28
by @gureenjoh
"Ya dai?"
Ammar ya tambaya yana ɗan kallonshi while driving.
Ya saki goshin yana zubawa titi idanu ya furta
"Babu, gajiya ce kawai"
Babu wanda ya sake magana cikinsu har suka isa gida, kusan mutanen gidan sun fito yi mishi maraba don suna da wannan ɗabi'ar a gidan idan wani yayi tafiya ranar da zai iso za su fito duka su jira saukarshi daga mota a yi maraba kan a barshi ya je ya shirya ya kuma bibiyi iyaye yayi gaisuwa da fatan samunsu lafiya.
Yanzu ma sun yi murnar ganinsa Sossai, cike da kaunar ahalinshi yake amsa sannu da dawowa da suke mishi tuni Mufida da sumayya sun ja trolley dinshi da jakar system sun nufi sashenshi kan ya gama ya nufi sashen ma sun fito, cikin natsuwa ya shiga sashen dake ta fidda kamshi ya san aikin kannenshi ne bisa umurnin Maamah don har abinci gashi an jere mishi.
A natse ya haura samanshi, ya wuce parlorn zuwa bedroom ɗin shi da sallama kan lips ɗin sa sai yake jin kaman ya shekara ba ya gidan yayi kewar Kano Sossai ashe bai farga ba.
Rage kayan jikinshi yayi don ba ya jin zai fita wajen ma sai azahar, farin dogon wando na yadi da farar shirt ya saka, shirt din irin mai roba da ke kama jiki ne don haka ya fitar da kirarsa gabadaya wuyan kuma V line ne mai guntun hannu, bayan ya feshe jikinshi da turarukansa masu sanyin kamshi ya nufi parlorn ƙasa a chan ya zauna ya karya don tun jiya sai a lokacin yake sa wani abu bakinshi.
Yana cikin cin abincin ne Imam ya shigo bai takura masa ba sai ya zauna a parlor har ya gama ya zo ya samesa yana zama hurairah na shigowa da gudu ya dauketa ya sakata kan cinyarsa yana shafa gashinta.
"Ya hurayr kaif haluki? Istaqtu ilayki..."
Ya furta da murmushi don da ma ba hausa yake yi wa kuliyar ba kuma jin yaren take tsaf na larabci
"Hurayr kina lafiya? Na yi kewarki"
Imam yayi murmushi yana miƙa gaisuwa Shehi na cigaba da shafa kuliyar suka gaisa, nan Shehi ya fara tambayar sa abubuwan da suka faru ba ya nan wani Imam din ne zai tuna ya faɗa masa wani kuma zai tambaya sun jima suna magana kan ya tafi, shi kuma Shehi ya haura sama yana ɗan sa hannu cikin gashin kansa da ya ji yana bukatar ragewa don ya fara damunsa, system ya janyo ya shiga inda ya tsaya da batun companyn Abbiey shawarar Sheikh Nasser ya bi sai gashi ya fara ɗaukar haske cikin kankanin lokaci.
****
Khalil ne tsaye kofar gidan da aka yi mishi kwatance sallama yake yi cikin ɗaga murya har aka amsa, bai jima yana tsaye ba wani yaro ya fito
"Yaro ina neman Malam Sule ne"
"Yana ciki"
"Ka ce mishi yana da baƙo"
Komawa yaron yayi chan sai gashi ya dawo
"Wai ka shigo"
Bin bayan yaron yayi zuwa ciki yana kallon gidan ganin yadda yake nan a rushe rabi da kwata daki daya ne na taɓo wanda aka rufe bakin da buhu daga gefen bishiyar tsada ya ga wani dattijo da wahala da talauci suka bayyana jikinshi zaune kan wani kujera.
Tsugunawa yayi
"Baba ina yini?"
"Lafiya yaro, ka zo lafiya?"
"Alhamdulillah baba"
Sai yayi shiru ya rasa me zai ce ya zubawa almajirin dake dibo ruwa daga rijiyar gidan yana zubawa a randar dake gefen ɗakin.
