SILAR HALLACI

Page 7

by @jamilaumarjanafty

*SILAR  HALLACI*

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*

        *🅿️7*

"Alhaji Bashir wambai Haifaffan garin kano ne,a wata anguwa da ake kira Kofar wambai,Alhaji Bashir ya taso tun yana karami a matsayin maraya ta bangaren uwa dana Uba Shiyasa ya girma a hannun kanwar Babansa mai Suna Tabawa,Alhaji Bashir Kaf Danginsu basu gaji kudi ba arzikinsa ya tarasu ne ta hanyar Sana"a da kuma Tukuri wajen neman na kanshi.

Alhaji Bashir yayi karatun Addini dana zamani har zuwa matakin Digree,da Taimakon wani kanin Tabawa wanda yake da Dan Abun Hannunshi bayan ya kamallah karatunsa ne yayi Service yana gida ba aikin yi,Sai ya fara amfani da kudin Da yatara lokacin yana Bautar kasa ya fara Saro kaya irinsu gwanjona da Sauransu yana Saidawa a bakin Hanya acikin kasuwar wambai,cikin Ikon Allah sai Allah ya sakama Abun albarka Domin Alhaji Bashir irin Mutanenan ne masu baiwan Duk Abunda suka Taba sai yayi albarka.

Bai Rufe Shekara ba ya Samu Nasaran samu hayan Shago anan kasuwar wambai din,Alhaji Bashir yana da Kokari wajen neman na kansa baya Raina Riba komai kankantarsa Shiyasa Abokan kasuwancinsa Yayi musu Zarra,suna ganin Duka Duka yaushe ya fara sana"ar ammh gashi yana neman zama wani abu,yau da gobe bata bar komai ba Sai gashi Alhaji Bashir ya mallaki Shaguna har guda uku a kasuwar wambai na kayan gwanjuna,lokacin ne kuma Alhaji Lere wanda dama abokinsa ne da Suke makotankan Shaguna ya Bashi Shawaran ya kamata ya Fara Harkan saida Atmafofi da lesuna kamar bazai karbi Shawaran ba sai da yayi mgana da Tabawa ta karfafamai gwiwa Kana ya fara taba kasuwancinsa Sarin Lesunan Daga lagos ake Zuwarmai dasu kafin ya Rufe Shekara Tini shaguna uku sun samu matsugunni a kasuwar kwari na Alhaji Bashir Kasuwanci ya Budemai Sosai ba kama Hannun yaro Cikin Lokaci ya Fara Fitowa gari inda Allah ke Taimakonsa kyauta da kyautatama na kasa Dashi Zuwa Lokacin ya Dauki yara masu mataimaka mai wajen zaman Shaguna da Sauran Lissafi,Samun Budinshi yasa ya Koma makaranta ya Dora master dinshi dama Business Admistration ya karanta sai ya Dora kawai zuwa Lokacin ya mallaki motar hawa ya siya katon Fili a gadon kaya yana gini bayan ya Buge gidan Tabawa ya gyaramatashi da kayan alatun Rayuwa Domin komai ya zama Silan ta ne aduniya.

Haka Rayuwar tacigaba da Tafiya cikin Rufin Asirin Allah Alhaji Bashir bai Shekara Biyar ba Sunansa ya Riga ya gama Famtsama a garin kano In ka shiga kwari shagunan Alhaji Bashir wambai kadai kake gani Hakama Kasuwar wambai Zuwa Lokacin kuma ya mallaki manya manyan Store na Saida kayan abinci da Abun bukatar Rayuwa,yayi Aure da Matarsa Hajiya Rabi tun Shekara biyu da suka gabata bayan Rasuwar Tabawa wanda sai da kudi suka zo Ta bar gidan Duniya ta tafi da Burin zuwa Saudiya ganin Dakin Allah komai na Tafiyarta Alhaji Bashir ya gamashi lokaci kawai ake Jira sai kuma ita kuma ta Riski Lokaci Yayi kuka kamar Ranshi zai Fita yana Tunanin ya sake zama maraya Tunda ya rasa Tabawa...

