ALWASHI 2

44

by @rufaidaumar

ALWASHI 

   69

KATSINA

Kausar ce ke faman zirga-zirga a falonta, ta kira layin Areef ya fi a ƙirga sai dai amsa ɗaya take samu, a kashe. Hankalinta ya yi mugun tashi ganin mintuna kaɗan ya rage ƙarfe sha biyu ta yi. Kusan za ta ce tun da suka yi aure bai taɓa yin daren da ya wuce ƙarfe goma a waje ba sai yau. Ina ya tsaya haka? Direba da ya karɓi muƙullin mota a hannunta ɗazu da rana, ce mata ya yi ai ofis zai kai mishi saboda zai dawo a yau ɗin duk da ba ta san ma inda ya tafi ba.

Hankalinta ya kasa kwanciya, ta ga ba za ta iya zama ba don haka kawai ta miƙe ta zura hijab ɗinta ta fito. Kai tsaye ɓangaren Laila ta nufa. 

***

Laila na zaune tana  bin hotunan da Suhailat ta turomata da kallo, murmushi kawai ta ke yi ranta fari ƙal. Wayarta ta yi ƙara, ganin Suhailat ɗin ce ya sa ta ɗaga har lokacin tana murmusawa. 

"Good job Suhailat, na yaba kwarai da ƙwazonki. Hotuna sun fita fes. Na kuma ji daɗi ta yanda fuskarki ba ta fita ba. Kamar yanda kika faranta min, zan cikamaki alƙawari yanzu, kuma ki jira abin da za ki yi nan zuwa jibi. Zamu yi waya."

Suhailat ta yi dariya. 

"Ai fiye da hakan ma zan yi maki Hajjaju. Amma fa guy din ya burgeni, ba don kar na karya dokarki ba ai sai na haiƙe masa."

Laila ta yi murmushi. 

"Babu wannan a tsarin namu, kika sani ba nan gaba ƙila da kansa zai kawo kansa gareki? Ai mai hali ba ya fasawa."

"Amma Hajjaju kinsan abin ds ya fi ban mamaki? Wallahi duk da ba a hayyacinsa yake ba, sunan Allah yake ta ambato. Jikina har fa sanyi ya so yi, don dai na tuna cewa da sauran numfashina, na fi buƙatar duniya yanzu fiye da ɓata lokaci a hango lahira, wannan kaɗai ya sa na tsira ban biyewa zuciya na fasa ba."

Taɓe baki Laila ta yi. 

"Wannan duk ba matsalata ba ce, zan turomaki saƙonki yanzu."

Daga haka ta kashe kiran saboda ba ta son jin ma me Suhailat za ta ƙara faɗi. Ba ta maraba da hakan. A take ta cika mata kuɗaɗen har da ƙari. Ta aikamata receipt ta whatsapp, ba ta ko saurari dogon voice note din da ta mata ba bayan tulun stickers na rawa da godiya. 

Lokaci guda ta hankaɗa hotunan zuwa group din da suka buɗe na su uku, ita da Na'eem sai ko Zakiyya. 

Daidai nan ta ji ana buga ƙofar falon nata. Ta ɗan yi tsai, tunaninta waye? Anya ya ci a ce Areef ne ya dawo? Mutumin da Suhailat ta ba ta tabbacin koda allurar kashe jikin da suka masa zai sake shi to fa sai ya kai washegari? Jik muryar Kausar na kiran sunanta ne ya sa ta miƙewa bayan ta yi saurin saka wayarta a lock ta ƙarasa ta buɗe. 

  Ganin yanayin Kausar ya sa ta nuna alamun mamaki a fuskarta. 

"Lafiya dai Kausar? Wani abu ya faru? Na ganki wani iri."

Kausar tana dan murmushin yaƙe ta ce.

"Bakomai Anti, dama na ji Hamma shiru ne shiyasa na zo jin ko kin yi waya da shi. Nikam ina kira amma ba ta shiga ana cemin a kashe." 

Laila ta ɗan buɗe idanu kaɗan. 

"Wai bai shigo ba? Ni ai nayi zaton ma ya jima da shigowa. To ko lafiya? Kin kira gida?"

Kausar ta girgiza kai, gaba ɗaya ta ƙara shiga damuwa. 

