BARRISTER SUHAIL

93

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️—93

Bayan Malam ya sanar da Suhail sunan da ya raɗawa jaririyar, ya ɗauki hanyarsa zuwa Abuja

Tun daga ranar kuwa, Ammi ta fara lura da wani sabon yanayi tattare da Iman

Da farko ta ɗauka gajiyar aikin tiyata ce

Sai dai kwanaki suna wucewa, abin maimakon ya ragu sai ƙaruwa yake

Ko da Khairiya ta yi kuka, Iman ba ta ɗaukar ta

Ammi ko Hafsat ne suke rige-rigen ɗaukar jaririyar

Idan lokacin shayarwa ya yi kuwa

Sai Iman ta ce

“Ammi… zafi yake min"

Ammi ta yi haƙuri.

Ta nuna mata yadda za ta riƙe jaririyar

Ta nuna mata yadda za ta ba ta nono

Amma kullum amsa ɗaya ce

“Ba za ta iya ba"

A hankali Ammi ta fara jin tsoro

Ta kan zauna tana kallon Iman

Yarinyar dai  ba ta da wata rashin lafiya

Jikinta yana ƙara samum sauki

Raunin tiyata ma yana warkewa

Amma zuciyarta kamar tana wani wuri dabam

Sau da yawa sai ta zauna tana kallon Khairiya kamar ba ’yarta ba

Hafsat ce ta fi yawan kula da jaririyar

Ita ce ke mata wanka

Ita ce ke canja mata kaya

Ita ce ke rarrashinta idan ta yi kuka

A farko Ammi ta ce a ranta

“Ko damuwar bayan haihuwa ce (postpartum depression)?”

Sai ta ci gaba da lallashinta

Amma bayan wasu kwanaki

Ta fahimci abin ya fara wuce gona da iri

Wata rana Khairiya tana kuka sosai Saboda yunwa

Ammi ta kawo ta gaban Iman

Ta ce

“Ki ba ta nono"

Iman ta girgiza kai

“Ba zan iya ba Ammi"

“Ammi… zafi yake min"

Ammi ta yi shiru na ɗan lokaci

Sai ta zauna kusa da ita

Cikin taushi ta ce

“Dole ne ki bata kuwa"

Da Iman ta ƙi

Sai Ammi ta rungumo ta

Ta taimaka mata ta zaunar da Khairiya a ƙirjinta

Da ta ciro mata nono da kanta

Sai Iman ta fashe da kuka

Hawayenta suka jiƙa fuskarta

Khairiya kuwa ta kama shan nonon cikin natsuwa

Ammi ma idanunta suka cika da hawaye

Ta san ba ciwon jiki kaɗai ne ke damun Iman ba

Har zuciyarta ma tana ciwo

Duk da haka

Ammi ta sami Malam

Ta ba shi labarin komai

Da yamma Malam ya kira Iman

Ta zo ta zauna gabansa

Ya kalle ta cikin natsuwa

Ya ce

“Khadija"

“Ko wani abu ya haɗa ki da mahaifin wannan jaririyar nan"

“Ba ita tai yi miki laifi ba"

“Ba ta san komai ba"

“Ba ki da ikon ɗaukar fushinki ki ɗora mata"

“Allah ne Ya ba ki amanarta"

“Idan kika kasa kula da ita… wa zai kula da ita?”

Hawayen Iman suka sake zuba

Ta sunkuyar da kai

“Ka yi haƙuri Malam"

“Ban san me yake damuna ba"

Malam ya ce

“Ki nemi taimakon Allah"

“Ki daina bari Shaiɗan ya rinjayi zuciyarki"

Tun daga wannan ranar

Iman ta fara ƙoƙarin kula da Khairiya

Ko da ba ta saba ba

Tana ɗaukar ta

Tana shayar da ita

Tana daukar ita tayi kuka 

A hankali soyayyar jaririyar ta fara shiga zuciyarta


A Abuja kuwa

Da Suhail ya isa gida, abu na farko da ya yi shi ne kiran Mami

Bayan sun gaisa ya ce

“Mami…”

