KADDARAR SOYAYYA

33

by @sheolly

đź’«KKADDARAR SOYAYYAđź’«
    
         By sheolly 
          🔥🔥
    


Bayan sun dawo daga makaranta, Fatima da ƙaninta Sadiq suka shigo cikin gidan cikin natsuwa. Fatima tana riƙe da littattafanta a hannunta yayin da Sadiq yake ta ba ta labarin abubuwan da suka faru a makaranta.
“Yaya Fatima, yau malaminmu ya yi mana tambaya mai wuya amma na iya amsawa,” Sadiq ya faɗa cikin farin ciki.
Fatima ta yi murmushi tana kallonsa. “Madalla Sadiq, ka ci gaba da ƙoƙari. Karatu shi ne makomarka.”
Da suka shiga falon, suka tarar da Ammi da khadija suna kallo.
“Fatima kin dawo kenan?” Ammi ta tambaya.
“Eh Ammi, mun dawo,” ta amsa cikin ladabi. sadiq yaje jikin Ammi yana hugging dinta yace "na dawo Ammi na!" Ammi tayi murmushi tare da cewa Aje acire uniform ayi wanka zaku fita idan Abba yadawo "khadija" help him please!. sannan ta juya ga fatima tace "kima sainace kicire uniform kizo kici abinci!"
miemi ta É—an yi shiru na É—an lokaci, sannan ta gyada kai.
"Ammi dan Allah aje dani na jima banjeba fa tun ina karama"
Ammi ta kalle ta tace Hala nafara wasa dake a gidan nan ko miemi!.miemi ta kalli Ammi sannan tace Aa ba matsala Ammi, zan zauna na yi karatu.” tana gama magana ta wuce sama dakinsu domin cire uniform,
Khadija da sadiq ne suke saukowa bayan ta taya sadiq shiyawa a lokacin Alhaji umar yashigo falon da sallama a bakinsa sadiq ya ruga da gudu yanawa Abba sannu da hanya khadija ta amsa kayan hannun driver daya shigo dashi yanzu tana cewa Abba "welcome back Abba" Alhaji umar yace "thank you" nanah khadija. A lokacin da Hajiya maryam tafito daga kitchen domin tana taya yan aikin ta girki ta karaso tana amsar kayan hannun khadija tana nuna musu abinci tana cewa barka da dawowa Alhaji. Alhaji Bashir yace "madam barka da gida" suna jira domin zuwa dakinsa.
Bayan Alhaji umar da Hajiya maryam sunfito Alhaji Umar yake cewa naganku ko kadai ina mamana Ammi tace "sadiq call her" sadiq ya wuce domin kiran miemi yana zuwa yayi knockin kofar dakinsu tabashi izinin shiga ko gama shiga dakin baiyiba yaga meime tayi tagume yashigo dakin tare da tambayar miemi "yaya miemi Ammice tahanaki zuwa gidan daddy Bashir ko I'm sorry kinji karki damu, kitashi Ammi nakira mekiwa miemi tayi tana murmushi ta kama hannun sadiq suka fita zuwa falon suna zama Abba ya dago kansa yana tambayar, Mamana meyasa baki fito ba, miemi tace Abba shiryawa nake.
Bayan kowa yagama cin abinci. Sadiq da khadija da Abba suka shirya domin zuwa gidan Daddy Bashir. Tun abakin gate ake girmamasu Alhaji Bashir ya fito harabar gidan domin tarbarsu fuskarsa ciki take da Annuri driver yafito ya bude musu kofa Alhaji umar yafito da murmushi akan fuskarsa Alhaji Bashir ya mika masa hannu suna musabaha sannan yabawa sadiq hannu yana cewa yaro ya girma Abokina Alhaji Umar yayi murmushi "yace my boy kana lfy" sadiq yayi murmushi tare da Amsawa sannan ya dube khadija. khadija tace ina wune daddy. Alhaji Bashir yace "yan matan daddy" Yaya kike lfy qlau daddy ina momyn ku sadiq yayi karaf yace tana gida daddy ita da yaya miemi Alhaji Bashir yayi murmushi yana cewa ka gaida da momy kaji my boy tare da jirawa dukanson suna shiga falon gidan Alhaji Bashir iyalan Alhaji Bashir suna falo kowa yasamu wurin zama ana kara gaisawa cikin farin ciki da Annashiwa. Hajiya Aisha tayi Umarnin masu aiki su kawo abin tabawa.
Alhaji umar yace â€śBashir, ina Muhammad? Ban gan shi ba tun da muka shigo.”
Alhaji Bashir ya sauke numfashi kaÉ—an sannan ya ce,
“Ya fita ne, amma zai dawo.”
Bayan ya faÉ—i haka, sai ya shiga wani tunani mai zurfi. A ransa yake cewaBayan ya faÉ—i haka, sai ya shiga wani tunani mai zurfi. A ransa yake cewa:
“Ko wannan shi ne mafita ga matsalar Muhammad? Wataƙila idan ya samu aure da yarinyar abokina Umar, abubuwa za su canza.”
Amma sai ya tuna da irin halin Muhammad da yadda yake guje wa batun aure.
Tunani ya ci gaba da yi masa yawa har lokacin sallar Magriba ya yi. Sai suka tashi suka nufi masallaci tare da Sadiq.Bayan an idar da sallah, sai Alhaji Bashir ya juya wajen abokinsa ya ce,
“Umar, ina son yin wata magana da kai.”
Alhaji Umar ya kalle shi ya ce,
“To Bashir, ina sauraronka.”
Sai Alhaji Bashir ya ce,
“Sadiq, shiga gida muna zuwa.”Sadiq ya amsa ya shiga, sannan suka ci gaba da tafiya a hankali.
Da suka samu wuri, Alhaji Bashir ya fara magana cikin damuwa,
“Abokina Umar, ka san Muhammad ɗana yana bani damuwa sosai. Yanzu shekarunsa sun yi, amma bai damu da maganar aure ba. Na yi ƙoƙarin magana da shi sau da yawa, amma har yanzu ban samu sauƙi ba.”
Alhaji Umar ya saurare shi cikin nutsuwa.
Sai Alhaji Bashir ya cigaba da cewa“Saboda haka nake neman wata alfarma a wurinka. Ina son ka ba ni auren ɗiyarka Khadija domin Muhammad.”
Alhaji Umar ya yi shiru na É—an lokaci, yana nazarin maganar abokinsa.
Daga nan ya ce,
“Bashir, kana ganin wannan auren shi ne mafita kuwa?”
Alhaji Bashir ya kalle shi cikin fata ya ce,“Na yi imanin haka. Ina ganin zai iya taimaka masa ya samu nutsuwa da canza tunaninsa.”
Alhaji Umar ya rasa abin cewa na É—an lokaci. Maganar ta zo masa da mamaki, domin bai yi tsammanin wannan ne zai tattauna da shi ba.
Sai Alhaji Bashir ya yi murmushi kaɗan ya ce,“Ba sai ka bani amsa yanzu ba, abokina. Ka yi tunani sosai. Duk yadda ka yanke shawara, zan girmama shi.”
Alhaji Umar ya gyada kai cikin nutsuwa, amma zuciyarsa cike take da tambayoyi.
   
   
Me zai faru idan wannan shawarar ta zama sanadin haÉ—uwar wasu rayuka? Kuma shin Muhammad zai amince da wannan aure?