"Babu wanda na kira, kar na tayar da hankalinsu a zo ba wani abu ba ne."

"A'a, ai ya kamata a kira. Bari na kira su na ji ko sun yi magana."

Ta juya da sauri, koda ta ba da baya wani murmushi ta yi kafin ta sa hannu ta ɗauki wayarta. Kausar ta ƙaraso jiki a saluɓe ta nemi wuri ta zauna. Zamanin nan na satar mutane dole hankalinta ya tashi. Yau idan wani ta kasance sace Hamma Areef aka yi ita ko ina za ta jefa kanta? 

Laila ta danna lambar wayar Abba kai tsaye. Ringing bai fi biyu ba ya ɗaga da sallama. 

"Abba, Sameera ce. Barka da dare."

"Ah, Sameera dai? Lafiya kuwa?" 

Cike da alamun tashin hankali da rashin nutsuwa ta amsa.

"Abba, Areef ne bai dawo gida ba har yanzu shi ne nake tambaya ko bai dawo ba ne?" 

"Anya? Yau muna tare da shi a ofis ai. Sun dawo. Kin kuma leƙa can wurin ita ƙanwar taki ba ya nan?"

"Eh Abba. Itama ga ta nan zaune a wurina hankali ba a kwance ba."
 Ta faɗi kamar za ta yi kuka. 

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Areef bai dawo gida ba? Kinga Sameera ku kwantar da hankulanku, bari na kira sa a way.."

"Ai Abba lambarsa ba ta shiga, wayoyinsa duka a kashe."

Ta katse Abban da faɗin haka. 

"Ya Allah, in sha Allah khairan. Ku kwantar da hankalinku, ku yi ta addu'a, bari na nemi Fareed mu ji."

Bai saurari amsarta ba ya katse kiran. Ta dubi Kausar wacce tuni hawaye ya wanke mata fuska.

"Abba ya ce mu yi haƙuri mu kuma yi addu'a. Kar ki damu in sha Allahu zamu ji alheri."

Kausar ta jinjina kai, suka ɗan yi zaman jim, Laila na ta ƙara gwada lambar Areef tana mai nuni da tashin hankali ƙwarai a saman fuskarta. Ta sanya wayarta a flightmode sakamakon kiran da Zakiyya ke faman jeromata. Can dai Kausar ta miƙe ta yi mata sallama ta fice zuwa ɓangarenta. 

Laila na rufe ƙofarta ta yi wani juyi da ƴar rawa tana dariyar farin ciki. Ta dauki wayarta ta shige ƙuryar ɗaki. Sai lokacin ta kunna, kamar kuma jira ake sai ga kiran Zakiyya ya shigo. Laila na dagawa cikin muryar dariya ta ce. 

"To ya aka yi? Saƙo ya isa kenan ko?"

"Laila, listen to me please. Laila hankalina ya tashi da abin da kika turo, ya yi muni da yawa. Please, please Laila 
we have to stop of all this before it leads to regret! Ina so ki goge hotunan nan, ki manta da komai ko don saboda Haidar."

"It's too late to stop Zakiyya! Ban ma ga wani dalilin da zai sa na fasa kudurin nan ba. Kina tunanin kin fi ni son Haidar ne? To ki sani, nan gaba Haidar will be more than happy kan wannan abu da ya faru. A tunaninki wai Haidar zai so Areef ne ko zan bari su rayu tare after all that he did to his mother?! Amsarki ita ce No! Har abada Haidar ba zai rayu ƙarƙashin zuri'ar mutanen nan ba, ba zai amsa sunan Areef Sada Bakori ba."

"Uhm! Laila ki farka! Ki farka haka! Ni dai kinga na tsorata, har ga Allah na yi nadamar zama cikin wannan plan din. Laila ina tsoron kar daga baya fa ki kamu da son..."


"Enough Zakiyya! Ya isheki! Kinsan Allah darajar Sameera ce ta sa ba zan zageki ba a yau! Ina mutuntaki saboda kin ci darajarta ne kawai! Amma wallahi ki kiyaye ni! Daga yau kuma idan har ba za ki iya cigaba da ganin ɓacin sunan familyn nan ba, mutanen da suka yi silar ƙawarki ba, toh kar ki ƙara shiga hurumina!"