"Sai dai ban sheda ka ba yaro"
Numfashi ya sauƙe kaɗan yace
"Sunana Khalil na zo daga Kano ne"
"Wai wai wai ashe daga nesa kake yaro sannu da zuwa! Kai Usmanu kawo masa ruwa"
"A'a Baba ai ba ma yau na zo ba tun jiya ne, da ma na zo ne kan maganan 'yarka Zubaidah"
Tuni jikin wannan dattijo ya fara rawa cikin rawar murya yace
"'yata? Ƴata Zubaidah?"
"Kwarai kuwa Baba..."
Sai dattijon ya fashe da kuka mai tsuma, kukan da ya ɗaga hankalin Khalil.
****
"Ranka ya dade akwai matsala fah!"
"Matsala? Meyasa za ka kiramin matsala?"
"Ranka ya dade wannan yaro ya fa fara shirin bankaɗoka idan ma bai bankado din ba kenan don bincike ne ke shigar da shi cikin wani binciken"
Da hanzari ya miƙe tsaye ya fara jeka ka dawo zufa na karyo mishi.
"Dole a yi wani abu! Dole a yi wani abu..."
Ya maimaita ya kai sau hudu kan ya katse wayan"
*****
Fadar gomnati, zaune yake yana nazari idanunshi na kan fai-fain videon da aka mishi playing na wa'azin Irshad na bayan magrib da ya dawo a ranar wa'azi ne da ya ɗaga masa hankali.
Musamman a lokacin da Irshad ya kalli camera ya ce
"Wannan saƙo ne zuwa ga kai shugaba marar adalci mai mantawa da Allah...
Ya kai shugaba! Ka tuna cewa kujerar da kake kai ba za ta bi ka kabari ba. Duk ikon da kake da shi a yau amana ce daga Allah, ba mallakarka ba ce.
Idan kana neman ci gaba da mulki saboda hidimar al'umma da adalci, Allah Ya taimake ka. Amma idan kana neman zarcewa ne saboda son mulki, girman kai, ko tsoron rasa iko, to ka tuna cewa ranar da za ka tsaya gaban Allah ba za ka zo da jami'an tsaro, kuɗi, ko mukamai ba.
Manzon Allah ﷺ ya ce:
"Kowannenku makiyayi ne, kuma za a tambaye shi game da abin da aka ba shi amana."
Shugaba ba sarki ne a kan bayin Allah ba; bawa ne da Allah Ya ɗora wa nauyin jama'a. Hawaye na maraya, kukan al'umma, yunwar talaka, da zaluncin da aka yi wa mabukata ba sa ɓacewa a wajen Allah.
Ka ji tsoron ranar da mulki zai ƙare, amma hisabi bai ƙare ba. Ka ji tsoron ranar da waɗanda ka zalunta za su karɓi hakkinsu a gabanka. A ranar ba kuɗi za su amfana ba, ba iko ba, sai ayyukan ƙwarai.
Ka tuna: mutane na iya tsoronka a duniya, amma kai ma kana ƙarƙashin ikon Allah. Wanda Ya ba ka mulki zai iya ƙwace shi a lokacin da bai zo maka a zato ba.
Saboda haka, ka yi adalci. Ka guji zalunci. Ka tuna cewa shugabanci ibada ce idan an yi shi da gaskiya, amma babban nauyi ne idan aka mayar da shi hanyar son kai da tauye haƙƙin mutane"
Masallacin yayi tsit babu tsoro ko shakku ya cigaba da jan hankalin mutane akan tashi tsaye su kwatarwa kansu 'yanci daga azzaluman shuwagabanni daga ƙarshe ya rufe da adu'a
"Allah Ya shiryar da shugabanninmu zuwa ga adalci, ya kare al'ummar annabi Muhammad (SAW) daga zalunci, Ya sa mu kasance cikin masu tsoronSa da kiyaye dokokinsa Ameen"
Kalaman sun zo wa Bashir dantani ta fuskoki biyu, dukda wani zuciyar na cewa ba da shi yake ba amma saboda ya san kanshi sai yake jin kaman da shi yake kai tsaye, ji yake kaman zai iya faduwa a yadda Irshad ke nusar da mutane da jan hankalinsu kai har sunanshi yaji yana amsa kuwwa da muryar Irshad na cewa mutane da shi yake kar su zaɓe shi.
