28
by @sadisakhna
______👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
👑*Warƙa ta (28)*👑
Har muka iso cikin Jami'ar jikina a sanyaye yake ina tsoron wacce irin haɗuwa zamuyi da Hammar,nima nayi zaton a ranar zan dawo,ban kawo a raina zan kwana ba. A bakin bangarenmu na Magani ya sauƙeni inda ya ɗaukeni.
Na kinkimo ɗaurin tsarabata da kayana na shiga. Da wasu bayi na haɗu wanda suke hidima a sashena,suna ganina suka tafi da gudu domin ƙirawo ummu hajar,sai gata kuwa da nufoni da sauri,ɗaurin hanunnawa na miƙa mata,tana karba tayi gaba dashi ta barni a wajen baki sake. Duk da daman hakan ba abun mamaki bane a wajena,haka tsarin yake idan bawa yayi aiki yasamu abin arziƙi to na mai gidansa ne,saidai idan yayi niyya yabashi wani. Wacewa nayi sansaninmu duk da ma tafiyar bawani gajiya ta taramin ba. Bayan naci abinci Na sauke sallah saiga saƙon kayana daga wajen ummu hajar. Buɗewa nayi nagani,bayan kayana dana tafi dashi ta barmin kayan saƙi ɗaya mai kyau ruwan Jibi,sannan da abun wuya na murjani da ɗankunnensu,awarwaro da sarkarsu. Sunyi kyau sosai kana gani kasan na manyan mutane ne. Hakan ma naji daɗi domin wasu ba lallai su bani hakan bama,kuma ni dama ba domin a bani abin duniya naje ba.
Nunawa su Addah rahila nayi suma sukayi ta tayani murna,naso ta bani kaman uku da suma zan basu,amma yanzu haka dasu ummu Asma'u zasu raba.
Sai bayan magriba na samu ƙarfin gwiwar shiryawa naje sansanin su Hammar. Naso na bari sai gobe da safe amma zuciyata sam ta gagara yin hakan,Fasihmman dana tambayi Addah rahila ya yake,hmmm kawai tacemin. Tun daga sannan jikina yayi sanyi.
Wanka nayi na ɗauki kayan da aka banin nasaka harda abun wuyan dukka,ina ayyana a raina ko idan yaga nayi ɗan kyau zaifi karban ban haƙurinnawa.
Jikina babu laka na kama hanyar sansaninsu,ji nake kaman lokaci yafi koyaushe gudu,hasken fitila na hango a ɗakinnasu. A haka na ƙarisa ƙirjina yana dukan uku uku.
Ɗaga asabarin ɗakin nayi na shiga,yana zaune a gaban gadonsa,da riga a jikinsa amma gabanta a buɗe yake ta bayyana faffaɗan ƙirjinsa, Ƙoƙon tsimin magani ne a gefensa,sannan duk da hasken ɗakin ba mai yawa bane amma ina gano yanda numfashinsa yake fita da nauyi. Lokaci ɗaya naji jikina ya sake yin sanyi domin nasan halinda yashiga bazai wuce ta dalilin tafiyata ba batareda na sanar masa ba,kuma hakan ma Masarauta inda Yerima Kabeer yake.
Tsugunnawa nayi a gabansa,daidai lokacin muka haɗa ido,sai a sannan nakalli yanda idanuwansa sukayi ja. Wannan wanne irin kishine dashi hakane na faɗa a raina.
A takaice ya kalleni ya ɗauke kansa zuwa wani wajen daban. Duk sai naji ɗakin yayimin girma.
Dukkan wani ƙwarin gwiwata na tattaro nace.
"Kayi haƙuri Hammar nasan ranka ya baci na tafiyar danayi batareda na faɗa maka,amma babu yanda zanyi ne tafiyar ce tazomin a sauri shiyasa na tafi,kuma banyi zaton abun har yakai haka ba da zai sakani na kwana"
"Taya zaki iya fuskantata ki sanar dani cewar zaki tafi wajen namiji daya nuna zai iya kashe miki ƙishirwa,nima kuma tunda farko da kin faɗamin ai dazaki samu hakan daga gareni idan shi kike so........Na ɗaga hankalina da tunanina,babu nutsuwa a tattare dani duk a zatona wani abune yasameki,a yanda naga rana haka naga dare sai daga baya labarin kin tafi Cikin Masarauta ya riskeni,ina nan zan kashe kaina ashe ke kina can kina tare dashi......."
