9
*SILAR HALLACI*
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
Contact Hijabs Corner by Janafty for all kind of Qualitative hijabs for women of class.
*** ZARIA/KADUNA Natio wide delivery.
*🅿️9*
"Washegari yaso ya Fita zuwa office ammh Abida taki barinshi ya Fita daya matsamata zai Fita sai ta Kira Abba ta gayamai wai bashi da lafiya kuma yaki zama agida nan da nan Abba ya Kirashi yace ya zauna agida ya samu Hutu bashi da yadda zaiyi Hakanan ya kwanta agida Abida na Kula Dashi,wanka ma ita ta taimakamai yana ta bari ya samu Sauki ammh taki bari Tsausayi take Bashi ganin bata da Ishashiyar Lafiyan Jikinta Tunda ta samu Cikin nan,ammh game da Abunda ya Shafeshi Abida bata wasa dashi ko Abinci a baki ta bashi tana lallabashi kallonta kawai yakeyi yana jin Wani Iri acikin Jikinsa na wani Abun daya kasa gane komene,ko ma mene Toh yana da Nasaba da Fargaba.
Washegari ma bai Fita ba sai yammah ya fita zuwa Gidan Lauyan Abba Barisster Sa"ed sukayi Mgana Daganan kuma ya Biya gidan Kawu maude ya gaishesu sunyi kwana biyu basu Hadu ba, yadan Jima Suna Hira da kawu mauden wanda yake gani a matsayin Mahaifiyarsa,domin Shi kadai ne ya sani daga Dangin Mahaifiyarsa Sai bayan mangariba yama Kawu maude da Anty Naja"atu sallama ya Fito bai koma gida ba sai da ya biya ya Siyoma Abida kaza da yoghourt ita da kaka,kafin ya Shiga Gida sai da ya tsaya yayi Sallar Isha"i kana ya Shiga Gida,Gari na wayewa kuwa yayi Shirin Zuwa Office Abida bata Hanashi ba ganin yaji Dadin Jikinsa Karfe 8am na Safe ya Fice bayan ya karya yana zuwa Office dinsa ko zama baiyi ba wayar Abba ta Shigomai yana Gayamai wai Samiha tace ya kamata suzo su Dubashi ido ya zaro gabansa na Faduwa cikin Rawan murya yake Fadama Abba Shi ya samu Lafiya ya Fito zuwa wajen aiki jin Haka yasa yace Shikenan Allah kara lafiya suka Rabu ahaka Ajiyar Zuciya Ahmed ya Sauke Acikin Ranshi yana Tunanin Tabbas Samiha na kulla wani Abu wanda baisani ba,yana Fatan Allah ya Tseratar dashi Daga kaidinta.
******
Yau din takama Monday ne Tushen aiki ko bature na Tsoranki,yau Ahned ya Makara bai Tashi da Wuri ba Shiyasa sai Wajen 8:30am na safe Abida ta Rakoshi Zuwa Dakin kaka wacce ke Zaune Bisa Cafet din Dake Dakin nata ta kurama Talabijin ido kamar tana jin me ake Fada Sallama sukayi batama jisu ba Dariya Ta kama Ahmed ya kalli Kaka yana Fadin"Kaka kina jin Abunda ake cewa ne kika wani kafe ma Tibi ido..'?
Sai alokacin Taji Shigowarsu Dagowa tayi lokaci Daya tana makamai Harara tana Fadin",Bansani ba..Allah Ahmadu in baka Fita Daga idona ba zakaji ba Dadi..Ina Ruwanka da ina Jin Abunda ake cewa ko bana ji..?Tafada tana wani Murgadamai baki,Mirmishi ya saki yana Fadin"Ah taya zan ko Fita daga Idonki kaka..,?ai ina ciki bazan Bita ba Ahmadu da kaka ai mutu ka Raba.."
