Chapter 13
*SILAR HALLACI.*
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
Contact Hijabs Corner by Janafty for all kind of Qualitative hijabs for women of class.
*** ZARIA/KADUNA Natio wide delivery.
*🅿️13*
"Ranar Monday tun Safe Abida Tagama Shirinta na zuwa Asibiti,bayan ta gama Taimakama Ahmed ya Shirya cikin Wani Farin yadi shara shara Wanda har farar vest din Jikinsa ana gani Aikin Jikin kayan baki ne Hakama Hulan kansa baka ce Agogon hannunsa baki ne na Fatar damisa haka Rufaffen Takalmin kafansa baki ne kallo Daya zaka ma Ahmed ka Fahimci yana cikin Walwalarsa ayau din sakamakon yana ji ajikinsa ya kawo karshen matsalansa da Samiha Tun Ranar dayayi mata kaca kaca bayan ya Daukota Daga Filin Jirgi bata kara Kiranshi ba,shiyasa sai Hankalinsa ya kwanta har yafara maida dan wuyan dayayi.
Tea da Buredi da Soyayyan Doya da kwai suka karya Dashi,Ahmed ke tsaye atsakiyar falon yana Jiran Fitowar Abida saboda shi zai kaita Asibitin kafin ya wuce office dinsa,Agogon Fatan dake hannunsa yake Kallo har 8 ta gota ammh Abida na ciki taki Fitowa Daga komawa Dauko Waya data manto ta aciki Kaka ta Fito Daga Dakinta tana Kokarin gyara Daurin zanin Atamfar dake Jikinta Ta kalli Ahmed tana Fadin"Kai kuma lafiyanka kuwa kayi tsaye kikam kamar wani Soja ko Dan sanda..?
Tafada tana Kokarin zama Bisa Daya Daga cikin Kujerun Falon,Ahmed ya kalli Kaka yana Fadin"Kaka ina kwana..? Yanzu nake Shirin na shiga mu gaisa kafin na wuce wajen aiki.."Tabe baki Kaka Tayi tana Fadin"Bawani nan Ahmadu nida kake gaba dani acikin Gidanan..!? Ido ya zaro yana kallon Kaka kafin yace"Ni Kaka gaba fa kikace..? Wani irin Gaba kuma ana Zaune kalau Hajiya Kaka..?
Baki ta Mele kafin tace'Eh koma wace iri ce kafini sani karyan Iskanci kakeyi Ahmadu ina gidanan ammh yaushe Rabon da kamin mgana ko Shigowa kayi na maka Mgana banza Dani kake Cikin Raina dai nace Oho dai Bani ka yi ma Banza ba Sama"ila kamawa ko Uwarka Zaliha.."Baki Ahmed ya kama kafin yace"Oh my God Tsakani ga Allah Kaka kina da matsala gagaruma wlh.."Yafada yana kallonta cikin Dan Tsuke Fuska Lokaci Daya kuma yana kara Duba agogonsa kafin ya waiga yana Kiran Sunan Abida.."Sweetheart kina ina ne..? Kiyi Sauri Allah na makara.."Daga cikin Daki Abida ta amsa tana Fitowa"Gani nan Hubby Marata ce ta Daure na Shiga Tiolet.."Tafada Daidai Lokacin data Fito tana gyara zaman mayafin dake kanta Kaka na Zaune tana kallonsu Kafin ta Daga Murya tana Fadin"Nice keda Gagaruman mtsala ko Ahmadu..?
Nunfashi ya sauke kafin ya waigo yana Kallon Kaka cikin Tsukewar Gira yace"Eh wlh Kaka..Haka kurum in ba mtsala ba kiyi ta faman Kiran sunan iyayena Alhalin kina sane sun rigamu gidan gaskiya Abun fa na kona min Rai bana nuna miki ne kawai.."Karamin Tsaki Kaka taja kafin tace"Nice gidan Haya ko Tsohuwar Mota karewar mtsala kenan kaji ko.."Tafada tana wani Gyara baki cikin alamun tana cike da Ahmed din ko kara kallonta baiyi ba ya yi gaba yana Fadin"Muje kawai.."Abida tabi bayanshi tana Fadin"Kaka mun tafi sai na Dawo...".
Galala Kaka tayi tana kallonsu kafin ta yunkura ta mike tana Fadin"Kai kai...Ku tsaya nan nace bangane muku bane..Ina zaku je ne dukkanku haka da Sassafe..?
