SILAR HALLACI

Page 10

by @jamilaumarjanafty

*SILAR  HALLACI*

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

        *🅿️10*

"Har Ahmed ya koma gida bai da Natsuwa,wuni daya har yayi wani Zuru zuru dashi Haka Abida ta Dinga kallonsa yana zaune kan daya daga cikin kujerun Falon dawowarsa kenan daga masallaci sallar Isha"i shine ya zauna anan ya Zabga tagumi Ta kawomai Daya daga cikin Favourite Food dinshi Wato Dambun shinkafa da Zogale,Ammh Ahmed bai iya ci ba yace ta bari zuwa anjuma Tsuru kawai tayi tana kallonsa cikin mamakinsa Domin Ta wahala wajen yimai Dambun bata jin Dadin Jikinta sai da Kaka ta hanata taki ji Saboda kawai ta Farantamai rai ammh kamar ta Lura Ahned din yana cikin Damuwa ba,duk da bashi da yawan Hayaniya da Surutu barkatai ammh Fuskarsa tana bayyana baya cikin Hayyacinsa Lokacin dayake Zaunen.

Har ta kariso gabansa bai sani ba Ta zauna kusa dashi,ma bai sani ba sai da ta saka Hannu ta Ciremai Tagumin Fuskarsa kana ya Dago a Firgice yana kallonta ganinta yasa ya saki Numfashi sama sama yana Fadin"Sweetheart baki kwanta ba.."? Ya fada yana Riko Duka Hannayenta Lokaci daya kuma yana Shafa hannayen nata,Rau rai tayi da ido kafin tace"Hubby wht Wrong wit u ne..? Nakasa gane kanka daga satin daya gabata zuwa yau..?

Saurin Sakin Fuskarsa yayi yana Fadin"Me kika gani..? Ba komai Sweetheart..? Mirmishi ta saki Lokaci daya ta saki Hannunshi ta kai Saman Fuskarsa tana Shafawa cikin Muryan sanyi tace"A"a Hubby kana cikin damuwa wani abu na Damunka sai dai indai baka san ka gayamin kawai.."ya bude baki zai yi Mgana ta dagamai hannu tana Fadin"Shikenan kawai Hubby tunda bakasan gayamin..Ammh plz ka rage damuwa kada ka samu wata mtsalan kodon saboda ni da Abunda ke cikina.."Tafada idanuwanta sun Tara kwallah Suna Shirin Zubowa,Kafadunta ya Dafa Duka biyun yana kallonta Cikin Muryan damuwa yace"Karki damu kanki Matata...Babu Abunda ke Damuna Kinji ko..? Duk da bata yarda ba ta dagamai kai Hannu ya saka yana Share mata kwallar data Zubomata Lokaci daya yajata Bisa Kirjinsa ya Rumguneta Tsam yana Shafa kanta Zuwa bayanta cikin Alamun Lallashi lafewa tayi tana Sakin Ajiyar Zuciya Shi kuma Idanuwansa ya Runtse yana so yayi yaki Da Tunanin Mganar da Samiha ta bijiromai dashi ammh ya kasa Saboda Tsabar Zullumi da Fargaban wani salo kuma zata Fito Dashi nan gaba.

Cak ya Dauketa suka Shige Bedroom dinsu yayi kokari ya Boye Damuwarsa,Ya dinga tarairayan Abida yana nuna mata Soyayyah awannan Daren Abida ta tabattar da tafi kowacce Mace samun Nagartattacen Miji Irin Ahmed bayan sun samu natsuwa tana Kwance Bisa Kirjinsa tana Sharar barcinta Shikuwa barci ma yaki Zuwa Cikin Idanuwansa Ceilling kawai ya Kurama ido yana Tunanin mafita ammh har gab da asuba yakasa samo mafita tashi yayi ya zame Abida daga kirjinsa ya maidata kan Filo ya fada Tiolet ya Dauro alwala yazo ya fara sallah yana kaima Allah kukansa da kuma Allah ya masa Tsari da Kaidin Samiha,sai da akayi kiran Farko ya Tashi Daga kan Darduma ya Tada Abida shi kuma ya Fice zuwa masallaci bayan ya Shiga Dakin Kaka ya tarar da tana Raka"atanul Fijir sai ya kadai kai ya Fita zuwa masallaci Gefe na Zuciyarsa ya samu Natsuwa Sosai.

