Page 14
*SILAR HALLACI*
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*🅿️14*
"Idanuwansa sun kurama Saman Cealling din dakin ido ammh azaharin gaskiya ba kallon wajen yakeyi ba Hankalinsa ya Tafi chan wata Duniya Tunanin Mafita game da Abunda Samiha take nemanshi Dashi.
Baisan iya adadin Wasu Mintina da awannin ya kwashe daga kwancen nan ba abunda dai kawai ya sani ya kan mulmula Daga hannunsa na Dama zuwa na Hagu yana fama da Nurfarfashi kamar wani mai Ciwon Asthma bai ankara ba sai da yaji masallacin kusa dasu suna Rangada kiran sallah Kasala ta gama Lullebe Ahmed kansa saramai yake Saboda Damuwa da Rashin mafita yana kwance Har aka Tada sallah bai iya Tashi ba Sai da aka idar kamar wanda Shedan ya Danne gabadaya Jinsa yake a sake kamar bashi ba.
Dakyar ya iya Saukowa Daga saman gadon yana Mika lokaci daya da Salati wayarsa ya cire daga Aljihu ya ijiye Bisa Side Drower din gadon tare da Link din Rigarsa,idanuwansa yakai Duba Bisa agogon Bangon Dake Cikim Daki yaga har 1:30pm na Rana ya wuce yana kwance bai samu Mafita ba kansa kawai ya Shafa yana Tafiyar Rangaji ya Nufi Tiolet Ruwa yafara kamawa kafin ya Dauro alwala ya Fito yana Goge Sauran Ruwan Dake Fuskarsa Sallaya ya shimfida ya Kalli Gabas ya Tada sallar bayan ya idar ya Dade yana Kwararoma Allah kirari kafin ya Dora da Addu"ar Allah yayimai gatan gan karfe da Samiha ya kuma Rufamai Asiri Duniya da lahira,bayan ya Shafa Addu"ar karamin Qur"anin dayake karatu Dashi ko da yaushe ya mika Hannu ya Dauko wanda ke saman Side Drower din gadon ya Bude Suratul yusuf yafara karantawa Cikin Muryansa mai Cike da Damuwa.
Sai wajen Uku saura kana ya Dakata lokaci Zuciyarsa tayimai Sanyi Maida Qur"anin yayi ma"adanarsa ya mike lokaci Daya yana Ninke Sallayar dayayi sallar da ita saman madubi ya Ijiyeta inda yagani ya koma ya kwanta bayan ya Cire Rigar Jikinsa ya Rage dagashi sai Singlet Gudun A.C yarage kafin ya Saka kanshi Bisa Filo yana maida Numfashi Daya bayan Daya Cikin Ikon Allah Barci mai Nauyi ya Daukesa wanda ya Dade yana yinsa baisan Lokaci ya Tafi ba.
Bangaren Samiha kuwa Tana Fita Ta fada Motarta dama ita kadai tazo yau bata nemi Direba ba Kwallah take Sharewa mganganun Ahmed na mata yawo acikin kwanyar kanta Har ta Fice Daga Haraban wajen tana Tsiyayan Hawaye Tun tana da Zarafin saka hannu ta goge har ta barsu sukayi ta Shatata ba kukan komai take ba sai na Bakinciki da Kishi da kuma gajiyawa Tsakani ga Allah tagaji hakanan itama tana Bukatar kwanjin Da Namiji a kanta ba kuma kowani Namiji ba Sai Ahmed wanda Tun bata Fahimci ya sha"awar Namiji yake ga Mace ba,akansa ta fara jin tana Sha"awar Namiji komai na Ahmed na irin Tsarin Mijin datake mafarkin Aure ne,Kaddara ta rabasu abaya kuma yanzu Kaddara ta kara Hadasu,saboda mutane kalilan Wanda basu da muhimmanci acikin Rayuwarta bazata Cuci kanta ba Dole ne tabama kanta da Zuciyarta Abunda takeso ko Ahmed yaso ko bai so ba yazama Dole ne kowa ya Fahimci Halin da Suke ciki.
