WAI YAU NI AKE CEMA 'YAR KWAL UBA; SAI KACE 'YAR BARAROJI

WAI YAU NI AKE CEMA 'YAR KWAL UBA; SAI KACE 'YAR BARAROJI

by @fatimadahirufuntuwa

WAI YAU NI AKA CEMA 'YAR KWAL UBA; SAI KACE 'YAR BARAROJI.

      Wani dan uwan mu  ne yazo daga 'kauye, ina zuwa wurin shi muka gaisa, gaisuwa ta 'kare, sai ya fara cewa

     "Wai ke yanzu Binta  ina matsaya ne game da zancen auren ki? koko haka kike so kita zama muna sa maki ido?"

    Na ce  "Baba wane aure kuma? Ai idan zanyi aure kune zaku fara sani, kuma kune masu d'aurawa, ni banyi wani zancen aure ba, ku dai taya ni da Addu'a Allah  ya kawo na kirki."

   A'ah Mutumin nan fa sai ya  kama fad'a.

   "Ai kullun dama haka kike cewa! Ba zaki ta'ba kawo mana magana mai dad'i ba! duk wanda Allah ya baki ba zaki aura ba? Kina nan  kina kawo mana zancen banza! Ina Maganar wannan yaron Sunusi mai gadi? Ba zaki maida hankali ayi hidimar nan ba, ko don kinga na sa maki ido? To kiyi maza-maza ki turo min Sunusin nan, yazo a tsaida magana."

    Na ce  "Baba wane Sunusi kuma zan aura? taya za'ayi ya iya ri'ke ni? bafa wata sana'a yake ba, Kuma gadin ma da yake dubu sha biyar ake biyan shi, a wannan zamanin da ake ciki taya za'ayi mai Al-bashin 15k ya iya rike aure?"

    "Ai dama ku tsiyar ku kenan son kudi! Da yake gadin ba'a can ake bashi ci da sha ba?"

    Na ce  "To kuma ranar da aka kore shi daga gadin fa?"

    Ya ce  "Ai ba zaki ta'ba  fad'in Al-kairi ba! Madadin kiyi mashi Addu'a yaci gaba, ya koma direban gidan ko ya fara yi masu wanki da guga, amma Addu'a kike yi ma a kore shi! Kufa Mata na lura haka kuke! daga zarar ba ku son abu ba zaku ta'ba fad'in Al-kairin shi ba, to duk ma abinda zakice-kice! Amma dai kice mai yazo."

    Naji gaba na ya ce rasss! Na ce  "Baba yana aure na fa 'kauye zai maida ni, kuma garin su ko Network ba bu."

   Wani irin kallo yayi mani cikin mamaki sannan ya ce  "To ba gara ma 'yar  'kauyen da ke ba! Miye marabar ki da 'yan 'kauyen?" Dame kika fi  'yan 'kauyen? Yaron nan kuma har noma ance yanayi, bara buhun masarar shi biyu ya bige, amma dayake ke ba jin magana kike ba, kin kawo mana 'kabli da ba'adi, to ba yarda zanyi ba!"

    Na ce  "Garin su fa babu Network."

    Ya ce  "To ba sai a siya a tafi da shi ba, da wani shegen kauce-kaucen ki."

    Na ce  "Baba ai ba siyen shi akeyi ba, idan gari 'kauye ne basuda shi, kuma ko 'yar wayar nan da nakeyi ba halin inyi, shiyasa, ayi dai ha'kuri in samu mai d'an gwa'bi-gwa'bi mai sana'a."

    Ya jefe ni da sandar da yake dogarawa, ya ce  "Tashi ki ban wuri! 'Yar kwal uba; sai kace  'yar bararoji."

    Nan dai na barshi yanata masifa.

πŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™‰πŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆ

    Idan zakayi aure ka bari sai kanada sana'a wadda kasan cewa zata iya ri'ke ka kai da iyalinka ba tare da kun tagaiyara ba, Sai kaga mutum ana ciyar da shi amma yana 'ko'karin ya d'auko  'yar mutane nauyin ta ya dawo kan shi, taya za'ayi ba za'ai ta samun mace-macen aure ba?

   So da yawa maza sunayin auren ne ba tare da lissafin cewa zasu iya ri'kewa ko ba zasu iya ri'kewa ba? Sai su dogara da cewa idan nayi auren wata 'kila hanyar samu ta bud'e mani, to ka ha'kura ta bud'e d'in mana.

    A matsayin ki na mace, kada ki yarda ki biye ma dad'in soyayya ki auri wanda ba zai iya d'aukar d'awainiyar ki ba, duk son da kike ma namiji idan kikaga ya gaza bayan aure, ko ba zai iya  ri'ke ki ba, to wannan soyayyar sai kin nemeta kin rasa.

   Ana gina rayuwar aure ne cikin kwanciyar hankali da jin dad'i, to idan ba shida sana'ar da zai iya ri'ke ki ina zaki samu wannan? Daga mazan har matan lallai mu zauna muyi lissafi, indai muna son a samu saukin mace-macen aure

  Wah! Ai ni yanzun munyi hankali

Fatima Dahiru Funtuwa Binta✍