Washe baki Kaka tayi tana Fadin"Wlh kuwa Ahmadu..Haba ai ni na sani Duk Duniya waya kaini Sonka Ahmadu..Kawai wani Lokacin baka da Mutumci ne.."Abida da Ahmed suka saka Dariya Ahmed na Fadin"Ni Kaka Nine Banda Mutumci kai Tsaye gaban Iyalina harda ya"ta ko Dana gashi. "yafada yana Shafa Cikin Abida Baki Kaka ta saki kafin ta fara Tafa hannu tana Fadin"Na Shiga goma ba Tara ba Ni Bara"atu Jikar Audi Basakkwace.Ahmadu Rashin kunyanka kara gaba kawai yake Mu lokacin mu ko haihuwa aka maka Boye kanka kake saboda kunyar Fari ammh kai kuwa baka data ido Ahmadu agabana Har kana Shafa cikin Saboda Tsabar tacewa irin naka na yaran zamani.."Baki ya Tabe yana Fadin"Allah ya kyauta Kaka boyewa kamar wani Cikin Shege..? Mutum baiji kunyar Shiga Daki da mace ba,sai kunyar Abunda suka aikata ya Fito.."yafada kai Tsaye Kaka baki Ta Rufe da Hannu ta juya baya Tana Salati Abida ma baki ta Rike tana Zakudan Jikin Ahmed Shiko ko Ajikinsa yar Dariya yayi kafin yace"Kaka ni zan Fita..Kina Bukatar wani abu ne..? Ko mgana Kaka batayi mai ba Banza tayi dashi Ta juya baya bai damu ba Illah Kafada daya zakuda yana Fadin"Sweetheart ki tsaya anan basai kin Rakani ba...Tanque.."
Ya juya yana Karban Jakar Briefcase dinsa Kaka ta waigo tana Fadin"Kai Ahmadu tsaya nan kaji ni dakyau.."Waigowa yayi yana Fadin"Na"am Kaka.."ido ta Kuramai Tana Fadin"Ahmadu ashe duk zaman da mukeyi Dakai Kar kake kallona Bansani ba..?"Tafada cikin Mamaki kamar zaiyi Dariya sai kuma ya matse yana Fadin"Sosai ma Kaka..Kinsan yanzu Lokaci ya chanza zamani yazomana da Komai Shiyasa.."Kada kai kawai Kaka keyi tana rike da Haba,bai Bata zarafin mgana ba ya juya Zai Fita cikin Alhini Kaka ke Fadin"Abida Ahmadu ya gama Lalacewa...uhmh...Ahmadu ya lalace yazama Dan iska.."Abida ta saki Dariya Shima yana Jinta Dariyan yayi Cikin Ranshi yana Fadin Kaka kenan.
Barayin Cikin Mall din ya fara Shiga sukayi Mgana da Nasir kafin ya Wuce Office dinsa,akwai wani Sako da zai Duba ta Email dinsu,ya Bude System din kenan wayar Abba ta Shigo wayarsa ya Dauka Suka gaisa nan yake Shaidamishi Sunyi Mgana da Alhaji Mande din,zai zo yau bayan mangariba Gidan Abba dashi da lauyansa da kuma Manaja Saboda haka ya Kira Baban Iman ya gayamai Da kuma Barrister Sa"ed anjuma su Hadu a gidan Umma Dake gadon kaya,Cikin girmamawa Ahmed ya amsa ma Abba kafin su yanke Kiran,bai kira Baban Iman sai da yagama Duba Sakon da aka Turomai ta Email kana ya Kirashi ya gayamai yace ba Damuwa sai sun Hadun,da haka Suka Rabu bayan sunyi sallama.
Yana cikin Office Dinsa yaji Masinjansa Daga waje yana Cewa Hajiya..Hajiya lafiya kuwa..? Bai gama mamaki ba kawai ta Bude Kofar Office din nashi ta Shigo Cikin Wani irin Taku Da Sauri Masinja ya Rufomata baya yana Fadin"Hajiya ya zaki shigo ma mutane waje ba Neman Izini..? Ahmed daya Dago kansa Suka Hada 4eyes da Samiha wacce ke Sanye da Wata atamfa Riga da Sikat,tayi Daurin nan Ture kaga Tsiya,Fuskarta ba kwalliya sai dai ita Samiha ko batayi kwalliya ba mai kyau ne Kayan akwai Kalan ja ajiki Sai ta sako wani Karamin Red din Vail bisa kafadanta,Kayan sun kamata sosai barin ma Siket din Jikinta yagama Fitowa da Surar Jikinta Kafarta sanye cikin Wani Red din Takalmi mai Tsini Hannunta wata karamar Red din Jaka ce tana Tsaye ta coge ta zubama Ahmed manyan idanuwanta mai Cike da Shauki.