Daga nan ba ta jira amsar Zakiyya ba ta katse kiran. Ranta ya yi mugun zafi da kalaman Zakiyya, hannunta har rawa yake ta shiga whatsapp ta cire ta a group din. Ya zamana daga ita sai Na'eem wanda bai ma hau ba balle ya ga saƙon. 

Wurgi ta yi da wayar tana jin wani tuƙuƙi a rai, haka kawai Zakiyya ta ɓata mata farin cikin da take ciki a yau.

 "Wai Haidar, kamar ta fi ni son sa. Mtsw!" 

Ta furta a fili gami da neman wuri ta zauna tana buga game a waya. Don ta ita bacci ma take son yi sai dai ba ta son fadawa zargi don haka ta koma falon ta zauna tana buga hamma. 

***
 A gefen Abba kuwa daren daga shi har Mami da duk waɗanda suka ji motsin safa da marwarsu a gidan cikin wannan dare sai da suka farka. Fareed kuwa koda Abban ya kira shi fitowa ya yi ya nemi ofishin ƴan sanda ya shigar da report sannan ya bi sahu zuwa ofis din nasu tare da jami'an. 

 Maigadin ya yi mamakin ganinsu, nan aka masa tambayoyi dangane da Areef din. Ya ba da amsa saboda har lokacin fitarsa ya gani da Magriba. Suka dai tabbatar Areef ya bar ofis din. Ɗan sandan ya dinga yi wa Fareed tambayoyi, Fareed na amsawa. Can dai suka yanke shawarar Fareed din ya je gida zasu cigaba da bincike tunda sun karbi lambar motar, da zarar sun ji wani labari za su sanar da su. 

Da haka Fareed ya juya zuwa gidan Abba. Labarin da ya ba su sam bai musu daɗi ba don har sun fito farfajiyar gidan jin ƙarar mota a zatonsu Areef din ne. Mami kuka kawai ta fashe da shi. 

 "Ni dama tun safe jikina na ba ni akwai wani abu da zai faru. Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Fareed babu wani wuri da yace maka zai je?"

Fareed jiki a sanyaye ya girgiza kai. Abba ya yi shiru yana juya maganganun Fareed. 

 Hajja da ke leƙensu ta window jin ƙarar mota ya sa ta buɗe ɓangarenta ta fito ta ƙaraso wajensu sanye da hijabi, idanunta alamun ta soma bacci ma. 

 "Lafiya? Fareed meke faruwa na ganka a nan cikin dare?"

Nan ya sanar da ita Areef ne ba a san inda ya shiga ba. Aikuwa ta hau salati da salallami. 

 "Kamar ya ba'a gan sa ba? Mutum sukutum kamar Areef ace ba'a gan sa ba? Ina zai shiga to? Ɗan uwanka ne fa, ba ya komai sai ya sanarmaka, za ka ce ba ka san inda ya shiga ba?"

Duka tana wannan zancen da nuna tsantsar damuwa da ruɗani a saman fuskarta da ma gangar jiki. 

 "Kinga Hajiya ya isa haka nan. Dare ya yi, da wannan tsayuwar da ake  gwara mu je mu yi sallah mu sanar da Ubangiji. In sha Allahu ba wani abun tashin hankali ba ne. Hankalina yanzun yana kan iyalinsa, na tabbata suna cikin matsanancin damuwa."

"Hakane Abba, ko za'a je a dauko su ne? Ko kuma a bari zuwa gobe da safe kar a je ya zo?"

Fadin Fareed, shi damuwa biyu ce a ransa, rashin ganin Areef yana jin tsoron kar a je matsalar daga Daddy Affan ne. 

Abba ya tafi a kan cewar a bar su din to, Mami ta dage lallai idan hakane sai dai ya kai Benazir ta taya Kausar kwana tunda tana kira tana ta kuka ta ce tsoro take ji. An kira wayar Laila kuma ba ta shiga. Dole haka Abba ya amsa, Fareed ya wuce da Benazir ya sauke ta a gidan ta shige ɓangaren Kausar. Daga haka ya ja ba tare da ya shiga ba. 