Saboda ya farantama Abida rai da Safe yasa ta Lumamamai Dambun Datayimai jiya yayi Breafast dashi ta Soyamai Doya da kwai da Ruwan Citta ya Hada dashi bai Fita da Wuri ba sai da ya jira Abida da kaka ya Daukesu ya kaisu gidan Umma gadon kaya yace in sun tashi Direba ya kaisu gidan kawu maude in yatashi aiki zai biya ya Daukosu Kaka sai washe baki take tana Fadin"Allah yayi yau na Fito naga Sararin Waje..Haba ace kullum mutun da kafarsa ammh sai a dinga killacesa a gida kamar yana kurkuku ina Dalili..".

Tafada bayan Sun gaisa da Umma,Kowa dariya yayi Banda Ahmed yadan kalli Kaka a dage yana Fadin"Allah ko..? Toh daga  yau sai kinyi Shekara zaki sake Fita domin nan kano ne bakisan ko"ina ba ba garin jega bane balle kice nan aka haifeki.."Kaka ta Daga murya tana Fadin"Kama isa Ahmadu.? Wlh kayi kadan ko Tsohon Mijina Zakariya bai isa yasamin Dokar fita ba balle kai karan kada miya.."Baki kawai ya Rike yana kallon Kaka Abida da Umma na Dariya bai kara mata mgana yasha kunu yana zaune yana danne dannen waya,zaman ma dayakeyi yana jiran saukowan Abba ne zai kaisa Kasuwar kwari ya duba kayan da aka kawo Shine ma Dalilin Zuwan nashi basu dAde da zuwa ba sai ga Abba ya sauko yana gyara zaman babban Rigan Jikinsa da Sauri Ahmed ya Mike alamun girmamawa Abida ma ta Duka tana gaisheshi ya amsa yana Fadin"A"a Abida tare da ku Ahmed yazo kenan..?

Kaka Tayi karaf tace"Allah ya ci damu yau Alhaji..Yaron nan Ahmadu danace in zai fita ya kaini gidan maude na Wuni zamam Shurun ya Isheni ni ba wata sana"ar cikin gida ba sai zaune kawai sun hadani da wata Talabijin kawai gashi ni bana Fahimtar me suke cewa danayi mgana sai yaron nan Ahmadu yace bazan shigarmai mota ba in na matsu na fita na hau adaidaita Alhaji Duk Tsufana yaron nan Ahmadu baya Darajani.."Ta karishe fada har da Share kwallah Abida da Ahmed suka hada ido suna Zaro ido Lokaci daya Abba ya kariso kusa da kaka yana Fadin"Gaskiya Ahmed bai kyauta ba Kaka zan mai Fada.."
Kaka tace"ahto kila in kai kayimai ya jika da kyau..Ni dama Tuni yagama Rainani Alhalin na mai Abunda ko uwar data kawosa Duniya zaliha bata mai ba ammh yaron nan baya Darajani.."Tafada tana Hararan Ahmed wanda ya Hade rai ya kauda kai gefe Abba ne ya juyo yana kallonsa Lokaci daya yana Dafa kansa yace"Ahmadu kaji Korafin kaka a kanka ko..?.
Rankwafawa Ahmed yayi yana gaida Abba lokaci daya yana Fadin"Naji Abba..ka kyale kaka Rigimartane kawaai.."yafada yana Bude ma kaka ido ganin ta wani waro baki zata fadi wata mgana kallonsa tayi tace"Nayi Shuru ubana kada na fadi ka Dakeni.."Tafada cikin gatse Shikanshi Abba sai da yayi Dariya kafin yace"Kiyi hakuri kaka zan mai fada sosai.."Baki ta kyafce kawai shi kuma ya nufi Hanyar Fita yana Fadin"Mun fita kasuwa.."Umma da Abida suka Bisu da adawo lafiya ita kuma kaka sai fada take da yar aikin Umma data kawo mata Maltina ta balbaleta da fada wai taga tana shan wannan Abun mai kama da Jini ne..?maza ta maida ta kawo mata Lemon nan mai kama da Madara,Abida da Umma mai zasuyi in ba dariya ba Diramar kaka sai ita.

