Hs 16
by @legendspen
_Page 16_
Taɓe baki Bhatool tayi ta nufi ɗaki tana cewa. " To ki kirasa ki masa faɗa mana, amma kin wani sakani a gaba kinamin faɗa da rungumeman cikin naki."
Yaya Karima ta ce. " Allah ya shirye ki idan mai shiriyar ce, amma ke kam Bhatool halinki sai ke, mijinki ya shiga uku."
Dariya Bhatool ta mata tana bud'e kofar ta lek'o ta ce. " Cewa za kiyi Senate ya shiga uku dan shine Nurul Hayat dina, kuma Zauj dina." Ta rufe kofar tana cigaba da dariya.
Girgiza kai kawai Yaya Karima tayi sannan ta wuce d'akinta.
*SENATE POV*
Tun da ya shiga d'akinsa bai fito ba sai guraren sallan Mangrib, dan sallan Azahar ma a d'aki yayi, haka kuma bai kula kowa ba ciki kuma har da Mom, dan yau jinsa yake wani iri duk a burkice.
Sauk'owa ya fara yi daga upstairs yana jin hayaniya, sake tamke fuska yayi lokacin da ya lura da su Juraij ne da Salman da Anas, sun tusa Mom a gaba suna hira kuma duk akan yanda za'ayi bikin Senate din ne.
Kallo daya ya musu yana tura baki a ransa ya ce. ' Gaibu kenan, ko accepting dina fa bata yi ba amma sun zage sai shirye-shirye suke.'
Mom ce tayi murmushi tana tasowa tazo gurin shi tana kama shi ta ce. " Son kazo mu zab'a wani event da wani event zamu yi."
" Mom kuje ku zaɓa." Ya faɗa yana wucewa ya fita daga parlon.
Baki a sake suka bisa da ido kafin Juraij ya ce. " Idan kun ga haka to shi da Bhatool ne."
" Kai da kasani kuma, kila ko bata masa magana bane yasa yau ransa duk a bace, kamar wanda aka masa bushara da wutan jahannama." Cewan Anas.
Salman yayi murmushi ya ce. " Ku dai gulma ne naku, ai gwara shi ya nemo wacce yakeso duk da tana bashi headache, amma ku fa? Ko ince mu fa? Kamar wanda basu da farin jini ko haske a rayuwar su."
Dariya Anas yayi yana cewa. " Cewa zakayi kamar wanda bakin iyaye ya bisu, ni fa tunda nake babu macen da ta taɓa cewa tana sona, anya ma ba aljana bace ta aure ni?."
Juraij ya daura da cewa. " Ko dai ta aure mu dai, dan nima haka ne lakamtu summa lakamtu."
Mom ta zauna tana fadin. " Ku tashi ku tafi masallaci, ku fake da cewa aljana ta aure ku, ku dai kuka auri aljanun tunda kune kuka ki auren."
Da haka suka tashi suka tafi masallaci.
Ana idar da salla ya fito ya nufi hanyar gidan Yaya Karima, Juraij na cewa ya jira shi amma yayi banza dashi.
Ƙwanƙwasawa yayi mai gadi ya buɗe, ya tambaye shi. " Bhatool na nan?." Ya ce. " Tana nan, dazu ta dawo daga Makaranta."
" Ban tambaye ka ba Malam." Senate ya fad'a yana nufan hanyar falon, dan shi fa jinsa yake dai-dai da kowa yanzu, duk haushin biyu ya taru masa ya masa yawa, ya rasa waye ne na Makarantar ga wanda ya kawo ta dazu.
A bakin kofar ya tsaya yana sallama.
Fitowan ta kenan taji sallaman shi, da mamaki ta ce. " Kamar Senate nake ji." Yaya Karima da itama fitowarta daga kitchen ta ce. " Shi ne ma ba kama ba."
Tabe baki tayi tana komawa d'aki dan dauko mayafi.
Yaya Karima ta amsa masa tana cewa. " Haba Senate gidan ne sai kace bak'on ka, ka wani tsaya daga waje."
Dan sosa keya yayi kafin ya shigo kansa a k'asa, ya durkusa yana cewa. " Ina wuni?."
" Lafiya ka tashi ka zauna."