Abida ce ta tsaya Ahmed Shi Har ya Fice Cikin Haushin kaka,Abida ce ta tsaya tana Fadin"La Kaka kin Manta jiya na gaya miki yau zan Fara zuwa awo..? kaka bata saki Fuska ba tace"Eh anyi haka.."Abida tacigaba da Fadin"Toh Shine Hubby zai kai ni kafin ya wuce wajen aikin Allahbarshi in nagama Abunda zanyi sai na hawo Napep na dawo gida Kaka.."
Wani irin Kallo Kaka ta Wurgama Abida kafin tace"Lalle kun isa daga ke har Mara mutumcin Mijinki Ahmadu..Wato zaku fice Abunku ga Yar aiki ko megadi da kuka bari ta muku gadin gida ko..? Abida ta sanyaya Murya tana Fadin"Ba haka bane Kaka ba Dadewa zanyi ba ina zuwa aka bude Fayel suka bani Ranar da zan Dawo Allah bazan tsaya ko"ina ba zan dawo gida.."Juyawa kawai Kaka tayi tana Fadin"Ku kuka sani koma Yaushe zaki dawo bai Shafe ne ba ,Nidai Abunda na sani Wlh kafata kafarku ban yarda ku Fice ku barni gadin gida ba Atoh.."Tafada tana Shigewa Dakinta kai kawai Abida ta Dafe Lokacin Daya kuma ga Hon din Ahmed ya isheta da Sauri ta Bude Kofar Falon ta Fice Zuwa Haraban Gidan.
Ahmed har ya Shiga Mota ya Daura Set belt,yana jiran Abida,sai gata ta Fito Cikin Sanyin Jiki ta leka ta Window mai zaman banza,Ahmed ya kalleta yana Fadin"Kina sane da cewa na makara fa.?ammh kina sane ina Jiranki ne kika zauna kina wani Shirme.."yafada yana Kokarin Tada Motar mirmishi Abida tayi kafin tace"A"a Kaka ce tace ba mai maida ita mai gadi kafarmu kafarta.."Baki kawai ya Tabe baiyi mgana ba Har Kaka ta Fito tana mita ita kadai Abida ta Bude mata gidan Baya ta Shiga Ita kuma ta koma ta bude gidan Gaba Shashin mai zaman banza ta Zauna Lokaci daya Ahmed yama motar key ya Zuba Hon Ghali Megadi ya Bude musu get suka Sulala waje yana Daga musu Hannu.
Har Suka isa Filin Haraban Asibitin Mallam Aminu kano Ahmed bai yadda ya sakama Abida magana kan lallashin kaka Datakeyi ba, sai Masifa take tana Fadin Wai Ahmed ya Rainata Tunda ta Shigo cikin Motarsa yake bata rai jin hakama sai yasa ya kara Hade Fuska ba Fara"a Abida nata mintsilinshi yayi mata Banza,Tare dashi suka Shiga Har cikin Asibitin Daya ke akwai wata Nurse kawar Anty Najwa tana aiki awajen ita Najwa tabama Abida nombarta kan in Zataje Asibitin tanemeta Tun Jiya ta Kirata ta Shaida mata Shine tace in ta Shigo Asibitin ta Kirata Suna shiga Babban Falon Abida ta ma Sister Suwaiba waya tace gatanan Zuwa Kaka kuwa Kalle kalle kawai take tana Rike baki Cikin Mamaki take cema Abida.."ke ya'nan ba"ana cewa Asibitin wajen zaman masu ciwo bane..? Abida tace"Kwarai kaka in ba Lalura ba mai zai kawo mutum Asibiti haka kurum.."..
Kaka tace"Tabdijam kinji ki da wata mgana..Ai sai mutum yazo nan ya tare ya samu gida kinga haduwar ko"ina ko gidan Ahmadu Albarka.."Yana jinta yayi kamar baiji ba sai gefe daya koma ya Fito da wayarsa yana Latsawa Abida kuma Dariya tayi tana Fadin"Kaka kenan.."Tafada tana kallon Matan dake Zaune awajen suna jiran ganin Likita basu Dade ba sai ga Sister Suwaiba ta kariso tana ganin Abida ta ganeta Domin Suna yanayi da Kawarta Najwa,Gaisawa suka farayi Cikin Sakin Fuska Da Sauri Abida tanuna Kaka tana fadin"Anty Suwaiba Ga kaka itace kakar Mijina Shima gashi chan tare dashi muke.."Tafada tana nuna Ahmed Dake bayansu yana Latsa wayarsa Mirmishi Sister Suwaiba tayi kafin ta Ramkwafa tana gaishe da Kaka ita kuma ta amsa tana Fadin'Ikon Allah kace asibitin ma akwai masu Fidda ran rayuwa har sun fara linkama kansu Likafinin Mutuwa..'
