94
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️—94
Bayan Alhaji ya tafi
Malam ya daɗe tsaye a ƙofar gida
Numfashi kawai yake saukewa
Abin da ya ji daga bakin Alhaji ya tsaya masa a rai
A hankali ya shiga cikin gida
Ya sami Ammi zaune tana rike da Khairiya
Ya dubeta ya ce
“Maryama"
Ta ɗago kai
“Na’am Malam"
“Ki kira min Iman"
Ba tare da tambaya ba Ammi ta miƙe
Ta nufi ɗakin Iman
Ta same ta zaune tana linke kayan su da Hafsat ta wanke
“Iman"
“Malam na kiranki"
Gaban Iman ya faɗi
Ta gyara zamanta
Ta miƙe ta bi bayan Ammi
Da ta shiga ɗakin Malam
Ta zauna a ƙasa kamar yadda ta saba
“Assalamu alaikum"
“Wa alaikumus salam"
Malam ya amsa
Ya ɗan yi shiru kafin ya ce
“Khadija"
“Na’am Malam"
“Yanzu kina cikin wani hali da ba na son in ƙara miki wani nauyi"
“Amma akwai magana da dole na gaya miki"
Iman ta yi shiru
Ta ci gaba da saurarensa
Malam ya sauke ajiyar zuciya
“Yau Alhaji mahaifin Suhail ya zo nan"
Nan take zuciyar Iman ta buga
Ta ɗago kai cikin mamaki
“Abba?”
Kai Malam ya jinjina
“Eh"
“Ya zo ne domin neman afuwa akan Abinda ya faru"
Idanun Iman suka cika da hawaye
Malam ya ci gaba
“Ya ce bai san abin da ya faru ba sai jiya"
“Ya kuma zo yana roƙon a sake haɗa aurenku"
Shiru tayi
Wani irin shiru ya mamaye ɗakin
Iman ta sunkuyar da kanta
Hawayenta suka fara sauka ɗaya bayan ɗaya
Malam ya ci gaba cikin nutsuwa
“Har ila yau"
“Ya sanar da ni cewa Suhail yana asibiti"
Iman ta ɗago kai da sauri Baba
“Asibiti?”
“Eh yana Asibiti"
“Likitoci sun tabbatar masu da ya kamu da ciwon zuciya"
Nan take fuskar Iman ta sauya
Ta dafe ƙirjinta
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un"
Ba ta san lokacin da hawayenta suka ƙaru ba
Sai dai ta yi saurin share su
Malam ya lura da hakan
Amma bai ce komai ba
Ya ce cikin sanyin murya
“Khadija"
“Ban kira ki nan domin in tilasta miki komawa wajensa ba"
“Ni ba zan taɓa tilasta miki abin da zuciyarki ba ta so"
“Ke ce Allah Ya ba zaɓi"
“Idan kin ce ba za ki koma ba…”
“Wallahi zan mutunta matsayinki"
“Idan kuma kin ce za ki koma"
“Haka ma zan tsaya a bayanki"
Ya ɗan yi shiru
“Kawai ina so ki yi istikhara"
“Ki nemi zabin Allah"
“Kar ki yanke hukunci saboda fushi"
“Kar kuma ki yanke shi saboda kinji tausayin sa"
“Ki yanke shi saboda Allah"
Iman ta kasa magana
Hawayenta ne kawai ke sauka
A hankali ta ce
“Malam"
“Ni yanzu ban san abin da zuciyata take so ba"
“Duk lokacin da na tuna abin da ya faru… zuciyata tana ciwo"
“Amma banji daɗin yadda aka ce yana asibiti kuma nasan saboda ni"
Ta rufe fuskarta da tafin hannayenta
“Ban san me yake faruwa da ni ba"
Malam ya miƙe
Ya ɗora hannunsa a kanta
“Allah Ya ya miki zabi mafi Alkairi Khadija ya kuma miki albarka dake da Abinda kika haifa dama wanda zaki haifa a gaba"
“Amin.”
