BARRISTER SUHAIL

96

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL"

🅿️----96


Suhail ya ci gaba da bin motar 

Zeenah ba tare da ta lura da shi ba

Ya bar tazara tsakaninsu

A zuciyarsa kuwa

Tambayoyi ne kawai suke yawo

“Ina take zuwa kullum?”

“Me take ɓoyewa?”

Motar Zeenah ta bar babban titi

Ta shiga wata ƙaramar unguwa da Suhail bai taɓa zuwa ba

Ya ci gaba da binta a baya

Bayan wasu mintuna…'

Ta tsaya a gaban wani tsohon gida

Ba wani katafaren gida ba ne

Gida ne irin na talakkawa

Zeenah ta fito

Ta ɗauki wata leda daga cikin motarta

Ta shiga ciki

Suhail ya faka motarsa daga nesa

Ya fito a hankali

Har yanzu zuciyarsa na bugawa

A hankali ya ƙarasa bakin ƙofar gidan

Tun kafin ya shiga

Ya ji muryar wata tsohuwa

"tana yiwa zeenah barka da zuwa"

“Allah ya saka miki da alkhairi, ’yata"

"yadda kike taimakana,Allah ya taimake ki duniya sa lahira"

Sai muryar Zeenah ta amsa cikin tausasawa

“Kar ki damu mama Allah baki lafiya"

“Na kawo magungunanki"

“Likita ya ce ki tabbatar kina sha akan lokaci"

Suhail ya tsaya cak

Cikin mamaki ya ɗan leƙa

Ya ga Zeenah tana zaune kusa da wata tsohuwa mai fama da rashin lafiya

Da hannunta take bata magani

Ta gyara mata filo

Ta kuma bata Abincin data kawo mata Babu girman kai

Babu ƙorafi da nuna ƙyama

Sai kulawa

Suhail ya lumshe idanunsa.

A hankali ya sauke numfashi

“Ashe ba abin da nake zato ba ne"

Sai kuma wata yarinya ta fito daga ɗaki

“Anti Zeenah"

“Likita ya ce yau za a sake zuwa dialysis"

Zeenah ta jinjina kai

“Eh ba manta ba zainab"

“Na riga na biya kuɗin yau"

"idan taci Abincin sai mu tafi"

Suhail ya sake zaro ido

Yana tsaye yana kallonsu

Ya fara jin kunyar zargin da ya yi mata

A hankali ya juya

Ya koma cikin motarsa

Ya jingina da kujerar direba

Ya dafe kansa

“Ya Allah…”

“Na zarge ta"

“Na yi ta tunanin ba daidai take yi ba"

“Ashe alheri take yi a ɓoye yaushe zeenah ta fara taimakon mutane"

Bai san cewa…

Tun watanni da suka gabata

zeenah ke fama da Rashin lafiyar da babu wanda ta sanarwa 

a lokacin da take zuwa asibiti ta ta hadu da wannan tsohuwar dake fama da ciwon koda

anyi masu bill sun kasa biya 

zeenah ce ta biya kudin komai sannan ta maidasu gida 

take kuma zuwa kullum tana duba lafiyar

duk sanda ta kuma kwana waje kuwa tana a asibiti likita ne ke riƙe idan condition din yayi worse 

A hankali Suhail ya kunna motarsa

Ya koma gida

Amma zuciyarsa

Ta ƙara nauyi fiye da yadda take.

Ya san dole ne

Ya nemi gafarar Zeenah

Bai san cewa

A wannan lokacin

Wata cuta mai tsanani da Zeenah ta daɗe tana ɓoyewa daga kowa

Ta fara shiga sabon mataki

Tun daga ranar

Suhail ya daina kallon Zeenah da irin kallon zargi da yake yi mata

Sai dai

Wata tambaya ta kasa fita daga ransa

“Me ya sa ba ta taɓa gaya min gaskiyar Abinda take aikata wa ba"

Da yamma

suhail Ya dawo gida da wuri

Khalil yana zaune yana wasa a falo

Da ganin mahaifin nasa ya ruga da gudu ya rungume shi"

“Abba"

Suhail dake gefe ya ɗauke shi yana murmushi

"jarumina?”

Jennifer ta fito daga kitchen

“Sannu da zuwa Sir"

“Yauwa Jennifer"

Ya ɗan yi shiru kafin ya ce,

“Ina zeenah"

“Ta na ɗaki Sir"

Kai tsaye ya nufi ɗakin Zeenah.

