Chapter 18
Juyawa ya yi ya buɗe ƙofar ya fita, jin an buɗe ƙofa ya sa Ilham ta ɗago da kanta a hankali ta kalli gurin, tana ganin ya fita ta sauke ajiyar zuciya. Da sauri ta tashi ta je ta saka wa ƙofar key ta dawo ta haye gadon ta yi kwanciyarta, tunani ta fara yi na idan ya dawo ya ji ƙofar a rufe fa. A fili ta ce "Kai ai ba ma zai dawo ba, ko wannan zuwan da ya yi suɓutar hanya ce."
Sudais na fita bedroom ɗinsa ya shiga, ya zauna a bakin gadon ya dafe kansa, yana tuna yadda ya ga Ilham ɗin. Da ya san zai tarar da ita a haka da bai shiga ɗakin ba. Shi ya rasa ma me ya je yi ɗakin.
Ilham kuwa tana can hankalinta a kwance, saboda ta san ba abin da Yaya Sudais zai yi mata, tana da tabbacin ba zai dawo ɗakin ba. Tunani ne yake ta zuwar mata daga wannan sai wancan, a haka dai har bacci ya yi awon gaba da ita. Sudais ya ɗauki tsawon lokaci kafin ya yi bacci. Ya so ya makara a gurin sallan asuba, a gaggauce ya yi alwala ya tafi masallaci. Ana idar da sallah ba wai ni daɗe a masallacin ba ya dawo gida. A falo ya kwanta saman 3seater, wajen ƙarfe bakwai da rabbi Ilham ta fito falon sai baza ƙamshi take yi, ba ta yi tunanin ganinsa a gurin ba, ta ƙaraso a hankali ta zo kusa da shi, tsawuyawa ta yi a kansa tana ƙare masa kallo, a zuciyarta ta ce "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya halicci wannan kyakkyawar halittar" tunda take da shi ba ta taɓa ƙare masa kallo kamar yau ba, ba ta taɓa tsayawa ta kalle shi da kyau ba irin yau, to ina ma mutum zai samu wannan damar. "Idan kin gama ƙare mini kallon sai ki wuce ai, ba na son shirme." Ta ji muryar Sudais ya yi maganar ba tare da ya buɗe idonsa ba, diriricewa ta yi ta fara kame-kame, babu shiri ta nemi guri ta zauna ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce "Barka da safiya Yaya."
Shiru ya yi bai amsa mata ba, har ta fitar da ran zai yi magana ta ji ya ce "Kin tashi lafiya?"
Ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah" bai sake yi mata magana ba, ita ma haka, shiru ya shiga tsakaninsu, tana nan zaune ta ji an yi knoking ɗin ƙofa, tashi ta yi ta je ta buɗe, Zahra ta gani hannunta riƙe da basket da yake nuna alamar breakfast ne ta kawo musu, murmushi ta yi, ita ma Zahran murmushi ta sakar mata tare da faɗin "Aunty Ilham amaryar Yaya Sudais, ina fatan kun tashi lafiya?" Ilham ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah Zahra da fatan kuma haka? Ina Mammynmu?"
"Alhamdulillah, Mammy tana ƙasa, ta ce a gaisar mata dake." Ilham ta ce "Allah Sarki Mammy, ki ce mata ina amsawa, yanzu nake niyyar zuwa in gaishe." Murmushi Zahra ta yi ta ce "To kafin nan, ga breakfast ɗinku nan, idan kika karya sai ki zo ɗin." Karɓa ta yi tare da yi mata godiya. Zahra ta juya, ita kuma ta koma ciki, ajiye basket ɗin ta yi ta zauna tana satar kallonsa, ta ma rasa me za ta ce masa. Sai can ta yi gyaran murya ta ce "Amm Yaya ga breakfast nan an kawo, in zuba maka ne?" Da ƙyar ya buɗe bakinsa ya ce "Zuba na ki ki ci." Shiru ta yi tana binsa da ido, jiki a sanyaye ta ɗauki abincin ta kai shi dinning, ta shiga kitchen ta ɗakko flakes ta zo ta zuba kaɗan ta fara ci a hankali, ko da ta ɗago da kanta sai da taga wayam babu Sudais a gurin, riƙe cokalin hannunta ta yi, tana mamakin yaushe ya bar falon? Ko motsin tafiyarsa ba ta ji ba, ci gaba da cin abincinta ta yi, sai da ta ƙoshi sannan ta tattara kayan ta kai kitchen, ta wanke waɗanda ta ɓata sannan ta fito. Ɗakinta ta koma ta ɗakko mayafinta ta fito, tsayuwa ta yi a falon tana shawarar shiga bedroom ɗinsa domin ta sanar da shi za ta je ta gaishe da Mammy, wata zuciyar ta ce "Ke Ilham ki rufawa kanki asiri, idan kika je kika same shi ba a daidai ba fa kamar yadda ya yi miki riski jiya." Ajiyar zuciya ta sauke ta koma saman kujera ta zauna, kusan minti arba'in da shigarsa ɗakin sai gashi ya fito cikin shirinsa na zuwa office.