Ta amsa cikin kuka
Malam ya juya ya fita daga ɗakin
Ya bar Iman ita kaɗai
Ta zauna tana kallon Khairiya da ke barci cikin natsuwa
A hankali ta rungume ta a ƙirjinta
Ta lumshe idanunta
Sai hoton Suhail ya fara yawo a cikin zuciyarta
Musamman ranar da ya ce mata
“You are my peace… my safe place… and my home"
Hawaye suka sake zubo mata
Ba ta san ko zuciyarta tana ƙoƙarin yafiya bane
Ko kuwa tana ƙoƙarin mantawa ne
Bayan tattaunawar Malam da Iman
Bai sake mata maganar komawa wajen Suhail ba
Ya bar ta da zuciyarta.'
Ya san akwai wasu yaƙe-yaƙe da mutum ba zai iya yi wa wani ba
Sai dai shi kaɗai zai yi da kansa
Kowace rana
Iman na ƙoƙarin kula da Khairiya
Amma duk da haka
Babu rana ko ɗaya da rana za ta faɗi ba tare da zuciyarta ta tuna da Suhail ba
Wani lokaci idan tana shayar da Khairiya
Sai ta tuna yadda ya riƙe hannunta yana mata alƙawarin ba zai taɓa barinta ba
Wani lokaci idan ta ji ƙamshin wani turare
Sai zuciyarta ta tuna da ƙamshin turaren Suhail wanda ya fi mata dad'i fiye da ko wanne
Sai ta yi saurin girgiza kanta
“Ya Allah…ka cire shi daga raina"
Amma hakan ya gagara
A gefe guda kuma
Suhail ya kwashe kwana uku a asibiti
Bayan likitoci sun tabbatar yanayinsa ya ɗan daidaita
Aka sallame shi
Abba bai kai shi gidansa ba
Kai tsaye ya wuce da shi gidansa
Ko a zuciyarsa ma
Ya manta ma cewa Suhail yana da wata mata
A gare shi yanzu
Abin da ya fi muhimmanci shi ne lafiyar ɗansa
A ranar da Khairiya ta cika kwana goma da haihuwa
Mubarak ya sake dawowa Kaduna
Bayan sun gaisa da Malam da Ammi
Ya ɗan gyara zamansa
Ya ce
“Malam"
“Akwai maganar da na zo da ita"
Malam ya ce
“Muna jinka"
Mubarak ya ce
“Abubakar da muka taso tare tun muna yara"
“Tun kafin aurwn Iman ya nuna yana sonta"
“Amma lokacin da aka ba Suhail ita… sai ya haƙura"
Ya ɗan yi shiru
“Yanzu da babu aure"
“Yana roƙon idan za a ba shi dama ya turo manyansa"
Ammi ta yi murmushi
“Masha Allah"
“Abubakar ai yaro ne mai hankali"
“Na san shi sosai"
“Mutum ne na kirki ga ladabi da biyyaya idan yazo gidan nan ko ido baya bari a hada da shi"
“Idan Iman ta aure shi… ta samu miji nagari"
Ta ci gaba da yaba masa
Malam kuwa
Shiru kawai ya yi
Bayan sun gama magana
Sai ya ce
“To"
“Amma ai ba mu ne za mu yanke hukunci ba"
“Ka je ka ji ta bakin Iman"
“Idan ta yarda sai a ci gaba magana"
Mubarak ya jinjina kai
Ya nufi ɗakin Ima
Ya same ta zaune a bakin gado.
Khairiya na kwance gabanta
Tana canza mata diaper
kodata gan shi
Ta yi murmushi
“Yaya Mubarak… yaushe ka zo?”
Ya ce
“Na jima da zuwa"
“Ina wajen Malam"
Ya zauna
Bayan ɗan taƙaitaccen shiru
Sai ya gaya mata dalilin zuwansa.
