SILAR HALLACI

Page 12

by @jamilaumarjanafty

*SILAR  HALLACI.*

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

        *🅿️12*


   Har Ahmed yaje Office bai yarda ya buɗe wayarsa ba saboda bayaso Samiha ta sake damunsa. Yaje Office kenan bai daɗe ba ya gama cin abincin daya taho dashi daga gida ya samu kira daga Baban Iman ta wayar office ɗin saboda ya kira wayarsa ya jita a kashe yace masa ya taho Wambai store an kawo kaya yazo ya duba, ya fito a gurguje ya shiga motarsa ya tafi kasuwar Kwari ya ɗauki Baban Iman ɗin acan suka tafi Wambai store dake layin Ganduje, suka je suka duba an kawo kayayyaki suka dudduba abubuwa. Bayan sun duba basu bar gurin ba sai da sukayi sallar Azhar, kafin su rabu da juna sai da suka biya restaurant suka ci abinci daga nan shi Baban Iman ya tsaya a kasuwar Kwari shi kuma Ahmed ya koma Office ɗinsa.

Bayan ya koma ne ya kunna wayarsa yana kunna wayar da Saƙon Samiha ya fara cin karo inda take cewa.

_Ahmed taurin kai zaka nuna min...? Toh shikenan banason inyi maka abunda zaka dawo ka tsaneni daga baya ne, ina so in bika a hankali amma tunda har ka nuna haka muje zuwa..._

Yana ganin text ɗin ya gama karantawa ya zauna akan kujera yana tunanin Wai me yarinyar nan ta maidashi ne..? Ji yadda take walagigi dashi da rayuwarsa..? Amma yasan yadda zaiyi mata, nan take kawai yaji wata jarumta tazo masa zuciyarsa ta dake yayi making ya fara rubuta mata reply da cewa.

_Samiha inaso in baki shawara ko kuma ince magana dake ta ƙarshe da zanyi karki ƙara kiran numbern wayata kuma karki ƙara turo min saƙo. Idan kuma haka ta ƙara faruwa zan saɓa miki, na gaya miki abunda kike nema bazaki taɓa samu ba, ana dole ne! Karki ƙara kirana kuma karki ƙara nemana, Ni dake bamu da wata alaƙa wanda ya wuce alaƙar zumunci.._

Yana gama tura mata daga nan ya goge numbernta ya goge saƙon da tayi masa da wanda ya tura mata.

Ita kuma a dai-dai lokacin da taga saƙon tana zaune akan kujerar madubi ɗaure da tawul ta fito daga wanka kenan tana kwalliya taga saƙon Ahmed ya shigo cikin wayarta. Data buɗe ta karanta sai da taji ƙwalla sun ciko idonta tace Wai yau itace Ahmed ɗinta yake mata wannan wulaƙancin..? Ahmed ɗinta dai wanda ta gama ƙwallafa rai da zuciyarta da komai nata akansa shine yake mata wannan wulaƙancin...? Toh shikenan mu zuba dani da kai Ahmed. Kasancewar dama Abba ba'a gidanta yake ba ranar a gidan Umma yake kawai tana gama kwalliyarta ta shirya cikin wani rantsattsen leshinta mai kyau da tsada wanda aka yiwa ɗinkin riga da siket tayi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu ta fito zata tafi Office gurin Ahmed domin taje ta sameshi, saboda ita maganar gaskiya bazata taɓa iya haƙuri ta fita daga harkarsa ba kamar yadda yakeso ba. Ta gama shiryawa kenan ta fito riƙe da makullin motarta a hannu, sai ta samu waya daga Hajiya Hansa'u inda take sanar mata Hajiya Mero bata da lafiya hawan jininta ya tashi har an kwantar da ita a asibiti. Take hankalinta ya tashi nan da nan ta kira wayar Abba ta gaya mai tace tana so yanzu yanzun nan don Allah zata tafi Jega. Yace toh shikenan bari yasa a nema mata flight sai ta tafi, nan da nan yayi waya da wani abokinsa aka neman mata jirgin da zata samu ta hau yayi waya akace masa akwai jirgin da zai tashi zuwa Birnin Kebbi nan direba ya ɗauketa zuwa airport tana zuwa ba daɗewa jirginsu ya tashi suka ɗaga zuwa Kebbi. Daga Kebbi suna sauka a airport ta ɗauki tashan taxi ya kaita Jega, koda taje ta iske Hajiya Mero a Asibiti an kwantar da ita amma jikin da sauƙi. Wannan dalilin yasa bata samu daman zuwa gurin Ahmed ba a wannan rana kamar yadda ta Ƙudurawa a ranta.