Fincikar hannuna yayi yajawoni jikinsa cikin zafin nama,zuwa lokacin idanuwansa sun zama ja tamkar wuta. Cigaba yayi da maganar sa cikin zafin nama tamkar gunjin Zaki.
"Kinsan wanne mataki nabi dan kareki daga gareshi watannin baya kuwa? Kinsan wanne irin hukunci nake jurewa a kullum idan ina tare dake duk ta sanadiyyar rabaki dashi danayi. Amma shine ki ka ɗau ƙafarki da kanki kikaje inda yake yayi miki abinda kikeso koh?"
Saurin jijjiga kaina nayi,har sannan jikina yana rawa kamar an jonamin wutar lantarki.
"Wlh Hammar ba wajensa naje ba,kuma koda muka haɗu guduwa nayi bayyimin komai ba,dan Allah kayi haƙuri nasan matsayinka a wajena wanda hakan yasa nayi alƙawarin bazan taba bawa wani ɗan adam dama akaina ba,dan Allah ka yarda da magana ta........."
"Ya isa haka Joda,shin wanne irin Zunubi na aikata aka jarrabeni dake,wataƙila watarana sai kinyi ajalina "
Jijjiga kaina nasake yi da sauri ganin ya lumshe ido numfashinsa yana fixga....bansan lokacin dana faɗa jikinsa na rungumeshi ba da ƙarfi.
Sauke a jiyar zuciya naji yanayi a hankali har numfashinsa yafara daidaita.
"Ina Azabtuwa da kasancewar ki a taredani,amma nesantarki dani yafi komai Illata rayuwata. Kula wani dazakiyi a rayuwarki bayanni Alhali ina numfashi abune na bazan iya yafewa zuciyarki ba Joda,Ba so nakeyi miki ba abinda yafi So ruhina yakeyi miki."
"Kayi haƙuri....."
Shine abinda na furta cikin sheshshekar kuka,dan bansan mai zance ba ida ba hakan ba.
Ina ji yafara yawo da hannunsa a jikina amma na gagara hanashi,saidai sheshsheƙar kuka danakeyi a hankali har abunnasa yafara nisa kuma yafara wuce tunani na.
Janyewa nake ƙoƙarin yi daga gareshi,amma naji ya riƙeni Gamm yahanani motsawa da wannan ƙarfinnasa. Sannan yacigaba da miƙamin saƙon da suka girmi ƙwaƙwalwata amma yaka nacigaba da ƙarba babu yadda zanyi.
Cikin sheshsheƙar kuka na haɗa ido dashi,wanda zuwa lokacin sai numfarfashi kawai yakeyi yanason fita a hayyacinsa.
"Dan Allah Hammar karka aikatamin abinda zuciyarka take faɗamaka a yanzun,wanda a zuwa gobe zamuyi danasani dagani har kai. Nasan da cewar ka taimaki rayuwata,sannan kana ƙoƙari wajen ganin ka taimakeni akan burina. To amma abinda kake shirin aikatawa bazaimin komai a rayuwata ba sai ruguzata da kuma maidata baya. Kafi kowa sanin babu wannan abun a cikin mafarkin rayuwata,kada ka zama mutumin dazai ruguza wannan mafarkin. Bazan yimaka turjiya ba kokuma gardama a matsayinka na mamallakina,amma kuma hakan zai bar yanka a cikin zuciyata wanda banajin zai iya warkewa"
Ina kallon yanda maganganuna suke tasiri a cikin kansa,amma kuma akwai wani abu a idonsa wanda tun lokacin daya fansheni yake girma a cikin idonsa,a yau naganshi sosai da har ya tsorita zuciyata.
Jijjiga kansa yayi kafin yayi magana cikin wata karyayyar murya.
