BIYU A ƊAYA

Chapter 11

by @barista

BIYU A ƊAYA 
       (Don't judge a book by its cover)

Page 11

By Sayyada barrister
***
YOTA 13 
TEAM FIVE INK LEGENDS

Alaja ta jima tana kafa musu dokokinta, da kuma sharuddan ta akan wannan manyan baƙin da za ayi, in dai sun bata haɗin kai to kakanta ta yanke saka, don yadda labari ya zo mata, wannan zuwan baƙin tare da haɗin manya manyan kungiyoyi ne na ƙasashe daban-daban, su ma in dai sun maida hankali sun martaba baƙin to za su samu alkhairi da basu taɓa samu ba, sai jawabi take yi tana sake nanata wa, sun fi awa guda ana abu ɗaya sannan daga bisani ta ɗaura da cewa

"Abi doka a zauna lafiya"

Suka amsa da 

"Za mu tabbatar da komai ya tafi kan tsari kamar yadda ki ke so"

"Yawwa, Laraba and Jummai ku da kuke kula da bangaren girke-girke ku tabbatar komai ya tafi normal, ku sake gyara girkin ku, find some cooking method please, ina so wannan karon komai ya zama special"

"Suka amsa da to"

Sannan Alaja ta ɗaura da cewa

"Cleaners ku tabbatar kuna tsaftace wajen, kada naji ko na gani ba a tsaftace dining areas ba"

Suka amsa da 

"Ok Maa"

Ta dawo da duban ta zuwa kan Bilqees ta ce

"Bilqees special chef you are in needed at both side, kitchen and serving"

Ƙirjinta ya buga shikenan Alaja zata kashe ta, tayi aiki a kitchen kuma ta yi serving mutane...

"Dake nake yi Bilqees"

"Ok Maa"

Shine abin da ta ce, hakan naiwa wasu daɗi ba, musamman Jummai da Laraba ta yaya Bilqees za ta yi aiki a bangarori guda biyu a lokaci ɗaya...

Alaja ta watsar da su, kowacce ta yi bangarenta, Bilqees ta iso bangaren Server's ta ji muryar Majada tana kiran sunan ta juyo ba tare da ta ce komai ba har Majada ta iso, ta yi magana cikin nuna damuwa 

"Friend sai kawai aka ɗauke mana ke"

"Uhm Majada ai duk ɗaya ne, kuma ana tare"

"Of course friend, amma kuma ba kamar a ko da yaushe da muke madafar abinci tare ba"

"Um haka ne Majada, mu yi yadda Alaja take so"

"Okay Bilqees, bye"

Ta wuce ciki, ita ma Bilqees ta wuce wajen Server's. kusan yau ma baƙi su ka yi masu yawa duk da daman Alaja restaurant a cike yake da customers a kowanne rana....


**********************************

A daidai inda ta ke sauƙa a mashin yau ma ta sauƙa, ta biya shi kuɗin sa, sannan ta iso wajen abokanta, ta tadda suna zaune suna hira suna ta sheƙe da dariya, tana isowa suna ganin ta suka yo kanta da oyoyo, nan suka kewaye ta, ta zauna su ma suka zauna ta sauke numfashi tare da cewa 

"Na tuna mu ku?"

Suka zuba mata idanu suna kallon ta, a take suka tuna, nan da nan suka haɗa baki wajen cewa 

"Ya kamata mu fara da gaisuwa"

Ta yi murmushi tare da cewa 

"Tabbas haka ne, ina jin ku"

"Barkan ki da safiya"

"Yawwa, sannu ku yara, kuna lafiya"

"Muna lafiya kyakkyawar Aunty"

Suka haɗa baki wajen faɗin hakan, ta yi murmushi tare da ɗauko Aicha ta zaunar da ita bisa cinyarta tare da cewa 

"Baby Aicha yau ba magana ne?"

"Tattawan (kyakkyawar) Aunty duka na Haneef ya yi"

"Oh! Sannu Aicha, kai Haneef me ta yi ka dake ta?"