Hajiya Rabi itama yar anguwar Kofar wambai ce Sunyi Soyayyah mai Zafi irin na Saurayi da Budurwa kafin Aurensu itama ta Fito Daga babban Gida ne mai Cike da Dangi kafin a Aurar dasu sai Mahaifinsu ya kaisu Makka sun sauke Farali Aurensu da Wata Tara Hajiya Rabi ta santalo yarta mace Taci sunan Tabawa wato Aliya bayan ita sai ta kara Haihuwan Najwa bayan Haihuwan Najwa ne Shida Hajiya Rabi suka kara Zuwa Saudiya suka Sauke farali Duk da Shi Zuwansa na Farko kenan,Daga Najwa sai Nabila sai Nazifa sai Adama Sai Auta Abida,duka matane Allah bai bata da Namiji ba Duk da Ko da Burin Alhaji Bashir na samun wanda zai gajeshi kan harkan kasuwancinsa da yanzu ya Bunkusa,ya riga ya zama Dila bayan manyan Shagunansa na cikin kasuwanni ya mallaki manyan plaza da kuma Babban Shopping mall wanda Jahar kano take ji dashi,Alhaji Bashir kowa ya sanshi Mutun ne na gari mai Dattako da Sanin ya kamata uwa uba kuma Mutum ne mai Hannun kyauta da Sanin Darajan iyalansa dana ya"yansa wanda suke ganin sunfi kowa sa"ar Nagartattacen Uba Duk da Sun kasance Mahaifinsu Dan kasuwa ne mai Tarin Dukiya bai sa su nuna Dagawa ba Dukkansu wata Private Sch sukayi mai suna Intercontinetal Collage sukayi Daga manyansu har yaransu Aliya da Najwa sai da suka gama Digree dinsu kana Sukayi Aure Najwa tana Auren wani Ma"aikacin Layin Etisalt ne a nan garin kano suna zauna Badarawa layout,Sai Aliya datake Auren mai bama gwannar Jahar kaduna Shawara akan Harkan Addinin Musulunci,tana kaduna ta zama sai Nazifa wacce tana level3 tayi aure a garin Abuja tana Auren ma"aikacin Gidan Talabijin na NTA,sai achan ta kare karatunta,Nazifa ce kadai ta tsaya iya matakin Secondry Saboda Mijinta Ustaz ne baya son Ta cigaba da karatu Alhaji bashir kuma yamara sa baya,tana Zaune a anguwar Buk Road a nan Jahar kano,Adama da Abida ne suke gida basu yi Aure ba Sune yara alokacin saboda Tsakanin Nazifa ma da Adama Shekara Hudu ne, ammh Tsakanin Adama da Abida basu da Tazara Sosai Shekara Biyu ne kachal,Suna karatu ne A jami"ar BUK Adama tana karantan Phamarcy ne ita kuma Abida Microbilogy ne.

Ya basu dukkan wani Jin Dadin Rayuwa mai inganci duk wacce zai ma Aure sai ya Siyamata motar Hawa na alfarma,fatan shi dai ki Zauna lafiya agidan Mijinki,Ganin Allah bai bashi da Namiji sai ya barma Allah komai ya Rumgume yaransa masu amanan ciki irinsu Nura Baban Iman,wanda suke tare tun  Lokacin  yana Saurayinsa Shiya yayimai Aure ya Siyamai gida da kuma Motar Hawa Shiyasa babu Abunda zai cema Alhaji Bashir Sai godiya haka kowa ke Fadi Domin ya goya marayu dadama Koda ka Cucesa baya Damuwa dakai sai dai yayi maka Fatan Shiriya,shiyasa yake ganin Cigaba kan Kasuwancinsa.