“Alhamdulillah"

“Iman ta haihu lafiya"

Mami ta yi farin ciki sosai

“Allah Ya raya mana"

“Ameen"

A ranar

Kwana biyar kenan da dawowar Mami gidan mijinta

Tun shigarta gida

Abba ya lura da wani babban canji a tare da ita

Ta daina tsawa

Ta daina raina ma’aikata

Har da Aunty Fauziya

Yadda take mata magana ya sauya gaba ɗaya

Abba ya yi mamaki

Ranar da Mami ta ba su labarin haihuwar Iman

Aunty Fauziya ta yi farin ciki

Ta ce

“Alhamdulillah"

“Ya kamata mu kai mata kayan barka"

Nan take ta haɗa kyawawan kayan jarirai
Da sauran abubuwan buƙata

Abba ya tambaya cikin mamaki

“Af… tana ina yanzu?”

Gaban Mami ya faɗi

Ta gane har yanzu bai san gaskiyar abin da ya faru ba

Da sauri ta ce

“Tana gidan su ne"

“Haihuwar ce ta zo da ɗan matsala"

Aunty Fauziya ta lura da yadda Mami ta rikice

Sai dai ba ta ce komai ba

Ta ce

“Ku ba ni kayan ni zan je"

“Driver zai kai ni"

Ba tare da ɓata lokaci ba

Ta kama hanyar gidan su iman

Da ta isa gidan Malam

tun a tsakar Iman ta ji muryarta

Nan take ta fito daga ɗaki

Ko da ta gan ta

Sai zuciyarta ta cika da wani iri

Ba za ta taɓa mantawa da alherin Aunty Fauziya ba

Ta gaishe ta cikin ladabi

Aunty Fauziya ta rungume ta

Ta ce

“Iman ashe an sauka"

murmushi iman tayi ta jata suka shiga dakin 

Hafsat Ta fito da Khairiya

Aunty Fauziya ta karɓe ta

Ta yi murmushi

“Masha Allah…”

“Allah Ya raya ki"

Amma yayin da take kallon Iman

Sai ta lura da wani abu

Fuskarta ta rame

Murmushinta ba ya fitowa daga zuciya

Idanunta kuwa

Sun cika da wani irin baƙin ciki

Ta juya ta dubi Ammi da gaisuwa ce ta shiga tsakanin su 

Ta ce cikin ladabi

“Ammi"

“Dan Allah idan ba damuwa"

“Ina so ni da Iman mu ɗan yi magana mu kaɗai"

Ammi ta fahimci akwai abin da ta lura da shi

Ta jinjina kai

Ta fito tare da Hafsat

Suka barsu su biyu."

Aunty Fauziya ta matsa kusa da Iman."

Ta kamo hannunta

“Iman"

“Lafiya kuwa?”

“Na lura akwai abin da yake damunki'"

“Na haɗa ki da girman Allah"

“Idan akwai wata matsala… ki faɗa min"

Nan take

Kuka ya ƙwace wa Ima

Ba ta iya ɓoye komai ba

Ta ba ta labarin komai

Tun daga ranar da mami ta dawo gidan su aka wulaƙanta ta

Har zuwa mutuwar aurenta da Suhail wanda mami ce tirsasa sa 

Watanni bakwai kenan da faruwar komai

Aunty Fauziya ta tsaya cak

“Subhanallah…”

“Wallahi ban san komai ba"

Hawaye suka cika idanunta

Ta kamo hannun Iman da ƙarfi

“Ki yi haƙuri"

“Allah Ya fi kowa sanin abin da ya faru"

“Allah zai gyara lamarin"

Ta rungume ta

Ta share mata hawaye

Bayan ta yi mata addu’a

Ta yi musu sallama

A hanya cikin mota

Tunani kawai take yi

A ranta ta ce

“Duk alamu"

“Abba bai san komai ba""

“Dole ne ya san gaskiyar abin da ya faru"

Ta jingina da kujerar motar

Ranta ya yi matuƙar ɓaci

Ta yi alƙawarin

Ba za ta yi shiru ba

Bayan Aunty Fauziya ta dawo gida

Tun daga shigowarta Abba ya lura da wani canji a tattare da ita

Ba fara’arta ta saba ba

Ba ta da walwala

Tunani ne ya mamaye fuskarta

Har bayan sun gama cin abinci tana cikin yanayin

Abba ya ajiye spoon ɗinsa

Ya dubeta

“Fauziya"

Ta ɗago kai

“Na’am"

“Lafiya kuwa?”