Ya tarar da ita kwance a kan gado

Fuskarta ta rame

Ba ta da kwalliya kamar yadda ya saba gani

Da ta gan shi, ta yi ƙoƙarin tashi

“Ka dawo?”

Ya ƙarasa kusa da ita

“Lafiya kuwa zeenah"

Ta yi murmushi mai rauni

“Lafiya lau.”

Ya lura hannunta na ɗan rawa

“Kin ci abinci"

Kai ta girgiza

“Ba na jin yunwa.”

Ya haɗe gira

“Tun yaushe?”

“Tun safe"

Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu

Can Suhail ya ce

“Na san inda kike zuwa"

Nan take idanunta suka ɗago

Ta zuba masa ido cikin mamaki.

“suhail ka biyo ni kayi"

Kai ya jinjina

“Eh Saboda ina san sanin inda kike zuwa"

Hawaye suka cika idanunta

“Ban so ka sani ba"

“Saboda me?”

Ta sauke numfashi

“Saboda ban yi shi don a yaba min ba"

“ina yi ne saboda Allah"

Suhail ya sunkuyar da kai.'

“Ki yafe min zeenah na zarge ki"

“Na yi tunanin wani abu dabam"

Ta yi murmushi

“Ba komai ya suhail"

“Da ni ma a matsayinka…nake watakila zan yi irin wannan tunanin"

Ya ce cikin sanyin murya

“Nagode da kika fahimce ni"

“Kin sa na ƙara sanin halinki"

Ta yi dariya kaɗan

“Ka makara da sanina zeenar da ka sani a baya ba ita bacw Yanzu a gaban ka"

Dukansu suka yi shiru

Sai kwatsam

Zeenah ta dafe ƙirjinta

Wani irin tari mai ƙarfi ya ƙwace mata

Ta ci gaba da tari ba ƙaƙƙautawa

Suhail ya yi saurin tallafa mata

“Zeenah!”

Ta yi ƙoƙarin cewa

“Ba...ba komai…”

Amma kafin ta ƙarasa

Sai wani ɗan jinin ya fito tare da tari

Suhail ya zaro ido

"Jini?”

Da sauri Zeenah ta share bakin nata

“Ba komai ne"

Ya ɗaga murya

“Ba komai bane kamar ya zeenah jini fa nake gani"

Ta yi shiru

Ya kamo hannunta

“Yanzu za mu tafi asibiti"

Da sauri ta girgiza kai

“A’a basai munje ba"

“Don Allah"

“Ba na son zuwa"

“Likitana ya san komai"

Suhail ya tsaya cak

“Likitanki?”

Ta lumshe idanunta

Ta gane

Sirrin da ta daɗe tana ɓoyewa dole yau ya fito

ta gyara zaman ta ce"Suhail ina fama da rashin lafiya long time ago"

Suhail ya dubeta cikin tausaya ya ce"zeenah miyasa tun farko kika ƙasa sanar dani har ciwon ya kai wannan matakin a jikin ki"

murmushi tayi ta Girgiza kai 

"ya suhail a lokacin kona faɗa maka batani kake ba"

"shiyasa naga fadin bashi da amfani"

jakar ta buɗe ta dauko takardun asibitin da take zuwa ta bashi

a hankali ya soma duba dan ciwon ya jima a jikin ta har ya kai wani stage da bai kamata ya je

Suhail ya rasa Abinda ke damunsa

ya tausayawa zeenah ya kuma ya tsani kansa duba da yadda yake nuna halin ko in kula a kan ta musamman tun bayan fitar iman daga gidan

a ganin sa Saboda bai zama namiji mai adalci ba

duk da haka taki fada masa abinda ke damunta

Cikin dare

Kwatsam Zeenah ta tashi da wani irin tari mai tsanani

Ta dafe ƙirjinta

Numfashinta ya fara ɗaukewa

“ Suhail…”

Da sauri Suhail ya tashi daga barcin da bai yi nauyi ba

“Zeenah!”

Ya yi saurin riƙe ta

Fuskarta ta canza kala

Numfashinta yana fita da wahala

Sai kuma ta fara tari

Jini ya fito daga bakinta

Gaban Suhail ya faɗi

“Jennifer ya kira a dakin ta"

tare suka dawo ya ce"

“Ki kawo ta mota da sauri!”