"Bakin titi ta kuma tafiya"

"Kana da gaskiya, amma ba duka za ka yi mata ba, faɗa za ka yi"

"To kyakkyawar Aunty"

Cewar Haneef ta juya kan Aicha ta ce 

"Ke ma kada ki sake zuwa ba kin titi, ba ki soron mota ta buge ki"

"Tau tattawan (kyakkyawar) Aunty"

"Yawwa baby Aicha, idan har ba ki zuwa ba kin titi to zan dinga kawo miki Alawa"

Murna Aicha ta yi, tana jin dadi saboda kyakkyawar Aunty ta ce za ta dinga kawo mata Alawa, tana dariya ta ce

"Tattawan (kyakkyawar) Aunty, na daina zuwa batin (bakin titin)"

Ta shafa kanta a hankali ta ce

"Yawwa good girl"

Nan ta ce su yi layi ta raba musu abin da ta kawo, su ka yi layi suna murna, ta raba musu kowa ta ba shi nasa, nan suka soma cin biscuits suna jin daɗi.

Yau kam ta jima zaune da su daga bisani ta mik'e ta ce su tafi, nan suka tafi ta yi saurin barin wajen ita ma.....


**********************************

Abuja Nigeria 

Kwanasu biyu a Abuja tun da suka zo basu huta ba, sun yi nan su yi cen, sai da suka tabbatar sun yi clearing da duk wani abin da ya kawo su Abuja sannan suka soma shirye-shiryen tafiya GHANA, Dr Waahab kwance a ɗakinsa dake hotel ya maida hankalinsa ba ki ɗaya kan wayar sa sai faman danne danne yake yi.

Tun da ya kammala shirya kayansa, ya hau online yana wani research, kira ya shigo ganin sabuwar number ce yasa bai maida hankali wajen ɗaukawa ba ya ci gaba da abin da yake yi, sai da aka sake kira kusan na huɗu sannan ya ɗauka tare da cewa, jin muryar da aka amsa masa ne yasa ya yi jim kaɗan da kuma mamaki...

"Ya Waahab barka da warhaka?"

Aka faɗa daga ɗayan bangaren, ya sauke numfashi a hankali ya yi magana 

"Ashfat barka dai, da fatan kowa yana lafiya"

'kowa yana lafiya"

"Ya yi kyau"

Shiru su ka yi na wani lokaci, sannan Ashfat ta katse shirun da cewa

"Tun a ranar da ka bar Maiduguri, nayi trying number ban same ka ba"

"Ok na yi busy ne shi yasa"

"Da fatan kun sauka lafiya"

"Lafiya kalau, gobe ma za mu wuce Ghana"

"Ya yi kyau, Allah ya kai ku lafiya"

"Amin"

Shiru ya sake shiga sakanin sannan Ashfat ta yi masa sallama ta katse wayar, ya sauke numfashi tare da lumshe idanunsa....

Nocking da aka yi ne yasa ya dawo daga tunanin da ya faɗa ya bada izinin shigowa, Dr Faisal ne ya shigo ya miƙa masa hannu suka yi shaking hand sannan ya ce

"Ka tashe mu je mu ci abinci, Amarya tana jin yunwa"

"Ok Dr Faisal duk da ba wani yunwa nake ji ba"

"Kuma fa ba abin da ka ci, sannan duk abin da aka kawo maka daga cikin wannan hotel ɗin baka ci"

"Masu aiki da ake turowa su kawo ne bana so"

"Why?"

"Bana son ƴan aiki kwata-kwata sun fita min a rai, gwanda naje na ci a waje"

"Ikon Allah, ƴan aiki ai suna taimakawa, ko ni a gidana ina da ma'aikata masu taya matata aiki da kuma masu taya ni"

"To ai duk ɗaya ne, na wajen ma ƴan aiki su ke yi, haka ma na cikin hotel shima ƴan aikin ne su ke yi"

"Haka ne, amma bana so su yi min na musamman saboda ni, mu haɗu gaba ɗaya sai mu ci ya fi"

"Any way, mu tafi kawai"

Suka fito, Dr Faisal ya wuce ɗakinsu ya suka fito da matarsa, sannan suka wuce cin abinci, sun jima a cen sannan suka dawo gida.

A gajiye ya dawo don haka, bai wani ɓata lokaci ba, ya hau bed ya kwanta, bacci ya ɗauke shi..