Scrolling yake yana duba comment section na wa'azin, wasu na tamabaya kan batun Diva ya dawo bai ce komai ba, wasu na kiran wasu daga cikin azzaluman shuwagabanni suna cewa ya kamata a saka musu don idan wa'azin nan bai shige su ba tabbas sun rasa imani.
Scrolling yayi biyu uku sai ya sake ganin wa'azin a duet wani matashi na kawo ayyukan da yayi ya rubuta daga sama BASHIR DANTANI DA KA SAURARI MALAM
Wa'azin na playing kwaltan da yayi commisioning a satin chan ruwa ɗaya aka yi mai karfi ya kwashe shi har ya fara rami rami, daga nan videon makarantun da ya ce ya kawo tsarin free education har da ikirarin ya kashe makudan kudade kan uniform da zai rabar kyauta sai aka hasko makarantun babu board, babu benchuna babu dai duk abin bukata na karatu yara na zazzaune a ƙasa suna karatu, aka sake hasko asibitoci babu gyara babu kayan aiki da wasu kauyuka da suke fama da rashin tsaro gomnati ta nuna ko-in-kula yana shiga comment dai da ya fi dubu biyu zagi ne da tsintuwa ake mishi wasu na cewa ya gama kenan babu shi ba zuwa senate har wasu na kawo shawarar a tilasta Irshad shiga siyasa ya zama gomna dukda ya nuna baya ra'ayin siyasa kila shi zai tallafawa ƙasar.
Ranshi idan yayi dubu ya ɓaci, Wayanshi ya fidda yana jin dole komai ya zo karshe wannan gaskiya da Irshad ke ikirarin yana faɗa sai dai ya cigaba da faɗarta a lahira. Kira yayi na seconds goma sha biyar kan ya ce
"Za ka ga saƙo"
Daga haka ya katse wayar yana jefar da na hannunshi ya koma ya kwanta kan kujerar dake juyawa da shi idanunshi a rufe.
****
"Pablo fa? Ni sai nake ga kaman bashi da lafiya don tun na dawo na kula yanayinshi ya chanza Sossai"
Diva tayi tambayar tana juya Idanunta a kansu ganin bata ganshi ba kaman yadda jiya ma bai yini da su ba.
"Bai shigo ba fa"
"Ya kamata ku duba shi ai!"
Bata gama rufe baki ba Skipo ya miƙe ya fice ita kuma ta zauna.
"Shugaba ya kamata fah ki ce wani abu kan wanchan banza gajan, me za'a yi masa?"
Tace
"Ya ma sunan shi?"
"Bullet"
Zubash ta faɗa tana kashe Sigarin da take sha
Ta Yi dariya
"Paskal ka duba inda za ka same shi daga yanzu zuwa gobe zai san ya shigo territory ɗin Diva har yana ikirarin shine shugaban wannan kwaltan"
Shaly tace
"Laifin Obafiya ne da bai tarwatsa shege tun kan ki dawo ba"
"Kin san Jagaban ya hana mu duk wani motsi ya ce babu ruwanshi idan wani abu ya faru a yanzu"
"kar ku damu da kaina zan ganshi in yi maganinshi duk inda ya shiga cikin wannan birni"
Dawowar Skipo ya hana kowa magana yace
"Pablo fah ba lafiya Diva!"
Duk Miƙewa suka yi tana tambayar
"Me ya same shi?"
Basu jira amsar shi ba ma suka wuce zuwa gidan sun yi mamakin yadda suka sameshi tuni Diva ta koma ta ɗauko mota Obafiya ya dauke shi zuwa motan suka bar unguwar zuwa asibiti.