Cikin ruɗani suka fito da ita

Khalil ya farka yana kuka

“Abba… Mama…”

Jennifer ta rungume shi tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali

Suhail kuwa

Kai tsaye ya garzaya da Zeenah zuwa asibiti da ta faɗa masa take zuwa

har ya tafi sai ya koma ya dauki Khalil da jennifer

Da suka isa

Likitoci suka karɓe ta cikin gaggawa

Aka shigar da ita ICU

Ƙofar ta rufe

Suhail ya tsaya a waje

Numfashinsa ya rikice

Bai san lokacin da ya ɗauki wayarsa ba

Ya kira mahaifiyar Zeenah 

“Umma…”

Muryarsa na rawa

“Don Allah ku zo asibitin haiiwan"

“Zeenah bata da lafiya"

tashin hankali ya mantar dashi dare ne ya kuma manta a abuja suke

Cikin ƙanƙanin lokaci

Alhaji Ibrahim da Hajiya Rabi suka iso garin Abuja map suka duba ya kai su har asibitin

Da suka ga Suhail

Sun gane abin ya wuce yadda suke zato 

Likitan ya fito daga ICU

Fuskarsa cike da damuwa

Ya cire safar hannunsa

Ya dubi Suhail da Alhaji Ibrahim

“su biyosa office"

Da suka shiga…

Likitan ya buɗe file ɗin Zeenah

Ya ɗora hannu a kai

“Mr. Suhail"

“Wannan ba shi ne karon farko da Hajiya Zeenah take zuwa wannan asibitin ba"

Suhail ya haɗe gira

“tun yaushe, Doctor?”

Likitan ya ce

“Tsawon kusan watanni shida muna kula da ita"

Suhail ya tsaya cak

“Watanni shida?”

“Eh 6 month"

Suhail ya tuna cikin watannin kusan kullum sai zeenah ta fita

likita ya cigaba da cewa

“Ta roƙe mu kada mu sanar da kowa"

“Hatta ku makusan tanta"

Suhail ya zaro ido

“Me take fama da shi?”

Likitan ya sauke numfashi."

“Zeenah tana fama da Lung Cancer"

“An gano cutar ne a mataki na uku"

“Mun fara chemotherapy"

“Da farko muna ganin za ta amsa magani"

“Amma…”

Likitan ya yi shiru

Ya buɗe sakamakon CT Scan

“Cutar ta jima"

“Yanzu tana Stage Four a jikin ta"

Alhaji Ibrahim ya kama kujerar da ke gabansa

“innalillahi wa inna illlaihir raji'un”

Likitan ya ci gaba

“Mun yi duk abin da ya kamata.”

“Mun ba ta magunguna"

“Mun yi mata chemotherapy"

“Amma jikinta ya daina amsa magani gaba daya"

Suhail ya dafe kansa

Hawayensa suka fara zuba

“Doctor…”

“Me ya sa ba ta gaya mini ba?”

Likitan ya ce cikin tausayawa

“Duk lokacin da muka ce ta sanar da iyalanta"

“Sai ta ce"

‘Ba na son su tausaya mini Ina so su tuna ni cikin murmushi, ba cikin ciwo fada ma makun san tanta zai daga daga masu hankali"

Suhail ya fashe da kuka

“Wannan wace irin rayuwa ce take zo masa cike da jarrabawa haka …”

Likitan ya ƙara da cewa

“Abin da ya rage yanzu"

“Shi ne mu rage mata ciwo kawai"

“Ku kasance tare da ita"

“Ku yi mata addu’a" 

don tafi buƙatar a halin yanzu

Bayan likitan ya gama magana…

Shiru ya mamaye office ɗin.

Babu wanda ya iya furta ko kalma ɗaya

Suhail ya jingina da bango

Idanunsa sun yi jajur saboda hawaye

Ya kasa yarda cewa duk wannan wahalar 

Zeenah ita kaɗai take ɗauke da ita tsawon watanni ba tare da ta sanarwa kowa ba

Alhaji Ibrahim ya dafe kansa

“Me ya sa kika ɓoye mana halin da kike zeenah,ko kina gani kamar bazamu saurare ki ba duk taƙurawar da muke maki ba wai dan bama sanki ba don ki zama ta Gari ce"

Hajiya Rabi kuwa

Tun da ta ji kalmar lung cancer, ƙafafunta suka kasa ɗaukarta

Ta zauna a ƙasa tana kuka."

“Zeenah"

Da me kika ji tsoron gaya mana?”

Likitan ya matso kusa da su

Cikin tausayawa ya ce

“Za mu iya shiga yanzu ku ganta"

“Amma kada ku sa ta gaji da magana"

“Yanayinta yana da rauni sosai"

Suhail ya share hawayensa

A hankali ya buɗe ƙofar ICU

ko ya shiga

like 
share 
and comment