SILAR HALLACI

Page 8

by @jamilaumarjanafty

*SILAR  HALLACI.*

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.


        *🅿️8*

"Suna Fita ta nufi Hanyar Kichen Cikin Takun ta na Takama Jinsa yana Biye abayanta yasa take wani Taku tamkar wata Wahainiya,Shi kuma yana Biye da ita yana kallonta cikin wani Shauki da Soyayyah sai da suka Shiga Kichen din kana ya Coge daga Bakin Kofar kichen din yana Kallonta,Tasha mur tana ta Faman Hada mai abinci Bisa wani katon Faranti.

Mirmishi ya saki kafin ya karisa Gareta Sai ji kawai tayi ya Rumgumota ta baya Lokaci daya yana Sakarmata Kiss agefen Wuyanta,Ajiyar Zuciya ta Sauke Tana Doramai Kofuna Bisa Farantin bayan ta jeramai Kololin Abincin da kuma Filet da Cokali,Cikin Muryan Shagwaba ya Fara cewa"Nace ayi hakuri ko..? Ko baza"a hakura bane sai angama Horani.."?

Kwace Jikinta tayi ta waigo tana makamai Harara baki ya kama yana Fadin"Mijin kuma yau ake Harara..Babban Mgana.."yafada yana yar Dariya Duka ta d'agamai a Gefen Cinya tana Fadin"Ba cewa kayi na Fita na baka waje kana Bukatar kadaichi ba..? Ko ba Haka kace ba..?tafada tana Zaro mai ido Lokaci daya tana karamai kai mai Duka baya yaja yana Dariya Lokaci daya yana kara Rikota ya Cukwikwiyeta yana Fadin"Afuwa....Bazan kara ba Kinji Abidan Ahmadun kaka.."Dariya ta kwace mata ganin yadda yawani Narkemata kansa ta Dungura tana Fadin"Be carefully.."Tafada a Shagwabe da Sauri yace"I carefully Madam.."Dariya suka Sheke Dashi kafin ta Dauki Tiren Abinci shi kuma ya Bita abaya har Zuwa Cikin Bedroom dinsu,Abincin ma Itake bashi abaki yana Zubamata Shagwaba tana Biyemai Duk domin yaga Abida ta saki Ranta ammh acikin Ransa fargaba damuwa da kuma Tunanin me Haduwarsu da Samiha akaro na Biyu yake Nufi,har zuwa Dare Ahmed bai kara bari Abida takara Fahimtar yana cikin Damuwa ba,Yayi kokarin Boye Fargabansa bai sake Fita ba sai Washegari ta waya kawai yayi ta bada Umarni Sai Baban Iman dayazo gida ya sameshi suka karishe Mgana Duk da Shima yaso yamasa Tambaya kan Samiha ammh ganin bai bashi Fuska bane yasa ya kyaleshi 

Shima Ahmed din yaso yayi ma Baban Iman Zencen ammh sai wata Zuciya ta kwabeshi,Domin dai bashi da wani abokin Shawara Tun Tasowarshi daga Kaka sai Kawu maude sai kuma Bayan Aurensa Abida toh ammh yanzu inma zaije musu da mgana yace musu mene..? Yaga samiha amatsayin Amaryan Abba..Ganin baida mafita ne yaso yama Nura manaja mgana ammh kuma sai ya Fasa Duk da dashi ne kadai yake good Time Sosai bayan Alaqan kasuwanci,Tunani yayi Ba amfanin gayama wani gwara yayi addu"an Allah sa haduwarsu ta Zamo alheri ba Sharrinta ba kamar yadda yake Tunani ba.

Ganin har Washegari yaje Office ba wata mgana yasa ya saki Ranshi kuma Sunyi waya da Abba kan kaya da zasu zo Daga Lagos,shiyasa bai kara saka Damuwa ba duk da kasan Ranshi yana Cike da Fargaba idanuwansa Samiha na yanzu Sunfi haka wayewa da Girma da Tasawa kalamanta Suna kokarin Sakashi Fargaba,tattara komai yayi watsar ya Cigaba da Harkan Gabansa...