Har ta isa gida tana kuka Sanda Ta Zuba hon a bakin tamgamemen Get din gidanta megadi ya Bude mata kuka take har ta Gama adana Motar a Parking space bata fito ba sai da goge kwallarta kana ta Fito ta Nufi Cikin gidan Ranta duk ba Dadi Abun takaichi tana Shiga Falon Taci karo da Abba sai da Ta ganshi ta Tuna yau yana gidanta ne,Bayan Fitatan kenan ya Shigo yana Kishingide yana kallon Tashar Sunna Tv ta shigo yana ganinta ya Gyara zama yana Fadin"Gimbiya kin dawo..? Na shigo Tun dazu ma"aikatanki suka ce min kin fita..'
Kallonsa Tayi cikin Wani Tsanarsa Da Takaichi Domin Tanaganin Shine mai laifin dayayi mata gatangan karfe da Masoyinta Ahmed Dakyar ta kakalo Mirmishin yake ta sakarmai kafin ta kada kai kawai ta Haura sama da Sassarfa da Kallo Abba ya Bita yana Tunanin toh meya batama Samiha rai baiyi Yunkurin Binta ba saboda Sanin Halinta ya koma ya kishingida yana Cigaba da kallonsa ammh gefe daya na Zuciyarsa na cike da Zullumi dama in zata fita ba kasafai take gayamai ba sai tayi Ra"ayi don kanta Shima kuma bai damu ba Domin Shi ya bata dama Tun Farko take Abunda taga dama yanzu ko yaso ya Hanata baza ta taba Hannuwan masa ba.
*****
Bangaren Abida da Kaka kuwa gidan Kawu maude sukayi sallar La"asar kafin suyi musu sallama su fito bakin Titi suka samu mai Adaidaita zuwa gadon kaya gidan Umma har ko bakin Titin Anty Naja"atu ta rakosu tana musu Godiya Hajiya Rabi tana jin Dadin Ganin yarda Abida Cikin kwanciyar Hankali gefe daya kuma Kaka,tana son zama da ita Saboda Kaka tayi ne arayuwa in ka Fahimceta zaku zauna lafiya Suna Zuwa Hira ta tsinke tsakaninsu Abida sai ta zama yar Kallo basu jima da zuwa ba sai ga Anty Nabila ita da gayyar ya"yanta Sun taso daga sunan kanwar Mijinta dake nan gadan kaya kusa dasu Umma Shine ta Biyo Abida taji Dadin ganinta Suka Rumgume juna cike da Farinciki tana musu Tsiyan ita da Ahmed suna Fushi dasu sun Dauke musu kafa daga zuwa gidansu.
Abida na Dariya tana Daukan Karamar yarinyar Anty Nabila Nadra take fadin"Kai Anty Muna nan zuwa insha Allahu Hubby ne baya samun Lokaci har Ranar Weekend fa kinsa yana Fita.."Anty Nabila ta gyada kai tana Fadin"Naji wannan...Bazan dai hakura ba sai kun wanke Laifinku ammh ai gaku a gidan Umma ko.."Tafada tana Hararan Abida wacce ke Dariya Kaka dake gefe tace"Kinga nan Nabila karki wani Damu zamu zo mu Wunin miki..Ai indai zamu biyema ta yaron nan Ahmadu sai mu Shekara acikin gida mu Rube bai damu ba Na rasa Dalilin Ahmadu baya kaunar yaji wani yace zai Fita ammh Shi kafarshi kullum tana hanyar waje kamar Wanda ya taka kafar kare..'Gabadaya suka sakama Kaka Dariya Anty Nabila ke fadin"Allah ya barma nake Kaka zan Roki Ahmed ya bani ke muje kimin kwana Biyu kaka.."
Kaka ta tabe baki kan tace"Wa..? Bari ma mganar nan Nabila dama kinyi Shunki kin bari sai nidake sai muyi mganar ammh yanzu kin yi shuka idon makwarwa."Tafada tana nuna Abida da baki Umma ta saki Dariya tana kallon Abida ta da bata Rai tana kallon Kaka tace"Ni ko kaka..? Ni da ma nake kokarin Lallaban Ahmed ya dinga bari in rika kaiki gidan kawu maude.."Kaka tayi Saurin Cewa"Nasani Abida ba Haka nake Nufi ba..naasan Ahmed da Shigen wayau tun yana yaronsa,Sai ya iya miki lauya tsakanin mata da Miji sai Allah naji zence ya Sauya.."Anty Nabila na Dariya tace"Hakkun Kaka in fadi gaskiya.."Bata rai Abida tayi Kaka ko ta koma gefe tana ma Nabila mganar ido tana Nuna Abida wai bakinsu daya da Mijinta Ahmed.