Ta yi saurin ƙaƙalo murmushi

“Lafiya lau"

Abba ya girgiza kai

“A’a.”

“Na fi shekar goma ina rayuwa da ke"

“Na san lokacin da kike cikin damuwa"

Ta yi shiru

Ta sunkuyar da kanta

Ta yi niyyar ɓoye masa gaskiyar

Ba don komai ba

Sai don ba ta son Mami ta ji cewa ita ce ta bayyana abin da aka ɓoye

Sai dai

Ta tuna cewa ci gaba da ɓoye gaskiya ba zai kawo maslaha ba

A hankali ta sauke ajiyar zuciya

“Alhaji"

“Akwai wani abu da ya kamata ka sani"

Abba ya daidaita zamansa

“Menene?”

Cikin nutsuwa

Aunty Fauziya ta fara ba shi labarin duk abin da ta ji daga bakin Iman

Tun daga ranar da aka kore ta

Har zuwa mutuwar aurenta da Suhail

Da zaman da ta yi a gidan Malam

Da cikin da take ɗauke da shi

Har zuwa haihuwar Khairiya

Kowace kalma da take faɗa

Sai fuskar Abba ta ƙara sauyawa

Lokacin da ta kai ƙarshen labarin

Shiru ya mamaye falon

Abba ya kasa cewa komai

Ya zauna kamar mutum-mutumi

Idanunsa sun tsaya wuri ɗaya

Tamkar ya kasa gaskata abin da kunnuwansa suka ji

Can kuma

A hankali hawaye suka fara cika masa ido

Ya girgiza kai

“innalillahi wa'inna illahir raji'un"

Muryarsa ta yi rawa

“Yarinyar nan"

“Yarinyar nan tana gidan Malam tsawon watanni bakwai"

“An raba aurenta"

“Ni kuma ban san komai ba?”

Hawayen da yake ƙoƙarin dannewa suka zubo

Ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa

Karo na farko

Aunty Fauziya ta ga Abba yana kuka saboda Iman

Ya ɗaga kansa cikin ciwo

“Fauziya"

“Ko na masu laifi ne"

“Ba su ga ya dace a sanar da ni ba?”

Ta girgiza kai

“A’a.”

“Ban ga laifinsu ba"

“Da alama ba su so ƙarin matsala ne"

Abba ya miƙe tsaye."

Cikin murya mai nauyi ya ce

“Allah Ya isa tsakanina da Laila"

“Da wani ido zan kalli Malam?”

“Mutumin da na je na roƙi auren Iman kuma ya bamu"

“Mutumin da ya amince da ni"

“Yau ga abin da ya faru"

“Ni kuma ban ma sani ba"

Ya share hawayensa

Sai dai zuciyarsa ta ƙi samun nutsuwa

A fusace ya juya

Kai tsaye ya nufi part ɗin Mami.

Aunty Fauziya ta firgita

“Alhaji"

Ta kira shi

Bai waiwayo ba

Ta sake cewa

“Don Allah ka saurare ni mana"

Har ta yi ƙoƙarin binsa

Amma ko kallonta bai yi ba

A zuciyarsa

Abu ɗaya ne kawai yake ta maimaitawa

“Ta yaya aka ɓoye mini wannan babban al’amari?"

Tun daga bakin ƙofar falon…

Mami ta ji muryar Abba cikin tsananin fushi.

“Laila!”

“Laila!!”

Gabanta ya faɗi

Tun kafin ya shigo ta san akwai abin da ya faru

A hankali ta miƙe tsaye duk da kafar robar dake jikin ta

Hannayenta suka fara rawa.

