KWATAR KAI PART 2
๐ฟ๐ฟ๐ฟKWATAR KAI๐ฟ๐ฟ๐ฟ
NA
FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA
PAGE 2
๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
Humff! Suwaiba tayi ajiyar numfa ta ce "To shikenan sai anjima, na gode."
Har misalin 'karfe goma sha biyu da rabi na dare, yana zaune a falo, yana tunanin halin matar shi da kuma mene ne ya sauya mata hali lokaci guda, kuma duk iya tunanin shi a kan ya gano wani abu da yakeyi mata wanda ba dai-dai ba ya kasa.
Shin me nakeyi ma Suwaiba ne? Ba haka take ba a da, me yasa ta sauya min yanzun? Wane laifi nake yimata?
Duk ya kasa samun amsoshin tambayo yin shi .
Kuma ni a iya sani na Hauwau mai biyayya ce, tana ba ta girman ta, suna kuma zaune lafiya,to ni me yasa take yimin haka?Saboda na 'kara aure kawai? Meyasa Suwaiba take dafa ni da ruwan dana kasa tantance na sanyi ne ko na zafi? Me take so inyi mata ne ta gane ina son ta? ta gane har yanzun yadda take a cikin zuciya ta bata canza ba, ta san cewa.......................
'Kamshin turaren tane ya fara katse mai tunani, ya d'ago da sauri yana 'kara kallon ta, tayi shirin kwanciya barci, jikin ta sanye da 'kananan kayan barci, wad'anda suka fito da ainihin halittar ta a fili, sai 'kamshin turare da yake tashi a jikin ta.
Ta 'karaso inda yake a natse, shi kau idanun shi na kanta.
Hannayen shi tafara kamawa.
ta ce "Love baka saba kaiwa wannan lokacin ba, meke faruwa? miye ne yake so ya hana min mujina barci?"
Ya janyo ta ya zaunar da ita kan 'kafafun shi.
Ya ce "Afuwan baby na, ba wani abu daya isa ya d'aga mani hankali idan ina tare da ke, domin kuwa keme share hawaye na ce a cikin ko wane irin hali, ina yima sauran maza Addu'ar samun mace mai kyawawan hali irin naki, domin kuwa duk wanda yayi dace da samun mace irin ki ya gamayin kuka, I LOVE YOU HAUWA'U."
Yayi mata kiss a kumatun ta.
Tayi dariya tare da 'kara narkewa a jikin shi," ta ce to muje kayi wanka ka kwanta haka nan, kaga dare yayi."
Yayi mata wani irin kallo cike da tsantsar son ta a cikin idanun shi.
Ya ce "To zakiyimin wankan ko?"
Ta ce "Wannan kuma ai ba sabon abu ba ne."
Sukayi dariya
baki d'aya, tare da shigewa uwar d'aka, yana sa'be da ita a kafad'ar shi.
Haka ya kasance cikin samun kulawa, a kwanaki biyun nan da yayi a d'akin ta, tana nuna mashi tsantsar soyayyar da sai kayi tunanin ma yadda take son shi; shi baya son ta haka, nan kau tsabar iya kula da muji ne kawai.
Misalin 'karfe biyar na yamma ya shiga d'akin Suwaiba, yanayin Sallama sai ya fara kwala mata kira, da cewa
"Sweety! Sweety!!Kina ina ne? Ki fito mana, ya 'kara tura kan shi cikin d'akin, tare da 'kara nanatawa
Ya ce "Haba Sweety na sai kace ba kowa?"
Kafe shi da idanu tayi cike da mamaki, tayi sororo tana kallon shi.
Ya ce "A'ah! Wai dama kina jina kikayi shiru?"
Ta ce "Yo ai ban san dani kake ba, yau kuma wata sabuwar yaudararce ka 'bullo min da ita?"
Ya ce "Yaudara kuma?"
Ta ce "Yo to ai ni ban ta'ba jiba, yau ka sanya min wannan sunan kuma?"
Ya kyalkyace da dariya, ya ce "To ai kinji matsalar taki, ko sunanma baki iya amsawa, to bari in kira ki da sunan da kika saba, Suwaiba, shikenan ko? ko shima yaudararce?"