Da Sauri Ahmed ya mike Gabansa yagama Saki yana wani Rawa kamar mazari,Hulansa kansa ya maida baya yana Kallonta cikin Fitan Hayyaci,Masinja ya tsaya yana kallon Ahmed zatonsa Fada zai mai sai yayi Saurin Rankawafa yana Fadin"Kayi Hakuri Ranka ya Dade bata.."Hannu kawai Ahmed yadagamai cikin Sanyin Murya yace"Bakomai Jeka kawai.."Godiya yayi ya Fice yana Kallon Samiha cikin Mamakin ganinta Office din yallabai Domin Mutum ne nagari karyane ka sameshi da wani Laifin Assha.
Ya Fita Ahmed ya Dago kansa yana Kallon Samiha Lokaci daya ya Hade Ransa yana gayyato Jarumta cikin Wani yanayi yace"Meya kawoki wajen aikina Samiha..?yafada yana Kauda kansa Daga kallon datake Jifansa Dashi Cikin Wani irin Salon Tafiyan Jan hankali ta fara Taku zuwa wajen Ahmed ta zagaya har wajen Kujeran sa tana kallonsa kafin ta wani juyamai har saida Tudun Hips dinta suka Shafi Jikinsa Saurin Barin barayin yayi Saboda Fargaba da kuma Tsoro Me Samiha ke Shirin aikatawa,Yar dariya ta saki kafin ta kada ido Jakarta ta ijiye saman Teburinsa kafin ta Daka tsalle ta haye saman Tebur din Tana Fadin"Miye naga kana wani Firgice..? Samihar kace fa..? Ai daman ka Riga ka sani cewa Dole sai nazo wajenka ko..? Toh miye Abun kuma Damuwa..? Tafada tana wani Sakarmai idanuwanta Baya ya matsa yana Damke Duka Hannuwansa saman Kirjinsa kafin yace"Baki da Dalilin da zaki zo Wajena Samiha..karki manta yanzu ba da bane yanzu kina matsayin matar Aure ce matar Auren ma bata kowa ba Mata ga Uban gidana wanda zamo Tamkar Uba gareni Kana kuma Surukina wanda nake Aure da yarsa ta cikinsa,ai inaga wannan Dalilin ya isa Dani dake mugane Cewa Dalilin Haduwarmu da Rabuwarmu duk Rubutattace ne daga Rabbil Izzati Samiha.."
Yafada yana Kallonta Domin ganin yadda zata Dauki mganarsa,Wani mirmishin gefen baki Samiha ta saki kafin ta Sauko Daga kan Teburin Tafara Taku tana Zagaye Office din Cikin Dariyan Rainin wayau take Fadin"Wai kana Nufin zaka kara Gujemin a karo na Biyu ne Ahmed..? Karkayi wannan Kuskuran domin wannan karom kalamanka basu da wani matsugunni acikin Raina..Ban dawo da wasa ba wannan karon sai na Tabbatar da Duka mafarkanmu sun zama gaskiya Ahmed."Tafada hankalinta kwance wani Kallo Ahmed ke bin bayanta Dashi kafin yace"Me kike Nufi dani ne..? Yakamata ki gane Cewa yanzu mu ba yara bane.Na tabbata mungama sanin Ciwon kanmu munsan Abu mai kyau da mara kyau.."Juyowa tayi tana Tafi Lokaci daya tana Fadin"ya bravo..Kowa yasan Ciwon kansa mana Ahmed sanin Ciwon kan nawa ne yasa zan karbi Abunda yake Nawa Tundama chan...yakamata ka tsaya ka Saurareni kafin ka katsemin Hanzari.."Wani irin kallo yake Jifan Samiha Dashi Lokaci daya yace"Ina Sauraranki me ya kawoki wajena..ki gaggauta fadin Abunda ke tafe dake ki Fice kibarmin Office bana so ki jamin Wata mtsala Arayuwata samiha.."Kai tsaye tace"Bazan ja maka mtsala ba Ahmed matukar ka Bani hadin kai...Ammh matukar kanuna min Taurin kai Toh Tabbas kuwa zakayi ta shiga mtsala,mtsala ma mai girma wanda zaka gwammace dama Hadin kai ka bani da Halin da zaKa Shiga.."Kallon na fara Tsoronki yashiga yi mata kafin yace"Ina Sauraranki."