Abida da Sister Suwaiba suka kalli Juna Kafin Abida ta saki yar Dariya tana kallon Sister Suwaiba ganin yadda tayi saurin Cewa tayi.."La Kaka ba irin wanda kike Tunani bane..Wannan Fararen kaya na aikinsu ne zaki ga Likitocinsu da Riga Fara suma na Yanayin aikinsu ne kinsan Abun Likitoci komai cikin Tsari ne.."Washe baki Kaka tayi tana fadin"Au hakane..Ba Shakka.."Take fada tana kara Kure Sister Suwaiban da kallo wacce ta dan kauda kai tana yar dariya Abida ce ta yafito Ahmed da Hannu ya kariso suka gaisa da Sister Suwaiba,nan tace Abida ta zauna ta jirata bari ta Siyan mata kati sai ta kai wajen Likitan da zata Dubata Dayake wannan ne karonta na Farko data Taba zuwa Babban Asibitin Mallam Aminu kano sunfi zuwa Asibitin private na cikin gari,Ganin haka yasa Ahmed yamusu sallama Abida ta rakasa Har waje ya Tafi bayan sun Rabu kan in sungama Takirashi ta gayamai yazo ya maidasu gida ita da kaka wacce suka baro acikin Asibitin sai bama idanuwanta abinci takeyi,tana ayyana Haduwar Asibitin da kuma asibitin India da aka mata aikin Ido ita kadai kawai take Zencen Zucci.
Sai After 9 ya isa Wambai Shopping mall,Ya makara Sosai Office din accounter yafara isa sukayi mgana kafin ya wuce Office dinsa Masinjansa na gaisheshi ya amsa Cikin Sakin Fuska yana Shiga Cikin Office din zama kawai yayi ya Fito da System Dinsa ya kunnata Saboda akwai sakon da yanzu Baban Iman yace ya Duba ya Turamai ta Email kafin ya kariso,ya fara Dubawa kenan yaji kishin Ruwa sai ya Tashi ya Isa ga karamin Firizan dake cikin Office din nashi ya Bude ya Dauko Goran Swan Water guda Daya ya Bude ya kafa kai sai da yasha kusan Rabi kana ya Rufe ya maida ciki ya Rufe ya koma ya Zauna kenan Telephone tayi kara yana Dagawa Masinja yake shaidamai ga Baban Iman yana son ganinsa kai Tsaye yace mai ya Shigo bai gama kife wayar ba Nura baban Iman ya Shigo,zama yayi kan kujeran datake kallo na Ahmed Lokaci daya sukayi Musabaha da Juna suna Tambayan kwanan iyalansu Baban Iman yace"Angon Abida ina Abida da kuma kaka.....?
Ahmed na Dariya yace"Kai dai baka Rabo da Zolaya koma mezakace angon Abida nake ba Suna bane..While suna lafiya yanzu na barosu a asibitin Aminu kano ita da kaka.."Da Sauri Baban Iman yace"Asibiti kuma...? Lafiya kuwa..?.."Kai Ahmed ya gyada kafin yace"Eh ammh ba wata mtsala bane zata Fara awo ne.."Dariya Baban Iman yana Fadin"Mutumina Congart..Zaka Tashi Daga Angon Abida zaka koma baban Yara kenan.."yafada yana bashi hannu suka tafa dariya Ahmed yayi yana Fadin"Baka da dama Nura Allah kuwa.."nan suka cigaba da Hiransu kafin su koma Mganar kasuwanci wasu Takardu baban Iman ya Fito dasu daga cikin Aljihu ya Tura ma Ahmed gabansa yana Fadin"Duba ka gani Duk da na Tura maka wasu bayanan ta Emai dinka ammh yakamata ka Duba wadanan First.."Karba Ahmed yayi ya Bude yana Dubawa cikin Lokaci ya Dago yana Fadin"Kai Nura naga Riba wannan Month din almost 3m nagani Daga duka Shagunanmu na kasuwar kwari Data wambai.."Baban Iman ya murmusa yana fadin"Yap..Kokarinka ne Ahmed..gaskiya kasan Harkan kasuwanci sosai Tun zuwanka kan kasuwanci Abba awata ba"a taba samun Riba kasa da 2m ba,na Jinjina maka.."Yafada yana Nuna mai babban yatsa alamun Jinjina Cike da Farinciki Ahmed yace"Ban yarda Dakai ba Nura..Wannan kokarinka ne fa kai ne kake kula da Duka Shagunan Abba na kasuwar Kwari Data wambai kuma ka Hada da kula da Sauran Store dinmu..Ni nawa kawai Shawara ne da kuma Taimako ammh mganar gaskiya u do a god job Wlh..Allah ya kara Arziki da Wadata kawai Mutumina.."yafada yana Dariya Baban Iman shima Dariyan yake yana fadin"Ameen tare dani dakai da Duk duka ma"aikatan da muke aiki dasu.."Ahmed bai samu Zarafin mgana ba Kamshin Turaran Samiha yayi mishi sallama Lokaci daya kuma da Shigowarta Office din Masinja na Biye da ita yana Fadin"Haba Hajiya taya zaki Dinga Shigarma Mutane Office ba Neman izinin haka fa kikayi Ranar da kika zo..'yafada cikin bacin Rai...