Shi kuma Ahmed tunda ya tura mata saƙon nan yaji ta shiru sai yayi tunanin cewa gargaɗin da yayi mata ya shige ta ne har ya ɗan saki jikinsa ya ga har an kwana an wuni Samiha bata ƙara kiransa ba, kuma bai ji wata magana daga gareta ba, kawai shiyasa ya saki jikinsa yake tunanin cewa barazanan da yayi mata na karta ƙara kiransa ƙila taji, kawai sai bai ƙara wannan tunanin ba, saboda haka ya maida komai ba komai ba ya cigaba da harkar rayuwarsa, har ita Abida ma taga ya ɗan saki tana ta jin daɗi.

Ashe ita kuma Samiha tana can Jega tana ƙara kula da mahaifiyarta, sai data kwana bakwai a asibitin kafin aka sallamota suka dawo gida ta cigaba da kula da ita yayyenta na nesa dana kusa suna ta zuwa dubata nan suka ce ita Samihan ta ɗan ƙara zama da Hajiyan mana ta samu sauƙi tukunna sai ta koma. Haka kuwa akayi Samiha ta zauna ta cigaba da kula da mahaifiyarta amma gaba ɗaya hankali da tunaninta kacokan suna kan taya zata ɓullowa Ahmed, ya zama dole idan ta dawo ta fito mai ta bayan gida ta yadda zai gane cewa a shirye take.

Samiha dai bata samu dawowa ba sai da tayi gurin sati biyu, lokacin shi Ahmed ma ya riga ya gama mantawa da ita kwata kwata, don shi azatonsa ma kota koma Gombe ne, don shi baiji ko alama Abba yayi maganar ba ko Abida baiji tayi masa maganar Samihan ba, sai yake ta addu'an cewa Allah yasa ta tattara kayanta ta koma Gombe ne.