Alhaji Bashi wambai Da Alhaji Muhammed Argungu abokai ne Sosai saboda suna alaqan kasuwanci Sosai Alhaji muhammed yana Saran kaya Sosai wajen Shagunan Alhaji Bashir sai bayan wani Lokaci mai Tsawo sai su buga Lissafi su warware sun dade tare Har Zumunci mai karfi ya Shiga Tsakaninsu wannan Dalilin ne yasa mahaifin Samiha yamai Tayin Auren Samiha alokacin Alhaji Bashir Bashi da Ra"ayi ko Burin kara Aure ammh kuma Shi mutam ne wanda baya maida Alheri baya Shiyasa ya karba azahirin gaskiya bai taba Zaton in yaga Samiha zata Tafi da imaninsa Lokaci daya ba sai daya ganta gata dai yarinya karama Domin bazata wuce Sa"ar Nazifa ba ammh kuma yaji ya kuma yagani Duk da Boren da Samiha ta nuna bata Sonshi ammh bai dameshi Ba Hajiya Rabi tayi mamakin Mganar Auren Alhaji Bashir wanda yazo bakatatan babu Zato balle Tsammani,ba ita kadai ba Duka ya"yansa Sunyi mamaki suna ganin tun yana da Kananan Shekarunsa bai ce zai kara Aure ba sai da ya girma ya kamashi sun so su nuna Borensu da kuma Taya Ummansu Kishi ammh baiyi Tasiri ba Basu Tsinke da al"amarin ba sai da Samiha ta tare a katon Flat din dake kallon nasu Farkon Zuwan Samiha gidan bata saki Jiki ba Kullum tana cikin kuka Duk da ko kayan alatun rayuwar da Alhaji Bashir ya kawata mata bangarenta dashi, dana iyayenta ta sani kaf cikin Gidansu ko babar yarsu Hajiya Uwani data ke Auren Grand gadi na Jahar katsina gabadaya bata kaita samun Jin Dadi da ba Domin Alhaji Bashir yayi alkawarin bata Duniya da Abunda ke Cikinta indai zata kwantar da Hankalinta Tashi Daya ya Siyamata Tsaleliyar mota Kirar Toyota Benz, da katuwar waya na yayi yakuma cikamata account din daya Bude mata da kudi duk don ta kwantar da Hankalinta ya Daukanmata yan aiki wadanda ke gyara mata Shashenta da girki da abunda ba"a rasa ba bata aikin Fari ballatana na baki sai kwanciya,kafin Lokaci kalilan Samiha ta chanza ta zama wata mace kamar Tawarda Saboda Hutu da Jin Dadi da taimakon mahaifiyarta Hajiya mairo tafara sakin Ranta da kuma Tarin Dukiya da gatan da Alhaji Bashir ke Nuna mata uwa uba bai matsa mata ba Tun Da farko daya nemi hakkinsa ta dinga mai kuka da Ihu bai kara Nema ba ganin haka sai ta maida kai kawai tafara zuba mulkinta Sonta Ranta ganin yadda Alhaji Bashir ke mutuwar Sonta,Hajiya Rabi ta raina kanta Sanda Tafara tozali da Samiha Sa"ar Nazifa ammh Alhaji Bashir ya zama kamar wani Rakumi da akala saboda ya Auri yarinya Samiha sau daya tataba Shigowa Bangarenta Shima Dakyar Alhaji Bashir din ya lallasheta ta Shigo haka Ta dinga musu wannan yamutsan tana wani tabe baki Ran su su Abida ya baci dama Tafi Adama zafin Rai,Tun Auren Samiha Alhaji Bashir ya zama Fadaci ko wajen kasuwansa kowa ya Daina gane kansa abu kadan zaka yi yayi ta maka fada wanda a baya ba Haka yake ba Samiha ta zama yar gold awajensa Ririta yake kamar kwai ita kuma tana ta amfani da wannan damar tana Tsula tsiyarta Son Ranta gefe daya kuma bata manta da Ahmed ba, kullum kwanan Duniya sai tayi kukan Rashin Ahmed arayuwarta ammh acikin Ranta batajin ta Rabu da Ahmed kenan tanaji ajikinta zasu kara Haduwa komai Daran Dadewa.