A kasuwa Abba da Ahmed suka Wuni suna Duba shagunan Daya bayan Daya baban Iman na musu karin bayani,Alhaji yama sauran yaransa na cikin kasuwa alheri suna ta godiya shiyasa suke son Shigowarsa, kasuwa daganan sai ka Suka karisa kasuwar wambai shima Abba yaga yanayin aikin nasu,sai da sukayi sallar la"sar acikin kasuwar kana suka koma gida,Ahmed da Abba suka zauna Falon baki suka ci abinci suna Cigaba da Hira domin Abba bashi da wani amintattace irin Ahmed baya Surukanta dashi sam Duk da Ahmed din yana da tsatsan ladabi koda yaushe zaka ga kansa na kasa in Abba na mgana sai bayan mangariba yabar Gidan Umma ya tafi gidan kawu maude domin koda suka Dawo gida da Abba Abida da kaka sun riga sun tafi chan sai yaje ya samesu nan ma basu tafi ba sai bayan isha"i Anty Naja"atu ta matsa musu sai da sukaci abinci kafin su tafi kaka kuwa kamar karta tafi ta samu kawu maude sai hira suke sai da Ahmed ya gaji yace Abida tatashi su tafi kana kaka tatashi ta Hakuran da Labaran nata har Waje suka rakasu suna musu fatan zuwa gida lafiya,yau agida yayi sallar isha",i bayan sun koma dukkansu akoshe suke basu da yunwa kayan barci kadai suka saka suka nemi makwanci Ahmed jiya bai samu barci ba ammh yau da wuri barci ya kwasheshi Abida ta Rufamai Blanket tana Shafa kanshi Cikin Tsausayawa da kauna mai tsanani.

**

Rashin zuwanshi office jiya yasa yau ya Fita da Wuri Breafsat dinshi ma dashi yatafi bai tsaya yaci ba saboda kada ya makara kai tsaye yau cikin mall din ya Shiga kowani bangare sai da ya leka yaga yanayin aikin yadda yake Tafiya nan ya bata Lokacinsa kafin ya koma cikin Office dinsa ya karya yana sakama Abida albarka domin in har ya zauna da yunwa shi yaso Ammh Abida gabadaya kokarinta akansa Shiyasa take da wani matsayi acikin Ransa Mganar samiha kuma ya tattarata ya watsar ya Cigaba da abunda ke gabansa.

Karfe shida kamar ko yaushe ya koma Gida ya iske Anty Najwa tazo ita da yaranta,nan ya zauna suka gaisa suka taba hira ya tambayeta megidanta tace yana gaisheshi kila yazo ya daukesu Tunda shi ya kaisu gidan Umma ya Ijiye ya wuce wajen aikin Shine daga gidan Umma Direba ya kawosu gidan Abida,Bedroom dinsu ya shiga yayi wanka ya Sauya kaya zuwa jallabiya mai Ruwan toka kiran sallar mangariba ya fitar dashi dama already ya dauro alwalarsa Tun daga Toilet,bai Dawo gidan ba sai da akayi sallar Isha"i yana dawowa ya iske mijin Anty Najwa yazo zasu tafi nan ya tsaya suka gaisa kafin su Wuce dashi da Abida har motarsu ta Fice suna Daga musu hannu.

Washegari bayan ya tashi daga Office yaso ya biya yaga Abba,ammh sai ya kirasa awaya bai Dauka ba sai ya kira Umma tacemai ai Abba baya gidanta yana Gidan Samiha sai da gabansa ya Fadi da sauri yama Umma sallama bai kara kiran Abba ba,ya Tarkata kayansa ya koma gida Abba kuma bai kirasa ba sai washegari suka tattauna Abunda zasu tattauna suka rabu batare da Abba yace yazo state road ba su tattauna Ahmed yaji Dadin haka Domin yana fatan kada Allah ya hadasa da Samiha,domin yana Tsoron Sharrinta da kaidinta.

*****

Bayan sati daya da zuwan Samiha Office din Ahmed tuni ya Tattara fargaba ya watsar yamayi zaton Samihar ta koma gombe ne baisan tanan nan Tana Shiri akanshi bai sani ba,da wuri yau ya tashi daga office dinsa ya Shiga cikin kasuwa wajen Baban Iman chan yayi sallar mangariba kafin suyi sallama yana Cikin Driving zai koma gida Wayar Abida ta shigomai tana tambayanshi yana ina ne..? Yace gashi bisa hanya nan take shaidamai dama Abba ne ya kirata awaya yace ta gayamai suje premiere hospital su duba Samiha anyi addmiting dinta yau da Safe bata da lafiya yakira wayarsa bai sameshi ba.

