23
Page 23
"Nazli wai ke ce haka?" Me ya faru ya na ganki haka?" Shin me ya sa miki kuma me ya sa kika yi dare har haka?" Ammie ke jefo mata waɗan nan tambayoyin na neman sani, ba tare da ta bata amsoshin tambayoyin da take mata ba ta ce. "Ammie mai adaidaita na waje ban ba sa kuɗinsa ba."
Daga haka ta tattara sauran ƙarfi da ya rage mata ta yi cikin gidan ta bar Ammie da Maman Sadiq cikin ɗumbin mamaki da tambayoyi fal ransu. Maman Sadiq din ce ta yi ƙarfin halin faɗin. "Ki barshi kawai Baba zan sallame shi ke dai bita ki ji ba'a si ban tunanin ƙalau take." Kaɗa kai kawai Ammie ta iya yi mata ba tare da ta samu zarafin furta komai ba ta mara ma Nazli da tuni ta yi shigewar ta ɗaki baya.
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, Nazli! Wai me ke faruwa ne me ya sa miki." Ammie ta faɗa a lokaci da ta shigo ta samu Nazli nannaɗe cikin bargo jikinta zafi rau ko ina na jikinta sai kyerma, ga kayanta da ke jiƙakku bata cire ba.
Hankalin Ammie ya kuma tashi jin Nazli ta riƙe hannunta gam murya a rarrabe ta ke fadin. "K..ka.karki rabu d..da ni, karki juya min baya Ammie ba zan iya dauka ba." Ammie ta ruɗe ta kasa magana sabida tashin hankali bata ko maida hankali kan abun da NaZli take faɗa ba ta barshi a zafin ciwo ne, murya a sanyaye cikin nuna tausayawa ta ce. "Ki tashi ki cire jikakkun kayan nan ki suma ai sun isa su ƙara miki ciwo."
Da taimakon Ammie Nazli ta cire kayan ta bata wasu kayan ta sa, Ammie ta haɗa mata shayi mai zafi ta bata ta sha kana ta ɓalla mata magani paracetamol ta bata ta sha kana ta gyara mata shinfiɗa ta kwanta.
Ko bayan da Nazli ta yi bacci Ammie ta kasa runtsawa jikin ta ya yi la'asar da yadda ta ga Nazli na ta surutai na rashin gado, abun ba ƙaramin tsorota ta ya yi ba har ta soma tunanin ko shafan aljanu ne.
Sai dai ga yadda Nazli ta tashi a washe garin ranar sai ya sanyaya mata zuciya, duk da ta fahimci ƴartata na ɓoye mata wani abu sai ta barshi a ya wuce ba dan ya wuce a wajen ta ba sai dan ganin yanayen ta a ɗazun da ta yi mata maganar ganin yadda yanayenta ya canza lokaci guda ya sa ta bar zancen a yanzu dai idan lokacin sanar da ita ya yi za ta same ta ne ta faɗa mata.
Tafiyar da ba'a yi a ranar ba kenan, sai washe gari da ta ware. Tun safe suka nemi akori kura suka haɗa yan tarkacen su dangin katifa matacin kai da tukwana, Nazli ce a kan gaba su kuma a bayan ta.
Boysqouter a ka ba su suka kakkaɓe da kuma share ko ina kana suka maida kayan su a ciki, rayuwar su a gidan dai gadaram gadaham. Ɓacin rai dai ba za'a rasa shi ba, sai dai suna taka tsantsan da shiga lamarin da bai shafe su ba. Musamman Ammie tun zuwan su da yadda aka amshe su sai ta sha jinin jikinta hakan ya sa ta ke kaffa kaffa da lamarin gidan baki ɗaya, ta ɗayan ɓangaren kuma suna cikin neman gida. Ƙalubale na farko da suka fara fuskanta a gidan shi ne rashin kunyar Farida, sam bata raga masu bata jin kunyar ta kalli tsabagen idon Ammie ta karta mata rashin kunya, wanda Nazli ma ta wannan bangaren bata raga mata ko kaɗan. Tana juran komai amma ban da wulaƙanta Ammie a kan haka har wata rana suka kusan dambatuwa kan Farida ta saka Ammie yi mata wanki ta haɗa mata undies ta wanke, bayan ta gama ta shanya ta koma na su sashen aka yi rashin sa'a Ammie ta manta da wankin har ruwa ya tadda kayan nan a waje ita kuwa ta saka Ammie a gaba da faɗa kamar za ta kai mata bugu Ammie na bata hakuri, a na cikin wannan badaƙalar ne Nazli ta same su inda bata yi wata wata ba ta dauke Farida da wawa mari.