Ta ce "Umfh!! Kai dai ka sani! Ni duk wata dubara da zaka 'bullomin da ita kallon ka nake karrr! Wai ni zaka d'auka mara wayau! yanzun ne kasan ka kira ni da Sweety d'in?"
Ya kama hannun ta tare da fad'in "Ajiye kayan nan zauna, muyi magana.
Ta ce " Amma dai ai kunne ke ji ko?
Ya ce "Na sani, amma dai zo ki zauna kiji."
Sannan ta zauna, tare da fad'in "Ina jinka."
.
Ya ce "yawwa to ko ke fa, me zaki bani inci?"
Ta ce "A'ah!wannan wace irin tambaya ce? ya wuce abinda ka kawo, kaga Nasser dakata! Duk wani kwane-kwane da zaka yimin na yaudara! Ko kuma munafunci! Ba zasu ta'ba wanke laifin ka a wuri na ba!!"
Ya maimata ya ce,, "Laifi, Suwaiba laifin me nayi maki? Don Allah sanar dani"
Ta ce "Nasser ai baza ka gane ba."
Ya matsa hannun ta da 'karfi, yadda ya tabbatar taji zafi, ya ce "Ko ba zan gane ba sai kin sanar dani."
Ya kuma d'aure fuskar shi alamar babu wasa, ya ce "Gara ayita ta 'kare yau!Suwaiba yau sai kin fad'a mani laifi na koda bazan fahimta ba!!
Idanunta sukayi rau-rau!! Suka ciko da hawaye, ta ce "Nasser da ni kad'ai ce a wurin ka, yanzun mun zama mu biyu, d'abi' arka da halayyar ka ta canza, ko ban fada maka ba, kai kanka kasan da ba haka kake ba, Nasser ka canza mani!"
Dai-dai nan hawayen dake kwance cikin idanunta suka ziraro.
Hakanan sai yaji tausayinta ya ka mashi, ya sassauta ri'kon da yayi mata, sannan ya ce "Har yanzun ban gane abinda na canza maki dashi ba, a kwai abinda nake yi maki da yanzun na daina? Ko kuma akwai abinda nake yima ki yanzun wanda ba kya so?"
Tace "A'a amma inaso ka fahimta Nasser kowace mace tana da kishi, yin auren nan da kayi naga ka 'bullo da wasu abubuwa da yawa, wad'an da ni ban san ka dasu ba, gaba d'aya Nasser rawar jikin ka a kan Amaryar nan taka ya'ki 'karewa, kullun d'okin ta kake kamar ranar aka kawo maka ita, ko an gaya maka cewa ni zuciya ta ta dutse ce? Ba na jin zafin komai idan anyi mani ba dai-dai ba? Ba wai ina nufin ince bana son auren ka da ita ba ne, ni ban isa ba, tunda Allah ya halasta maka, amma na lura soyayyar da kake yi mata ni baka yimin irinta, ba burina in rabu da kai ba, a'a so nakeyi ka kwatanta adalci a tsakanin mu".
Ya ce "Akwai abinda ki kaga na ba ta ke ban ba ki ba?"
Ta ce "A'a.
Ya ce "Akwai abinda nayi mata ke ban yi maki ba?"
Ta ce "A'a.
Ya ce "To wane adalci kike so ayi yanzun?"
Ta d'ago idanun ta jajur ta 'kara kallon shi, tausayin ta ya 'kara kama shi, duk da ya kasa gane laifin shi a wurinta.
Ta ce "Akwai! Duk ranar da zaka koma d'akinta a kwai bam-banci da ranar da zaka zo d'aki na."
Ya 'kara kallon ta a razane ya ce "Wane irin bam-banci kuma?"
Ta ce "D'oki-zumud'i-da-kuma 'kosawa."
Ya ce "Waye ya fad'a maki haka?"
Ta fashe da kuka tare da fad'in "An gaya maka ni bani da hankali ne da bazan gane ba!! Itace babyn ka, itace love d'in ka, itace sweetyn ka, har a gaban kowa kana fad'a mata haka."