***
 WASHEGARI...

Areef ya farka cikin wani yanayi, kansa ya yi nauyi kwarai. Ya dinga bin inda yake da kallo, motarsa ce dai, kansa da ke juyawa da ya ɗago ya sanya shi komawa a hankali ya jingina da kujerar. Ji ya yi gaɓɓansa duka sun masa nauyi, bai samu damar yin kowane irin tunani ba. Motarsa a kunne take ga ac an ware, sanyi sosai a motar, sanyin da yake jinsa har cikin ƙasusuwansa. 

  Daƙyar ya buɗe ƙofar motar ya sanyo ƙafafunsa waje. Ji yake kamar ya sha wani abun ya bugu saboda koda ya miƙe ƙafafunsa ne suka harɗe shi ya faɗi a gefen hanya. Sarawar da kansa ke yi kuwa bai hana shi gane cewa bakin titi yake ba, sai dai ba zai ce ga wurin ba. 

Wata mota ce ta zo wucewa ta tsaya, sai ko daidaikun mutanen da suke a hanyar wadanda suka ƙaraso. Mai motar ke tambayar lafiya? Suka ce ba su sani ba. 

"Ƙila shaye-shayensu na zamani ya je ya yi."

"Duk da haka yana buƙatar taimako. Zai fi kyau a sanar da hukuma."

Da wannan suka sanar da ƴan sanda, ta dalilin wannan har labari ya kai ga iyalin Sada Bakori. Su kuma suka wuce asibiti da Areef. 

Kafin ka ce me, iyalan gidan Sada Bakori har da matan Areef din sun nufi asibitin. 

Kowa idan ya ji a buge aka tarar da Areef kuma babu wayoyinsa a jikinsa, abin da suke kawowa kawai ɓarayin waya ne. Hajja dai tana ta satar kallon Laila wacce alamu suka nuna ba ta wani damu sosai ba. Jikinta ke ba ta cewar akwai wata a ƙasa sai dai ta bar wa ranta sai sun keɓe da Lailar. 

Awanni kaɗan Areef ya yi ya dawo daidai, aka sallame shi. Duk wasu tambayoyin ƴan sandan ya amsa, abin da kawai ya iya riƙewa shi dai ya ga wata za ta tsallaka titi ta yo gaban motarsa, hakan ya sa shi cin burki. Daga nan ya ji an shaƙa masa abu a hanci bai ƙara sanin inda kansa yake ba. 

 Ɗan sandan ya nuna zasu yi bincike, ya bisu da toh don shi bai ga abin bincike ba tunda har ya tsira da rai da lafiyarsa. 

Da wannan aka tattara aka wuce gidan Abba da shi. Hankula kuma suka kwanta. 

***
 "Duk wani aiki mu tsaida shi sai nan da sati biyu, kar mu ba da ƙofar da za'a ɗago mu, mu bari har wannan ƙura ta lafa."

Zakari ya dubi Hajja mai masa wannan bayanin. 

"To wai Hajja ni abin da ke ɗaure min kai. Ta ya ya ɓarawo zai sace waya kuma bai haɗa da mota ba? A zamanin nan don a kashe mutum ma a ɗauke wayoyinsa ba wani abu ba ne ballantana kuma mota, anya kuwa babu lauje cikin naɗi?"

Hajja ta sauke ajiyar zuciya. 

"Tabbas nima na yi wannan tunanin, na kasa gano meyafaru. Koma dai mene ne ba banza ba. Sai abu ɗaya, ka kula Laila ba ta wani ji ɗarr sosai ba da wannan lamari? Duk da na sani dama ba za ta yi baƙin ciki da baƙin cikin yaron ba, amma halin ko'in'kular ya yi yawa. Anya ba wani abun ta ke shiryawa ba?" 

Shiru ya ɗan ratsa kan Zakari ya ɗaga kafaɗa. 

"Komai zai iya yiwuwa Hajja, amma ku yi waya mana ki ji me za ta ce maki."

Girgiza kai ta yi.

"Ba yau ba, tana gidan nan ai. Idan ma suka koma gida dare ya yi, bari zuwa gobe."

Da wannan suka haɗiye dukkan wasu tambayoyinsu sai sun tuntuɓi Laila.

***
  
 
 
 
©Rufaida Umar