Abba ya shigo falon fuskarsa cike da baƙin rai

Idanunsa sun yi ja

Ya tsaya gabanta

Na wasu daƙiƙu bai iya cewa komai ba

Sai kawai ya ɗaga hannu sama

“Allah Ya isa tsakanina da ke Laila!”

Mami ta sunkuyar da kai

“Alhaji"

Kar ki kira sunana!”

Ya katse ta da ƙarfi

“Kin cuce ni!”

“Kin yaudare ni!”

“Kin haɗa baki da yaran ki kuka ɓoye mini magana mafi girma da ta taɓa faruwa a gidana"

“Har tsawon watanni bakwai… ban san cewa Iman tana gidan iyayenta ba"

“Ban san an raba aurenta da ɗana ba"

“Da wani ido zan sake kallon Malam?”

“Da wani fuska zan sake kallon iyayen yarinyar?”

Mami hawaye suka fara zubo mata

Ta san wannan ranar za ta zo

Sai dai ba ta yi tunanin za ta yi zafi haka ba

Cikin rawar murya ta ce

“Alhaji… na yi kuskure"

“Wallahi na yi nadama"

“Ka yi haƙuri"

“Ban yi hakan don in ƙi ka sani ba…”

“Na rasa yadda zan gaya maka ne"

Abba ya yi dariyar takaici

“Kin rasa yadda za ki gaya mini?”

“Ni mijinki ne ko ba ni ba?”

“Ni uban gidan nan ne ko ba ni ba?”

“Yanzu har irin wannan magana za a ɓoye mini?” saboda ke kika hada komai ko

Ya dafe ƙirjinsa

“Wallahi Laila… kin karya amanar da na ba ki"

Mami ta durƙusa gabansa

“Don Allah ka yafe mini"

“Wallahi ba zan sake ba"

“Na san na yi laifi"

Abba ya ja baya

“Ba na son jin komai"

“Tun daga yau"

“Na sake ki"

“Saki ɗaya"

“Ki bar mini gidana"

Nan take Mami ta saki wani irin kuka

Ta riƙe ƙafafuns

“Alhaji!”

“Don Allah!”

“Kada ka yi mini haka"

“Na tuba"

“Na yi nadama"

A daidai lokaci

Aunty Fauziya ta shigo cikin sauri

“Alhaji!”

“Don Allah ka kwantar da hankalinka"

“Idan hankali ya gushe, hankali ake sawa a nemo sa"

“Ba daidai ba ne a yi saki cikin wannan irin fushi"

Abba ya juya ya kalle ta

Idanunsa cike da fushi

“Fauziya!”

“Wallahi idan kika sake saka baki a kan wannan muguwar matar…”

“Zan haɗa da ke"

Shiru ya mamaye falon

Aunty Fauziya ta yi shiru

Ta fahimci ba wannan ne lokacin da zai saurare ta b

Abba ya juya

Ba tare da ya sake kallon Mami ba…"

Ya fita daga falon

Ƙarar rufe ƙofar ta kara firgita Mami

Ta zauna a ƙasa

Kukanta ya ƙaru

Ta dafe kanta da hannayenta biyu

“Na shiga uku…”

Ta furta cikin kuka

“Yanzu ina zan dosa?”

“Na’ima ba zan iya komawa gidanta ba…”

“Shi ma Suhail ba zai yi farin ciki da zuwana ba…”

“Na rasa mafita.”

Aunty Fauziya ta zauna kusa da ita

Ta kama hannunta

“Ki kwantar da hankalinki.”

“Da izinin Allah… wannan ba ƙarshen komai ba ne"

“Za mu nemi hanyar gyara abin da ya lalace

Sai dai Mami ta san… wasu ƙofofi idan an rufe su, ba kalmar “yi haƙuri” kaɗai ke sake buɗe su ba karo na farko a rayuwarta, ta fara jin tsoron sakamakon abin da hannunta ya aikata

like share and comment