Ya ce "To ke yanzun ba gashi na kira ki da Sweety d'in kin 'ki amsawa ba, Suwaiba ba wani abu ne yake damun ki ba, KISHI NE, kuma duk abinda kika lissafo min a matsayin laifi na; ba laifi ba ne, ba zance Allah ya raba ki da kishin nan nawa ba, domin hakan ya tabbatar min da cewa kina so na sosai, sai dai ince Allah ya rage maki zafin kishin, Suwaiba ina son ki, daga kan harshena har cikin zuciya ta, abinda nake fad'a maki gaskiya ne, kada ki d'auka cewa auren nan da nayi ya rage wani abu daga cikin son da nake yima ki, har yanzun kina nan kamar yadda kike a cikin zuciya ta, ki kawar da idanun ki daga kan Hauwa'u, ki d'auka tamkar babu ita a cikin gidan ki, ki manta da ita, ki share ta a cikin zuciyar ki, sai kiga kin zauna lafiya, amma idan hankalin ki na kan ta, duk wani motsin ta kina sanya mata ido, to ba yadda za'ayi ki zauna lafiya, domin kuwa abinda ba'ayi ba ma sai zuciyar ki ta raya maki cewa anyi, to kinga daga nan sai shed'an ya samu wurin zama a cikin zuciyar ki, yana sa'ka maki sawu abubuwa daban a cikin tunanin ki, a binda ma bai faru ba saiya 'kawata maki shi da cewa ya faru, to daga nan shikenan bazaki 'kara samun kwanciyar hankali ba."
Ta ce "To yanzun kana nufin duk abinda nace kanayi bai zama laifi ba?"
Ya ce "Toh! in kin d'auke shi a matsayin laifin shikenan, idan har laifi nayi maki"
Ya sauko 'kasa ya tsugunna da gwiwoyin shi, ya ce "Na d'auki laifi na da kuma kuskure na, don Allah Suwaiba kiyi ha'kuri, ba zan sake yi ba, amma ina ro'kon ki da ki kawar da hankalin ki a kan mu, ni-da-Hauwau, idan kikayi haka zaki zauna lafiya, ba kiga ita harkar ta kawai takeyi ba, bata damu damu ba? "
Ya mi'ke tsaye tare da kamo hannayen ta ya tada ta tsaye, suka fuskanci juna, ya kafe ta da idanun shi, yana 'kara nazarin fuskar ta, har yanzun ba ta sauko daga irin zafin kishin da take kai ba, yayi mata murmushi
Ya ce "Suwaiba kina so na da yawa fa."
Ta ce "Ai shi yasa kake wahalar dani."
Ya ce "To Daga yau na daina, jeki shirya kiyi wanka ki sanya turare me 'Kamshi, barci zanyi da wuri yau".
Ta yi dariya tare da an she hannayen ta daga nashi, ta juya ta shige d'aki, don tayi wanka.
Shi kuma nan ya zauna bisa kujera yana tunanin irin wannan kishi na Suwaiba, sai dai yana 'kara gode ma Allah da abin ya tsaya a kanshi kawai, duk iya fad'an ta da fitinar ta, ba ta yima Hauwa'u, tsakanin ta da shine kawai.
Yayi dariya, tare da girgiza kai ya ce "Watankan tunda ni nayi mata laifin bari ta huce a kaina ni kad'ai, humf! Suwaiba rigima!"
Lokaci guda kuma ya tuna ranar da Hauwa'un ta samu kwana bakwai a gidan, a wannan ranar itace ranar da za'a raba kwana, ya kuma tuna iyakar abinda ya faru a wannan ranar.
**** **** **** **** **** ***** *****
Bayan ya taso masallacin Sallar isha'i ne, ya nufi d'akin Hauwa'u, ya ce
"Baby kizo ki same mu a falo, zamuyi magana."
Ta ce "To shikenan gani nan zuwa".
Sai ya juya ya koma falo inda Suwaiba take zaune tana jiran su, wuri ya samu ya zauna tare da saurarawa, domin suna jiran fitowar Amaryar shi Hauwa'u.
Lokaci kad'an ta fito, cikin hijabin ta, tare da zaunawa kan d'aya daga cikin kujerun falon, sannan ta kuma gaishe su.