Ilham na ganinsa ta ce "Sannu da fitowa Yaya, da ma kai nake jira ka fito in sanar da kai ina son zuwa in gaishe da Mammy." Kallonta ya yi kafin ya kawar da kai ya ce "Zan hana ki zuwa ganinta ne?"
Ilham ta girgiza kai ta ce "A'a, wai gani na yi ƙara na sanar da kai ne, kar sai na fita ba ka sani ba ka zo ka na nemana ba ka ganni ba, ko kuma kana buƙatar in yi maka wani abu."
"Wani abu kamar na me?" Ya tambaya yana tsare ta da ido.
Sunkuyar da kai ta yi, ganin irin kallon da yake yi mata ta ce "A'a ba na komai ba." Ya ce "Ai ƙarya kike yi sai kin faɗi wane abu zan ce ki yi mini?" Ta ce "Yi haƙuri Yay..." "Shhhi" ya katse ta, tare da faɗin "Ba na son jayayya kin sani, ki gaya mini wane abu zance ki yi mini?" Cikin inda- inda Ilham ta ce "Gyaran ɗaki"
"Gyaran ɗaki kamar yaya? Ke kika saba gyara mini ɗaki da zan zo in ce ki yi mini yanzu?" Ta girgiza kai, shiru ya yi yana kallonta, Sudais so yake ya tabbatar da me take nufi da maganar da ta yi? Kar ya zamana tana tunanin zai zo neman waccan abin ne a gurinta, shi da ma wannan rainin ne yake gudu tun farko, "Oya tashi muje" ya ce yana ci gaba da binta da ido, tashi ta yi jikinta a sanyaye kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Sudais ya ce "Ke, me ye haka kike yi ne? Dalla saki jikinki mana, ko a haka za ki je gurin Mammy salon ki sa ta yi tunanin wani abin na yi miki, ko kuma dukanki na yi." Daidai ta natsuwarta ta yi sannan ta yi gaba ya bita a baya.
Tunda Mammy taga suna sauke take murmushi har suka ƙaraso cikin falon, Ilham ta je za ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafunta. Da sauri Mammy ta riƙo ta ta zaunar da ita a kusa da ita tana faɗin "Haba yarinyar kirki ya za ki zauna a ƙasa sai ka ce wata baƙuwa?" Ilham wani irin nauyin Mammy take ji wanda ko a baya ba ta taɓa jin irinsa ba, cikin jin kunya, tana sinnar da kai ta ce "Barka da safiya Mammy." "Yawwa barka dai ƴar Mammy, kin tashi lafiya?"
Ilham ta ce "Alhamdulillah"
Gyaran murya Sudais ya yi ya ce "Mammy ni ba ki ganni ba ne? Naga gabaɗaya ba ta ni kike ba." Dariya Mammy ta yi ta ce "Na ganka mana, bari na yi sai na fara tabbatar da lafiyar ƴata." Zahra ta saka hannunta ta toshe bakinta gudun kar dariyar da take riƙe wa ta fito, "Ina kwana Yaya." Faruk ya ce yana murmushi, "Faruku ka tashi lafiya?" Sudais ya ce yana kallonsa, ɗan ɓata fuska ya yi ya ce "Faruk dai Yaya." Ƙin kula shi ya yi, ya mayar da dubansa ga Mammy ya ce "To Mammy tunda dai naga alamar yau ba ki damu da ni ba, bari na tashi, zan wuce gurin aiki ne ina da abubuwa da yawa a office." Mammy ta ce "Haba dai? Ka na angwancin ne za ka je gurin aiki? Maimakon ka ɗauki hutu ko da na sati ɗaya ne domin ka bawa yarinyata kulawar da ta dace." Ɓata fuska ya yi ya ce "Haba Mammy a gaban yara muke fa, ki bari sai na dawo ma yi maganar." Daga haka ya tashi ya fice daga falon, yana jin Mammy na faɗin "Waye yaro a nan? Sai dai Zahra, don yanzu Ilham ta wuce zama yarinya a gurinka." Amma bai tsaya ba gudun kar ta jawo masa raini a gurin Ilham. Yana fita su Mammy suka ci gaba da hira cikin farin ciki da annashuwa, tun Ilham na ɗan jin kunyar Mammy har ta saki jikinta.
.....