"Kiyi haƙuri Joda,ni kaina idan za'a tambaye ni sau dubu bazan zabi aikata abinda zan aikata a yanxun ba,to amma akwai wasu abubuwa dasuka faru a rayuwata a cikin watannan da ban faɗamiki shi ba. Sannan bugu da ƙari bazan iya sake ganinki kina yawo a tsakanin maza ba kina matsayin mallakina kuma ban mallakeki ba,nikaina a rayuwata abinda zan aikata fentine da bazai taba gogewa ba.
Soyayyar ki,ƙaunarki,haushinki dakuma kishinki da nesa dani da kikayi sun tashi wani abu a cikin kaina dana jima ina ƙoƙarin sakashi bacci. Dan haka karki zargeni ni kaɗai saida nidake dukka gabaki ɗaya"
Yana gama faɗin hakan naji yaratsa ƙofar mutuncina,darajata yashige yana iyo a ciki. Ko kaɗan na hana jikina yimasa gardama,duk da kuwa tsananin azabar danakeji yana shiga har cikin kaina. Runtse idona nayi ina karba hakan da hannu bibbiyu,idan shine ƙaddarata na karba kuma na godewa ubangijina duk da haka,saboda nasan ni'imomin dayayimin a matsayina na baiwa ya ninka na bayi bila adadin irina. Duk da zuciyata tana jin haushinsa a lokacin amma nazabi kawo uzuri nayi masa,domin bakowane za'a saka a takalminsa cikin manyan mutane ba yayimin abinda yayimin.
Ina jin yanda yake sambatu yafita hayyacinsa amma nakasa buɗe ido na kalleshi,idan na tunda na rasa kimata bata hanyar aure ba sai naji Zuciyata tana zafi,amma kuma idan na tuna Ubangidana na bawa kuma mamallakina bawai zina nayi ba sai naji hakan ma nagode Allah.
Munkai kamar sa'a ɗaya da rabi ina karbar ƙaddarata a hannunsa,sai daga baya bayan komai yalafamasa kafin ya zube akaina yana maida wani irin numfashi,nan da nan jikinsa yaɗau wani zafi mai tsanani. Taba kumatunsa nayi sannan ga wani numfashi dayake furzawa a wuya na. Tattara ɗan ƙaramin ƙarfin daya barmin nayi na mirginashi gefe kan gadon. Kafin nima na tashi na maida suturata.
Cikin dauriya da kuma sabawa da rayuwar ƙalubale na miƙe na fita daga cikin ɗakin ina daddafa bango.
Har sannan babu kowa a sansanin,ko ina abokinnasa yatafi oho, saidai nagode Allah da babu wanda yaji ihun dayayi tayi. Kallon jikina nayi kana na sauƙe ajiyar zuciya,yanzu idan na nufi sansaninmu a haka wanne irin kallo zasuyimin kenan. Shin wacce amsa nima zan basu,ballantana idan suka kalli jinin dayake bin cinyata. So nake na fashe da kuka amma zuciyata taƙi bani haɗin kai sam.
Wajen da suke haɗa wuta na nufa ina jan ƙafafuna da sukayimin nauyi da sanyi ƙalau.
Allah yasa akwai itace da komai a wajen,sannan tukunsu a cike yake da ruwa,dakuma wani a ƙarami a gefe ba komai a ciki.
Wutar na haɗa na ɗora ƙaramin tukun ruwan akai,wanda dama dashi suke dafa ruwan zafi,ina kallon yanda take ci,da haka har yayi zafi na diba naje na gasa jikina sosai a bayan gidansu. Sannan nayi wankan tsarki na fito.
Har naji wani karfi ya jiyarceni ba kaman ɗaxun ba da jikina yake mace.
Niyya nayi na kama hanyata nabar wajen,amma kuma sai wata zuciyar ta hanani. Komawa nayi cikin ɗakin,yana nan inda na mirgani shi bai sauya kwanciya ba. Gashi ya tuƙuƙune jikinsa sai karkarwa yake. Mamaki abin ya bani,kardai bai taba sanin mace ba kai sai yanzu. Amma haka zai yiwu kuwa,yace yanada mata kodai yana faɗane kawai.