Dalilin da ya haddasa ƙiyayya tsakanin su kenan dama Farida na mugun jin haushi da kuma ɓakin cikin Nazli ta fita kyau, sai haka ya ƙara wutar ƙiyayar da take mata tare da ɗaukan kudirin sai ta ɗau fansa kan abin da Nazli ta yi mata. Kasancewar rana babu kowa a gidan Hajiya Binta da bata gari tana maiduguri bikin yar kanwar aminyar ta da ake yi, ya sa ta yi lagwas sanin bata da gaskiya kuma da yadda Nazli ke hayayyaƙo ta sani tsab sai ta zaune ta ba me ƙwacen ta.
Sai dai Alhaji na dawowa ta same shi ta labarta masa ƙarya da gaskiya ya sake bata rashin gaskiya, inda ya fuffutaketa kana daga ƙarshe ya saka dan dolen ta ta baiwa Ammie haƙuri ba don ta so ba. To daga nan fa suka soma takun tsaka da Nazli ta ɗau alwashin ko ba juma ko ba daɗe sai ta rama abun da Nazli ta yi mata wannan alƙawari ne.
Haka kurum ta ke cakalar Nazli da rigima sai dai ita bata biye mata bayan dogon kasheɗi da Ammie ta yi mata da su rufawa kansu asiri su zauna lafiya har zuwa sanda za su bar masu gidan su lafiya dan zaman su na ɗan lokaci ne kar ta biye mata.
Da wannan ta ke kauda kai ga dukkan iya shege da Farida ke kawo mata, sai kuma yaran, Abla da Araf, ba laifi sun sake da ita sosai dan a yanzu har homework take taya su. Dama Abla ce me matsalar da ta ke biyewa Farida suna rashin mutunci a gidan amma tunda Farida ta tattara ta koma school komai ya sarara, tuni ta ware ta saki jiki tamkar ƙaninta duk da wani bin idan ƴan halin sun mutsa haka take zuba tsiya ba mai tankawa.
Sai dai fa duka wannan ƙalubalen ba su kai abin da ta lura da kuma fara fuskanta a wajen Alhaji Badamasi ba, tun tana shiru da da kauda kai tana masa uzuri har abu ya soma fin ƙarfin ta. Abu na farko da ta fara fuskanta a wajensa shi ne, yawan ƙiran ta a landline da ya ke. Duk minti sai ya ƙira ya ce kawo wannan yi mini wancan. Ko kuma haka kurum ya ce yana so ta yi masa hira.
A farko dai babu ruwansa da ita, ko ta gaishe shi bai amsawa ƙarshi ma sai dai ya daka mata tsawa ko yayi tamkar bai ganta ba. Haka take kaffa kaffa da lamarin sa da na matarsa kullum take cikin nikab kamar yadda Hajiya Binta ke so, ba abin da ke gaban ta sai aikin ta.
Inda a ka soma samun matsala shi ne, wata rana da Alhaji ya yi manyan baƙi da ita da Ammie kawai suka yi aikin abincin tarban baƙin, abinci ne kala kala tun safe suna kitchen.
Sabida kar ƙaurin abinci ya fita palo suka ja ƙofar kitchen, ga zafin rana da weather ta haɗa da zafin gas ya sa ta cire nikab da hijab dinta ta rataye a kan cabinet ta soma jajjagen kayan miya a greater, hakan ya sa jikinta motsawa, kansu ya yi zafi da aikin da ke gaban su har ba su san da turo ƙofa da aka yi.
Alhaji Badamasi ya sauƙo ƙasa dan tarɓan baƙin na sa ya liƙa kitchen dan sanar da Hajiya Binta da zuwan su a nan ya yi kyakkyawan gani, sai ya rasa hankali da nutsuwar sa na wucin gadi.
Sai ya ji ba abun da ya ke so da burin ji kalan ya ji shi a jikinta ya lugwe gweyata son ransa, nan fa hankalin sa ya tashi ya ji duk duniya babu macen da ya ke son kasancewa da kamar ita. Duk iya yawon barikinsa bai taɓa ganin kyau da diri kalan wannan ba, ya kuma tabbatar wa da kansa ko sama da kasa za ta haɗe to sai ya maida kwadayin sa.