Ya faɗa mata maganar Abubakar
Har ya gama
Iman ta yi shiru
Ta ci gaba da kallon Khairiya
Daga ƙarshe ta ce cikin sanyin murya ta ce
“Yaya…”
“Don Allah"
“Kada ka sake kawo min wannan maganar aure yanzu"
Mubarak ya haɗe gira
“Saboda me?”
Ta ɗaga kai
“Saboda yanzu…”
“Aure ba ya gabana.”
“Abin da yake gabana shi ne tarbiyyar diyata"
Ta rungumo Khairiya
Ta ƙara da cewa
“Don Allah… ku bar ni da rayuwata"
Mubarak ya yi ƙoƙarin sake magana
Sai ta girgiza kai
“Don Allah"
“Kada ka matsa min"
Ya fahimci ba za ta saurare shi ba.
Sai ya miƙe ya fita
koda ya fita…
Iman ta tsaya cak
Ta jingina da bango
Tunani ya fara yawo a ranta"
“Ta yaya"
“Ta yaya zan haɗa rayuwata da wani namiji"
“Da ba Suhail ba?”
Wannan tunanin kaɗai
Ya sa zuciyarta ta karye
Nan take ta fashe da kuka
Ta rungume Khairiya tana zubar da hawaye
A dakin Malan kuwa…
Mubarak ya ba su labarin abin da ta ce
Ammi ta ɓata rai
“Ni tun tuni na san hankalinta yana kan Suhail"
Malam ya ce cikin natsuwa
“To… ki barta mana
idan tana son komawa"
“Lokaci yana warkar da abubuwa da yawa"
Ammi ta juya da sauri
“Ni kuwa ban yarda ba"
“Wallahi ba za ta koma wajen Suhail ba"
“Ko da zan mutu"
Ta juya ta kalli Malam
“Ni kam ina ganin kamar kana goyon bayan mutanen can"
“Shi ya sa lokacin da ake maganar Abubakar ba ka ce komai ba"
“Amma ni a matsayina na uwarta"
“Idan har iman zata sake yin aure"
“Abubakar zan ba ta"
Malam bai ce komai ba
Ya sunkuyar da kai
A zuciyarsa kuwa
Ya san dole ne a bar Iman ita ce za ta zaɓi makomar rayuwarta
Domin a wannan karon
Ba zai sake zaɓa mata ba
Tun bayan zancen Abubakar…
Gidan Malam ya kasu gida biyu
Ammi ta dage kan cewa Iman dole ta manta da Suhail
Malam kuwa
Bai sake cewa komai ba
Sai dai duk lokacin da Ammi ta fara maganar aure
Sai ya ce
“Ki bar yarinyar nan ta huta"
“Ba ta cika ma kwana arba’in da haihuwa ba Amma kun kawo mata maganar aure"
“A yanzu ba lokacin wannan maganar ba ne"
Ammi ta girgiza kai
“Shi kenan.”
“Ku ci gaba da lallashinta"
“Ranar da Suhail ya sake zuwa neman ta ne za ku gane"
Malam bai tanka mata ba
Ya miƙe ya fita zuwa masallaci
A ɗaki kuwa…
Iman tana zaune tana jijjiga Khairiya dake kuka
har ta yi barci cikin kwanciyar hankali
Iman ta shafa ƙaramar fuskarta
A hankali ta yi murmushi
Sai kuma murmushin ya ɓace
Ta tuna maganar Mubarak
“Abubakar yana son ki…”
Nan take ta girgiza kanta
“Ba zan iya ba"
Ta furta a hankali
“Ba zan iya kallon wani namiji a matsayin mijina ba…”
Ta rungume Khairiya
A gidan Abba kuwa…
Suhail ya fara samun sauƙi
Sai dai ba a bar shi yana fita yadda yake so ba
Abba ya hana shi zuwa ko ina '
“Hutawa za ka yi"
“Lafiyarka ta fi komai"
Suhail bai yi musu ba
Amma zuciyarsa…
Ba ta nan take ba
Kullum tunaninsa yana wajen iman da khairiya
Yana son ya kira Hafsat
Sai ya tuna alƙawarin da ya yi mata
Ya ajiye wayar
Ya sake ɗauka
Ya kuma ajiye ta
Daga ƙarshe ya ɗaga kai ya dubi Abba
“Abba…”
“Na’am"
“Ina son zuwa gidan malan.”
