BARRISTER SUHAIL

97

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL"

🅿️----97

ko ya shiga…

Ya ji zuciyarsa ta tsaya

Zeenah ce kwance a kan gado

An saka mata oxygen

An haɗa ta da na’urori

lallai duniya ba komai bace bar Ganin kana Rayuwa cikin ta ka guji sanda zata yi maka gwatson mage

Sautin na’urar bugun zuciya ne kawai ke tashi a hankali

Ta buɗe idanunta a hankali

Da ta ga Suhail…

Sai ta yi wani ɗan murmushi mai rauni mai Cike da zallar soyyayar sa da zuciyarta ta ginu a kai

ta masa alamun da "ya shigo…”

Suhail ya matso kusa da ita

Ya kama hannunta

Hannunta ya yi sanyi sosai

cikin kuka,ya ce

“Me ya sa kika boyeman yi min wannan Wannan Babban al'amarin"

Ta girgiza kai a hankali.


“Saboda…”

“Ba na son ka rayu cikin tausayina"

“Ina son ka tuna da ni…”

“A matsayin Zeenah…”

“Mai dariya, Wanda ta sadaukar da Rayuwar ta a gare ka"

“Ba mara lafiya ba"

Suhail ya fashe da kuka

“Kin zalunce ni da wannan sirrin.”

Ta yi murmushi

“Na kare ka ne.”

“Na san…”

“Da ka sani…”

“Ba za ka sake yin murmushi ba.”

Ta yi tari

Likita ya matsa ya duba ta

Bayan ya gama

Ya ba Suhail alamar ya ci gaba

Zeenah ta juya idanunta zuwa wajen mahaifiyarta

“Umma…”

Hajiya Rabi ta kama hannunta

“Ina nan, zeenah"

“Ki yi haƙuri"

“Ki yafe min"

Hajiya Rabi ta girgiza kai tana kuka

“Ni ya kamata in nemi gafararki"

“na Ya yafe miki"

Sai ta kalli mahaifinta

“abba…”

Alhaji Ibrahim ya kasa magana

Ya riƙe hannunta yana hawaye

“Kada ka yi kuka kaji kayi min addu'a,Abba inaso na fada maka zeenar ka ta shiryu ta daina duk wasu abubuwa marassa kyau"

Ta faɗa da ƙyar

“Na gamsu da ƙaddarar Allah"

"kuma na gode da ya bani ikon gyara Rayuwa ta kafin na koma gare sa"

Sai idanunta suka koma kan Suhail

“Ka kawo min Khalil"

Da sauri Jennifer ta shigo da Khalil

Yaron bai san abin da ke faruwa ba.

“Mama…”

Ya kira cikin farin ciki

Da ƙyar Zeenah ta ɗaga hannunta

Ta shafi kansa babana

Ta sumbaci goshinsa

“Khalil…”

“Ka zama yaro nagari "

“Kada ka ɓata wa Abbanka rai.”

"Allah yayi maka albarka"

Sai ta kalli Suhail

Cikin raunanniyar murya ta ce

“Na rubuta wasiƙa"

“Tana cikin drawer na gefen gadona"

“Ka ba Iman"

“Don Allah…”

"Sannan matar nan marar lafiya da kaga naje gidan ta ka rinƙa zuwa akai kai kana Dubasu"

Sai ta tsaya saboda numfashinta ya ɗaukaka

Suhail ya matso

“Ina jin ki zeenah go aheda"

Ta ci gaba da cewa

“Ka fadawa iman…”

“Na roƙe ta…”

“Ta kula min da Khalil"

"kar ta duba yadda mukaga zauna tare,duk da naso neman tafiyar ta fuska da fuska Amman da alama hakan bazata samu ba"

“na roke ta Ta ba shi soyayyar da za ta ba ɗiyar ta"

“Na san"

“Ba za ta taɓa nuna bambanci tsakaninsu ba"

Suhail ya kasa riƙe kukansa

Ya durƙusa a gefen gadon

“Na yi miki alkawari"

“Zan cika duk abin da kika roƙa"

Zeenah ta lumshe idanunta

Wani irin natsuwa ta bayyana a fuskarta

A hankali ta fara furta

“Ashhadu an la ilaha illallah…”

“Wa ashhadu anna Muhammadan Rasulullah…”

Muryarta na ƙara raunana

Kowa kuwa ya tsaya yana hawaye

Yana kallonta

Ba tare da sanin ko wannan ne numfashinta na ƙarshe ba


idanunta sun rufe rufewa ta har abada

Numfashinta ya fara ja da wahala

Idanunta suka sauka kan fuskar Suhail

Ta yi masa wani ƙaramin murmushi

Murmushin da ya fi kama da bankwana

A hankali

Ta lumshe idanunta

Shiru

Na’urar dake a gefenta ta fara canza sauti

“Beeeeeeeeeeep…”

Suhail ya matsa kusa da ita

“Zeenah"

Babu amsa

Ya sake girgiza hannunta

“Zeenah"

Har yanzu babu amsa

Hajiya Rabi ta zuba mata ido

Da ta fahimci abin da ya faru

Sai ta saki wata irin ƙara mai firgitarwa

“Wayyo Allah na!”

“Na shiga uku!”

“Zeenah ma ta tafi!”

Ta faɗi jikinta kan gadon tana rungume da ’yarta

“Ya Allah…”

“Me na yi maka?”

“Ka ba ni ’ya’ya huɗu…”

“Duk ka karɓe su!”