*****
Tunda ta koma gida ta Kule kanta Cikin Bedroom dinta tana Gunjin kuka mai Cinrai kukan Soyayyah da kauna ta gaskiya wacce Ta  Ahmed Tun tana Cikin Kuruciya,Tayi kuka kamar Ranta zai Fita Daganan sai kanta ya Fara sara mata ta Dauki paracetamol tasha ta koma ta kwanta Har Abba ya Shigo tana kwance tana Barci yayi mamakin ganin yanayin kwanciyarta kamar ba cikin Son Ranta  barcin ya kwasheta ba,gyaramata kwanciya yayi ya Fita Zuwa Falo itakuwa sai bayan La"asar tatashi,Sai da tayi Sallar Azahar kana ta Hada da La"asar,Tunda tatashi ya kasa gane kanta Domin yayi mganan Duniyanan tayi mai banza Sai yayi Tunanin ko Ahmed din ne bai Bata Hakuri ba ya Daga waya zai Kirashi ta Dagamai Hannu tana Fadin"Karka kira kowa a kaina plz...Kaina ne ke Ciwo bana son Hayaniya.."Jin haka yasa Ya Fice ya barta bayan ya gama magiyan tazo suje asibiti tamai banza karshenta ma baya ta juyamai yana Fita taje ta kulle Kofar Bedroom dinta ta Cigaba da kuka Ranar kwana tayi batasama Cikinta komai ba,gashi dama Tana da Ulcer da gari ya waye Taji yunwa ta Fita Zuwa Falo ta kwalama yar aikinta kira tace ta Hadomata Tea,ta hadomata ta kawo mata Kurba Daya Biyu uku ta Shiga Kelaya amai,gashi Abba bashi gidanta gidan Hajiya Rabi yake yan aikin natane Suka Taimakamata ta mike ta koma Dakinta Su kuma Suka Tsabtace wajen,Toilet ta Fada tayi wanka ko Abban bata Kiraba ta Shirya ta Fito Direba yajata zuwa Wani private Hopital Mai suna primiere Hopl,suna zuwa aka bata gado aka Sanyamata Drip da alluran barci saboda ta Galabaita Sai da Ruwan ya kare ne,bayan tatashi ta nemi wayarta ta kira Abba ta Sanar Dashi iya Rudewa ya Rude haka ya bazamo zuwa Asibitin Hankalinsa tashe yana faman Jera mata sannu ita batashi take ba Tunanin yadda zata neman ma kanta mafita kawai take da yarda zata mallaki Mafarkinta.

Kwana Daya tayi a asibitin kafin ta koma Gida,ita ta matsama abata sallama ta koma Gida batason zaman Asibiti,tayi ta amsa wayoyin yan gidansu Kila Abba ne ya Kira Abbanta ya gayamai Shikuma yagayama Hajiya mairo labarin ya Fita ammh Daga bangaren Hajiya Rabi da ya"yanta Nabila ce kadai ta Kirata ta mata ya Jiki ammh Sauran ko Sannu bata damu ba Ko abayama kananan kwari take Daukansu balle yanzu da Ahmed yasha gaban komai atare da ita.

Ahmed yaji Labarin Rashin lafiyan Samiha a bakin Abba,Ranar ma da zata koma Gida suna tare a babban Shagon Alhaji na kasuwar Wambai Suna Duba Dilan da aka Sauke sai ga wayarta an sallameta zata koma Gida kuma Abba bai zo da Direba,dama Agidan Umma Ahmed yaje ya Daukosa suka Taho kasuwar nan da Abba yace Ahmed yazo ya kaishi Asibitin Ransa bai so ba ya Daukesa suka Tafi Asibitin inda Allah ya Taimakeshi suna Zuwa sai ga Direban Samihan ya iso dauke da Daya daga cikin yan aikinta wannan Dalilin yasa Abba yace Ahmed ya koma kasuwa Direba zai kwashesu Zuwa gida ai Ahmed ko sallama bai ma Abba ya Fiki mota ya Fice da Sauri Yana Sakin Numfashi Duk da Tsakaninsa da Samiha Allah ne kadai ya sani Samiha itace Mace ta Farko dayafara so ya Shaku da ita tun ko yana da kananun Shekaru Tsawon Shekara goma bazai ce ya manta da Ita ba..Ammh Lokaci bayan Lokacin yakan mata Fatan alheri Domin yasan Har Abada samiha tamai Nisa,ammh sai gashi sun sake ahaduwa awaje daya wanda Ahmed baya kaunar ya sake ma ganin Samiha balle su hada ido addu"a kadai yakeyi Allah yasa ta koma Gombe Cikin Satinan Hankalinsa zai fi kwaciya.