Abba ya girgiza kai
“A yanzu ba za ka je ko’ina ba.”
“Likita ya ce kana buƙatar hutu.”
Suhail ya sauke numfashi
“Amma zuciyata ba zata sam hutawa ba"
Abba ya yi shiru
Ya fahimci abin da ɗansa yake ji.
Sai dai bai nuna masa ba
Ya ce
“Ka yi haƙuri"
“Allah yana tare da masu haƙuri"
Da dare…
Abba ya zauna shi kaɗai a falonsa
Tunani kawai yake yi
Ya tuna ranar da ya je gidan Malam neman auren Iman
Ya tuna irin farin cikin da Suhail ya nuna ranar da aka ɗaura auren
Ya tuna yadda Iman take girmama shi
Sai hawaye suka cika masa ido.
Ya ɗaga hannayensa sama
“Ya Allah…”
“Idan akwai alheri a cikin komawar aurensu"
“Ka haɗa zukatansu.”
“Idan kuma babu alheri…”
“Ka ba kowa haƙurin jure ƙaddararka"
“Amin"
Ya share hawayensa
A zuciyarsa ya yanke hukunci guda ɗaya
Ba zai matsa wa Iman ba
Ba kuma zai tilasta wa Malam ba
Zai jira
Har sai lokacin da zuciyar Iman ita da kanta za ta yanke hukunci
Kwana biyu suka sake wucewa cikin shiru
A gidan Malam
Khairiya na ƙara girma da kyau
Idan ta yi murmushi
Sai duk wanda ya gan ta ya tsaya yana kallonta tsagen kyauwunta
Ammi ce ke cewa
“Wallahi yarinyar nan akwai wani irin haske a fuskarta"
Hafsat ta yi dariya
“Ammi ai tun ranar farko na ce miki kyakkyawa ce"
Iman kuwa
Murmushi yaƙe kawai take yi
Sai dai idan ta kalli Khairiya sosai
Sai ta tuna wani
Mutumin da bai san irin yadda ’yarsa take ƙara kyau ba
Sai ta yi saurin kawar da tunanin.
A wannan ranar
Da yamma
Wata mota ta tsaya a ƙofar gidan Malam
Hafsat ce ta leƙa ta taga Abba
Ta yi mamakin Ganin sa dan ko a baya da yazo taje katsina duba jikin Mahaifin ta
Da sauri ta shiga cikin gida
“Ammi…”
“Ga baban Suhail ya zo"
Ammi ta ɗan haɗe gira
“Alhaji… mahaifin Suhail"
Malam da ke zaune ya ɗaga kai.
“Ki buɗe masa ƙofa hafsat"
Hafsat ta fita
Ta tarbe shi cikin girmamawa
“Barka da zuwa.”
Abba ya yi murmushi
“Yauwa ’yata.”
Ta raka shi har falon baƙi
Bayan sun gaisa
Na wasu mintoci babu wanda ya yi magana
Daga ƙarshe Abba ya sauke ajiyar zuciya
“Malam"
“Na sake zuwa ne domin neman gafara"
“Na san na zo sau da yawa"
“Amma zuciyata ta kasa yin hakuri"
Malam ya ce cikin nutsuwa
“Alhaji, ka kwantar da hankalinka"
“Ba ni da fushi da kai"
Abba ya girgiza kai
“Amma ni ina da fushi da kaina"
“Na gaza kare amanar da aka ba ni"
Ya ci gaba da cewa
“Na ga yadda Suhail yake"
“Wallahi ba shi da walwala.”