“Ko ɗaya ba ka bar mini ba!”

“Ya Allah…”

“Wane laifi na yi maka da kake mini wannan hukuncin?”

“Zeenah…”

“Ke nake ganin zan tsufa tare da ke…”

“Ke ma an ɗauke mini!”

Kukanta ya cika ɗakin.


Alhaji Ibrahim ya tsaya kamar mutum-mutumi

Ya kasa motsi

Ya kasa magana

Sai hawaye kawai suke gangaro masa

Ya miƙa hannu

Ya shafi goshin Zeenah

Cikin rawar murya ya ce

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un…”

“Allah Ya karɓi shahadarki zeenah na yafe miki …”

A karo na farko

Mutumin da ba a cika ganin hawaye a idanunsa ba

Ya fashe da kuka

Suhail kuwa

Ya durƙusa a gefen gadon

Ya riƙe hannun Zeenah da ya fara yin sanyi

“Zeenah"

“Ki tashi mana"

“Don Allah"

“Ki ce wani abu"

Ya girgiza hannunta

Amma

Shiru

Sai lokacin ya fahimci cewa

Ta tafi har abada

Ya sunkuyar da kansa kan gadon

Kukansa ya cika ɗakin ICU

Likitan ya shigo tare da wasu nurses

Ya duba idonta

Ya duba bugun zuciyarta

Daga ƙarshe

Ya sauke ajiyar zuciya

Cikin tausayawa ya ce

“She is gone"

A hankali nurses suka fara cire mata na’urorin da ke jikinta

Likitan ya ja farin zanin asibiti

Ya rufe fuskarta

Duk wanda yake ɗakin

Sai da yasake fashewa da kuka

Alhaji Ibrahim ya share hawayensa

Ya dubi likitan

“Ku shirya motar asibiti"

“Ina son a kai gawarta Kaduna"

“A can za a yi mata jana’iza.”

Likitan ya jinjina kai

“Allah Ya jikanta"


Ba a cika awa guda da rasuwarta ba…

Labarin ya bazu ko’ina

Kowa na cewa

“Zeenah ta rasu"

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.”

An yi mata wanka

An lulluɓe ta cikin farin likkafani.

Aka ɗora ta cikin motar asibiti

Suka kama hanyar Kaduna.

A gidan Mahaifin ta 

An cika gidan da masu ta’aziyya

Kuka ne kawai ake yi sai dab da mutuwar Allah ya saka kaunar ta cikin zuciyoyin mutane

Alhaji Ibrahim na zaune gefe

Kansa a sunkuye

Hajiya Rabi kuwa

Har yanzu ana lallashinta

Ta kasa yarda cewa Zeenah ba ta nan gani take kamar zata dawo


Abba, mahaifin Suhail, da Malam ma sun isa gidan

Sun yi jana’izar tare da sauran al’umma

Bayan an kammala jana’izar

An binne Zeenah

Kowa ya watse cikin jimami Rashin ta

Da yamma

Malam da Abba suka dawo gida

Iman da Ammi suna falo

Da ganin fuskar malam

Gaban Iman ya faɗi tun safe take jin faduwar gaba da batan dalilin taba

Ta miƙe tsaye

“Baba…”

“Me ya faru?”

Malam ya sauke numfashi

Cikin sanyin murya ya ce

“Khadija…”

“Allah Ya yi wa Zeenah rasuwa"

Nan take

Idanun Iman suka cika da hawaye

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un…”

Ta dafe baki

Ta tuna ranar da suka yi rigima

Ta tuna ranar da Zeenah ƙo  ta ba ta Khalil

Ta tuna cewa duk da komai

Zeenah uwa ce

Ta zube a kan kujera tana kuka

“Allah Ya gafarta maki zeenah"

“Allah Ya jiƙanki ya yafe miki"

Ammi kuwa ta dafe ƙirjinta

Ko da yake ba ta ji daɗin abubuwa da dama da suka faru tsakanin Zeenah da Iman

Sai mutuwa ta sa komai ya canza

Ta share hawayenta

tace cikin raunin murya

“Allah Sarki…”

“Mutuwa gaskiya ce…”

“Allah Ya sa ƙarshenmu ya zama mai kyau"

Hafsat ma har da nata hawayen

Gaba ɗaya gidan ya yi shiru

Sai sautin kukar Khairiya da ke neman a ɗauke ta

Shi kaɗai ne yake katse wannan jimamin

tunda aka gama jana'izar zeenah khalil bai bar jikin Suhail ba Lokaci zuwa lokaci yakan tambaye sa 

"Abba,ina mamana ta ce zata kawo min chocolate da sweet gashi ban ganta taba"

Suhail ya shafa kansa ya ce"maman taje unguwa she will be back soon"



Rayuwar fa kenan,Allah ya sa mu cika da kyau da imani wannan kadai ya isa mutun ya zauna da kowa lafiya , Mutuwa bata sanarwa takan zo ne ka shirya mata ko baka shirya ba Allah yasa mu koma ga Allah muna masu tsakakar zuciya

kar ku duba nishadin dake cikin littaffin nan fatana zaku dauki dukkannin darussan dake tattare dashi

ina maku fatan alheri masu jin haushin zeenah to kunga dai Duniya ba matabbata bace dan Allah ayi kokarin a zauna da kowa lafiya a daina gaba da ƙiyyaryar da babu gaira babu dalili

like 
share
comment