Ƙarisawa nayi inda yake na jijjigashi,idonsa biyu amma bai juyo ba.
Ganyen shuwaka dana Darbejiya,sai dogon yaro na saka a karamin ƙoƙo na ɗora a kan wutar,tunda zazzabin nasa bana wani ciwo bane sosai suma zasu iya taimaka masa.
Farin tsumma na ɗauka da ruwa nashiga ɗakin ina goge masa jikinsa. Saida naji zafin ya ragu sosai kafin na dawo na ɗauki ɗebi maganin nakai na ajiye domin yayi sanyi.
"Katashi kayi wanka zazzabin ya ragu,kazo kasha magani kafin ya dawo"
Buɗe jajayen idonsa yayi yana kallona,nasan bazai wuce yana mamakin mai yasa ban tafi ba duk da abinda yayimin laifinsa mai girma ne.
Tashi yayi shima cikin dauriya ya nufi bayin,dama na kai masa ruwa bayan dani nayi. Ya ɗau ɗan lokaci sai gashi ya dawo daure da mayafi a iya kunkuminsa,ɗauke idona nayi har yaxo ya zauna a gefena yana rawar sanyi. Ɗaukar wani mayafin nayi na yafa masa kafin na miƙa masa ƙoƙon maganin. Karba yayi batareda musu ba yafara sha,bai shanye ba amma yasha da yawa kafin ya ajiye ƙoƙon a gefe.
Kallona yakeyi yana so yayi magana amma yakasa,wanda nasan bazai wuce haƙuri zai bani ba,domin duk da alamar danasani da kuma amsar laifi sun nuna a fuskarsa,tunda ya mallakeni na kula wani abu yana jansa gamedani,to yau gashi nan yacika burinsa ya cika. Banyi ƙarya ba idan nace ina jin haushinsa,dan yanzun ma tafiya zanyi,domin banason jin kowacce irin kalma daga gareshi.
Numfasawa nayi kafin na yunƙura na tashi.
"To tunda kasha maganin nasan zazzabin zai lafa maka da ikon Allah,ni bari zan tafi gida saida safe"
Nazo wucewa ta gabansa naji yakama hannuna,
"Dan Allah kiyi haƙuri Joda wlh........."
"Dan Allah karka cemin komai banason jin komai daga bakinka, kada kaga wai na tsaya taimaka maka kayi zaton wai banji zafin abinda kayimin ba, naji zafinsa fiyeda yanda kake zato,dan haka ka barni natafi shine abinda nake matuƙar buƙata a yanzu"
Ina jin yasake hannuna nayi hanyar waje da sauri na nufi sansaninmu. Kaina sai tariyomin abinda yafaru tsakanina dashi yake, ina zuwa zan haɗa maganin kashe zafi nasha,nasan idan ba haka ba kafin gobe idan wajen yayimin tsami to kowa sai yasan abinda na aikata. Yanzunma tunani nake shin da wanne irin ido zan kalli Su Addah rahila idan suka gano abinda na aika ta,don nasan dole sai sun gane. Wayyo Allah na wayyo ni Joda.
(Hammar)
Jikina sanyi yayi danaji furucinta,hakanne yasa na saketa badan inaso tayi nesa dani ba ko don nagaji da ganinta ba. Nayi zaton idan na aikata abinda zuciyata ta daɗe tana muradi zan samu nutsuwa,amma sai naji kamar an huramin wutar ruruwar soyayyarta da kuma buƙatar kasancewa da ita a kodayaushe cikin rayuwata har abada.
Ban taba sanin ya ƴa mace take ga namiji ba sai a yau,ji nake kaman bazan iya kaiwa gobeba batareda da sake kasancewa da ita ba. Saboda tsabar yanayin dana shiga har zaucewa nayi bansani ba. Ƙishirwa dake cina a yanzun har ta ninka ta wanda naji kafin komai ya faru. Tabbas tayi gaskiya da tace zamuyi nadamar faruwar hakan,gashi inayi tun kafin aje wani lokacin.
Sauran ruwan maganin na ɗauka na shanye ina kallon cikin ƙoƙon,ji nake inama ta sauya tunani ta dawo gareni,a yau ɗin ina jina a cikin kaɗaicin da ban taba tunanin samun kaina a ciki ba.