Kadan ya Rage Ahmed bai bugama wani mai mashin dake gabansa saboda Yadda mganar Abida ta daki kansa da Zuciyarsa,har Abida tagaji da Hello Hello ta yanke kiran baisani ba Dakyar ya iya Daidaita kansa da Hannunsa dake saman Sitiyari,Zufa kawai ke Ketomai kamar an watsamai Ruwa duk da Sanyin A.C dake cikin Motar baya Shigansa Tuni Kwakwalwarsa ta bashi wani makircin Samiha ta kullah kuma Innalillahi Allah gani gareka allah ka tsareni da jin kunyar Duniya data Lahira,har ya isa gida baya cikin Natsuwarsa ya dade acikin motarsa bayan Ghali ya Budemai get ya Shigo sai da yadan Daidaita kansa kana ya Bude mota ya Fito yana Rangaji kansa ya Dafe yana sakin Numfashi,Wayarsa ya Dauko Karamar Jakar system dinsa ma cikin Motar ya barta saboda bashi da Natsuwa.

Falon babu kowa ko Dakin Kaka daya saba shiga in ya Dawo yau bai Shiga ba,Direct Bedroom dinsu ya wuce yana Shiga yaji motsin Abida acikin Tiolet sai ya samu gefen gado ya zauna yana Sabule sawu cikin kafarsa da safa ya ijiye gefe yana maida Numfashi Tagumi kawai yayi Gabadaya kwakwalwarsa ta Tushe ya rasa mafita,Sai da yaji Abida ta yarfamai Ruwan wanka dake Diga ahannunta kana ya Dawo Cikin Hayyacinsa Ajiyar zuciya ya Sauke yana kallonta da Idanuwansa da suka Fara Rinewa  saboda damuwa Mirmishin karfin Hali ya saki yana Fadin"Na shigo kina wanka Sweatheart.."

Baki ta tura tana Fadin"Umh..Abba toh ya kira yana ta Fada wai sai ya sabamana in bamu zo mun Duba yar gold  dinsa ba yanzuma Umma ta kirani tace in ka dawo muyi kokari muje mu Duba kilama Ita ya kira ya balbale da Fada na rasa mai wannan matar take ba Abba ne yafi ganinta da kima Fiye da Umma.."Abida ta Fada tana isa gaban madubin Dakin Ahmed jinta kawai yakeyi bai ma Sauraranta Tunaninshi na wani wajena Dabam,Har Abida tagama Mitan tatayi Shuru bai tankata ba,da kanta ta gaji tayi Shuru kuma bata damu ba sanin Halin Miskilancin Ahmed har ta Shirya yana nan Zaune yarasa mafita Sai da tazo kusa dashi ta Zauna tana fadin"Hubby wai ni don Allah meke damunka ne..? Tafada tana Leka Fuskarsa baima san tayi ba sai da tamai tafi acikin kunnansa kana ya Dawo Cikin hayyacinsa afirgice ya kalleta yana Sauke Numfashi,Har ta Shirya cikin Doguwar Rigar wata Atmafa mai klan green da Fari,taci daurinta na Zahra Buhari,ajiyar zuciya ya Sauke yana Fadin"Wani lissafi nan kikaga inayi shiyasa ban jiki ba..Bari na shiga wanka in na Fito bayan munyi sallah sai mu tafi ko..? Yafada yana mikewa Da kallo ta bishi tana karantarsa Shikuma ganin haka sai ya Shafa kumatunta yana Fadin"Cute angle...kinyi kyau matata.."Mirmishi ta sakarmai batayi mgana ba ya Fada wanka bayan ya Tube kayansa yana Shiga ta mike tatattara kayan ta Ninke ta saka cikin Wardrope wajen da suke tara kayan wankinsu kafin mai wanki yazo ya karba kafin ya Fito taFito mai da wasu kayaan,Ita tataimaka mai yasha fa mai ta gyara maasa kansa dayaketa maiko,Ta taimakamai ya saka kayan data fitomai dashi kananan kayane kirar Armani Duk da Ahmed ba ma"abocin saka kananan kaya bane yafi son manyan kaya ammh kuma Abida tafi so ya saka kananan kaya Saboda sun fi mai kyau sun kuma fi fitomai da yarintarsa da Zatinsa,Dayaso yayi gaddama ammh Gudun karya zama cikin mazaje masu gwasale Matansa yasa ya sanya Wandon Kalan Dark Blue ne Rigar kuma blue ce ammh Ligt mai layi layin Fari tana da Dogon Hannu ta sanyamai bakin agogo na Fatar damisa,tagama Shiryashi kenan tana Zuzuta kyan dayayi harda Daukansu Hotuna aka kira sallar Isha"i nan ya fice ya barta itama tayi bayan ya dawo abinci kadai zasu ci su su tafi,haka ko akayi yana Dawowa sama sama,suka ci Abinci kaka dama dakinta Abida ta kaimata dama yau yan Tsiyan sun tashi tun safe take fada da Ahmed wai yaki barinta ta cigaba da sana"arta ya barta tana zaman banza ita bata saba dalalaci ba, Tun tana yarinyarta ta gaji neman na kanta,shikuma kaka mamaki take bashi hala ta Dauka kano kamar Jega ne in chan ta samu masu siya nan waya santa balle ya Siya kayanta Saboda Haushin hakama Da suka mata sallama zasu tafi Asibiti ko kallonsu batayi ba Ahmed kuwa yafi kowa jin Dadin Haka domin ko Kaka tace zataje bazai yarda yaje da ita ba Yasan Tabbas kaka taje taga Samiha gaban Mutane zata tona Mishi Asiri Abunda bazai taba so wani yaji Labarin yataba sanin Samiha ba