Anty Nabila bata tambayi Abida ya Lafiyan Cikinta ba sai da suka kebe Kana take tambayanta cikin kunya Abida ke fadin"Lafiyata lau Anty Nabila yau ma na Fara zuwa awo nan Asibitin Aminu kano Anty Najwa tace naje inda ta Hadani da kawarta,kuma Alhamdulillah naga Likita kuma ba wata mtsala yanzu sai After 4 weeks zan koma."Kai Anty Nabila ta gyada tana Fadin"Masha Allah Allah kara lafiya munyi mgana da ita,tace ta hadaki da Sister suwaiba baki da damuwa tana da Kirki.."Abida tace "Nagani kan Anty Nabila.."Nan suka Cigaba da Zencensu na zumunci har suka gangaro kan zencen Adama datake da Ciki Tsoho haihuwa ko yau ko gobe Abida nata Zumudin zuwa Sunan Adaman wannan karon,domin na farinta ta haifeshi babu rai ne.
Tunda 6pm na yammah Tayi Abida ke faman kiran wayar Ahmed,sai dai tana Ringing baya Daga kiranta hankalinta ya Tashi ta kirashi almost missed calls 20 ammh bai Daga balle ya Biyo baya Tana zaune gefen gadon Umma tana Rike da waya Anty Nabila ta Fito daga Tiolet din Dauke da Nadra ta cire mata pampers Dinta data batashi da Fitsari ganin yadda Fuskar Abidan ta bayyana Damuwa ne yasa Anty Nabilan zama kusa da ita tana Dora Nadra Bisa Jikinta take Fadin"Abida meya faru ne..?
Abida ta saki Ajiyar Zuciya Kafin tace"Wlh Anty Nabila Ahmed nake ta Kira bai daga kirana ba Alhalin mun Rabu dashi kan in yatashi daga wajen aiki zai biyo ta gidan Umma ya Daukemu mu koma gida.."Tafada cikin Fuskar Damuwa Anty Nabila ta saki Numfashi Tana fadin"Toh shine me Abida..? Kila baya kusa ne ko wani aiki ya tsareshi ki dinga hakuri Abida karki manta Dukiyar mahaifinmu ne fa yake kula da ita kinga kuwa ya kamata ki Dinga bashi Uzuri.."Tafada tana Rike da Hannunta Abida ta Bude baki Zatayi Mgana kenan Anty Nabila tace"Shiii..Karki ce komai...Basai kin ce komai ba in dai mganar komawa gida ne kuyi sallar mangariba yanzu sai Direba ya maidaku ni ina nan sai wajen 9 baban Nadra zai zo ya Daukemu.."Abida tace"Toh Anty Nabila muma sai mu bari mu tafi tare ko..? Kumatunta ta Shafa tana Fadin"A"a gwara ki Tafi da Wuri batun yau ba na sani Ahmed baya barin ki Fita ki kai dare kome ake ciki 6 nayi zai ce ki koma gida ko kuma yazo ya Tafi dake ko ban Fadi gaskiya ba..?
Abida tayi Mirmishi tana Fadin"Hakane Anty Nabila.."Itama Dariyan tayi kafin ta mike tana fadin"Ki shiga ki Dauro alwala yanzu za"a kira sallah bari na sauka falo na samu kaya na sakama Nadra jakata tana cham.."Dakai Abida tayi mgana kafin ta mike ta Fada Tiolet ita kuma Anty Nabila ta Fice Daga Dakin ta sauka kasa zuwa Falo.
Haka ko akayi suna idar da sallar mangariba Lokacin har pass 7 kana Direban gidan Umma ya dauki Abida da kaka zuwa gida bayan sunyi sallama da Anty Nabila,har suka isa gida Abida bata cikin Natsuwarta sai dai Abunda ya bata mamaki suna Shiga Haraban gidan suka ci karo da Motar Ahmed cike da mamaki ta Fito take bin Motar da kallo kenan Ahmed ya Dawo gida,toh meya faru ne baya Daga Kiranta..? Bata samu amsa wannan Tambayar ba ta sallami Direbansu suka Nufi Cikin gida Kaka na Fadin yau Ahmed yayi dare bai dawo da Wuri ba ko yagayamata inda zashi Abida na jinta bata tankata ba Domin kila Kaka bata lura da Motar Ahmed din bane dake kusa da tata dake parking Space aharaban gidan ba.