Samiha Dake sanye cikin Wata Doguwar Rigar yadi mai kalan maroun Fitted ce Rigar kuma ta kama ta Fitar mata da Duka Shape din jikinta sai ta yane kanta da karamin Vail Fari Hakama karamar jakar dake Hannunta fara sai Takalmin kafanta mai Tudu,Fuskarta tana kyallin Makeup wanda yagama yima Fuskarta kyau da Tsari,key din Motarta ta kada Lokaci daya tana Sakin karan Cimgam din bakinta tana kallon Fuskar Masinjan daya kusa Haihuwanta Domin tana cike da Furfura Cikin Raini tace"Baba ina ganin mutumcinka kadan karka Bari na Daina gani fa."
Tafada tana wani juya ido cikin Wani Salo,Ahmed dake zaune gabadaya suman zaune yayi Zufa ta Shiga ketomai kota ko"ina Duk Da Sanyin A.C Dake kadawa Baban Iman kuwa mamaki da al"ajabi ya kasheshi ganin Amaryan Abba office din Ahmed kuma harda mganar ma ba Ranar tataba zuwa ba,Ahmed bai da bakin Mgana kuri kawai yayi ma waje daya da ido Zuciyarsa na Bugawa Masinja kuwa baya yaja yana fadin"Allah baki Hakuri Hajiya Abun bai kai haka ba Dama saboda yallabai ne.."yafada yana kokarin Fita Tsaki Samiha ta saki Katon Tsaki Tana Fadin"Ameen...Har ni ka isa ka min wannan Rainin dakai da wanda kake karkashinsa Duka kuna karkashin Iko nane in naga dama Sai na saka achanza ku akawo wasu."Tafada cikin Wani isa da Izza tana wani Hura Hancin zai sake mgana Baban Iman ya Dagamai hannu yana Fadin"Jeka kawai abunka Baba.."yafada da Sauri Cikin girmamawa Masinja ya Fice yana Fadin"Afito lafiya ranka ya Dade.."
Yana Fita Samiha ta Juyo tana Fuskantar Ahmed da Baban Iman Mirmishi ta saki ganin yadda Ahmed din yayi kafin tafara Taku zuwa kusa da kujeran dake Fuskartan Baban Imam tazauna Lokaci daya ta Dora kafa daya kan Daya Baban Iman ya saki baki kawai yana kallon Ikon Allah Lokaci daya kuma yana kallon Ahmed wanda ya jike da Zufa ganin Nura Manaja na kallonsa ne yasa ya gayyato dakewa da Juriya yana Fadin"Ha..ji..ya bar..ka dazuwa.."
Yafada yana Rawan Murya Samiha tawani kalli Ahmed a karkace tana wani mele baki bata amsa ba sai ma idonta datakai kan Baban Iman tana Fadin"Ba wannan ya kawo ni ba..Kasan dai Abunda ke tafe dani ko..?