Alhaji Bashir yana gina wani Gida a anguwan Ahmadu bello way mai kyau da Tsari da Sunan Hajiya Rabi ita ta zabi Yanayin Tsarin gidan datakeso ammh Rana tsaka Samiha tace Tana Bukatar gidan in angama ginin tana so ta koma chan,Saboda bazata iya zama acikin Gidansa da matarsa da ya"yansa mara kunya ba basa gaisheta ga Rashin kunyar da Suke mata Dalilin haka Sai da Abida suka gane Kuransu domin kaca kaca yayi musu Daga karshema ya Hada da Hajiya Rabin Ita ce ke daure musu gindi,hakuri tayi ta bashi bai Hakura sai da suka taka sukaje sukabata Hakura Dakyar ta Hakura tana wani Kallonsu adage,Bata koma gidan ba sai da suka dawo daga Saudiya Samiha ta karo Wulakanci Sosai,ba wanda yasan ta koma gidan Domin Taga Filin Jirgi direct chan Suka wuce sai Daga bayane yake gayama Hajiya wanda Saboda Takaichi sai da tayi kwallar Takaichi,nan Alhaji Bashir ya Shiga Fadan Wai da girmanta tana kishi da karamae yarinya yana ce gidan nan da Kudinsa ya gina da Farko yace natane kuma yanzu Samiha tagani tana so ya bata sai tayi Hakuri ta zabi wani Cikin Gidajenshi ta Dauka Saboda Takaichi tace bata Bukata bai damu ba yace ta Rasa,gabadaya abubuwa sun Dakule sun daina Tafiya Daidai dama Alhaji Lere ne kebama Alhaji Bashir wasu Shawaran Shima yaja baya Dashi Dole kowa ya kawo ido ya sakamai masu gadi da Direbobin da Alhaji ya kora basu da adadi saboda Samiha kuskure kadan zakayi ta saka a koreka kuma ka Kore kenan,Hatta da Wajen kasuwancinsa ya kore yaransa da yawa Wanda kawai basu mai komai Samiha ce zata bashi Shawaran ya kamata ya chanza su Barin ma in ya Dawo yana Fadan sun mai wani Shirme kafin Samiha ta Rufe Shekara Biyar tare da Alhaji kowa yasan girma da matsayin yar gold awajensa In tana mgana baya iya Musa mata yadda yake Ririta ko Kwai sai haka,Zuwa Lokacin daga Hajiya Rabi har ya"yanta Sun Fara gajiya da wannan al"amarin na gidama bai kyale ba ballatana na gidan Aure nan Najwa Saboda Sun Hadu da samiha wajen wani biki bata gaisheta ba,Tana dawowa gida ta gayama Alhaji Bashir shi kuma yamata Takkakiya gaban mijinta da ya"yanta yaci mata Mutumci yana Fadin yadda zata daraja Hajiya Rabi haka zata Daraja Samiha Mijinta ne ma ke bashi Hakuri itako Najwa sai kuka ba baki,bayan ya Tafi ne ta kira Hajiya Rabi tana kuka tana gayamata Jin haka yasa Abida da Adama daga makaranta sukama Samiha takakkiya har gida suka Cima mata mutumci suka gayama Juna mganganu Suna Tafiya ta kira Alhaji Bashir tana kuka tana gayamai Kuma tace bata son kara zama a garin kano ya Siyamata wani gida agarin gombe,bai mata musu ba ya saka a Bincikamai wani dan Madaidaicin gida anan gombe Su kuma su Abida ya Dirarmusu Ya ci musu Zarafi Sosai kuma ya Hada da Hajiya Rabin Domin yace ita ke Zugasu wannan Dalilin Shine yasa Samiha ta koma garin Gombe da zama ammh Duk lokacin dataga dama zata zo Kano tayi Hutunta tana Zuwa Jega Lokacin bayan Lokaci Duba iyayenta,Maimu ta yi Aure a Birnin kebbi harda ya"ya Biyu kuma sai da ta kamallah karatunta,ammh Samiha bata taba bari Alhaji Bashir ya Kusance ba Domin barazana ta tabamai Tun Farkon Aurensu tace in yace zai kusanceta zata kashe kanta ya Dauka wasa ne ya Taba nemanta ta karfi aiko ta Farke hannunta da Wuka sai da ta kwanta a asibiti aka mata Dinki Tunda ga Lokacin ya Cire Tunanin kusantar samiha acikin Ransa,burinsa daya Ta zauna Dashi Saboda yana Sonta bawai Domin Samiha tayi ma Alhaji Bashir wani abu ba A"a sai domin kamar ta zame mai matar Kaddarace 