WASHEGARI

Ga ba ki ɗayansu kamar haɗin baki suka kammala shirin su lokaci guda, duk suka fito farfajiyar hotel ɗin, Dr Faisal da Amaryarsa suna daga gefe riƙe da luggage nasu, tun da suka sauka a Abuja hotel suke zuba soyayya, har suka ishe su, Dr Isma'il ne ya juyo don haushi ya ce

"To tattaɓaru wannan soyayyar a barta a nan Nigeria, ba zayyu mu je GHANA kuna mana ita ba"

DR Faisal dake riƙe da hannun matarsa ya maida masa da

"Ai ko America muka je za mu yi ta, ballantana nan GHANA"

Murmushi Dr Isma'il ya yi ya ce

"To sannun ku Romeo and Juliet, iyayen soyayya"

Dr Waahab ya iso sanye da ƙananan kaya sun yi masa kyau, a daidai lokacin da ya iso babbar motar da zata kwashe su zuwa airport ta iso, nan suka shiga, kowannen su ya zauna, Dr Faisal ya ce

"Ka ji ni da Dr Isma'il"

"Me ya ce?"

Cewar Dr Waahab yana gyara zaman sa, Dr Faisal ya ce 

"Wai saura mu yi soyayya a Ghana"

Murmushi Dr Waahab yayi ya kalli Dr Isma'il da shi ma kallon nasa ya ke ya ce

"Me ya shafe ka da soyayyar su?"

"Su yi fah, su zama Sharukhan da Kajol"

DR Faisal ya fusata ya ce

"To sarkin sa ido, kai me ya hanaka zuwa da matar ka"

"Tsohon ciki gare ta"

Dr Isma'il ya ba shi amsa, suna wannan hirar ne har motar ta iso airport, Dr Waahab bai sake sanya musu baki ba, indai Dr Faisal ne Dr Isma'il sun saba.

Suka fito kai tsaye aka kammala shirya musu komai, suka wuce cikin jirgi, ba a ɗau lokaci ba, jirgin su ya wuce GHANA......


*****************************

GHANA 

Bilqees tun da ta tashi da asuba bata koma bacci ba, ta kammala aikinta da sauri kamar zata tashi sama, tun kan gari ya yi haske ta ji fitan su Alaja, nan ta ƙara hanzarin ta don ta kammala shirya wa ta tafi kada ta makara...

"Bilqees lafiya kike aiki kamar za ki tashi sama?"

Ta sosa keyarta tare da cewa 

"Baƙi za mu yi yau a restaurant kuma Alaja ta ce mu fito da wuri"

"To gaggawa kuma ai ba daɗi, yanzu ki nutsu ki karya tukuna"

"A'a Mama zan ci abinci acen"

Sauke numfashi Maman Bilqees ta yi sannan ta ce

"Ke ma kin san ba za ki samu a cen ba, ko ki ci a gida ko ki zuba a flask ki tafi dashi ki ci"

"Mama akwai biscuits a jakata zan ci da na isa cen, abincin rana"

Babu yadda Maman Bilqees ta iya haka ta hakura, Bilqees ta kammala shiri ta fice, da sauri ta tsaida mashin ta hau ya kawota Alaja restaurant.


ALAJA SPECIAL RESTAURANT

Tana sauƙa a mashin ta sallame shi ta shigo cikin sauri, ta tadda duk an hauka ce ana aiki, ta wuce ciki ta ajiye jakarta ba tare da taje inda Alaja take ba, ta wuce dining areas tana shirya dining, table cloth ɗin take gyara wa, a nutse tana jera duk wani abin da ake buƙata a wajen, pen, tissues spoons, forks and memo....

"Bilqees"

Cewar Alaja, a nutse ta bar abin da ta ke yi ta iso wajen ta, tare da cewa 

"Bonjour Maa"

Ta gaida ta, barka da safiya, good morning, maimakon ta amsa mata ta ce

"Viens avec moi"

Come with me ta faɗa, ta biyota kenan, cin sauri Bilqees ta bi bayanta zuwa kitchen, nan Alaja ta yi ta nuna mata abubuwan da za a buƙata, sannan an ce baƙin abinci dare kawai yau za a shirya musu, ta nutsu ta shirya komai, ta amsa da to. Su Laraba kamar su shaƙota haka suke ji. Jin cewa aikin sai yamma yasa Bilqees kwantar da hankalinta, ta ci gaba da aikin a nutse har customers da suke zuwa cin abinci suka fara zuwa. ALAJA sai nan da cen ta ke yi tana gyare-gyare, duk ta kiɗeme saboda Alert da ta gani na Manager jiya da daddare, wannan ya tabbatar mata baƙin na musamman ne....