Bayan sati biyu ne bayan Samiha ta dawo ta sauka a Malam Aminu Kano airport ta kira Abba tace masa gashi nan ta sauka don Allah ya turo direbanta yazo ya ɗauketa, yayi ta kiran wayar direban nata amma bai samesa ba, shi kuma gashi yana gida, kuma bai saba yin driving da kansa ba, ko'ina zashi dama direbansa ne ke kaisa, gashi direban Hajiya Rabi shima ta aikesa gidan Najwa, so babu direban da zaije ɗaukarta, kawai sai yace bari ya kira Ahmed. Gurin ƙarfe 4pm bayan sallar La'asar Dai-dai lokacin Ahmed yana gab da shirin tashi ma daga Office yama shiga cikin Mall ɗin ne ɓangaran inda suke saida kayan ado da kwalliyar mata, kasancewar dama babban mall ne ba abunda ba'a saidawa, akwai ɓangaren lesuna, ɓangaren takalma, ɓangaren kayan gado, da komi da komai, har da ɓangaren yadikan maza da ɓangaren turaruka. Sai ga wayar Abba ya shigo masa inda yake ce masa don Allah yana so yaje filin jirgin saman Malam Aminu Kano ya ɗauko masa Samiha ta dawo daga Jega ya kawota gida, shi yanzu yana gidan Hajiya Rabi ne, kuma direba baya nan ta aikesa babu wanda kuma zaije ya ɗaukota, don Allah yaje ya taho da ita. Ai Ahmed daya ji haka sai dayaji wata muguwar zufa ta wanke masa fuska, jin shiru yasa daga can ɓangaren Abba yace "Kaji ko Ahmed...?" Cikin fisgar magana yace "Shikenan naji Abba.." Ya faɗa yana sauke wayar daga kunnensa, ya rasa ina zai saka Ransa, ya fito cikin sassarfa daga cikin ma yaga ko akwai Sani ya bashi makullin motarsa yaje ya ɗaukota, amma ya duba bai gansa ba, yayi ƙoƙarin kiran manaja Baban Iman da sukayi waya yace masa wlh baya nan ya tafi Gwarzo gaida baban wani abokinsa yace baya kusa, Ahmed ya rasa mafita haka nan babu yadda zaiyi ya faɗa mota ya nufi Malam Aminu airport Kano ɗauko Samiha. Ita kuma Samiha tana filin jirgin gurin da matafiya suke ɗan zama kafin azo ɗaukarsu tana zaune, shi kuma lokacin ya ƙaraso ya faka motarsa a gurin amma ya kasa fitowa, gaba ɗaya jikinsa rawa yake ya rasa ta ina zai fara saboda bayason abunda duk zai haɗasa da ita, wata zuciyar tace "Haba Ahmed taya bazaka zama namiji ba ka daure ka dake ka nunawa Samiha kaima namiji ne inta kawo maka wargi kaja mata kunne..." Cikin ƙwarin gwiwa ya buɗe motar ya fito ya ƙaraso cikin filin jirgin, ita kuma tana zaune tana ta danne dannen waya, hangota da yayi yasa ya ƙarasa ya tsaya daga ɗan nesa kaɗan da ita da ƙyar yace "Am idan kin gama ki taso mu tafi.." Ta ɗago kai ta kallesa ta ƙara kallonsa tace "Ah Ahmed kaine..?" Yayi shiru bai mata magana ba ya juya, zuruf ta miƙe tana dariya cikin muryarta mai sanyi take cewa "Dama ai nasan bazaka guje min ba... Ai wannan karon haɗuwa ce ba mai rabuwa ba Ahmed..." Shi dai bai kulata ba ya wuce ya shiga mota ya zauna, itama da sauri ta ƙarasa ta buɗe gidan gaba ta shiga ta zauna tana kallonsa shiko kallonta baiyi ba ya ɗaura sit belt itama ta janyo ta ɗaura ya tada motar suka fice daga filin jirgin ta ƙura masa ido ƙirr bata ko son ƙiftawa tana ta kallonsa ta ɗan matsa kusa dashi sosai har kafaɗarsu tana gogan ta juna tana Zakuɗa kafaɗarsa, ya kauce da sauri ya janye jikinsa yana kaucewa ta ƙara matsoshi sosai yace "Samiha wai mene ne haka... Ke bazaki daraja aure ba? Karki manta fa kefa matar aure ce, akwai igiya uku akanki... Haba ya kamata ki dinga abu da tunani kamar baki da ilimin addini...! Ta juyo ta kallesa tace "Ai idan banda ilimin addini ai laifinka ne Ahmed, balle ma nasan cewa kasan inada dai-dai gwargwado, kayi ƙoƙari akaina nasassan wasu litattafan kuma na haddace ayoyi Alkur'ani daga gurinka, kosu kaɗai ai sun isa su mun amfani..." Ta faɗa tana dariya, shi kuma daga nan ya sha kunu bai kulata ba, ta ƙara kallonsa tace "Inata kiranka saika dinga kashe min waya baka ɗaukan wayata kwata kwata, kuma kaga saƙona ka karanta shine ka turo min da wata amsa... Uhm kalaman naka sun so su yi tasiri a raina amma fa basuyi ba Ahmed, wlh tallahi ba abunda zaka gaya min yasa ni kauce maka har ka sake kuɓuce min a karo na biyu, tunda yanzu na riga na gane