Kafin su isa asibitin sai da suka tsaya Bisa hanya suka Siya kayan Dubawa su lemo dasu kankana da ayaba kana suka karisa Abba sukama waya yagayamusu sunan Dakin Ahmed da Abida suka jera kowanne hannayensu rike da manyan Ledoji Tana Aminity ne,Abida ce agaba ta Tura kofar dakin ta Shiga Ahmed na binta abaya,Da Samiha suka fara cin karo dayake gadon na kallon Kofar Shigowa ne Tana kwance an saka mata Drip tayi wani laushi da ita,Abba na gefenta yana Rike da Hannunta yana lallashinta tatashi tasha ko Ruwan tea ne,Sai daya daga cikin yan aikinta dake gefe tana Hado tea din,Abida ta karisa bayan tayi sallama su Abba sun amsa Ahmed kuwa bayan Abida ya Dinga lebewa bayaso su hada ido da Samiha ammh hakan bai samu ba Domin Abida ta kauce bayan ta duka ta gaida Abba ta ijiye ledan Hannunta ta karisa tana cema Samiha"ya jiki..? Cikin Siririyar murya ta amsa da Sauki Abida tace Allah kara lafiya Ahmed kuwa dakyar ya karisa Shigowa dakin yana Sadda kansa kasa Shima Dukawa yayi yana gaida Abba ya amsamai cikin Sakin Fuska ammh daka ganshi zaka Fahimci yana cikin Damuwa kin Dagowa Ahmed yayi bayan ya ijiye ledan Hannunsa Saboda yana jin Idanuwan Samiha suna kara kaina akansa.

Itakuwa Samiha Tunda suka Shigo take nacin kallon Ahmed tana so su hada ido ammh yaki bata dama ko Damuwa ma Mutanen dake dakin batayi ba Ta maida hankalinta da kallonta kacokan kam Ahmed wanda ya mike dakyar yana Fadin"Ya karfin Jiki hajiya..?