Suna Shiga Falon Abida ta kunna Wutar wajen haske ya bayyana Dama kafin ta fita sai da ta kashe komai na Wuta saboda gudun wata mtsala Kaka kichen ta Wuce tace zata Dauko Ruwa tana jin Kishi itakuma Abida ta Nufi Bedroom dinsu cikin Fargaba,tura Kofar tayi ta Shiga da guntuwar sallamarta Dakin ya Fara Duhu duhu saboda dare yafarayi tana daga tsayen ta saka hannu ta kunna Fitilar dakin Haske ya bayyana ido ta zaro ganin Ahmed kwance kan gado yayi kwanciyar Ringingine yayi matashi da hannayensa Filon kuma ya Dora Kafafunsa akai Daga ganin yanayin barcin zaka Fahimci yana jin Dadin barcin nashi.
Cike da mamaki ta karisa gareshi tana Cire mayafin kanta da Jakarta lokaci daya ta ijiyesu kan Side drower din gadon,wayarsa dake wajen ta Dauka ta Latsa gefe haske ya bayyana 40missed calls tagani yana yawo asaman Wayar nashi ido ta zaro tana Bin Ahmed da kallo gabanta ya fadi tana Tunanin ko wani abu ne ya faru dashi wayar ta maida inda ta gani ta zauna gefensa tana dan Bubbuga hannunsa Lokaci daya tana Fadin"Hubby..."Take fadi tana Kuma Taba goshinsa taji ko da Zafin zazzabi sai taji sanyi alamun dai lafiyansa kalau.
Shiko Ahmed cikin barcinsa yaji kamar ana tashinsa Lokaci daya da kiran sunansa Cikin Gajiya da kasala,ya muskuta yana kokarin Bude ido Abida ta kara Riko hannunsa tana Fadin"Hubby lafiyanka kuwa..? Kara watstakewa yayi yana bin Abida da kallo cikin muryan Barci yace"Kun dawo da wuri ne..?naga baki kirani ba kamar yadda nace ba.."Abida tayi mai Zuru kafin tace"kalli agogo fa yanzu almost pass7 fa shine zakace mun dawo da Wuri kuma kira,guda nawa kakeso nayi maka banda Tarin Misssed cllss din dana tara maka.."Tafada tana kuresa da ido Cikin mamaki Ahmed ya Dago jikinsa yana Bin agogon dake dakin da kallo 7:40pm na yamma zaro ido yayi lokaci daya yana Fadin"Innalillahi Abida wani Bakwai din nake gani na safe ko na yammah.?"Cikin Tsoro Abida tace'"Na safe kuma..? Nadai dare ko Hubby.?
Da Hanzari Ahmed ya Ture Hannun Abida ya Sauko daga kan gadon yana salati da Sauri Abida ta mike tana fadin"Meya faru ne..? Ahmed ya dafe kansa yana Fadin"Kinsan tun wajen 11na safe na dawo gida na samu Hutu kaina na ciwo kinganni ko babu Abunda na sakama cikina nidai Tun wajen uku na rana na kwanta wlh ban kara sanin kaina ba sai yanzu da kika tasheni..Na bani ko sallar La'asar fa banyi ba Sweetheart balle Mangariba.."Numfashi Abida ta Sauke kafin tace"Ikon Allah..Wannan wani irin barci ne,ga kuma yunwa duk lokaci daya kayi taking pracetamol ne..?bai bata amsa ba kawai ya kada kai ya Fada Tiolet da Sauri da kallo ta bishi kafin ta kada kai kawai Rigarsa ta Daukemai ta ninketa ta saka cikin Wardrope tazo takara gyara gadon kafin ta Fice zuwa Kichen saboda ta Dafamai Abu mai sauki da zai samu yaci tunda ya Wuni da yunwa.