“Yana rayuwa ne kamar mutum wanda aka cire rabin ransa"
Malam ya yi shiru
Abba ya ɗora da cewa
“Ban zo ne domin a tilasta Iman komawa ba"
“Na zo ne domin in roƙi izinin magana da ita"
“Ko da minti biyar ne kawai"
“Idan ta ce ba ta son gani na… zan tafi.”
Ammi ta yi saurin cewa,
“A’a Alhaji"
“Ba zai yiwu ba"
“Yarinyar nan yanzu tana samun kwanciyar hankali"
“Ba za mu sake buɗe mata tsohon ciwo ba"
Abba ya sunkuyar da kai
“Na fahimta.”
“Amma ina roƙonku"
“Ko ta ji abin da zan faɗa ne kawai"
Malam ya kalli Ammi
Sannan ya kalli Abba.
Ya ce
“Alhaji"
“Ba ni da ikon hana ka magana da khadija"
“Amma kuma ba ni da ikon tilasta mata ta fitowar"
“Zan shiga in sanar da ita@
“Idan ta yarda… za ku yi magana"
“Idan kuma ta ƙi"
“Sai mu karɓi hukuncinta"
Abba ya jinjina kai
“Hakan ya ishe ni"
A ɗaki kuwa…
Iman tana zaune
Malam ya shiga a hankali
“Khadija…”
Ta ɗago kai
“Na’am Malam"
Ya zauna
Ya ce cikin sanyin murya
“Alhaji yana waje"
“Ya zo ne"
“Yana roƙon ya yi magana da ke"
Da jin haka
Jikin Iman ya yi sanyi
Hannunta ya tsaya cak kan bayan Khairiya
Numfashinta ya ɗan canza
Ta daɗe ba tare da ta ce komai ba
Malam bai matsa mata ba
Sai bayan wasu daƙiƙu
Ta ɗaga kai
“Malam…”
“ya zo ne saboda Suhail…?”
Malam ya jinjina kai a hankali.
“Eh"
Hawaye suka cika idanun Iman."
Ta rungume Khairiya sosai."
Zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi
Ba ta san ko za ta iya fuskantar mahaifin Suhail ba
A hankali Iman ta fito daga ɗaki
Khairiya na hannun Hafsat
Da Abba ya hango ta
Ya tsaya yana kallonta
Ta rame
Ta yi sanyi
Fuskarta ta rasa walwalar da ya saba gani
Wani irin tausayinta ya kama zuciyarsa
A hankali ya ce
“Iman"
Da ƙyar ta ɗago kai
“Na’am Abba"
Ya yi shiru
“Na zo ne domin neman gafara"
“Ba zan ce ban yi kuskure ba"
“Na yi kuskure"
“Na gaza kare ki"
“Ki yafe min"
Tun kafin ya ƙarasa
Hawayen Iman suka gangaro
Ta buɗe baki za ta yi magana
Amma kukanta ya hana ta
Ta kasa furta ko kalma ɗaya
Abba ya fahimta
Bai ƙara matsa mata ba
Ya miƙe tsaye
“Ba zan tilasta miki komai ba yanzu"
“Zan sake dawowa"
Ya yi sallama
Ya juya ya fita
Da ya isa gida…
Kai tsaye ya shiga ɗakin Suhail.
Ya same shi zaune yana karatun Al-Qur’ani.
Ya ɗaga kai
“Abba…”
Abba ya zauna
Ya dubi Suhail
“Tambaya zan yi maka.”
“ina ji Abba"
“Suhail"
“Saki nawa ka yi wa Iman?”
Suhail ya yi shiru
Ya runtse idanunsa
Ya fara tuna ranar
Yadda ya faɗi
Yadda zuciyarsa ta tsaya
Yadda aka garzaya da shi asibiti
Can kuma
Ya buɗe idanunsa da sauri
“Abba!”
Abba ya haɗe gira.
“Me ya faru?”
Suhail ya dafe kansa
“Wallahi Abba…”
“Ban sake ta ba"
Abba ya yi mamaki.