Tafada tana sakarmai manyan Idanuwanta,Ahmed yaji kamar Zuciyarsa Tadaka tsalle ta Fito Saboda Firgita da Zullumi Cikin Nauyin Ido ya saci kallon Baban Iman wanda ke kallon Samiha yana kallon Ahmed ganin haka yasa yasaki Fuska yana Fadin"Ok..Munyi mgana da Abba da Safe bari na saka a hada miki..Baban Iman baka gaishe da Hajiyar Abba ba.."yafada yana gayyato Jarumta Numfashi Baban Iman ya saki kafin ya saci kallon Samiha yana Fadin"Sannu da zuwa ina kwana.."Ta leben bakinta ta amsa lokaci daya tana wani Dauke kai Wayarta dake cikin Jaka ta Dauki kara ta Bude da Sauri ta Daga tana Fadin"Anty Uwani zan kiraki in na koma gida.."Tafada tana katse Kiran Lokaci daya tana Fadin"Ahmed kaji dani yau bana zo na bata Lokaci bane..Sauri nake yi.."
Tafada kanta tsaye da Sauri Ahmed ya Mike yana Rawan Jiki Bakinsa na rawa yake fadin"Toh..Toh.."yama kasa mgana sai ya bude chan Dirowan ya Rufe ya Bude wanchan gabadaya Zufa yagama wankemai Jiki ana iya gane Halin Firgita da Razanar dayake ciki,Ganin haka yasa Baban Iman ya mike yana Fadin"Ahmed bari na barka,zan koma kasuwa in kagama Duba komai sai muyi mgana ta waya.."Da sauri Ahmed yace"Ok Nagode Nura.."yafada yana mika masa Hannu sukayi Musabaha,kafin ya fice yana waigen samiha wacce take wani cin Mgani kamar Taga kashi,Har ya sauko Daga saman yana mai cike da mamaki me ya kawo Amaryan Abba office din Ahmed,sai wata zuciya tacemai baka sani ba,domin Ahmed yafika kusanci da Abba Surukinsa ne wanda yake Aure da yarsa ammh kuma Firgitan mecece Ahmed yayi da yaga Samihan tazo office dinsa Haka yayi ta Tunane har ya Shiga Motarsa ya fice Daga wajen Zuciyarsa namai wasu sake sake bai bata dama ba ya watsar da Abun kawai.
Shi kuwa Ahmed Baban Iman na Fita ya kalli Samiha ya Daki Teburin gabansa cikin Bacin Rai harda sai da wasu Takardu suka Zube kasa Lokaci daya da Telephone din kan wajen ta Daka tsalle ta dawo Cikin Tsoro da Mamaki Samiha ta mike tana Bin Ahmed da kallo Shi kuwa cikin Wata irin Zuciya ya Kariso gabanta yana Nuna ta da yatsa yake Fadin"Ban miki kashedi akan Bibiyata ba... ..?Ehe nace ban miki Iyaka dani ba Samiha kina amsamin ban gargadeki da karki kara nuna ma kintaba sanina abaya ba..?ki amsamin nace Samiha...?
Yafada cikin Tsawa da Bacin rai ga Jijiyon kansa na mikewa Saboda Bacin rai idanuwansa sun chanza Launi saboda Bacin rai Baya Samiha taja tana Fadin"La wai duk wannan Jijiyar Wuyan da Hayaniyar duk ta mecece..? Na samiha ta Rabu dakai Ahmed... ?Tafada tana kallonsa kafin ta saki Siririyar Dariya tana Fadin"U are So Funny in har kana tsammamin Ni Samiha zan kyaleka ne toh ka farka daga wannan mafarkin Domin Bazan Taba sauka Daga kan Kudurina ba,Kuma nasan saboda mene kake wannan Zuciyar saboda wannan Mutumin dana samu tare dake..Hhh toh meye na Tsorata kaida lokaci kadan kowa zai san Halin da muke ciki.."Tafada tana kokarin komawa ta Zauna afusace Ahmed ya janye kujeran ya Turata baya tayi Taga Taga kamar zata Fadi sai da ta Rike bango ta Dago tana kallon Ahmed baki Bude wanda ya kankance idanuwansa yana Fadin"Na Rantse har ga Allah Samiha zanmiki Rashin Mutuncin da Tunda kike wani Mahaluki bai taba yi miki shi ba..Zaki gwammace dama baki sanni ba indai kika kara Zuwa min Wajen aikina kina neman jamin Wani bala"in kinji ma nagaya miki.."yafada yana kankance Idanuwansa masu cike da bacin rai.