Itako Samiha suna Motane zasu koma Abba ke Shaidamata Ahmed ne ya kawosa da shi zai kai su ma gida sai ga Direbanta Wani bakinciki ya kama Samiha sai da taji kwalla wato yanzu Ahmed baya sonta ya Tsaneta Har yaji bata da lafiya kuma yasan Dalilin mikin Sonshi ne ammh ya kasa Shigowa yayi mata sannu da Jiki,saboda yana Auren Abida,Lalle nema yayi Kuskure Domin in wachan karon an Fi karfinta wannan karon zata iya karawa da koma waye akan Ahmed ta lashi Takobin sai ya Zama nata ko ta Halin kaka ne, bata ta Abba ma Domin Tanaganin iya Hallaci tayimai Tunda ta Zauna Dashi Shekara goma yana Ragemata Kuruciya,Saboda haka gwara ta nemanma kanta mafita domin tafi kowa Bukatar Ahmed awannan lokacin.

*****
Bayan kwana biyu.

Karfe shidda da wani abu na yammah yake Barin Office dinsa yana Tattara kayansa Abba yamai waya kan yazo gida ya Sameshi bai kawo Tunanin Abba na State road ba ya amsa mai da Toh Wayarsa ya Dauka sai System dinsa Domin akwai Sakonnin da zai Duba in yaje gida Masinjansa ya bari ya Rufe wajen Shi kuma ya gangara Office din Accounter sukayi Mgana Shima yana Shirin Tashi ne tare ma suka Sakko,bai Fita Daga Cikin Mall din ba sai da ya Leka shashen kayayyakin sakawa kamar su lace,shadda,atamfa,material,domin ganin yadda komai ke Tafiya bai Dade ba yayi musu sallama ya Fito ya Shiga motarsa,ya Fice Daga wajen ya Dauki hanyar Gidan Umma gadon kaya Abba ya sake Kiranshi yace yana ina ne? yace gashi gabda da gadon kaya Sai Abba yace"A"a yana State Road.."Ahmed yaji Bugawan Gaba kamar yaji wani sako mara Dadi Jikinsa ba kwari ya juya kan Mota zuwa Titin da zai Sadashi da State Road yana tafe yana Tunanin wani Abu.

Hon ya Zuba a kofar Tamgamemen Get din Megadi ya Wangalemai get ya Sulala ciki Zuwa parking space sai da ya Faka Motar ya Fito kana ya Daga waya ya Kira Abida ya gayamata bazai iso gida yanzu ba yazo State road Abba ya Kirasa tace ba Damuwa sama sama suka Taba Hira kafin suyi sallama,Wayar Abba ya Kira shi kuma Daidai lokacin Daya Fito daga Bedroom Dinshi yana gyara zaman Hulan kansa Samiha na Zaune Afalo tana Chart Abaya bata Damu da Duka Harkokin Abba ba, ammh yanzu idonta na kanshi,yanzu ma Dagowa tayi tana Fadin"Alhaji ina zaka ana gabda Kiran mangariba kuma..?

Shikuwa Cikin Sauri yace"Ba mafita zanyi ba Gimbiyar mata nan Falon baki ne Ahmed yazo zamuyi Mgana dashi.."Cike da mamaki Hade da jin Dadin zata ga Sanyin Idanuwanta tace"Ahmed..? Cikin sanyi da Rauni Shiko bai damu ba sai ma kara cewa Dayayi "Eh Ahmed dai da kikejin Labari mijin Abida.."yafada yana Kokarin Amsa Kiran Ahmed din daya Shigomai Saurin Sakin Mirmishi tayi kafin tace"Aoh...naganeshi..Gaskiya Alhaji dakace ya Shigo ciki ne ai Ahmed Dan gidane bai kamata yana Tsayawa awaje ba Suruki guda.."Bai Daga kiran ba ya Dakata yana kallonta Cikin mamaki da Murna yace"Ko gimbiyata..? Ido kawai ta kadamai ya saki Dariya yana Fadin"Hakane kuma Domin Ahmed ba Surukina na bane ina masa Kallon Tamkar D'an dana Haifa da Cikina ne..Bari nace kawai yashigo Ciki.."Kai ta kada tana Mikewa Lokaci daya tace"Ok..Bari na Shiga ciki in ya Shigo sai nazo dai yau mugaisa Suruki guda Bantaba ganinsa ba kada mu Hadu watarana bamu gane Juna ba.."Yana Dariyan Jin Dadi yace"yakamata..Kenan Ranar da kike je Mall baku hadu dashi ba.."?