Taliya ta Dafamai da Kifi ta hadomai da Zobon datayi Tun jiya ta saka Cikin Frigde,bata kai mai ba sai da ta leka ta tambayi Kaka ko zataci kaka na zaune kan gadonta tana Shafa hantsi a kafafunta tace aci lafiya ita daga nan sai kwanciya Shima Ahmadun ne da Shigen Rigima ina laifin ya tsaya waje yaci sai yazo gida ya wahalar da mai ciki itadai Abida batayi mgana ba ta mata sai da Safe ta ja mata kofa ta koma kichen ta kashe komai ta kwashi Tiren abincin Ahmed ta Nufi Bedroom dinsu koda ta Shiga Har yafito daga wankan ya saka wata bakar jallabiya yayi sallar La"asar yayi mangariba Isha"i yakeyi domin an kira itama bata zauna ba tana ijiye Tiren ta bude Wardrope ta Dauko hijabinta ta tada sallah dama tana da alwalanta,Ya rigata idarwa,abincin ta jawomai gabanshi batare datayi mgana ba ta Dauki Filet ta zubamai ta Turamai gabansa baiyi gaddama ba ya gyara zama yafara ci saboda tsakani ga Allah yaji yunwa yana cikin ci ta zubamai zobon ta mikamai yasha yaci Taliyan sosai kafin ta doramai da Ruwa yasha yayi gyatsa lokaci daya ya kalli Abida yana Fadin"Alhamdulillah..Nagode Matata Allah yayi miki albarka."Abida na mirmishi ta amsamai da Ameen kafin ta kwashe komai ta maida kichen ta fito falo ta kashe komai ta koma Bedroom din ta iskeshi zaune gefen gado yana Duba wayarsa batamai mgana ba ta fada Tiolet tayi wanka koda ta Fito har ya kwanta tana gaban madubi tana Fesa Spry tace"Karfa ka kwanta baka sha panadol ba Hubby.."
Yana Daga kwancen yace"Karki damu...in bai lafamin ba gobe sai naje asibiti.."Batayi mgana ba sai ma wucewa datayi gaban wrodrope tana neman Rigar barcin da zata saka ta gefen idanuwanta take kallon Ahmed na tsawon Lokaci kafin kawai ta girgiza kai ta Cigaba da zakulo Rigar barcin da zata saka.
*****
Bayan Sati daya da Faruwar Haka Samiha ta maida Office din Ahmed wajen zuwanta Abunda yake Tsoro na kada Ma"aikatan wajen su fara Fahimtar abunda ke Faruwa,komai ya Dagule domin Tuni suka fara Dora ayar Tambayan game da yawan zuwan Amaryan Abba Office din Ahmed in ma wani bai sani ba,wani ke sanar dashi in Suka ganta ai Amaryar yallabai ne,mganganu yafara yawo tsakamin ma"aikata da kuma ayar Tambayan,Hatta Baban Iman Sau uku yana cin karo da Samiha Ranar dayafi yima Ahmed kallo Zargin Ranar daya Shigo Office dinshi ya Tarar da Samiha Durkushe gaban Ahmed tana Kuka,daya shigo Ahmed ne kadai ya Firgita ammh banda Samiha,mamaki yakama Baban Iman ya dade yana kallon Ahmed wanda ya sadda kan kasa yana ji kamar ya saka kuka Saboda kunya da nadama da kuma Firgita.,gabadaya duk ya Fige ya lalace tsauye kawai yake ammh kuma Jikinsa kamar yana da Wata Lalura sai dan Wuya kawai yake gabadaya samiha tagama Dagulamai Lissafi ta nace mai shi kuma ya gayamata har ga Allah bazai taba mata Abunda take Bukata ba ita kuma tana nan akan bakanta,kira na yau Dabam na gobe dabam Duk da yayi Blooking dinta da dayan layinsa na Farko ammh sai da ta kara samun Dayan layin nashi tana kiranshi kwata kwata tahana Rayuwarsa sakat.
*****
Bayaso Abida ta Fahimci Akwai wani abu Shiyasa ya maida wayar a silent amma Samiha bata daina kira ba, ƙarar Shigowar saƙo yasa ya ijiye Cokalin Hannunsa ya ɗan kalli gefen Abida yaga bata kallonsa Hankalinta na wajen Kaka dake Ƙorafin Tagaji da Cin Abincin Turawa, Kai duba yayi zuwa ga Saƙon Samiha wacce bai san ina ta samu Nombar wayarsa ba kai Tsaye wata Zuciya tace "A wajen Abba mana.."