Hannu ta Dagamai tana Fadin"plz can u Seat..?"Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Zauna itama kujeran dake Fuskatanshi taja tazauna tana Fadin"Tanque..."Bai mata mgana ba Illah kallonta kawai dayakeyi Ammh Cikin Zuciyarsa ta cika da Tsoro yana Tunanin wasu daga cikin ma"aikatan wajen nan Ranar sun ga Samiha amatsayin amaryan Abba ya Tabbata wanda ma baisani ba Ranar ya sani yana jin Tsoron Faruwan wani abu mutane zasu Dinga mamakin meya kawota Office dinsa adaidai wannan Lokacin Abunda baitaba Faruwa ba ko ya"yan Abba Nabila ce kawai tataba zuwa wajen ko Abida datake matarsa bata taba zuwa ba balle Umma ammh Zuwan samiha wajensa Babban Barazana ne garesa wani amsa zai bama Mutane in suka Tambayeshi Dalilin Zuwanta.
Katsemai Tunani tayi ta Cewa.."ina so Dani dakai mu Dauka Allah ya sake hadamu ne Saboda mu mallaki Junanmu,Abunda nazo maka Dashi Shine zan matsama Alhaji ya Sakeni saboda Shikanshi ya sani bantaba Sonshi ba Duk iya wannan Shekarun,kai ne acikin Raina Ahmed...Don Allah karka ce bazaka yarda da Shawarata ba,Ina so bayan na matsamai yasakeni bayan nagama Idda sai muyi Aure Mafarkinmu su Tabbata Ahmed.."Tafada tana kallonsa Cikin Rauni Hawayen idanuwanta suka gangaro Bisa kumatunta.
Mutuwar Zaune Ahmed kawai Ahmed yayi yana kallon Samiha cikin Rashin Hayyaci,tunanin wani irin Zuciya samiha take dashi kawai yakeyi wai kuma saboda Tsabar Rashin Hankali da kuma Rashin ta ido da kuma Rashin Tunani tana Nufin In Abba ya saketa shi ya Aureta saboda Shi ya zama mara hankali,sai kuma ya Fito yace zai Aureta ai koda Soyayyar Samiha zata kasheshi ne ya hakura da ita Saboda Silar hallacin Abba,balle kuma Tuni yagama Cire Samiha acikin Ransa Tunda tayi mai Nisa.
Cikin Lokaci kadan ya Ji Jarumta ta Shigeshi mikewa yayi yana Kallon Samiha cikin Wata murya mai Cike da Bacin rai ya Shiga Furta.."Samiha ashe haryanzu Baki girma ba..? Wannsn Mganar taki tayi kama data yara kanana masu Tatsuniya wacce bazai taba Faruwa ba...Ki chanza Tunani Ni Ahmed yau ko Mutuwa Abba yayi Samiha bazan iya Auranki ba saboda ana barin Hallas kodon Kunya.."
Mikewa tayi tana Kallonsa Cikin kuka tace"Ahmed ka manta Wacece ni...? nice fa masoyiyarka Samiha..? ka manta alkawarinmu...? ka manta yadda muka Tashi muna gina Yadda Rayuwar Aurenmu zata kasance..? ammh yau rana daya sabosa wani Dalilinka mara tushe ballatana makama kakeso kaki amfani da damar data Samemu Ahmed...?
hannu ya daga mata lokaci daya yana Fadin"Ya isa haka Samiha..!Nace ya isa Haka...? ya kikeso nayi dake ne eh..? karki manta ke matar Aurece yanzu Duk wadanan Buranka namu sun yanke daga Lokacin da Mahaifinki ya bada ke..! taya ya zan iya Bin Bukatarki alhalin kina matsayin matar Uban gidana..! kuma nima ina matsayin Surukinsa ina Auren yarsa ta cikinsa kuma sai na biye miki naci amanarshi.? A"a bai zai Taba faruwa ba bazan Taba yima Megidana Haka ba SILAR HALLACIN dayayi min bazai Taba barina na iya cin Amanarsa ba SAMIHA...
kiyi Hakuri...!
Wani irin kallo take Jifan Dashi Lokaci daya manyan Idamuwanta na Tara kwallah cikin Takaichi da wani taku ta tafara takawa zuwa gabanshi shikuma yayi Saurin Juyamata baya yana Boye Siririyar kwallar dake Cikin Idanuwansa,mirmishib dayafi kuka ciwo ta saki kafin tace"Ahmed karma ka fara wannan ganganci...Karma ka fara Tunanin wannan karon zaka iya Gujemin..Baka isa ba Wlh Tallahi na yi ma kaina alkawarin sai na mallakeka Ahmed a matsayin Mijina ko ta Halin kaka.."Tafada Lokaci daya tana Zurama bayansa Ido Cikin mamaki ya Juyo yana Fadin"Me kike Nufi Samiha..?Karki manta kefa yanzu ba yarinya bace kin zama babban mace kin mallaki hankalin kanki..Balle nace yarinta na Damunki kiyi gaggawan barinmun office kafin na saka afitarmin Dake.."yafada yana Hade Ransa Lokaci daya yana Nuna mata hanyar waje Wani Mirmishin Mugunta ta saki kafin tace"Ni kake kora Ahmed...?