“Yaya ba ka sake ta ba?”
Suhail ya ce
“Wallahi ban furta saki ba"
“Na faɗi ne kafin na iya cewa komai.”
A hankali ya ba Abba cikakken bayani
Tun daga ranar da Mami tace ya saki iman
Har zuwa lokacin da ya yanke jiki ya faɗi
Abba ya yi shiru
Ya fara tuna duk abin da aka ba shi labari
Daga ƙarshe ya ce
“Alhamdulillah"
“Ka shirya"
“Yanzu za mu koma gidan Malam"
Ba su ɓata lokaci ba
Suka kama hanyar gidan Malam.
Bayan sun zauna
Suhail ya ba Malam cikakken bayani
Malam ya tsaya cak
“Innalillahi…”
Ya dafe goshins
Bai ce komai ba
Sai ya miƙe
Kai tsaye ya nufi ɗakin Iman
Ya same ta tana zaune
“Khadija…”
Ta ɗago kai
“Na’am Malam.”
Ya zauna
Ya ce
“Suhail ya ce bai sake ki ba"
Iman ta girgiza kai da sauri.
“A’a Malam"
“Ya sake ni ai da bai sake ni bazan taho ba"
Malam ya tambaye ta cikin nutsuwa
“To"
“Saki nawa ya yi miki?”
Nan take Iman ta yi shiru
Ta fara tunani
Ta tuna komai
Sai ta kasa tuna kalmar saki daga bakinsa
Malam ya ce cikin taushi
“Khadija…”
“Ki faɗa min gaskiya"
“Ba wanda zai cutar da ke"
Hawaye suka cika idanunta
Cikin kuka ta ce
“Ni ma…”
“Bayan na yi tunani…”
“Na tuna bai furta saki ba"
“Shi ya sa"
“Ko da Yaya Mubarak ya kawo min maganar aure…”
“Na ƙi yarda"
“Saboda a raina…”
“Na san har yanzu ina ƙarƙashin aurensa"
Malam ya yi shiru
Ya jinjina kai
Lamarin ya fara bayyana masa
Iman ta share hawaye
“Wallahi Malam…”
“Na yi iya ƙoƙarina na kare aurena.”
“Ko da ban gaya wa kowa ba.”
Malam ya ce
“Ki ɗauko mayafinki"
“Mu je"
Bayan watanni masu yawa
A karo na farko
Iman da Suhail suka sake haɗuwa
Da Iman ta shigo falon…"
Suhail ya ɗaga kai
Idanunsu suka haɗu
Dukansu suka tsaya cak
Suhail ya rame ƙwarai
Fuskarsa ta nuna gajiyar rashin lafiya da damuwa
Iman ma ta rame
Idanunta sun yi zurfi
Na wasu daƙiƙu
Babu wanda ya iya magana
Sai kallon juna suke yi
Kallon da ya ƙunshi kewa
Kallon da ya ƙunshi nadama
Kallon da kalmomi ba za su iya fassarawa ba
Hawaye suka cika idanun Suhail."
Iman ma ta kasa riƙe nata."
Ta sunkuyar da kai
Malam ya karya shirun
“Iman ta tabbatar min cewa…”
“Suhail bai furta saki ba"
A daidai wannan lokacin…"
Ammi ta shigo falon."
Abba kuwa ya sauke wani irin numfashi
“Alhamdulillah"
Ya faɗa cikin farin ciki
Malam ya ci gaba cikin nutsuwa."
“To"
“Ga Iman nan"
“Ga Suhail nan"
“Tun da babu saki tsakaninsu"
“Idan Iman ta yarda… za ta koma gidan mijinta"
“Sai dai…”
Ya dubi Suhail.
“Idan kuma kai har yanzu ba ka son ci gaba da auren"
“To a nan gabanmu za ka bayyana matsayinka"
Falon ya sake yin tsit
Kowa ya mayar da hankalinsa kan Suhail
like
share and
comment