"Ka ɗauki wayata..muyi magana ko kuma na zuba ma Alhaji gubar da na siyo gata atare dani...In jami'an tsaro suka kamani zan ce kai ka sani na kashe Alhaji saboda kana sona kaga kuwa dani da kai za'a kashemu.."
Wani Rass! yaji gabanshi ya Faɗi Cikin Firgici da Tashin Hankali ya miƙe duk ya Haɗa Zufa Abida da kaka suka Bishi da kallo ganin ya Nufi ɗaki Cikin Sauri har yana cin Tuntuɓe Kaka ta kalli Abida tace "Shi kuma wannan Halan Saƙon mutuwarsa ne yaji yake ta wannan Uban Rawan Jikin har yana neman Faɗuwa.." Cike da mamaki Abida ke Faɗin "Mutuwa kuma Kaka...?"
Kaka tace "Eh mana toh in ba sakon mutuwa ba Uban me zai Firgita Ahmadu lokaci ɗaya haka.." Ta faɗa tana gyara zaman Gilashin Idonta jikin Abida na sanyaye ta miƙe tabi bayan Ahmed sai dai tana zuwa taji ya garkame ƙofan baki ta riƙe Cikin mamaki tana bin ƙofar Bedroom ɗin nasu da kallo.
Yana Shiga Cikin Bedroom ɗinsu ya maida ƙofa ya kulle saboda kada Abida tabi yo bayanshi daidai lokacin da Wayarshi ta ƙara Ɗaukan Tsuwa jikinsa na ƙara ɗaukar Rawa ya ɗaga kiran bai samu Zarafin Magana ba Samiha ta kece da wata dariyan Nishaɗi da Nasara tana faɗin "Dama na faɗa maka..Zan mallakeka Ahmed mallaka na har Abada..."
Cikin Wani irin Faɗuwar gaba Ahmed yace "Samiha...! Samiha me kikeyi hakane wai..? Samiha ya kamata ki daina Bibiyata haka nan Abunda kike nema bazai samu ba na Riga na gaya miki tun Farko.." Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin tace "Naji Aurena dakai bazai yiwu ba Ahmed...Amma ai Haɗuwa mu zama Abu daya zai yiwu ko..?" Ta faɗa cikin Wata murya mai cike da kissa.
Ahmed na goge zufan data keto mai Bisa goshinsa yace "Ban..ga..ne Abun..da kike nufi ba...?" Ya faɗa cikin Rawan murya far tayi da ido kamar yana Gabanta kafin tace "Laaa baka gane ba..? Toh ina nufin Budurcina danake ta maka tanadi Shekara goma babu Abunda ya tabashi shi zaka iya amsanshi koda yaushe ka Shirya..." Wani zaro ido Ahmed yayi Cikin Rawan baki yace "Innalillahi..." da Sauri Samiha ta katseshi da Faɗin "Mu hadu a Hotel ɗin Tahir guest palace gobe da Misalin ƙarfe goma na Safe.." Ta faɗa kai Tsaye da Sauri Ahmed ya Sulale kan gado yana fadin "Sassamiha...Sasssmiha karki min haka..." Cikin Wata murya tace "In baka zo ba..Nikuma zan cika ƙudirina zan ba Alhaji guba yaci ya mutu..." Da sauri Ahmed yace "A'a karki haka Zanzo...Zan zo karki Bama Abba guba don Allah Samiha..."
Dariyan Jin Daɗi ta saki kafin tace "Sai da safe angona...Karka manta ɗaki mai lamba Ashirin da biyu sai mun haɗu.." Ta fada ta sakin mai kiss ta waya kafin ta yanke kiran Wani Tuma Ahmed yayi Bisa gado ba inda Jikinsa baya Rawa cikin Firgici da Tashin Hankali yake Furta.. "Na shiga uku ni Ahmed..Yarinyar nan zata kasheni Lokacina baiyi ba..Wazan kai ma kukana.? Wazai bani shawara kan wannan Abun daya Tunkaroni kaicona..Ni Ahmed kaicona...ya zanyi da Rayuwata..." Ya faɗa lokaci ɗaya wasu Siraran Hawaye suna Zubo mai Bisa Fuska gabadaya ya jiƙe da Zufa kamar wanda ya Buga wasan Tsere.
*Aisha Alto*
*Janafty*