cewa wannan matakin dana ɗauka bai maka ba, toh ni zan ɗauki matakin daya dace, idan kaji kirana kawai ka ɗaga! Wlh idan baka ɗaga ba zan zartar da duk hukuncin da yazo a cikin raina..." Ba tare da yayi aune ba ya taka wani uban burki ya tsaya yana kallonta a fusace ya fara faɗin "Me kika ɗauki kanki Samiha... Kiyi duk abunda zaki yi idan kin isa... Me kika isa kiyi min..? Ko kin ɗauka zanji tsoron barazanar da kike min ne in biyewa banzan tunaninki na ƙasƙantattun dabbobi...? Wai ma me kika ɗauki kanki ne Samiha...? Me kike ji dashi ne...? Me kuma kike taƙama dashi...? Me kike ɗaukan kanki...? Ke bazaki taɓa ɗaukan ƙaddara ba kenan a rayuwarki..? Toh ki sani Samiha tun daga ranar da mahaifinki ya aurar dake na cireki a raina na mantar da kaina komai daya shafeki, na kuma rufe babinki kwata kwata acikin rayuwata... Samiha na daɗe damantaki a cikin rayuwata, tuni na manta dana taɓa saninki a rayuwata haka komai daya danganceki na daɗe da gogeshi a zuciyata... Balle yanzu dana ganki a matsayin matar uban gidana kuma mahaifin matata wanda ya ɗaukeni tamkar ɗan daya haifa... Samiha idan mafarki kike gwara ki farka daga wannan mahaukacin barcin daya ɗaukeki Ahmed ɗin da kika sani da bashi bane yanzu... Wannan Ahmed ɗin ba Ahmed ɗinki bane, wannan Ahmed ne mijin Abida 'ƴar mijinki, saboda haka nake baki shawara daki ɗauke kanki a kansa ki Rungumi aurenki da mijinki ki zauna lafiya, idan kuma kina tunanin cewa Ahmed yana sonki ki gaggawar ƙaryata wannan gidahumar zuciyar taki da bata da tunani balle lissafi kije can kiyi rayuwarki nima ki barni da matata muyi rayuwarmu cikin salama... Haba daga dawowarki rayuwata komai na neman ya rincaɓe mana. Kullum bani da walwala matata bata da natsuwa komai nawa ya canza bana cikin kyakkyawan yanayi duk saboda ke... Toh ki sarara min! Ki kuma fita a harkata ki barni in zauna lafiya...! Idan kuma kina tunanin har yanzu ina sonki ne toh ki cire wannan bazan tunanin nason cikar burinki a kaina... Samiha bana sonki! Na daɗe da rufe babinki, na manta dake tun tuni balle yanzu dana sake haɗuwa dake a matsayin matar aure kuma matar auren ma ta ubangidana... Saboda haka inaso ki maza maza ki nisanta kanki dani ki kuma rufe shafina a rayuwarki kamar yadda na daɗe da rufe naki..." Ya ƙarasa faɗa cikin tsananin zafi da tsantsar takaicinta. Dariya kawai tayi tana kallonsa kafin ta dake tace "Haka kace Ahmed..?" Yace "Eh haka nace Samiha.." Ya faɗa lokaci ɗaya tare fizgar motar da gudun bala'i ya wuce, sai gidanta na state Road inda take zaune, yana zuwa yayi fakin ya tsaya ya ɗauke kansa, ta juya ta dubesa tace "Ahmed..." Bai juyo ya kalleta ba a fusace yace "Fitar min daga mota Samiha... Banason ganinki..." Tace "Zakayi nadaman korata da kayi, kuma zakayi nadaman maganganun daka gayan min, Ahmed kai nawa! Ahmed kai nawa ne! Kuma insha Allahu Bi'izinillahi koda zanyi sanadiyan rasa ran wani ne sai na mallakeka..." Tana gama faɗa haka kawai ta fita daga motar bayan ta shafa kumatunsa. Tana ficewa ya fizgi motarsa da gudu ya fice da gidan ta tsaya ta bishi da kallo tana sakin wani miskilin murmushi, kafin ta juya ta shige cikin gidan 'yan aikinta suka dinga mata sannu da zuwa, ta ƙarasa cikin Bedroom ɗinta dake saman bene ta ajiye jakarta da ɗan ƙaramin akwatinta, ta cire kayan jikinta ta ɗaura tawul ta faɗa toilet tana tunanin Ahmed, don duk waɗannan maganganun daya faɗa mata babu wanda ya shigeta balle tayi tunanin zasu ɓata mata rai har taji haushinsa ta fasa Ƙudirinta akansa... Yanzu ta riga ta gama gano ya zata ɓullowa Ahmed acikin wannan lamarin insha Allahu, don yanzu zuciyarta ta ƙeƙashe bata tsoron kowa yaji labarin ita dai kawai Ahmed ɗinta takeso ta mallaka aka karo na biyu, don yanzu bazata iya jure rashinsa ba. Balle ma dawowar nan da yayi gaba ɗaya tsohuwar sha'awarsa data ɓoye gaba ɗaya ta taso mata, tana buƙatar ɗa namiji a tare da ita, tana buƙatar namiji don ita ba dutse bace. Haka ta cigaba da wankanta tana saƙe saƙe a cikin zuciyarta.