Tun daga wannan rana ya saka ma Nazli ƙahon zuƙa duk inda ta ƙibta cikin gidan to idan sa na kanta, duk da tana cikin nikab hakan bai hana sa ƙura mata ido da wassafa yadda za ta kasance a haka zinɗir ba tare da sutura a jiki ba. Sabida barikanci ya hana ta ƙiransa yalla ɓai sai Daddy a cewarsa ai tamkar ƴa take a wajensa dan haka Daddy za ta na ƙiransa.
Hajiya Binta kuwa ta shaƙa ba kaɗan ba, dan har tutse Nazli ta yi da zancen me ke tsakanin ta da mijinta ta yi mata rantsuwar ba abin da ke tsakanin su sai girmamawa da mutunci, tana mutun ta sa ne a matsayin sa na uban gidan ta da ke biya ta a duk wata, sai a lokacin Hajiya Binta ta ji sanyi a ranta, ta kuma sake jan kunnenta da ta kiyaye mijinta kar ta kuskura, kar ta ji kar ta gani.
Daga ƙarshe ta bata aikin saka ma shi ido ga dukkan wani abu da ya ke. "Yauwa kina jina, ina son ki saka min ido sosai cikin gidan nan. Zan yi tafiya ta kwana uku ina son ki saka min ido cikin shige da ficcen Alhaji, duk abin da hankalin ki bai kwanta da shi ba to ƙira ni ki faɗa min. Sannan ina son ki maida hankli sosai dan ganin ko yana kawo yan mata sanann ina son sanin lokacin fitan sa da dawowarsa cikin gida."
Cike da mamakin lamarin ta kaɗa mata kai ta miƙe ta bar mata ɗakin, a ƙasan zuciyarta kuwa tana neman tsari da wannan ahali tana Allah Allah su samu su bar mu su gida ita da su har abada kenan dan aje aikin za ta yi ta kama sana'a ba ita ba aiki a ƙarƙashin wani aradu. Dan lamarin ba mai sauki bane.
Lamari na Alaji Badamasi ya ƙarfafa yanzu har Ammie idan ya gani sai ya tsuguna har ƙasa yana gaishe ta, Ammie sai ta ke ganin abun bambara kwai wai namiji da suna Hajara, wani ƙato da shi ta tabbata dai a girme dai zai girme ta daɗin daɗawa ma a ƙaeƙashinsa suke shi ne ya ke wani tsuguna mata. Abin da ya fi bata mamaki da tsoro ma bai fi yadda ya ke fakan ido Hajiya Binta ya shiga har sashensu da sunan ya zo gaisuwa ne, ya zo yana sunne kai kamar sabuwae amarya. Idanuwansa kuwa a gwale cikin lugu da saƙon gidan yana duba gilmawarta.
Abun sai ya ba Ammie tsoro sai ta soma kafa kafa da ƴarta ta, ta dai na barin ta zauna a farfajiyar gidan muddin yana nan, hatta garden da take yawan zuwa tana jin dadin wajen ta hana ta zuwa tun sanda ta je neman ta a wurin ta ga ya tutuse ta a gaba da magana da sam hankalin ta bai kwanta da hakan ba, girkin ma ta ƙarbe mata na ta iya shara wanke wanke da mopping.
Nazli kuwa har gaji da ƙiran take, a hankali ya soma bayyana mata ƙudirinsa cikin tsantsan yaudara ya furta mata kalmar aure. Tabbass ta razana da furucinsa ta kuma tsorota da lamarin dan bata manta yadda suka yi da Hajiya Binta ba kan ta kiyayi mijinta, ita kam ko giyar wake tasha ta aminci masa ne. Ai hanyar jirgi daban ta mota daban, ita ba za ta iya da masifar Hajiya binta ba kuma ita a tsarin ta babu aure a yanzu, kuma yau maganar aure ya kama to ba da Alhaji Badamasi ba.
Da ya ga hakan ba sai ya koma kama ƙafa da Amme ba, ya dinga siya kaza kayan cima yana kai mata da sunan ai ita ma kamar mahaifiya ce a wurinsa. Hankalin Ammie ya sakw tashi ta soma tunanin mafita cikin gaggawa dan ba za ta yafewa kanta ba idan har wani abu na cutarwa ya same yar mutane, amana ce a wurinta har zuwa ranar da Allah ya ɖibanci lamarinta ya sa ta tuna da wacece ta, daga inda kuma ta fita za ta yi tattaki har gida ta damkawa iyayenta ita cikin salama da aminci.