Tana wani yamutsa Fuska tace"Eh ban bari ya Fitoba Raina yagama baci nace Direba ya Dawo dani gida.."Bata bashi Zarafin Mgana ba ta Haura sama Inda Bedroom dinsu yake Shi kuma Cike da Murna ya Kira Ahmed yace kai Tsaye ya Shigo Cikin Gida,lokacin Da Abba ya gayamai Haka Tuni Zuciyarsa ta kara Tsinkewa ammh Ya nuna alamun Mazan Duniya ya Dake kawai ya tura wayarsa Cikin Aljihun Blue din yadin Dake Jikinsa ya Tunkarin Babban Kofar Falon da zata sadashi da ainihin Cikin Gida gefe daya kuma yana maimaita kalmar Hasbunallahu wani"imal wakil.."

Yana Shiga yaci karo da Daya daga Cikin ma"aikatan gidan bayan ta gaisheshi tamai jagora zuwa Falon ta gefen ido yake karema Gidan kallo aransa yana Tunanin wani so Abba kema Samiha da zai kera mata gida mai kyau kuma ya cika mata su da alatun rayuwa haka bai tsinke da lamarin ba sai da suka Shigo Falon,Wasu manyan Rolay Chairs ne masu kyau da Tsari Seti uku suka ma Falon kwanya batare da wasu sun matsu wasu ba ,Ahmed ya saki baki galala kawai yana bin Ko"ina da kallo har Zuwa upstair shi kanshi Abun kallo Tsakani ga Allah wannan Gidan yataka na Umma haduwa yana nan Tsaye yana Faman kalle kalle sai ga Abba ya Dawo Falon,Da Sauri Ahmed ya Duka yana Fadin"Barka da Fitowa Abba mun Wuni lafiya..?..

Abba ya Karisa garesa ya Saka hannu ya Dagosa yana Fadin"Wai bana Hanaka wannan Rankwafawan ba..Nifa babanka ne Ahmed yakamata ka gane wannan."Kansa ya Sadda kasa yana Fadin"Nadade da sanin na wuce matsayin Suruki awajenka Abba matsayin da nake ammh bana iya gaisheka daga Tsaye kana Tsaye kabarni na Cigaba da Girmama Nargattacen Uba.."Abba ya saki mirmishi kawai Domin Harga Allah Ahmed mutum ne mai ladabi da Biyayyah da sanin ya kamata jawosa yayi ya zaunar Dashi kan kujera yana zama gefensa da Sauri Ahmed ya zame kasa yana Sunkuyar dakai Kallonsa kawai Abba yayi bai baata bakinsa wajen mai mganan ya Dawo kan Kujera ba Domin bazai Dawo ba Masu aikin Samiha ne suka Cika gabanshi da kayan Sanyi Sannu da aiki kadai yayi musu ya kauda kai Domin Hakikanin gaskiya Zuciyarsa tana Rawa ya matsu Abba ya sallameshi ya kara Gaba.

Zama Abba ya gyara yana Fadin"Sha ruwa mana Ahmed..Ka taso daga aiki ga gajiya yakamata ka taba wani Abun.."Baiyi gardama ya Tsiyaya Ruwa cikin Kofi yasha Abba ya kallesa yana Fadin"Kaga yau nace mu Shigo Cikin gida ko..? Kan Ahmed na kasa ya Gyada kai Abba ya cigaba da Fadin"Antynka ce tace ace ka Shigo ciki kawai kana Dan gida bai dace kana Tsayawa iya Falon baki kaji mace mai Hikima ni banta tunanin haka ba.."Ahmed yaji Zuciyarsa ta Daka Tsalle ta Dawo waje Daya Cikin Ransa yace Allah Raba nagari da mugu kawai.