Misalin ƙarfe goma sha ɗai da rabi, Jamila ta yi sallama a gidansu Ma'u, hannunta ɗauke da ƙatuwar kula, a bakin ƙofa ɗakin Inna ta tsaya tana sake yin sallama, amsa mata Inna ta yi tare da ba ta izinin shiga, da sallamar ta sake shiga ɗakin, ganin Yaya Aliyu a zaune ya sa gabanta ya buga da ƙarfi, zama ta yi saman tabarmar dake shimfiɗe a gurin, ta gaishe da Inna cikin girmamawa, amsa mata ta yi tana murmushi, sannan ta mayar da dubanta ga Aliyu ta ce "Barka da rana Yaya Aliyu." Ba tare da ya kalli inda take ba ya ce "Yawwa barka dai." "Ƙawata lafiya dai yau na gane a gida ba ki tafi makarantar boko ba?" Jamila ta ce tana kallon Ma'u, yunƙurawa ta yi ta tashi tana yamutsa fuska ta ce "Wallahi yau ba na jin daɗi ne, na tashi da wani irin zazzaɓi ne. Jamila ta ce "Ayya sannu Allah ya ba ki lafiya, ni ma kwana biyu ne ban zo na duba jikin ƴata Abida ba shi ne yau na ce bari in zo in duba ta." Ta yi maganar tana kallon Abida dake kwance kusa da Ma'un. Inna ta ce "Allah Sarki ai jikin na ta da sauƙi sosai" Ma'u ta ce "Abida tashi ga Aunty Jamila nan ta zo duba ki." Buɗe idonta ta yi, ta tashi tana murmushin ganin Jamila, ta ce "Ina kwana Aunty Jamila" ita ma murmushin ta yi ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah yarinyar kirki, ya jikin na ki?" Abida ta ce "Alhamdulillah na ji sauƙi."
"Ma sha Allah haka nake fata" cewar Jamila tana ɗakko kular abincin da ta zo mata da shi, shinkafa jolofce ta ji kifi sai ƙamshi take yi, Inna ta ce "Ke dai Jamila ba ki gajiya da ɗawainiya, to Allah ya saka da alkhairi." Ma'u ta ce "Rabu da ita Inna, ai kanta ne take yi wa yaƙi." Aliyu na zaune dai bai sake magana ba, amma har cikin ransa yake jin daɗin yadda Jamila take nuna tsantsar kulawarta ga Abida tun bayan rasuwar Halima, yana kallo ta zuba abinci ta saka Abida a gaba tana lallaɓa ta ci, sosai ta ci abinci, kafin ta ce "Ta ƙosahi". Inna ta ce "Ma'u tunda kin kasa cin komai yau, ki gwada ɗibar wannan abinci mana ko za ki iya cinsa." Girgiza kai ta yi ta ce "Inna ba na son cin komai ne, ni ƙamshin abincin nan ma tayar mini da hankali yake yi." Da sauri Aliyu ya dubi ta, sannan ya kawar da kansa, tashi ya yi ya fice daga ɗakin. Inna ma ta tashi ta fita waje saboda akwai aikin da za ta yi.
Ma'u ta dubi Jamila ta ce "Sannu maraƙisiyya, kin dai rantse sai kin jawo hankalin Yayana a kanki ko?" Dariya ta yi ganin Abida zaune a gurin ya sa ba ta biye wa Ma'un ba, nan suka ci gaba da hira, ta daɗe sosai a gidan kafin ta yi musu sallama ta fita. Tana fita Inna ta ce "Boyar Allah, yarinyar nan tana son Gadanga sosai". Ma'u ta ce "Hmmm, sai ma kin ji irin abin da take faɗa a kansa, tun Aunty Halima na raye." Inna ta ce "Ikon Allah, ai bari na yi a ɗan kwana biyu, daidai ya samu natsuwa tukuna sai in yi masa zancenta." Haka dai suka ci gaba da tattauna zancen.
......
Da sallama Zuhura ta shiga ɗakin mahaifinta, fuskarta ɗauke da murmushi ta zauna saman kujerar 2seater dake cikin ɗakin tana faɗin "Abbina barka da hutuwa, ashe yau ba ka fita? Dawowata kenan daga gurin aiki naga motarka a waje, shi ne na tambayi Mama ta ce mini ka na ciki yau ba ka fita ba." Shi ma murmushin ya yi ya ce "Eh Zuhuran Abbi, yau ba ni da ayyuka ne da yawa shi ya sa na zauna a gida in huta." Ta ce "Ai kuwa dai Abbi ka kyauta, gara ka yi kana hutuwa." Dariya ya yi ya ce "To ya gurin aikin na ki? Ina fatan dai babu wata matsala ko?" Shiru ta yi kafin ta ce "Abbi" tsare ta ya yi da ido sannan ya ce "Zuhura idan akwai wata matsalar ki sanar da ni mana, ba fa don ki yi aiki kaɗai ya sa na samar miki aiki a asibitin ba, ina son hadda saka ido ki dinga yi sosai a kan abin da yake gudana a gurin." Murmushin ya ƙe ta yi ta ce babu komai Abbi." Ya ce "To shikenan Allah ya taimaka ya yi jagora" ta amsa da "Amin" tana miƙewa tsaye za ta bar ɗakin. Sardauna ya ce "Zuhura kun yi magana da mutuminki kuwa?" Rufe fuskarta ta yi tana dariya ta ce "Eh Abbi, jiya da yamma na kira shi."
Ya ce "Ok to madalla, ya sanar dake batun aurensa da ya yi jiya?".
Dim! Gabanta ya buga da ƙarfi, ta fuɗe fuskarta tana kallon mahaifin nata. Lokaci ɗaya ƙwalla ta cika idonta, wani irin abu ne mai masifar zafi ta ji ya ta so tun daga tafin ƙafarta ya tokare mata ƙirji, nan take jikinta ya ɗauki rawa.
Amanarcool
***