kuma sayi kayan ciye-ciye da kayan marmari domin Iman
Bayan ya gama
Ya loda komai cikin motarsa
Kai tsaye Kaduna ya nufa
Da ya isa gidan Malam…
Ya tarar da Malam zaune a kofar
Ya yi sallama
Malam ya amsa
Ba tare da wata magana mai yawa ba, Suhail ya sauke kayan daga mota
“Malam"
“Na kawo waɗannan ne'
Malam ya kalli tarin kayan.
Ya girgiza kai.'
“Ka shigo ciki"
Wannan ne karo na farko
Da Malam ya ce masa ya shiga cikin gida tun bayan rabuwarsa da Iman
Zuciyar Suhail ta fara bugawa da sauri
Ya bi Malam a baya cikin nutsuwa
Ba tare da sanin abin da zai gani a ciki ba
Suhail ya bi Malam cikin nutsuwa har suka shiga ɗakinsa
Bayan sun zaun
Malam ya miƙe tsaye
Ya nufi ɗakin da Iman take
Ya buga ƙofa a hankali
Ammi ce ta buɗe
Da ya shiga, ya kalli Iman
“Ki ba ni jaririyar Mahaifin ta yazo"
Ba tare da ta yi tambaya ba, ta miƙa masa ita
An saka ta cikin wani ƙaramin baby dress pink colour
An sa mata ƙaramin hula pink mai ɗauke da farin fur
Ƙafafunta na sanye cikin safa ƙanana masu taushi
Ƙananun hannayenta suna fitowa daga cikin rigar, suna motsi a hankali
Har yanzu tana cikin barci
Malam ya karɓe ta cikin kulawa
Ya juya ya fita da ita
Da ya shiga ɗakin
Kai tsaye ya miƙa jaririyar hannun Suhail
“Ga ta"
Hannun Suhail na rawa
Da ƙyar ya karɓe ta
Karo na farko kenan da ya ɗauki ’yarsa
Da ya ke sauke idanunsa a kanta
Sai zuciyarsa ta cika da wani irin tausayawa
Ta yi kyau matuƙa
Fuskarta ƙarama ce tamkar wata
Fatarta fara sol
Ƙaramin hancinta ya yi daidai da nasa
Dogayen gashin idanunta sun kwanta bisa kumatunta
Labbanta ƙanana jajaye ne
Ƙananun yatsunta sun naɗe a hankali, kamar suna neman su riƙe yatsansa
Sai ƙamshin jarirai mai daɗi yake tashi daga jikinta
Suhail ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta
Hawaye suka cika masa ido
A hankali ya shafi goshinta da babban yatsansa
Ya sumbaci kanta
“Alhamdulillah…”
Shi kaɗai ya iya furtawa
Malam ya yi murmushi
Ya ce
“Ka raɗa mata suna.”
“A matsayinka na mahaifinta.”
Da jin wannan kalma
Mahaifinta
Sai zuciyar Suhail ta cika da farin ciki
Ya ji kamar an dawo masa da wani abu da ya daɗe yana nema
Ya kalli jaririyar
Ya yi murmushi
A hankali ya yi mata raɗa a kunnen dama
“Allahu Akbar"
Ya yi mata Adhan
Sannan ya juya zuwa kunnen hagu
Ya yi mata Iqamah
Bayan ya gama
Ya ɗaga kai
Ya ce
“Sunanta…”
“Ummulkhairi.”
Shiru ya ɗan ratsa ɗakin
Sai Malam ya yi murmushi
“Masha Allah"
“Suna ne mai albarka.”
“Allah Ya sanya ta ta zama kamar ma’anar sunanta"
“Ameen"
Suhail ya amsa cikin sanyin murya
Malam ya karɓi jaririyar daga hannunsa
Kafin ya fita
Ya juya ya dubi Suhail.
“Haba Suhail"
“Wannan siyyayar da kake ta kawowa ai ta isa haka"
“Ka riƙe kuɗin ka"
“Rayuwa tana da gaba"
Suhail ya yi murmushi
Ya girgiza kai
“Ba komai Malam"
“Duk abin da zan yi mata kaɗan ne"
“Allah ne Ya ba ni ita"
“Ni kuma ina son na yi abin da zan iya"
Malam ya dafa kafaɗarsa
“Allah Ya ƙara maka arziki
“Ameen"
Ya fita da jaririyar
Da ya mayar da Ummulkhairi ɗakin
Ammi ta karɓe ta
Ta miƙa wa Iman
koda iman ta rungume ta
Sai ta ji wani ƙamshi sananne
Ƙamshin turaren Suhail
Nan take zuciyarta ta buga
Ta lumshe idanunta
Wani irin raɗaɗi ya ratsa zuciyarta
Ba tare da ta ce komai ba
Ta miƙa jaririyar ga Hafsat
“Hafsat"
“Ki canza mata kayan nan"
Hafsat ta yi mamaki
“Me ya faru?”
Iman ta kau da kai
“Don Allah kawai ki canza mata"
Hafsat ta karɓi jaririyar cikin mamaki
Bayan ɗan lokaci…
Malam ya shigo
Ya zauna."
Ya ce cikin natsuwa,
“Suhail ya rada mata suna.”
“Ya sa mata"
Ummulkhairi
Nan take fuskar Iman ta sauya
Ba ta ce komai ba
Sai dai zuciyarta ba ta ji daɗin hakan ba
Domin tun tana ɗauke da cikin…
Ta yi niyyar idan Allah Ya ba ta ’ya mace
Za ta sa mata sunan Ammi
Ta sauke ajiyar zuciya
Shiru ta yi
Hafsat kuwa ta lura da canjin fuskarta
Sai ta yi murmushi
Ta ce
“Ni dai zan riƙa kiranta…”
Khairiyya
Nan take walwala Ammi ta ragu
dan so tayi malan ya rada mata sunan
Duk da ba ta ce komai ba
Sai ta ji sunan ya kwanta mata a rai kuma