Abba na kallonsa yace"Tama ce yakamata tazo ku gaisa kada ayu abun Kunya Suruki da Suruka su hadu awani waje basusan juna ba.."Gaban Ahmed ya sake Bugawan yayi Zuru kansa na kasa Yana jin Zaren Mgana Cikin dinkewan baki ya Furta."Allah sarki.."Daga haka ya kasa cewa komai Shiko Abba fadi yake"Ashe kuma Ranar baku hadu ba..? Kai Ahmed ya Dago yana kallon Abba cikin karfin Hali ya gyadamai kai bai bashi Zarafin Mgana ba yacigaba da Fadin"Tace kafin ka Fito tasa Direba ya maidota gida..Kasan ita haka take tana da Saurin Fushi wanda bai zauna da ita sai yamata wani Fahimtar kaima nasan zaka ji Dadin Gaisawarku da Ita.."yake kawai Ahmed kema Abba ba bakin Mgana,Zuciyarsa Gabadaya rawa take yana Tunanin Wani Abu samiha ta Shirya game da Shigowarsa Falon Aurenta,yana wannan Tunanin Abba yace ya tashi su Tafi masallaci in sun Dawo sai su Fara tattauna mganar da yayi Kiransa akai,ba haka Ahmed yaso ba yaso ne sugama komai da Abba yana Fita kafin ya Isa Gida ya biya masallacin anguwansu yayi sallar Mangariba da Isha"i in ya koma gida yayi Shafa"i da Wuturi,ammh Abba duk yagama Cinye Lokaci a hirar Samiha ba yadda ya iya Haka ya mike Suka Fita Zuwa masallaci kasa da gidan Abba sukayi alwala suka bi Jam"i.

Itako Samiha tana Shiga Daki ta Daka tsalle ta Fada gado Lokaci Daya tana Rumgume Filo Lumshe ido tayi tana Fadin"Ahmed..Wannan karon bazaka iya Lankwasa Samiha ba..Samihar dakasani abaya Tana da kuruciya batasan Ciwon kanta ba..Samihar daka hadu da ita yanzu ta gama cika mace ta kuma san Ciwo da Mutumcinta zan bama Zuciyata abunda takeso Ahmed ko kana so ko baka so kuwa Dole ne na amshi Abunda yake dama mallakina.."tafada tana Wani runtse ido Cikin Wani yanayi ta Dade ahaka kafin ta mike ta Fada Tiolet tana Rangaji kamar wahainiya Wanka tayi Tazo tayi sallar mangariba ta Chaba ado Cikin Wata Ubansu Doguwar Rigar Leshi,dama Samiha tafi son Dogayen Riguna Kaf Rabin kayanta haka suke,Leshin kalan Blue da pick ne an mata Dinkin Bubu Rigar ta kamata kuma ta bayyana Suran jikinta waje,Bata cika saka kayan da suka kamata ba in Abba na gidanta ba Saboda yanayinsa duk sai ya chanza ya Fara wani kamata sai ta sakamai kuka tana Fizge fizge yake kyaleta Abun yayi ta bata Haushi mutum ya Tsufa ammh kuma sai Son  ya kasancewa da mace shiyasa bata ma sakarmai Fuska bata Kaunar Abunda zai Rabata da Burdurcin data gama Tattalama Ahmed Abunshi.