GHANA international hotel 

Tun da jirgi ya dire su a airport, mota ta musamman ta iso ta ɗaukosu kai tsaye sai international hotel, suna isowa cikin hoten din an kammala shirya musu komai, tsaf an tsaftace ko'ina sai ƙamshi yake. Hotel ɗin ya yi bala'in haɗuwa su kansu sun jinjina wa wajen, duk kuɗin su sai da suka ga ashe nasu wasa ne.

Kowannen su an ware masa bangarensa guda, tsarin ya matuƙar burge su, Dr Faisal ya ji daɗin hakan sauran likitocin ma suka ce da sun san haka wajen yake da ko da matan su za su zo.

DR Waahab ya wuce bangaren sa, komai ya yi yadda ya kamata, ya rage kayan jikinsa, ya watsa ruwa ya ɗauro alwala sannan ya fito ya shirya cikin jallabiya kirar Dubai sai ƙamshi yake, ya gabatar da sallah sannan ya hau kan bed ya mik'e nan bacci ya ɗauke sa....


*******************************

Zaune suke sun yi tagumi, da alamun sun gaji da zama, tun suna saka ran ganinta amma shiru haka yasa suka yanke shawarar barin wajen. Sun mik'e tare da nufar hanyar tafiya gida, suka ji muryarta kamar daga sama 

"Abokaina"

Suka juyo cikin farin da gudu suka iso inda take tsaye, nan suka kewaye ta, suka rungume ta, suna

"Kyakkyawar Aunty ta dawo! Kyakkyawar Aunty ta dawo!"

Murmushi ta yi, tun da wuri take son zuwa amma bata samu damar fitowa ba sai yanzu, ta ce

"Ku yi hakuri yau na daɗe ko?"

"Eh kyakkyawar Aunty, har mun ce ko ba ki da lafiya ne"

"A'a Haneef, abubuwane yau suka sha min kai"

"Ku zo mu zauna"

Suka dawo suka zauna, da mamaki take bin wajen da kallo ganin ƴan sanda suna sintiri yasa ta ce

"Haneef me ya faru naga ƴan sanda da yawa suna kewaye wajen?"

"Mu ma bamu sani ba, muna zaune aka shigar da mutane da yawa cikin hotel ɗin, ba mu san me za su yi ba"

"To ni ma zan koma gida, don haka ku yi layi na raba muku biscuits da Alawa"

Nan su ka yi layi ta raba musu, suna karɓa suka wuce gida, ita ma ta yi sauri ta tari machine ta tafi....


********************************

La'asar na yi Alaja restaurant ya kauraye da hidimar ma'aikata, nan da nan suka soma suma aikin tarɓan baƙi, cleaners suka tsaftace ko'ina sai da suka tabbatar babu ko ɗigon datti a restaurant ɗin suka bari, reception sun shirya, waiters/Server's duk sun shirya, chef's su ma ɓangaren su sun shirya abinci kada daban daban da abin sha.

Bilqees da take bangare biyu tafi kowa jin jiki, ta nutsu ta shirya traditional food na gani na faɗa, duk da tana da ƙanƙanta shekaru a cikin su amma girki baya bata wahala ko kala nawa ne ta kan girka shi.

Sai da suka kammala girke girke-girken sannan suka tsaftace kansu. ALAJA ganin komai yana tafiya kan tsari yasa ta soma sakin fuska tana jin farin ciki ko ba komai wannan karon ma ba zata ji kunya ba.

Bilqees tana shirin fitowa Majada ta ce 

"Special chef"

Ta tsaya ba yabo ba fallasa fuskar ta a sake, ta ce

"Na'am Majada, ya aka yi?"

"Yunwa nake ji"

Ta taɓe baki, tare da cewa 

"Ga ki ga kitchen"

"Wannan abincin ya ko zan mutu ba zan samu ci ba, don Allah na san ba a rasa abin taɓawa a jakar ki ba"

Sauke ajiyar zuciya Bilqees ta yi ko ita ba a bin da ta ci tun safe ban da biscuits da ta ci ta sha ruwa akai ta dubi majada tare da cewa 

"Mu je side na Server's jaka ta tana cen"

Suka fito suka wuce, Laraba da Jummai suka sauke numfashi tare da kallon junansu suna ayya abubuwan da za su yi wa Bilqees su huce.

Bilqees suna isowa ta baiwa Majada biscuits ita ma ta ci suka ɗaura da ruwa, sun jima suna hira sannan majada ta tafi bangaren su........

____________________________

A dinga yin comments wajen ƙarfafa min gwiwar yin typing please, much love you fan's.


Comments and share fisabilillah