Sallamar fasih naji yashigo,har ya tsugunna yana gaisheni ban ɗaga kai na kalleshi,saida naji yayi wata magana tukunna.
"Ranka ya daɗe wannan fah a gefenka kamar abun wuyan Mace"
Kallon wajen nayi,murjanin Joda ne wanda tashigo dashi,kafin nayi magana ko motsi yaje ya ɗauka,daidai lokacin yakalli jinin dayake kan mayafin kan gadon,ni gabaɗaya ma na manta ban ɗauke ba.
"Ranka ya daɗe.........."
"Na Joda ne,Kasan matsayinta kuma a wajena,sannan kasan bazan aikata zina ba dai ko da ƴar wani ko baiwar wani idan ba tawa ba"
"Ta dawo kenan,amma ranka yadaɗe Allah yasa ba halinda kake ciki kwanannan bane yasa ka haike mata da ƙarfi ba,bari to a gyara ɗakin naga kaman yanayin ya haddasa maka zazabi,dama yanayi wa wasu a karo na farko,sannu yallabai"
Yana yiwa wasu haka a karon farko,kenan shiyasa bata tambayeni mai yasakani zazzabi ba,ashe tasani.
Saurin katse tunanin nayi na nufi fasih da sauri ganin yana shirin ɗauke mayafin dayake ɗauke da budurcin Joda.
Ɗaukewa nayi da kaina,domin ji nayi baxan iya barinsa ya taba ba.
"Wannan barshi zan wanke ko zuwa gobe da safe idan na samu sauƙi"
Da mamaki yake kallona dayaji nace zanyi wanki,amma haka na basar na tashi nayi sallahr ishe kafin na kwanta.
Kwanci tashi anyi sati guda da faruwar wani abu tsakani na da Joda,kuma har yau bata kara zuwa inda nake ba,kuma tun daga wannan ranar nake ƙishirwar zumar data lasamin a bakina ta tafi ta barni. Ga wani irin ciwo da marata takeyi,jarumtakar gidan sarautar danayi shekara da shekaru banidashi,shine ya bude sanadiyyar sanin mace danayi yakemin rubdugu a lokaci guda.
Naje sansaninsu Bayan kwana uku nemanta tacemin nayi haƙuri bazata fitoba,tun daga nan bansake nemanta,sai wasiƙa danake tura mata na ban baki kawai. Shima bata taba meyarmin da amsa ba. Iya fasih ne kaɗai yasan halinda nake ciki,nazama wani iri ko abinci bana ci sosai.
Washagarin satin muna zaune da murjanin data bari a wajena a ina kallo naji muryarsa.
"Yallabai yanxu haka zaka zauna da rana kayi ta tunaninta idan dare yayi kuma kayi ta juyi na buƙatarta,gashi nan da sati ɗaya za'a fara Gasar dakazo dominta,kasan kuma ba ƙaramin abin dariya bane ga maƙiya idan kaje baka samu nasara ba. Taya zakayi nasara bayan baka da nutsuwa,karatun da kakeyi ka daina. Wajen Guru ma kadaina zuwa fah. Ni inaga mai zai hana naje Kasuwa na fanso maka baiwa wacce zata debe maka kewa kafin lokacin,ko kuma........"
"Fasih fasih karka sakemin wannan zancen a halin yanzu,banajin akwai wata mace dazan iya sake kallo bayan ita,sannan nayi mata laifi sosai bai kamata kuma nace sai tayimin yanda nakeso ba,duk da kuwa tana a halin baiwa ta. Zan iya jure yanayin danake ciki dan haka kada ka damu"
"Ranka yadaɗe to Gimbiya Hillah fah,takanas kayimin aike nakai takardar cewar ka zabi tashiga gasar Sarauniyar gobe,idan tasan cewar kana Son Joda kuma baiwarka yaya zata kaya kenan"
"Fasih ka dainamin maganar abinda baizo ba,kuma wanda banida iko akai, ƙaddarata nakebi wanda Allah yariga ya zanata"
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow