JA DA BAYA...

The lion

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 13✍️*


***


*AYZAAN MUHAMMAD MAI RABO*  
*(The Lion)*

Shaharren dan kwallon kafane, wanda ya shahara sosai a fadin duniya.  
Mutum ne mai masoya da yawa wanda mutane suke kira da suna: *THE LION*, sabida kwarewarsa a wasa. Sam bai faduwa ba, fitaccen dan kwallo ne. Yana taka leda a kungiyar *ROYAL STORM FC* ⭐.

Yana buga wasa a kasar England, sannan shi din tauraro ne na kungiyar shiyasa suke kiransa da Lion.  
Matasa da yawa suna kwaikwayonsa salonsa, jaridu kuwa kullun cikin rubuta labarinsa suke. Sedai babu gidan jaridar da suka taba hira dashi. Hasali ma yafi saka face mask domin sam shi ba mutum bane mai son kallo. Shiyasa yawanci duk inda zashi da wannan abu a fuskarsa. Mata suna matukar kaunarsa, sedai shi Sam babu wannan atsarinsa.

Kamar ko yaushe yauma kananan kayane ajikinsa: bakin wando da riga itama baka.  
Ya daure gashinsa kamar yadda ya saba kansa babu hula. Hakan ya bayyana gashinsa mai kyau da daukar hankali. Fuskarsa sanye da face mask sedai yasauke shi kasa, kasantuwar yana driving ne.

Inarah zaune a gefensa ta waigo tace:  
"Zaki na, kasan labarin da gidan jaridar mu ya wallafa shekaran jiya?"  
Daga mata kai kawai yayi.  
Takara da cewa: "To, yaya, yarinyar jikar babah Adama ce, baigowaba."  
Yana ci gaba da driving tacigaba da magana:  
"Amma zaki na kasan wani abu?" Bata jira amsarsa ba taci gaba:  
"Gaskiya naji matukar tausayin iyayen yarinyar musammam. Danani ta kasance jikar babah Adama. Amma jiya dana koma station din da aka kai mai laifin, se na tadda wai ya mutu. Gashi bamu samu wani bayanai daga jamian ba. Yanzu dai gawarsa na morgue wai se anyi autopsy.

Ni yaya duk kaina yadaure game da wannan lamarin. Sannan yaya gashi yanzu bacewar yara yanata yawaitar. Kullin se ansamu cigiya. Ko dazu munsamu cigiyar batan yara har uku. Ni banga aikin da jamian tsari sukeyi ba. Allah."

Bece komai ba yaciga da driving, ita kuma taci gaba da bashi labari.  
Kallon shi tayi tare da riko hannunsa tana fadin: "Yawwa zaki na, yaushe ne tafiyarka?"  
Yace mata: "Se karshen wata."  
"Yaya, amma bazaka dade ba ko?"  
"2 months." Shine kawai abinda ya furta.

"Gaskiya zaki na ban yadda ba. Har 2 months? Ni dai saidai in bika."  
Parking yayi bayan sun karaso inda zasuzo. Gyara face mask din fuskarsa yayi tare da cewa: "Kijirani a mota."  
"To yaya" ta amsa tare daukar wayarta ta shiga kiran lambar Zarah.

Taku yake cikin izzah daka gansa bazakaso kadena kallo ba. Tafiya yake a natse kasantuwar wurin babu yawaitar mutane. Wani babban eatery ne, yashiga.  
Wani guri na musamman ya samesa zaune. Abokinsa ne Junaid. Zama yayi tare da mika masa hannu suka gaisa. Tashi yayi yadan rungumesa tare da fadin: "Dude I miss you." Murmushi kawai Ayzaan yayi.

Junaid abokin Ayzaan ne tun suna yara. Ansan juna sosai da sosai hasalima cause daya suke. Junaid dan jaridane wanda yana da gidan jaridar sa ta kansa. Baya kasar jiya ya dawo hakan yasa suka hadu da Ayzaan anan don tattauna wata magana mai muhimmanci.

Sun dau lokaci kamar minti sha biyar kafin su taso gaba daya su fito. Duk inda sukayi kuwa binsu da kallo ake. Duk da ma wajan ba yawaitar mutane amma ahaka wasu sunso su gane Ayzaan.

Sun kusa karasowa inda suka faka motarsu, kawai wasu mata suka sha gabansu tare da fadin: "Hy big guys."  
Hankalin Inarah dake motane yadawo kansu. Tsayawa sukayi suna kallonsu. Inda Meerah ta kalli Ayzaan tare da fadin: "Hy handsome, can you give me your number?"  
Ko kallonta baiyiba. Kawarta na gefe ita ka kasa cewa komai. Kwarjini yayi mata sosai. Ita kuma Meerah kamar zata cinyesa dan kallo.

Wayarsa ce tayi ringing tare da sa hannunsa a aljihunsa yaciro. Kasa yayi da face mask din fuskarsa tare da kokarin yin gaba yana sa wayar a kunnensa.  
"Wowwwww the champion" shine abinda yafito daga bakin Meerah. Dasauri tasha gabansa tare da kokarin rike hannunsa. Kallo daya yayi mata taja burki ta tsaya.

Junaid ne yakaraso bayan ya gama waya suna sallama da Ayzaan wanda yakusa karasawa bakin motarsa.  
Dan hugging dinsa yayi tare da bubbuga bayansa sukayi sallama. Junaid yashiga mota, Ayzaan ma haka.

Inarah wacce take kallon duk abinda ya faru, wani irin bakin ciki taji ya tokare mata wuya. Bata sani sanda ta fashe da kuka ba.  
Yana shiga motar yasame ta tana ta rusa uban kuka. Kallonta yayi with surprised tare da fadin: "Ke kuma lfy?"  
Kara volume tayi tana kara fashewa da kuka. Bilhakki da gaskiya.  
Tada motar yayi yana waigawa ya kalle ta.  
Kallonsa take bilhakki tana rusa kuka. Sun kurawa juna ido. Shi bai dauke idon sa ba, ita kuma bata dauke nata ba. Kuma bata daina kukunba.

"Chuchu please" ya furta tare da marairaice fuska.  
Kara ta kwalla tare ta fadin: "A'a, harda make karfafa. Aikuwa bazaki kara bina ba tunda ke kin iya kukan banza."  
Ai sai ta kwanta a kujerar motar harda birgima take. Cikin kuka take fadin: "Kuma duk inda zaka Sena bika, da wasu yan matanka. Ko kyau basu dashi, munanan banza. Dayar ma lukuta, ita kuma dayar da idonta kamar mayya. Dama duk in ka fita yanmata tareka sukeyi. Sena gaya ma Abbah."  
Ta karashe maganar tare da sheshahekar kuka.

Baisan sanda murmushi ya kubce masa ba. Kawai ji yayi tana kara fashewa da kuka.  
"Ya Allah" shine abinda ya furta tare da miko mata hannunsa daya. Kama hannun tayi ta gantsara masa cizo. Kuma duk da haka bata dena kukan ba.

Yau ba kanta ya furta tare da yin murmushi. Tun tana karama yasan ko me ya mata intana kuka: kama hannunsa take ta cijesa. Shikenan zakaga tayi shiru tana goge ido alamar ta huce kenan. Wani sa'in harda murmushi zakaga tanayi. Kuma haka harta girma bata dena wannan dabiar ba. Shiyasa da yayi mata laifi ko tatashi kukan banzanta yana mika mata hannun ta cijesa. Shikenan aganinta ta rama.

Haka dai yau suka karasa gida. Suna shiga a daidai apartment dinsu yayi parking. Da gudu ta fito tana kuka tayi falon da gudu tare da kwala kiran ummee.  
Shi ya dakko mata wayarta tare da da rufe motar yana shiga cikin falon tare da fadin: "Fitinanniya" kawai a zuciyarsa.

Da sauri ta karasa jikin ummee tare da kwanciya tana kuka.  
Kallonsa ummee tayi tare da fadin: "Lafiya, kun fita da yarinya lafiya yanzu tadawo tana kuka. Me kayi mata?"  
"Ummee to ita kuka yana mata wuyane?"  
"Tambayarka nayi, me aka mata?" Ummee ta fada tana shafa kan ta alamar rarrashi.  
"Ummee ba komai." Ya fada tare da zama akan kayataccen rug din dake dakin.