Bai mata mgana ba illah Nufar Teburansa dayayi yana Danna wasu lambobi bisa Telephone din dake kan Teburin Wata karamar Dariya ta saki Lokaci Daya tana Fadin"Zan tafi ba.ammh ba domin zaka kiramin Jami"an Tsaro ba sai domin Soyayyar da nike maka ta gaskiya ne ina sonka Ahmed kuma ina son kasancewa dakai..ammh ba domin haka ba zan Kyaleka ka kira wanda zaka Kira kafin su taho nayi Tsirara agabanka suna zuwa zan Fara kuka nace kai ne kake neman yimin Fyade,daga nan in Alhaji yaji komai ya lalace maka..'Tafada tana wani Sakarmai Idanuwanta.
Tsam yayi kawai yana Kallonta bai samu Zarafin mgana ba ta kara Taku zuwa gabanshi sai da ta wani juyamai kafin tace"Karka damu bazan yi haka yanzu ba...Matukar kabani Hadin kai komai Zai tafi yarda na Tsarashi in kuma ka cigaba da Taurin kai......"
Ta Karishe fada tana Shafa Sajen Fuskarsa Saurin Kauda kai yayi Cikin bacin Rai jakarta ta Dauka da wayarta dake saman Kujera ta kama Hanyar Fita tana Kadamai Mazaunanta Saurin dauke kai yayi yana ta"awizi acikin Ransa Kafin ta Fita ta Waigo tana kallon Ahmed kafin tace"Zan dawo...Akwai dawowa.."Daga haka ta Fice kansa ya Dafe yana maimaita Kalmar Innalillahi wa"inna illaihirraju"un...
Kan kujera yafada yaraf yana Sauke Numfashi Cikin Fesar da Numfashi ya Furta"Samiha...Wani bala"i ki ke neman Jefani ciki..Allah gani gareka ka tsareni daga Sharrin mace.."yafada yana Runtse Idanuwansa Cikin Halin damuwa da Rashin mafita.
Mikewa yayi jikinsa na Rawa ya Zage labulen Window din Office din nashi yana kallon Haraban wajen,yana kallo tashiga Mota Direba yajata suka Fice daga Haraban wajen ajiyar zuciya ya Sauke ganin babu mutane wajen sai masu Shiga da Fita,komawa yayi Bisa kujeransa ya zauna ya Cire Hula ya Dafe kansa kamar ya Kurma ihu saboda Takaichi da bakinciki,wuni yayi ya Rasa mafita ko Abinci bai iya sakama Cikinsa ba Saboda Halin dayake Ciki sallah kadai ke tadashi,su kansu ma"aikatan wajen sun Fahimci Ahmed baida walwala kamar kullum,Sai karfe 6 ya tashi Daga office bai koma gida ya Biya kasuwar kwari Wajen Baban Iman sai ya iske an sauke Diloli,suka tsaya suka duba komai da Lissafi anan cikin kasuwar sukayi sallar mangariba kafin kowa ya Shiga motarsa Zuwa gidan Abba dake gadon kaya,koda suka isa har su Alhaji Mande sun iso suma sun iso ba Dadewa sai ga Barrister Sa"ed aka Zauna afalon baki na Abba akayi Mgana da Rubutu kowanne Bangare ya saka hannu Abba ya Rubuta cek na Miliyan30 aka bama Lauyan Alhaji mande,Abba bai bari sun watse ba sai da sukayi Dinner gabadaya Ahmed dai sama sama yaci Abinci bakinsa baya mai Dadi gabadaya bashi da walwala,Har sai da Abba yamai mgana sai yace kansa ne ke ciwo cikin Tsausayawa Abba yamai sannu yace kuma yaje gida yasha mgani ya kwanta ya Samu hutu Daga haka suka Rabu kowanne ya Shiga Motarsa ya tafi gida.
*Aisha alto..*
*Janafty*