Bata ma Fuskarta wata kwalliya ba ammh Tashafa Hoda ta saka Liptick,sai gashinta data Tattara waje Daya,ta Daure da Band tayi Daurin nan na zamami mai Tuntu ta saman goshi tsakiyar kuma gashi waje Flat shoe din ta saka bayan tagama yima jikinta wanka da Turaran Jiki dana kaya Ta dauko wayarta Ta Fito tana Taku Daya bayan Daya Tun Daga saman Upstair take karema Ahmed kallo Cikin Wani yanayi na Soyayyah kawai sai ta coge awajen Ta kurama bakinsa ido yana Duke gaban Ahmed cike da girmamawa suna mgana kan wani mai kamfanin Kayan yara ne toh kamfanin nashi ya Durkushene yana neman ma mutuwa ne,shine yana son ya Farfado da kamfanin nashi yaa nemo Abba domin ya saka mai Hannun Jari domin Taimakon kamfanin Daga mutuwa kayan yara ne yake Shigo dasu daga waje masu kyau Shine Abba ya Kira Ahmed suyi Shawara cikin Girmamawa Ahmed ke Fadin"Abba nidai aganina ka saka Hannun Jarinka Tunda dai bamu taba Harkan kayan yaran nan ba mu gwada mu gani in abun ya Tabbata sai mu rika Kawowa Shagunanmu na Cikin kasuwa mu gani yanayin kasuwar in sun amsu hakan zai Taimaka maka Shima kuma kamafinsa zai Farfado Daga Faduwa.."Jinjina kai Abba yayi yana Fadin"Dz very gud Ahmed..Akullun ina Alfaharin kasancewa dakai amatsayin D'a na kuma abokin Shawarata  kana da Hangen nesa da Hikima yanzu Abunda za"a ayi ka kira Lauyana awaya kuyi Mgana zan nemi shi Alhaji Mande din nace na amince sai ya Zabi Ranar da zamu hadu ga lauyansa ga nawa  gani ga ka Nura manaja sai ayi Rubuta na saka Hannun jarin nawa Allah Ya Shigemana gaba.."yafada yana Buga kafadan Ahmed cikin Jin Dadin Mimirshi kawai Ahmed keyi yana kara Sadda kai Dariya ta kama Samiha Cikin Farinciki ta Fara Saukowa ko"ina na Jikinta na Kadawa tun Kafin ta kariso Ahmed yaji Kamshin Turaranta ya Daki Hancinsa Ya Dago da Sauri suka hada 4 eyes Dashi Wani Mirmishin yaudara ta sakarmai tana Dage mai gira Daya Saurin kauda kai yayi yana jin Faduwar gaba Abba kuwa jiki na Rawa ya mike yana Fadin"A"a gimbiya kin Fito.."?

Yafada yana kafeta da ido Cikin Sha"awa kan Ahmed na kasa bai Dagoba Samiha ta wuce ta gabanshi Zuwa kujeran datake Fuskantashi ta Zauna tana Fadin"Eh Alhaji nazo mu gaisa da Surukina ko D'ana ne ma zance.."Ta fada tana Dora kafa daya kan Daya bayan ta Cire kafar takalminta guda Daya lokaci Dayatana Jifan Ahmed da wani kallo kasa kasa Abba na Faman Rawan Jiki ya Zauna gefenta yana Fadin"Duka ne Ranki ya Dade..D"anki ne kuma Surukinki ne..kai Ahmad ga Antynka nan dai yau ka ganta Samiha kenan Amaryata dana Aura Shekara goma da suka wuce kagatanan bata Tsufa kullum Cikin yarinta take.."yafada cikin Zolaya Wani kallo tamai kafin tace"Ai ni dama chan ayarinta ka Auroni..Kuma haryanzu ina cikin Yarintata."Tafada kai Tsaye tana Sakarmai manyan Idanuwanta,Saurin Cewa yayi"Afuwan gimbiyata da Zolaya na Fada.."Ko kallonsa batayi ba kanta ta maida gefe tana Nazarin Ahmed din wanda kansa ke Duke yana Faman Rawan Zuciya Bai taba Sanin Haka Abba ke ma Samiha Rawan Jiki ba sai yau yasha dai jin Abida na mitan Amaryan Abba tamaidashi kamar wani Sakaranta Kunya ce ta kamashi da kuma Fargaba Lokaci daya.

Ganin yayi Shuru yaki Mgana ne kuma bai Dago kanshi ba Tun bayan da suka Hada ido Daga Farko yasa ta kalli Abba tana Fadin"Wai nikam Alhaji Dan'namu ko nace Kurma ne?.."