Sakowar Abbah ne yasa Inarah dagowa. Jin yana fadin: "Meyafaru kuma, yau waya taba uwar masu gida. Dole ma ya kwana a kulle yau. Me girma maman D.I.G guda yau aka tabo fa."  
Ya fada tare da zama yana kallon Ayzaan kamar zai zanesa dan yasan akanshi Inarah ke wannan kukan.

Sassauta kukan tayi tare da fadin: "Abbah ba yaya bane." Ta fada cikin shagwaba.  
"Ahaf nasan dama shine" inji Abba yana fadin: "Ba wani dogon bincike. Hukuncinka kwana uku a rufe a cell fakat angama. Ko mamana?"  
Ya fada yana kallon Inarah data mike tadena kukan ta zauna.

Hannu sama Ayzaan ya daga alamar yayi saranda.  
Ummee ta shafa kanta tare da fadin: "Kidena kuka da yawa kinji. Rabin rai na, kiga idonki har yayi ja."  
"Ummee yayane fa. Yayi wasu yanmata baki gansu ba. Kamar aljanu ko kyau basu dashi."  
Ta fada hadi da so tasake wani sabon kukan. Dagani dai kasan abin yana ci mata rai.

Jauhar ce da shigowarta falon kenan. Ta amshe batun da fadin: "Ahh kace munkusa shan biki bobo yau da budurwa."  
"Ba ruwana dake Didi. Daga yau ko gidanki ma na fasa zuwa. Kuma ban kara zuwa gidanki."  
Ta fada tare da matso hawaye. Ummee ta kalli Didi da harara a fuskarta.  
Didi tayi saurin rufe baki tana fadin: "Afwan lillyna, ayafemin."

Ayzaan dai yana zaune yana jinjina rigima irinta Inarah. Yanzu akan abinda ya faru ne take ta wannan uban kukan.

Abba yace: "Yi shiru mamana. Ankara masa kwana hudu. Sati daya zaiyi a kulle."  
"Yawwa Abbah" ta fada tare da cewa: "Kuma Abbah ahanasa fita harna tsawon wata daya. Kuma duk inda zashi sedai na rakashi. Sannan kuma nikabi zai dinga sawa ko Abbah?"  
Dariya Abbah yake boyewa tare da fadin: "Hakan za'ayi mamana."  
"Yawwa Abba, kuma kace ba ruwanshi da su."  
"Eh, ba ruwanshi dasu" inji Abbah.

Waigawa tayi ta kalli Ayzaan tare da fadin: "Kayarda da sharadinmu ko yaya?"  
"Dari bisa dari" ya furta tare da fadin: "Harda na zuwa gidan yari ma."  
"Ai min yafe masa wannan ko Abbah?" Ta fada tare da kallon Abbah da sigar tambaya.  
Abba yace: "A'a mamana, yaka mata mu lullesa ko na sati dayane." Shima ya fada kamar gaske.  
"Ayyah Abbah mudai yafe masa ko? Kaga Allah ma yanason me yafiya ko ummee?"  
Tafada tare da kallon ummee da fuskar tausayi.

Dukkansu dariya ce ta kufce musu in banda Ayzaan kawai dayayi murmushi rashin wayonta har mamaki yake basa.  
Abba ne yace: "Eh hakane mamana. Allah yanason me yafiya. Munyafe maka Zaki. Amma karka kara."  
Yafada tare da kallon Ayzaan.

Kwanciya tayi jikin ummee inda ummee ta cigaba da shafa kanta a hankali har bacci ya soma daukarta.  
Abba ne ya mike tare da fadin: "Bari nashiga gurin hajja. Daga nan zani gurin innah."  
Amsawa sukayi da: "Seka dawo." Yafice a falon.

Shima Ayzaan tashi yayi yana cewa: "Ummee ze shiga yayi wanka."  
"Kayi kafito kazo kaci abinci" inji ummee.  
"To" yace tare da shigewa bangarensa.

Kallon Inarah ummee tayi wacce har ta fara bacci ajikinta.  
Hakika tana matukar tausaya musu duk su biyun. Domin an haliccesune da kaunar junansu tun asali. Sedai kaddara batasan wannan ba. Ahalin yanzu dole Inarah da Ayzaan su rabu. Inarah zatayi aure dole wataran. Iya tinanin hakan kadai yana fadar mata da gaba domin ta sani akwai rikici sosai da sosai.

---