Shi kuma Ahmed bayan ya fito daga state Road yana tafe kamar yayi ƙwallah haka yake tuƙi har ya kusa bugawa wani mai mota anata mai magana ya fito yana ta basu haƙuri yace su gafarcesa. Yana komawa cikin motarsa kiran Abba na shigowa wayarsa inda yake tambayarsa ya ɗaukota, cike da ladabi ya amsa masa da eh ya ɗaukota har ya ajiyeta a gida. Suna gama waya shima Abba daga can ya yiwa Hajiya Rabi sallama yana rawar jiki tace "Wai don Allah Alhaji meke damunka ne ina zaka ne kake wannan rawar jikin..?" Yace "Haba Hajiya ya kamata ki dinga yin uzuri, yau kwana nawa Samiha bata garin nan..? Don yau ta dawo kuma nace zanje sai kice ina rawar jiki..? Nidai ki daina min haka banaso..." Tace "Toh Allah ya kiyaye hanya.." Yace "Ameen..." Yasa hularsa ya fita, direba ya ɗaukesa ya kaishi can gidan Samiha. Shi kuma Ahmed ya ɗauki hanyar komawa gida, yana tafe a hanya wata zuciya tace "Ya kamata kayi ƙoƙarin danne damuwarka, idan ba haka ba Abida zata gane kana cikin damuwa kuma hakan ba daɗi bane tayi ta fahimtar cewa wani abu na damunka. Da wannan tunanin ya isa gida ya dinga basar da komai ya saki jikinsa ya nuna babu abunda ke damunsa, cike da jin daɗi Abida ta taimaka mai yayi wanka, bayan yayi wanka yazo ya shirya yasa ƙananan kaya, tajashi suka tafi Dinning inda zasuci abinci. Toh dama ita Kaka ba kullum take cin abinci ba in taga dama taci in taga dama wata rana tace bazata iya ba'a kai mata ɗaki, don haka Abida ta haɗa ta kai mata ɗaki. Bayan sun gama cin abincin Ahmed ya fita yaje yayi sallar Isha'i bayan ya dawo ya shiga ɗaki ya zauna Abida ta shigo tace "Hubby yauwa daman inaso na gaya maka ya kamata fa na fara zuwa awo, saboda kaga cikina ya wuce fa wata huɗu.." Yace "Toh shikenan. Yaushe zaki fara zuwa..?" Tace "Mu bari Monday, idan zaka fita aiki saika ajiye ni, sai inje inga likita.." Yace "Toh shikenan Allah ya kaimu..." 





*Janafty*
*Aisha Alto*