Tashi yayi ya zauna yana ta kwakulo murmushin dole, Yaya Karima ta danyi murmushi kafin ta ce. " Bari na kira maka mutuniyar taka, yanzu ta shiga ciki."
" To Nagode." Ya fad'a dan dama ya rasa ta ya zai fara tambayar ta ina Bhatool.
Yaya Karima na k'ok'arin shiga dakin, Bhatool ta fito sanye da Hijab har k'asa Maroon color dinkin jalbab, matsawa gefe Yaya Karima tayi tana binta da ido, dan rabon da taga Bhatool da hijab har ta manta idan ba Sallah zatayi ba.
Kamshin turarenta ne ya fara masa sallama kafin tayi sallama tana zama nesa dashi.
Amsawa yayi yana d'aga kai ya kalle ta, murmushi ta sakar masa wanda ya ratsa zuciyarsa da gangar jikinsa gabaki daya, lokaci daya ya nemi fushi da bacin ran da yake yi ya rasa, yaji zuciyarsa tayi haske furannin cikin sun samu ruwa.
Lokaci daya ya tsinci kansa da furta mata. " Kinyi kyau sosai."
Murmushi ta masa tana sunkuyar da kai kamar munafuka kafin ta ce. " Nagode."
" Ba godiya a tsakaninmu ai."
Jinjina kai tayi tana tashi ta mika masa card guda hudu, dan ta kaiwa Yaya Karima guda biyun tace baza su je ba, karba yayi yana kallo kafin ya ce. " Na mene ne?."
" Na auren Suhaima ce, da Dinner da Kamu, ko zaka bawa friends naka coz you're also invited." Ta karashe tana komawa gurin da ta tashi ta zauna.
Murmushi yayi yana cewa. " In Sha Allah I will be there."
Shuru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa komai, can ya dago kai ya kalle ta yana cewa. " Kina da matsala da wani ne a school naji kuna hira? Sannan waye ya kawo ki dazu?."
Da sauri ta dago manyan idanunta ta sauke masa tana cewa. " Kenan ranar kaji komai?."
Shuru yayi dan shi kawai yaji ta ce akwai wanda takeso ne, amma ga dukkan alamu da ya tambaye ta yaga tsoro kenan akwai bayani, hakan yasa ya ce. " Eh naji komai."
Marairaice fuska tayi ta fara cewa. " Wai fa Dr Hashim ne yake sona." Kalman da ya caki zuciyarsa kenan *SO NA!!!*, ta cigaba da cewa. " Shi ne nace masa ina da wanda nakeso, wai yace bai damu ba ya bani nan da kwana daya nayi tunani ko kuma duk abunda na gani ni na jawowa kaina."
Ta karashe tana kallon yanda yanayin fuskarsa ya canja lokaci daya, daga fara'a ya dawo bacin rai zalla, amma sai ya dake ya ce. " Shi ne kawai?."
Gyada kai tayi tana turo baki gaba ta ce. " Eh."
Murmushi ya mata ya ce. " Solve, idan dai wannan ne angama da shafin shi."
" Thanks."
" Dm." Sannan ya daura da cewa. " Wanda ya kawo ki fa?."
" Abdul ne fa, kanina ne uwa daya uba daya."
" Ohh 😲." Ya fada yana sosa keya a ransa ya ce.' Ina kishi da kaninta kenan.' Kafin a fili ya ce. " Akwai wani abu ne?."
Girgiza kai tayi ta ce. " Bakomai kuma, kawai so nake kuzo events din duka biyu."
" Idan shi ne baki da matsala an gama." Kafin ya mike tsaye yana cewa." Nikam bari na tafi." Tashi tayi tana rakasa, a bakin get ta tsaya tana ciki shi kuma yana waje.
" Ba ki bani amsa ba."
Sunkuyar da kai tayi ta ce. " Accepted." Ta koma ciki da sauri tana dariya.
" Yessss!!!." Yana sakin dariya, juyawa yayi sukayi ido hudu da su Anas sun zuba masa ido.
Saurin tamke fuska yayi dan yanzu zasu mayar dashi karamin mahaukaci, ai kuwa bai gama ba suka fashe da ihu Anas na cewa. " Senate na Bhatool."
" Bhatool na Senate." Cewan Juraij suna sake sakin ihu.