Duk iya Kokarin Samiha na samun Labarin Ahmed Abun ya gagareta,lokacin dataji Labarin Sun saida gidansu sun bar garin Jega sai da Samiha ta kwana Uku tana kuka Alhaji bashir duk ya Susuce yakasa gane kanta bata da wanda zata tambaya balle Taji ina suka koma Dole ta saka ma Ranta Hakuri ta cigaba da Famtamawarta Cikin Rayuwarta da Alhaji Bashir ta shiga ta Fita ta saka mai kyau taci kuma mai kyau,bata da damuwar komai sai na Kewar Ahmed da Kuma Soyayyarsa dake cin Ranta.

Bayan komawar Samiha Gombe ne Aka kawoma Alhaji Bashir Ahmed ya karbesa hannun Bibbiyu ya kuma Dorashi kan Harkan kasuwancinsa,Alhaji Bashir ya yarda da Ahmed Sosai Saboda yadda yake Daukansa Tamkar mahaifinsa Abba yake Kiransa Shiyaasa Lokaci kadan Ahmed ya samu Matsugunnin da ko su Baban Iman manaja basu samu ba,yanuna sa ga iyalansa Shima Ahmed din kaka ba inda bata sani ba a gidan Alhaji Bashir,yana Daukansa kamar Dan daya haifa acikin cikinsa,Haka Shima Ahmed domin yana ganin Alhaji Bashir ya gama mai dukka gata Shiyasa baya wasa wajen kula da kasuwancinsa Cikin Shekaru uku Riban kasuwancin Alhaji Bashir ya ninka Sau biyar din dayake samu aduk Shekara ba kuma Dalilin kowa bane sai Dalilin Ahmed wanda ko Sauran yaran Suna Jinjina ma baiwarsa,wannan Farincikin ne yasa Alhaji Bashir wambai ya Biya Ahmed da kawu maude da Kaka Sukaje suka Sauke Farali bayan ya Dawo ne kuma Alhaji bashir ya bashi Ragamar kula da komai nashi already dama Lokacin Ahmed ya gama karatunsa har Ya kamallah Bautar kasa,sai  Alhaji ya Shafe wata bai leko kasuwa ba sai dai duk Abunda ake Bukata asamu Ahmed Shi ke kula da komai in ma wani abu ne sai dai Ahmed din yazo gida ya samu Abban su Tattauna akwai Shakuwa da amana mai girma a tsakaninsu,Ahmed yasha Zuwa gidan Abba na Ahmadu bello waya in Samiha tazo Hutu basu Taba Haduwa ba,duk da yasan Abba nada amarya ammh bai damu ya santa ba,itama samihan tana jin Sunan Ahmed a bakin Alhaji ammh bata damu dashi ba tadai san cewa kowaye Ahmed din Alhaji ya yarda dashi Sosai, Gidan Umma dai Wato Hajiya Rabi nan ne kamar Gida a wajen Ahmed Tsakaninsa kuwa da su Abida suna da kyakyawan Alaqa,Abida ta fara son Ahmed Tun kafin Alhaji Bashir ya bayyana mata shi a matsayin wanda ya zaba mata,lokacin har ta fara aiki a Lab din mallam Aminu kano Adama kuma sai bayan Auren Ahmed Da Abida kana tayi Aure a Bauchi.

Ahmed yaji kamar yayi kwallah Lokacin da Abba ya Kirashi yana gayamai ga Abida nan ya bashi yazo su daidaita da juna,haka yayi ta mai godiya shiko kansa ya Dafa yana gayamai Shi Babansa Saboda haka ya Daina godemai bayan ya koma gida yayi kuka Sosai na Farincikin dana Bakinciki dana kewa da Kuma Tunanin Samiha ammah adaran ya Kulle Zuciyarsa daga Tunanin Samiha ya maida hakan a matsayin wani Hani ga Allah baiwa ce,Abida bata sha Wahala wajen jawo hankali Ahmed zuwa gareta ba Domin yayi alkawarin bazai watsama Abba kasa a ido ba,kawu Maude da kaka har gida suka zo Godiya Hajiya Rabi kuwa tafi kowa murna Domin Ahmed kowa yasan Mutum ne,Abba shi ya siyama Ahmed gidan da Suke ciki Motar Hawa ce kadai ya Cika ya Siya wata da kansa Aurensu ba Dadewa ya Fita da kaka india saboda matsalan ido inda aka mata aiki aka kuma yankamata glass suna chan suka samu labarin Rasuwar Alhaji lere basu je gaisuwa ba sai da suka Dawo Shida da Abida,bayan dawowarsu ne kuma ya Budema kawu maude Shago anan kasuwar Kwari babban Shago ya Zubamai yara Saboda shima an kwana Biyu suna tayasa gudanar da komai,Samun cikin Abida mai laulayi yasaka Ahmed ya Soke Zuwanta aiki kuma dole ta Hakura mafarin daya sa ya Dauko kaka kenan ta dawo gidansa da zama Saboda Abida Bata son yar aiki ba yarda baiyi ta bari yama Umma mgana ko za"a samo mata wacce zata tayata wasu ayyukan ammh Abida taki Dayake mace ce mai Tsananin Kishi ga Mijinta kaka kadai ta yarda da Zauna da ita koda kaka ta Tsufa bawai ta Daina Halinta bane bata Daina ba, kullum sai tayi fada da Ahmed watarana ma harda Abidan take Hadawa tama Tatas,in Tagaji ne take Hakura,ammh mganar Jin Dadin Rayuwa kan ba Abunda kaka zatace da Ahmed sai sam barka Domin ko Sama"ila da bafashi na Raye iyakar Abunda zasuyi mata kenan.

Wannan kenan.

*****

Ajiyar Zuciya ya Sauke bayan ya Dawo daga Dogon Nazarin mafarin komai,kwanciya ya gyara Cikin kasala Lokaci daya yana kai Duba Zuwa agogon Bangon Dake bedroom din ido ya Zaro ganin 3:30pm har tayi ammh yana kwance ba Sallah ba salati balle mganar cin Abinci,mikewa yayi da Hanzari wayarsa ya Dauka nan yaga Tarin Missed clls bai tsaya Dubawa ba ya Wuce Tiolet yana Cire Links din Rigar Shaddan Dake Jikinsa Ruwa yafara,kamawa kafin ya Dauro alwala ya Fito darduma ya Shifidama ya Tada sallah ya idar da Azahar kenan ana Kiran sallar La"asar batare da bata Lokaci ba ya mike ya gabatar da Sallar La"asar ya Dade zaune yana Addu"an Allah ka karesa daga Sharrin Samiha domin kwata kwata sake Haduwarsu a karo na Biyu bai wani kwantamai acikin Ransa ba.

Cikin kasala ya Mike ya Fice Daga Bedroom din Kichen ya Fara Dubawa baiga Abida ba ya koma Bedroom dinta nan ma bata ciki mganarta yaji Daga Dakin kaka kai Tsaye ya nufi chan da sallama ya Shiga kaka na Zaune a kasa Abida na gefenta tana matsamata kafan sun dan Tashi Lokaci daya tana Shafa mata man Zafi, daga ganin yadda Abida ke dariya zaka Fahimci Wani Tsegumin Kaka ke yi Fadi ba"a Tambayeka ba.

Kaka ce kadai ta amsa Sallaman Ahmed Ammh Abida dauke kanta tayi gefe lokaci daya tana Hade Ranta,Karisowa yayi Tsakiyar Dakin ya zauna daga gefen kaka su ka sata atsakiyar kenan,wanda gabadaya idanuwansa na kan Abida ne yana nacin kallonta ita kuwa taki yarda su hada ido..

Kaka ce ta kalli Ahmed tana Fadin"Wai kai Ahmadu me aka maka ne ka dawomana gida kana Kumbure kumbure..?ko wani ne ya maka Bugun Tsiya chan wajen aiki yau yasan cewa kai jikan Bara"atu ne jikar Audi bassakwace ne.."Tafada tana gyara zaman gilashin Idonta Fuska ba Walwala yace"Duka kuma kaka.?kamar wani yaro..Bakomai.."Kallonsa kaka tayi kafin"Ji wata mganar Banza Toh Allah Na tuba Ahmadu ai baka Wuce duka ba Wlh tallahi ko ni nayi Niyya tsab zan saka ka daki na baka kashi sai ka ma kasa Tashi kana wata mgana chan Dabam.."Yar dariya ya saki yana Fadin"Lalle Kaka wuyanki ya isa yanka.."Keyarsa ta maka tana Fadin"In Sama"ila nada Rai ai Bazaka cemai Wuyansa ya isa yanka ba ko..? 

Baki ya Tabe yana Kallon Abida yace"Wai ni kaka mai Sunan Babanki ne..?Kaka ta zata abun kwarai ne tace"Allah Sarki..Allah jikan Hudu Dufadufa.."Dariya ta kama Ahmed da Abida Wanda tayi Saurin kaneewa shiko Kansa ya Shafa yana Fadin"Toh kinsan Allah in har sunan Ubana bai bar Bakinki ba haka zan dinga kiran sunan naki.."Baki ta Rike tana Fadin"Na Shiga uku karshen zamani ni Bara"atu yanzu Ahmadu Saboda lalacewa agaban Idona kake cewa zaka dinga kiran sunan Mahaifina wanda ke kasa Turbuya ta Rufemai ido. '

Kai tsaye yace"Ni nawa Uban kila ke kika Rufamai idon ai ba Turbayan ba.."Banza Dashi tayi bata kara mgana ba ta dai kume tana ta hararansa Daure Fuska yayi yana kallon Abida kafin yace"Madam ina jin yunwa a taimaka abani abinci ba domin Halina ba.."yafada yana sakarmata manyan idanuwansa,Tsuramai ido tayi Suka kura ma juna ido suna kallon Juna Cikin Fitan Hayyaci kaka ce Datagaji da kallonsu ta Saki katon Tsaki tana Fadin"yau naga katon lalacewa ni Bara"atu,ke yanzu Banda kina sakarya yagama Wulakantaki dazu ammh yanzu yazo yana wani kafeki da ido kamar maye kema kin wani biye tatashi kina wani kallonsa kamar wasu Tamtabarun Soyayyah.."Ahmed ne ya Lumshe ido kafin ya Bude yana kallon Kaka lokaci daya ya mike yana Fadin"Toh ina Ruwanki Kuma..yaushe na mata Wulakanci Allah kaka in kina Shiga Harkan miji da mata watarana idonki zai makance.."kyafi taci kafin tace"Toh yanzuma mai yayi Saura Ahmadu...Ai Wlh Ranar Lahira akwai zama agaban Allah dani dakai.."Kallon Abida yayi yana marairaicemata bai bi takan kaka dake sababi ita kadai ba Janye kafarta Kaka tayi tana Fadin"Ke tashi kibishi ku Fitar min daga daki..Wannan Jarababben yaro ne bashi da ta ido ni ko kunyata bayaji yana wani Maida ido kasa kamar Mage taso gulma bishi ku tafi nagode.."Abida na Dariya ta mike tayi Gaba Ahmed ya marata baya da Sauri kaka ta rakashi da ido tana Fadin"Dama iskanci ne ba abunda aka mai mu yadawo gida yana mana cika da batsewa domin ya Rainamu..Koda yake Abidar ya Raina don yaga tana sakarmai da irinmu ya samu Zamaninmu a da ai irinsu Ahmadu ba"a musu da wasa...







*Aisha alto...*
*Janafty*