Shuru Samiha tayi tana Bin Ahmed da kalli zatayi mgana ya Dakatar da ita lokaci daya yana Dagamata Hannu yace"Bana son Jin komai Daga bakinki...Get out Of my Office Now kafin na saka awulakanta ki acikin wajen nan.."yafada yana nuna mata Kofar Fita Cikin Bakinciki da kunar Zuciya Samiha ke kallon Ahmed Lokaci daya hawaye suka wanke mata Fuska ta gyada kai kawai ta juya ta Dauki Jakarta ta wayarta ta Doshi hanyar Fita gabda Zata fita ta tsaya tana Fadin"Ahmed...Ahmed...Zan dawo..Wlh Tallahi sai na dawo matukar baka amince da Bukata ta Toh sai kowa yagama Fahimtar Abunda ke Tsakanina dakai kuma office din nan yanzu na Fara zuwa in kuma ka yanke Hukunci daina zuwa ne sai mu koma gidanka mu karishe mganar achan..kayi Tunani Ahmed akan mganata Tunkafin Lokaci ya kure maka na barka Lafiya.."Daga haka ta fice tana Sharan Hawaye kai Ahmed ya Dafe yana Sakin Numfashi kamar yayi kwallah haka yake ji Ruwan dayasha Dazu ya Dauko ya Shanye gabadaya kafin ya koma kujeransa ya zauna bayan ya Tattara Takardun da suka watse akasa yana kokarim zama kenan yaji wayarsa na Kuka daga gaban Aljihunsa ya zaro da Sauri harta katse 11 misseds call yagani na Abida ido ya zaro Cikin Faduwar gaba yabi bayan Kiran Lokacin da wayar Ahmed ya Shigo wayar Abida suna cikin Keke Napep ita da kaka Domin sun gama Tundazu tana ta Kiran wayar Ahmed baya Dauka Kaka tace tagaji su hau abun hawa su koma gida.
Ranta ba Dadi ta daga Kiran tana Fadin"Haba Hubby kafasan kace in mungama mu kiraka zaka zo ka maidamu gida.."Numfashi Ahmed ya sauke yana Share Zufan dake kansa yace"Am Srry Sweetheart na bar wayar a office dina ne na je office din accounter muna Lissafi sai yanzu na Shigo naga tarin Kiranka dom Allah kiyi Hakuri.."Ajiyar Zuciya ta Sauke batayi mgana ba Jin haka yasa yace"Kuna ina ne yanzu .?kun gama ne..? Cikin Sanyin Murya Abida tace"Muna cikin Napep zamu koma gida mungama tun dazu.."Kai Ahmed ya Dafe kafin yace"Am Srry yanzu kinsan Abunda nake so dake..? Bai bata Zarafin mgana yacigaba da fadin"Ku Sauka gidan Kawu maude ku gaishesu Daganan sai ku tafi gidan Umma da yammah zan zo na maida ku gida kinji Abidata.."Mirmishi ta saki kafin tace"Shikenan Sai kazo.."Daga haka suka yanke Kiran Abida kuma tagayama Kaka yadda sukayi da Ahmed kaka ta washe baki tana Fadin"Allah yama Ahmed albarka..Kamar yasan nagaji da zaman gida.."Abida dai batayi mgana ba Mirmishi kawai tayi Zuciyarta ce kawai ba Dadi batasan Dalili ba...
Ahmed kuwa suna gama waya da Abida ya Dauki Takardun da Baban Iman yakawomai ya Tura cikin Dirowan dake wajen harta da System din anan ya barta Makullin Motarsa kadai ya Dauka ya Fice bayan yace ma Masinja ya Rufe Offce din sai gobe zai Dawo haka ya Fito agurguje kamar kuma a firgice Hatta sani ya gansa yana gaisheshi bai ma Jisa ba yabisa da kallon Mamaki har ya Shiga Motarsa ya bata wuta ya yi kwana lokaci daya da Zuba Hon masu gadi suka wangalemai get ya Sulala waje.
Gida ya koma Ko ghali megadi sai da yayi mamakin Dawowar yallabai har yana cemai su Hajiya basu dawo ba bai bashi amsa ba ya Wuce cikin Gida yana Cire Hulan kansa Direct Bedroom dinsu ya Shiga ya Fada kan gado yana Sakin Numfashi Sama sama kamar wanda yayi Tsere Zuciyarsa na cike da Fargaban Allah yasa Baban Iman bai Fara Fahimtar wani abu ba.
*Aisha alto..*
*Janafty*