An karɓeshi amma bayan tsawon lokaci Likitan yana fito yana kallonsu
"Lafiya Dr?"
Diva tayi tambayar har ranta tana jin tashin hankali don bata son komai ya sami dayansu tana kaunarsu tamkar jininta.
"Patient da kuka kawo ba za mu iya yi mishi komai ba"
"Why? Meyasa alhali ba ya cikin hayyacinshi?"
"Na sani yana sume, kai tsaye zan iya ce muku ya kamu da cutar da ake kira Nerve damage jiyoyinsa sun yi damage duk wani hanyar da za mu bi don basa taimako ba zai yiwu ba don mun nema mun rasa sun ɓace"
"innalillahi wainna ilaihi raji'un"
Yadda suka hada baki suka faɗa sai da Likitan ya sake kallonsu yana jin dariya na shirin taso masa ba na mugunta ba sai don tsantsar mamaki ji yadda suke ambaton Allah.
"A matsayinka na likita na san akwai hanyoyin da za ka iya bi don taimakonsa don Allah ka taimaka ka sake duba shi kar mu rasa shi"
Diva ta faɗa hawaye na cika Idanunta a Karon farko.
Da gangan ya zo ya ce musu ba yadda za su yi dukda hakan ne babu wani jijiya da za'a samu lafiyayye a jikinshi duk sun lalace amma ba shi ya hana suka taimaka masa numfashinsa ya dawo daidai ba, yayi hakan ne don ya tsorata su akan bayanin da zai musu in anjima akan illar Penta da suka gama gane abinda ya kashe duka jijiyoyin Pablo kenan har ya fara haddasa ruɓewar tsokokinsa.
"Ina zuwa"
Ya faɗa yana komawa don ba zai yarda su san da gayya ya tsorata su ba tsaff sai su illatasa a yadda hankalinsu ya tashi.
*****
Shi kam Shehi na haurawa shirin azahar yayi bayan sun gabatar ya dawo yayi bacci bai tashi ba sai la'asar yayi sallah kan ya dawo cikin gida ya fara da shiga sashen Daddah ya gaishe ta ya jima nan har ya ba Mufida Atm akan Malam Bala ya kaisu shopping su sayi abin da suke bukata as tsaraba, manyan kuma a wurin yayi musu transferm kudi masu tsoka su Goggo hindatu na ta godiya don yana da wannan kyauta a kai a kai.
Daga nan wurin Maamah yayi suka gaisa ta mishi godiya kudin da ta gani yayi murmushi kawai, sai ya nufi wurin Ammiey karshe sun taɓa hira ya kuma ci sa'a bata kawo mishi zancen Wanchan yarinyar da ya mance layin ta a inbox don Ammar ya tura mishi tun jiya.
Daga nan ya dawo ya shirya ya fita sallar magrib bayan nan ne ya yamutsa hazo da wa'azin da yayi don ya sosawa mutane ne inda yake musu ƙaiƙayi, bayan isha kuma ya nufi parlorn Abbiey da ya san a chan zai same su da Abba ya ci sa'a kuwa suna nan zaune har da uncle Ishaq da ya fara mishi tsiyar yana mantawa da su saboda shi gidanshi a jikin gidan ne ta waje kuma Shehi gaskiya bai cika shiga ba ribibinshi na dayawa sai in sun haɗu cikin gida a gaisa. Haƙuri ya bashi kan ya zauna suka shiga gaisuwa cikin tsanaki.
Ya sanar da Abbiey batun zuwan Sheikh Nasser duk sun yi murna Abba yace
"Ai to dole a ɗaga batun zuwa neman auren nan sai Ubangidanka ya iso a yi da shi Irshad"
Abbiey ma yayi na'am don wannan aikinshi shine uba ga Shehi.
Sun taɓa hira kan ya bar su ya wuce sashenshi yana tunanin da gaske fa suke auren nan dai shi suke shirin dole sai yayi. Layin yarinyar ya zubawa idanu na seconds kan kuma ya sa hannu yayi copying ya mayar calls ya ƙira.