Kamar yayi kuka ya ce. " Ku dena kiranta da sunanta ai wannan raini ne."
Dariya suka sake yi Salman na cewa. " To Zahra na Senate."
Bai kulasu ba ya shiga gida yana kwalawa Mom kira, da sauri Mom ta fito daga daki tana cewa. " Lafiya wannan kiran Senate."
Nuna mata su Anas yayi wad'an da har yanzu suna dariya ya ce. " Mom ki ce su daina kiran sunanta haka raini ne."
Da mamaki Mom ta ce. " Ban gane ba, sunan waye za'a daina kira haka?."
" Sunan Bhatool suke kira fa babu cewa Anuty."
" Ikon Allah." Kafin Mom ta dube su tana cewa. " To dai kunji Anuty Bhatool zamuna kiranta dashi."
" Mom ban da ke, su kadai."
Bata kula shi ba ta koma dakinta dan dama gyara kayanta take.
Ya juya ya kalle su ya ce. " Kuka kara ce mata Bhatool duk sai na kaiku kara police station." Ya karashe yana nufan d'akinsa.
Juraij ya ce. " Prison za'a kaimu kawai yafi ai."
Nan ma dariya suka masa, yayi kwafa ya shiga daki ya danna sakata.
Bhatool kam, tun fitar Senate ta koma ɗaki tana famam xancen zuci. "Tabbas Senate mai kyau ne, ɗan gayu, mijin nuna wa sa'a, mijin shiga taro, idan har nayi sa'a na aure Senate mai zai dame ni a duniyar nan?." Ta yi wa kan ta wanan tambayar. "Babu fa." Ta sake bawa kan ta amsa, tana cikin wanan tunanin wayarta ta hau ƙara alamun kira na shigowa, hannu ta kai ta ɗauka tare da ɗagawa bayan ta ga Sunan Amrah a kai. "Hello Amrah." Ta faɗa bayan ɗaga wayar. "Bhatool ya garin?."
"Normal Amrah is everything okay, na jiki wani kala?."
"Not Okay, wallahi Bhatool kuɗi nake nema urgently dan Allah ki aramun ko 30thousand ne."
"Haba Amrah, ai kinfi ƙarfin haka ki bani account ɗin zansa miki."
"Na gode sosai Bhatool, bari na samiki."
"Okay." Bhatool ta faɗa tare da kashe wayar, yanzu hankalinta ya koma kan na ta bikin dan ta san dai Senate son ta yake, Abinda ya rage kawai ya yi proposing asha biki, ."Kai zan ta shi kan munafukan 'yan uwan Abbanah, har na hango Goggo larai ta ga Mijinah, su Fure da hari sun suma, ƙila ma baƙin ciki ya kashe su, wallahi ba za a fasa bikina ba ko sun mutu." Bhatool ta faɗa tana miƙewa zuwa Toilet.
Wayarta ta ɗauka ta yi wa Senate Sallama ta whatsapp, yana kwance kan gado tun da ta shigo tunanin ta yanda zai yi proposing, sanan shi bai son Auren ya wani daɗe ayi a huce wajen kawai, ga kuma matsalal wanan malamin na su da ta ce. "Ƙila fa neil Abuja zan mai da ta kawai." Ya faɗa dai-dai lokacin da ya kai hannu zai ɗauke wayarsa, sakamakon ƙarar shigowar saƙƙoni da ta ishe shi. Idonsa ne ya sauka a kan message ɗinta da ta ce. "Salam Yaya Senate." Da sauri ya shiga yi ma ta Reply da faɗin. "Wa'alaikussalam Bhatool."
"Na'am Yaya senate, barka da dare."
"Barka Bhatool ya su Yayan?."
"Suna lafiya ƙalau, ya su Mom?."
"Alhamdulillah Bhatool."
"Daman Yaya Senate dan Allah Account ɗin Amrah ƙawata xan baka ka tura ma ta 30k, da safe sai na baka Cash, banda kuɗi a account kuma Yaya ta hanani fita Pos🥹🙏."
"🤩Okay badamuwa turu."
"Na gode🙏❤️22xxxxxxx42."
idan bakuyi following kuna comment ba, kuna sagar min da gwiwa😫