CHAPTER SEVEN :TARKO A DUHU
๐**ZUNUBIN UBA**๐
**Novel by secretwriter **๐
Gidan su Jannat ya tsinci kansa cikin wani irin shuru da fargaba gabanin faduwar rana. Jannat na zaune a tsakiyar gadonta a kulle cikin daki, ta rungume kafafunta tana kuka mai ban tausayi. Jikinta har yanzu rawa yake yi saboda tasirin tsoro da azabar da ta sha a dakin tiyata (*Theater Room*) na asibitin.
A tsakiyar falo kuwa, mahaifiyarsu Hajiya Jawahir, tare da kannenta Nazra da Noor, duk sun rasa ina zasu sa kansu saboda tsananin damuwa.
Nazra, wadda ta dawo daga asibiti ta tarar da yayar tata cikin wannan halin, ta juyo tana kallon Hajiya Jawahir. "Umma... Na yi-na yi ta bude kofar ta fito ta ci abinci amma ta ki. Tunda ta dawo daga asibitin nan take kuka! Na tambaye ta ko wani abu ya faru a ofishina ta ki fada min. ta kashe wayarta gaba daya."
Noor kuwa, wadda duk lokacin da za ka ganta a gida cikin shagwaba,take yanzu fuskarta babu alamar wasa ko alamar miskilanci. Ta bata fuska tare da buga kafarta a kasa cike da damuwa. "Wallahi Umma idan har wani ne ya bata mata rai a waje ko a asibitin nan, kawai ta gwara fada mana! Yanzu duba yadda ko abinci ta kasa ci!"
Hajiya Jawahir ta sauke nauyayyen numfashi, fuskarta dauke da tsananin tausayinsu. "Bari na sake gwada knocking kofar... Ba zan zuba ido na kalleta tana cutar da kanta ba."Ina ga fasa tafiyar nan zanyi Nazra
Nazra ta juyo da sauri tace Aโa mama dole zaki tafi ba wani Abu bane zan kula da aunty Jannat,driver da Noor Su raka ki,ni kuma zan kula da aunty Jannat anan kije kiyi ta mana Adduโa kawai,kema Ai Kina bukatar hutu
Hajiya jawahir tace shikenan Tohm Amman komai ya faru ku Kira ku fada mun
Noor dake gefen Su tace dole ne mah mamana ko Su ba Su Kira ba ni zan Kira
A daidai lokacin a wajen gidan, a cikin duhun dare, wasu bakaken motoci guda biyu sunyi fakin a nesa kadan da kofar gidan. A ciki, ma'aikatan tsaron Saif ne sanye da bakaken kaya da makamai masu sarrafa kansu, suna sanya idanu a kowace kusurwa ta gidan domin ba su kariya daga mutanen A.A Rumfa, duka daidai umarnin da Saif ya ba Rayyan.
A bangaren Sarki Saif kuwa, agogon babban falon maboyarsa yana shirin dukan karfe sha daya na dare.
A tsakiyar teburin dakin, wata babbar taswira ta sirri ce shimfide. Saif yana tsaye sanye da bakaken kaya na alfarma masu sulke (*bulletproof*), fuskarsa tayi ah bace ba Alamun wasa kamar garwashi. Rayyan da Zaid suna tsaye a gefensa cike da shiri da fargaba.
"Sarki... Na'urorinmu na sirri sun gano cewa A.A Rumfa ya jibge fiye da mutane hamsin sanye da makamai a kewayen *warehouse* din," Zaid ya fada yana nuna taswirar. "Kuma sun dasa tarkuna da na'urori masu fashewa a babbar kofar shiga. Bayyanarka a wajen tabbas yana nufin shiga tsakiyar wuta!"
Saif ya saki wani murmushi mai cike da hadari na shugabanci, idanunsa suna walkiya. "A.A Rumfa ya manta cewa ni ne nake rubuta dokokin fada. Yayi tunanin ta babbar kofa zan shigo saboda yana rike da Nusaiba?"
Ya daura yatsansa a kan wani lungu na taswirar da ke haษe da teku. "Zaku raba mutanenmu gida biyu. Zaid, kai zaka yi amfani da jirgin ruwa mai sauri ka shigo ta bangaren bayan *warehouse* din ta hanyar ruwa. Ni kuma zan shiga ta sama ta hanyar rufin karfen wajen."
Rayyan ya gyada kansa. "To Sarki... Amma me za mu yi game da sakon da Laila ta bar wa Nusaiba? Shi ne kadai abin da A.A Rumfa yake nema a yanzu."
Muryar Saif ta koma kasa-kasa cikin fushi. "A.A Rumfa ba zai taba samun wannan sakon ba... saboda a daren yau, zan amshi Nusaiba a raye, kuma zan tabbatar na rushe dukkan shirinsa kafin ma ya ankara!"
A can boyayyen dakin karkashin kasa na *warehouse* din, Nusaiba tana zaune a kan siminti, jikinta yana rawa saboda sanyin dare da tsoro. Karan takun takalmin A.A Rumfa ya fito daga bakin kofar karfen.
A.A Rumfa ya shigo yana gyara agogon hannunsa, fuskarsa cike da alfahari. "Sauran mintuna kalilan karfe sha biyu ta cika, Nusaiba... Yanzu zamu gani ko 'gogan naki ' Saif zai iya sadakar da rayuwarsa ya zo cetonki, ko kuwa zai bar ki ki mutu tare da asirin Laila!"
Nusaiba ta dago idanunta da suka kumbura saboda kuka, muryarta na rawa. "Ko ka kashe ni... Saif ba zai taba barinka ka ci nasara ba!"
A.A Rumfa ya saki wata muguwar dariya da ta amsa a dakin. "Muma muna jiran sa... domin daren yau, gidan mutuwarsa na tsara masa!"
๐**ZUNUBIN UBA **๐
**Novel by secretwriter **๐