~~~~~~~~
Yau lahadi, Nazli na backyard gaban ɗakin su ta haɗa kayan ta da na Ammie tana wanki. Riga ce shirt me ƙaramin hannu a ajikinta ta daura zani a kai, yanaye na jiki kalan na ta ya sa rigar ta ɗan ɗameta ƙirjinta na ɗan fitowa daga saman rigar. Ammie ce ta fito hannunta riƙe da plate ta gama cin abinci kenan tun ɗazu take da nazli ci amma ta ce ita sai ta gama wanki da ta ci jikinta zai mutu da wankin, hakan ya sa ta kyale ta ta zuba na ta ta ci.
Kamar an ce Ammie ta ɗaga kai ta kalli sama sai ta hangi Alhaji Badamasi zaune cikin balcony na bayan gidan, tsaye ya ke ya harɗe hannye biyu idonsa ƙuri kan Nazli da ke wanki hankali kwance ba tare da ta ankare da shi tsaye a wajen ba.
Idonsa har jaja suka yi dan jaraba kalar ta shi, tsawar da Ammie ta daka ma Nazli ne ya firgita daga ita har shi. Ammie ta nuna mata ɗaki cikin fushi ta ce. "Ban hana ki saka wannan ba kuma ina hijabin ki, wuce ciki na sake ganin kin fito a haka."
Sum sum Nazli ta aje kayan ta yi cikin ɗaki kanta na ƙasa tana tunanin abin da ya fusata Ammie har haka, fitowr da bata yi ba kenan dan ko wankin ma Ammie ce ta idda shanyawa.
Ɓakin ciki ne ya hau shi iya wuya, na ganin yadda Ammie ta ɓata masa jin ɗadi nan ya soma tunanin yadda zai samu abin da ya ke so ko ta halin ƙaƙa ne ya rantse sai ya samu abin da ya ke so daga gareta. Dan ya lura daga ƴar har uwar na da taurin kai da duk yadda ya bi da su ba nasara, kuma shi a yadda ya ke bai taɓa neman wani abu daga mace ya rasa ba dan haka ba za a fara a kan ta.
Ya ja kwafa tare da taɓe baki da faɗin. "Da ni da ku ne, na ga wanda zai fidda ke daga tarko na " daga haka ya koma ciki, sai dai duka wunin ranar cikin ɗaura da kuncewa ya ke na ganin cikan burinsa ya cika.
~~~~~~
"Kai Ammie, zan tashi fa kawai minti biyu za ki bani da zarar an tafi tallah zan tashi." "Ke kika sani, ni dai na faɗi nawa gwara ki tashi tun wuri ki je ki tsabtace masu wuri bana son zuwan ki wurin da dare."
Cewar Ammie a sa'ilin da ta gama iddar da sallar isha ta shafa fatiha, Nazli da ke kallon wani series mai suna MARRIED AGAIN da ake haskawa a tashar Zeeworld ta ce. "To Ammie." Sai dai haka bai sa ta tashi ɗin ba sai da ta jira an tafi tallah ta daka tsalle ta fita da gudu Ammie ta tasaida. "Dawo dawo haka za ki tafi zikau ba kallafi?" Maza dawo ki ɗauki hijabi."
Da gudu ta koma ta ɗauki hijabin Ammie da ke kan darduma ta ruga aguje tana cewa Ammie. "Ammie ki duba min kar a wuce ni please." Daga nan ta nufi cikin gidan, da palon ta soma ko ina kaca kaca kai ka ce an yi watanni ba gyara, kana ta koma dinning shima ta gyara ganin yadda su Abla suka ɓata shi da abinci.
Daga nan ta koma kitchen shima ta soma tsabtace shi, gama wanke wanken ke da wuya ta kawo ruwa da mopper za ta yi mopping ta ji shigowar mutum ko kan ta ɗaga kai ta ga yana maida ƙofar ya rufe tare da saka ma kofar key. Dumm!!! Gaban ta ya faɗi ganin sa a kitchen. Murya cike tsoro da fargaban da ya dirar mata lokaci guda ta furta. "M..me ya kawo Nan?"
Wani ɗan iskan malalacin murmushi ya sakar mata, kana cikin bariki ya ya shafa gemunsa me cike da furfura ya soma takowa gareta yayin da ta soma ja da baya...