Jin Haka yasa Ahmed ya muskuta yana Fadin"Arm ina wuni..",yafada cikin Sanyin Murya Mirmishi ta saki kafin tace acikin Ranta komai nashi bai Chanza ba Cikin Wata murya tace"Lafiya lau ya office..?kana fa Kokari Alhajina na yawan Maganarka angode Allah saka da alheri.."a lebensa ya amsa da Ameen Abba da Ameen ya amsa yana Fadin"Ai in nabaki Labarin Kokarin Ahmed ankaina da Dukiyata gabadaya sai kin kara jin ya Burgeki.."kai tsaye tace mai "Na Sani..."Abba bai damu ba Ya cigaba da bata labarin Waye Ahmed mirmishi kawai take saki ita kadai tana Fizgan kallon Ahmed wanda yagaji da zaman Rashin Dalili ya mike yana Fadin"Abba zan koma..Zan kira Barrister yadda mukayi zan Kira ka ta waya na sanar maka.."

Mikewa Abba yayi yana Fadin"Harzaka tafi Ahmadu baka Taba komai na Abun shan da'aka kawo maka ba,sai ruwa.."Kai tsaye yace"Eh Abba bana jin yunwa ne..Innaje gida zan ci,"Abba baiyi Mgana ba Samiha ta mike tana Kallon Ahmed cikin Wata murya tace"Haba kai kuwa Ai yakamata ka Tsaya muyi Dinner ko..? Bai kalleta ba yace"Na..nagode Hajiya zan karisa gida mai Dakina bata jin dadi.."Samiha tayi Sororo kawai tana kallonsa Abba ne ya kalleta yana Fadin"Kiyi Hakuri gimbiyata ki barshi ya Tafi watarana in ya Dawo sai yaci..Abida bata jin Dadi Tunda ta samu cikin jikinta Shikenan Jiki yaki Dadi yanzuma haka Kakarsa ta koma gidansa da zama Saboda Haka.."

Dam! Gaban Samiha ya Fadi Ciki Ahmed yayima Abida..Sai kuma Jin Labarin Ashe kaka nada Rai bata mutu ba,wannan Tsohuwar mai bala"in Saka ido,Idanuwanta da Suka chanza Launi ta sakarma Ahmed cikin Takaichi da Kishi Wato ma Ahmed zai iya Aure har ya saki jiki yama wata mace Ciki Bai damu da ita ba bayan ita Shekara goma tana fama da Tsinuwan mala"iku akansa Lallenema Ahmed ya Dauko ma kansa Dala ba gammo Bata Jira Cewar su ba kawai ta Juya Tafara Haura Stepa cikin Fushi Abba ya Bita da kallo yana Fadin"Ahmed yau ka batama Gimbiya rai.."

Yake Ahmed yayi kafin ya Rankwafa yana fadin"Mu kwana lafiya Abba.."Bai ma amsamai ba Ya Fice Daga Falon Shi kuma Abba yabi bayan samiha yana Kira ko da yaje ta Rufe Kofar Bedroom din tana ciki ta Fada Bisa gado tana kukan Takaichi da Kishin Ahmed.

Shiko Ahmed bai sauke Numfashi ba sai da ya Bar gidan bayan ya Daidaita Motarsa Bisa Kwalta ajiyar Zuciya ya saki yana faman kada kai shi kadai kawai yake Tsausayama Rayuwar Abba baitaba Tsammanin Samiha zata Zama haka ba mara Tsausayi tana Wahalar da Rayuwar wanda ya Haifeta gaskiya sam bai taba Zaton Tana da hallayar data Fito dasu yanzu ba baisani kila bayan Rabuwarasu ne ta Fito da Sabbin Hallayah.


Har ya iso gida bai da Walwala Haka Abida ta ganshi data Tambayeshi sai yace mata Ya gaji ne kansa ke Ciwo yau ko Dakin Kaka bai Shiga ba yadai leka sungaisa yana jinta tana Faman Caccakarsa don ya Tankata bai Tankata ba,ya koma Daki sama sama yaci Tuwan Semo din da Abida tayi musu Saboda shi don ma yana so ne Shiyasa yaci kadan Ta bashi mgani bai kwanta ba sai da yayi sallar Isha"i Shafa"i da Wuturi Dai bai samu yin su ya kwanta Abida ta Rufamai blanket tana Shafa kanshi Tsausayi yake bata kwata kwata Ahmed bayason zama agida ya Huta ko Ciwo yake sai ya kwantar dashi Magashiyanta a gado yake Hakura da Fita,ammh na yanzu kam Damuwa ne da Tunani da Fargaba suka samai Ciwon kai.




*Aisha alto...*
*Janafty*