JA DA BAYA...

Kudi da iko

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 12✍️


***


Zaune suke a wani gidan gona, ba abinda kake ji yana tashi sai kida, da kuma warin hayakin dake tashi. Yayan masu kudi masu fada a ji a kasar. Mata da maza, kowanne yana abinda ransa ya keso,Sam Babu tsari amatsayin yayan musulmai,Amma su agaresu wannan shine wayewa da Kuma gata.

Haisam ne zaune, ga budurwarsa zaune akan jikinsa. Karar wayarsa ta dawo da shi hayyacinsa. Ya dauka tare da kara wa a kunnensa. "Hello." Daya bangaren aka amsa cikin fada tare da fadin: "Ka yi gaggawar barin inda kake, ka zo yanzu! Ina nemanka." 
"Ohh sheet, Daddy. Ina wani uzuri ne fa." Ya fada cikin sangarta. 
Amsa aka ba shi da cewa: "Ko me ka ke yi, ka yi maza ka zo yanzu!" Aka kashe wayar.

Budurwarsa ta kallesa tare da shafa fuskar sa. "Ya aka yi, babe?" 
Ya ce mata: "Dad ne yake nema na yanzu." Tare da tureta gefe yana mike wa. 
Tambayarsa aka fara: "Yana zuwa yanzu shine abinda ya fur." Tare da ficewa. Wani ne acikin samarin ya ja wannan budurwa da take jikin Haisam tare da shigewa wani dakin, suka cigaba da sabgarsu.

Yana fita ya shiga mota tare da janta da gudu. 
Mintina kadan suka ka isa gida. Wani mahaukacin hon da ya yi yasa mai gadin da gudu ya tashi ya wangale gate din. Ko gama faka motar bai yi ba, ya fito ya shiga falon. 
Mommy ce zaune, sai Husnah akan jikinta tana daddana waya.

Yana shiga falon, ba bu ko sallama, haka ya shiga tare da fadin: "Daddy, what happens?" 
Daddy ne ya kallesa fuska a cushe, ya ce: "Ban hanaka driving in kayi shaye shaye ba? Amma ba ka ji, dazu kun bige wata mata da yaron ta da mota. Kuma saboda ba ka da hankali ka bari har mutane suka ganka, kuma suka tabbatar abige kake. Me hakan zai jawo, iyeh? Me hakan zai jawo? Ka san hakan koma bayane a harkar siyasata?"
"Ohh Dad, wannan fa dan karamin issue ne kake damun kanka. 
Su talakawa dama me amfaninsu? Ita ce fa ta shigo min hanya, da alama ba ta da hankali, shi yasa na taka ta."

"Bance ka yi kuskure ba ai Haisam. Amma barin fuskarka har wa su su shaidaka shine kuskuren." Alhaji Gali ya fada haka, bayan ya ga yadda Haisam yake magana yana cije cije. Ko kadan bai son ganin bacin ran 'yaran sa, hakan ya sa duk abinda su ka yi dai-dai ne.

"Ok my boy, je ka abinka. Na san yadda zan ji da case din." 
Dago, Mommy ta yi tare da fadin: "My boy, je ka abinka." 
"Haba, his Excellency, akan haka kake damuwa? Ko da mutuwa matar ta yi ya ka she banza. But yanzu ko dan siyasarka, a tura abincin ka. Sannan a kai matar asibiti, a ba su kudi wanda bakinsu zai rufe. In sun ki hakan a tsorata su. Se a yi hira da yan jarida akan matar ta fada cewa ita ce ta shigo ma boy, sannan ya kai ta asibiti kuma ya kula da su. 
Hakan zai sa kimarka ta karu, domin na tabbatar abinda ya faru zai ya zaga media. Kuma ka ga tattaunawarka gobe ne da yan jarida, dole za su sako wannan maganar. Ka yi cancelling na appointments din da ka ba su gobe, ka je gidan jaridar su. Hakan zai fi."

Jinjina kai kawai ya yi cikin gamsuwa tare da fadin: "Kin kawo shawarar mai kyau. 
Tabbas haka za a yi. Shi yasa nake matukar alfahari da ke. Hakan za a yi, bari na tura musu sako." Ya fada hakan tare da daukar wayarsa.

Bayan ya gama, sai ya kira P.A dinsa tare da ba shi bayanin abinda ya faru, kuma ya sa shi akan ya bincika sannan a yi abinda ya dace.

Tattaunawa suka cigaba da yi, inda son zuciya ne kawai acikin maganar tasu, kuma abin haushi a gaban 'yarsu. Wanda su kuma hakan normal ne. 
Ita kuwa 'yar lelen tana jikin uwarta tana danna waya.


Alhaji Gali ya Kalli matarsa tare da fadin"gaskiya kinyi tunani me kyau hajiya kaltum, shiyasa kome zanyi nake Sako ki aciki domin kina warware min matsalolina cikin sauki."yafada da alamar farin ciki a muryarsa.
Murmushi tayi cikin Jin dadi da alfari tace"karka damu Excellency,ni nasan yadda zan sarrafa duk Wani Mai tunani,ba wannan bane karon farko da muka Saba wasa da tinanin su,insunsan wata ai basusan wata ba.
Husnah ta Kalli iyayen nata tare da fadin"daddy Amma Kai Kace zaka tsaya takarane domin al'umma da Kuma talakawa,but kaima kayi hakan Dan amfanin kankane?
Murmushi yayi Yana cewa" bazaki ganeba daughter,komai zanyi domin kudinannan ne so kiyi shiru kinji.
"Ok" ta fada tana cigaba da danna waya.
Mikewa yayi Yana tambayar hajiya kaltum,Ina ameerah?
Ameerah ta tafi birthday din Wani abokinta a abuja since yesterday,but I think yau tadawo.
"Ohhh ba damuwa seta dawo shine abinda ya furta tare da shigewa.

Acan kuwa Gefe guda har ansamu Wanda yadaura video din abinda yafaru a social media,sedai ko minti biyar wannan video baiyi ba aka saukeshi.
Dan  haka wadanda suka San abinda yafaru ma basu da damar wata magana akai domin kuwa anmusu gargadi Mai girma hakan yasa dole basu da ta cewa.
Sedai Kuma kamar sunyi shuka a idon makwarwane domin tabbas akwai Wanda yake da wannan video.