Yafada yana kallon Gefe,Mirmishi ta saki tayi kamar batajishi ba ya kara fadi nan ma tayi mai banza Sai da Abba yace"Gimbiya bakiji Ahmed na miki sannu bane.?"lum da ido tayi kafin tace"Au dama dani yake..?Na dauka da gefe yake mgana naga yana gaisheni yana kallon Hagunsa.."Tafada da muryan irin Ciwon nan Abida dake gefe ta tabe baki tana fadin"Haba dai kema dai da wani abu kike..Akwai wani mara lafiya acikin dakin nan ne bayan ke..? Tunda kikaji yana mgana kema kinsan dake yake.."Tafada kai tsaye tana Hararanta Mirmishi Samiha tayi kafin tace"Oh Srry na manta Ashe masu miji na kusa kuyi hakuri Kai mijin Abida jiki na da Sauki nagode.."Tafada tana kallon Ahmed wanda ya Dago da Niyyar kallon Abida suka hado ido Gira ta kannemai tana mai karamar Dariya Saurin sadda kai yayi yana Salati a Cikin ransa Abba kuwa fada yahau Abida dashi yana fadin"ina ruwanki dake take mgana..? Abida haryanzu baki daina Rashin kunya ba ko..? Zan sabamiki wlh maza ki bata hakuri.."Abida na kunkuni tace kiyi hakuri Mirmishin Mugunta samiha tayi kafin tace"Ah karki damu ya wuce.."Abba kuwa Ahmed ya kallah dake tsaye yana fadin"Ahmed ka zauna mana.."Da sauri yace"A"a Abba yanzu zamu wuce.."Kai ya jinjina mai bai samu Zarafin mgana ba Anty Najwa da mijinta sukayi sallama suka Shigo dakin,sai Ahmed ya matsa gefe suka karisa suna gaisheta suma da Ledoji niki niki Abba yaji dadi sai washe baki yake yana fadin" gimbiya ciwonki yayi albarka ya"yanki da Surukanki sun zo gaisheki" yafada yana kallonta wani mele baki kawai tayi batayi mgana ba Abida da Anty Najwa suka koma gefe suna mgana Ahmed da mijin Anty Najwa suna gaisawa Abba kuma yana lallaban Samiha datasha Tea din haka take wani narkewa yana bata tea din Abun zakk kunya wlh Mijin Anty Najwa kiransa akayi awaya Ya fita zuwa waje Abba kuma ya Shiga Toilet wanke Hannayensa da Ruwan madara ya bata sa Samiha ta fakaici idon Mutane ta Zura kafarta guda ta Zunguri Ahmed da Sauri ya Dago yana Kallonta Hannu ta dagamai kafin ta Manne mai ido daya a Hankali ta Furta" ya mganar mu..? Ina nan fa akan bakana.."

Tafada tana wani mai Shu"umin kallo mai cike da wani ma"ana Abida da suke mgana da Anty Najwa taga kallon da Samiha take ma Ahmed shi kuma yayi Saurin Kauda kai yana Hade rai Galala Abida tayi tana kallonta bata samu zarafin mgana ba Abba ya Fito da Sauri Ahmed yace"Abba zamu wuce..Allah kara lafiya.."
Abba yace"Shikenan Ahmed..Allah ya kiyaye hanya.." 

Bai tsaya wani Sauraran Kallon da Samiha kemai ba ya fice yana Jinta tana ma  Abida godiya ita kanta fuska ba Walwala ta musu sallama Anty najwa ma basu tsaya ba tare suka Fito da Abida ganin dare yayi ne yasa basu tsaya wata hira ba sukayi sallama kowacce ta Shiga motar mijinta suka Tafi gida.

Har suka kai gida Tsakanin Ahmed da Abida ba wanda yama wani mgana Ahmed zuciyarsa bata tare da Abida sam yana chan yana Tunanin wani irin mataki yakamata ya Dauka game da Amaryar Abba samiha,Ita kuwa Abida tunaninta meya hada Ahmed da Samiha datakemai wannan kallo kuma ba kallon Tsana bane wani kallo ne mai cike da ma"anoni masu yawa bata samu zarafin mgana ba sai bayan sunyi shirin kwanciya sun kwanta Ahmed yayi Shuru kawai yana Tunani Abida ta kallesa tana fadin"Hubby niko in tambayeka mana..?

Bai juyo ya kalleta ba yace"Ina jinki.."Tajuyo tana kallon cikin idanuwamsa tace"Meke tsakaninka da amaryan Abba ne wai.. ? Dawani Firgici Ahmed ya kalli Abida gabansa na fadi cikin Rawan murya yace"Ban ga..ne..ba..?
Numfashi Abida ta sauke kafin tace"Naga tamaka wani kallo ne kuma kallon bana tsana bane..Wani kallo ne wanda Zuciyata bata yarda dashi ba."Tafada tana kallon Ahmed Saurin Sakin Numfashi yayi kafin yace"Ohon mata bansani ba..Ni babu komai tsakani da ita wannan shine ganina na biyu da ita.."Daga haka kawai ya gyara kwanciya Abida zatayi mgana kenan ya saka dan yatsansa Bisa bakinta yana Fadin"Shiii...Oya Sleep.."Mirmishi ta saki kafin ta dora kanta saman kirjinsa tana fadin"gut nite hubby..." rumgumeta yayi yana sauke Boyayyiyar ajiyar zuciya yana Fadin"Nite..Sweeheart.."yafada yana Jin Faduwar gabansa ya Tsananta Tunda Abida tafara Fahimtar wani abu dole sai ya kara kiyayewa in ba Haka ba ya Shiga matsala Domin Abida Smart girl ne tana da Saurin karantar mutum da yanayin dayake ciki.




*Aisha alto.*
*Janafty*