Nasser ne ya fara magana da cewa .
"Al-hamdulillah!sallu alannabiyyul Kareem."
Ya bud'e masu taron da Addu'a, kana ya ci gaba da cewa.
"Kamar yadda Addinin musulunci ya tanadarma ko wad'anne ma'aurata , ya kuma gina rayuwar su a kan tsari, musamman rayuwar aure, yau Hauwa'u ta cika kwana bakwai a gidan Auren ta, kamar kuma yadda yake a hadith
( Idan ka auri budurwa a kan bazawara, zaka kwana da ita tsawon kwana bakwai, sannan ayi rabon kwana.
Idan ka auri bazawara akan budurwa zaka kwana da ita tsawon kwana uku, sannan ayi rabon kwana.)
A matsayi na, na auri Hauwa'u budurwa, kwanakin ta sun cika, a yau ne za'a raba kwana, to amma kuma ra'ayin naku ne, yadda kuka tsara, iya adadin kwanakin da kuke so to sai a tsaya a hakan.
Wannan shine dalilin tara ku, domin jin naku ra'ayin, kwana nawa-nawa kuke ganin za'a raba?"
Suwaiba ta ce "Toh! Yadda dai mafi yawan mutane suka d'auka, muma haka zamu bi, kwana biyu-biyu ko kuma uku-uku."
Nasser ya ce "Hakane, sannan ya maida kallon shi ga Hauwa'u, ya ce "My love bakice komai ba."
Ta d'ago idanunta tare da yimai wani irin fari mai d'aukar hankali, ta ce
"Yo ai Aunty Suwaiba ta gama magana, duk yadda ta yanke d'aya ne."
Tunda take maganar nan hankalin shi na kanta, irin yadda take sarrafa harshen ta cikin wata irin yanga da kissa mai d'aukar hankali, shi kanshi ya rasa abinda yasa komai nata birge shi yakeyi, lokaci d'aya ta tafi da zuciyar shi, ya dad'e yana kallon fuskar ta, sannan daga baya ya numfasa,
ya ce
"Hakane baby na."
Sannan ya juya ga Suwaiba ya ce "Suwaiba kinji abinda ta fad'a, ta ce duk yadda kika yanke yayi, to amma abinda nake so in fahimta, shine kwana biyu-biyun ko uku-ukun?"
Suwaiba ta ce "biyu-biyun sunyi, amma sai-dai inada magana, a matsayi na na mace d'aya, wadda ta shekara Hud'u a wurin mujin ta, koda yaushe muna tare, sai naga ya kamata in 'ka rama ka wad'ansu kwanaki daga cikin kwanakina, domin itama ta sake da mujin ta sosai, kuma a matsayin ka na wanda yayi sabon aure, gaskiya kwana bakwai sunyima kad'an, ace ka gama cin angoncinka, gara in barku ku 'kara sakewa da juna sosai.
Don haka bayan kwanaki bakwai d'in nan da ku kayi, na yarjema, ka 'kara *WATA GUDA A 'DAKIN AMARYAR KA,* wad'an nan kwanaki *TALATIN* d'in kyautar su na baka, aci amarci lafiya."
Falon ya yi shiru na wani lokaci.
Sannan Nasser ya ce "To shikenan Suwaiba na gode , Allah ya had'a min kanku, ya zaunar daku lafiya.
Baby kinji abinda Auntyn ki ta fad'a ko? To don Allah a zauna lafiya, ki bata girman ta da matsayin ta, da take dashi na *UWAR GIDA,* sannan idan kin...............
**** **** **** **** ****** *****
Suwaiba ta ta'ba shi tare da shafa mai ruwan da yake hannunta,cikin dariya tace tunanin me kake ?
Ya ce "Tunanin ki, tunda kika shiga na 'kosa inga fitowar ki, ina nan inata tunanin ki mai masifar dad'i, daya d'auke min hankali na, kinyi kyau sosai, sai 'kamshi kike."
Ya mi'ke tsaye tare da fad'in "Muje, ina so inyi barci da wuri yau, inada aikin da zan fita tunda safe."
Ya shiga gaba tana biye dashi a baya, suka wuce d'akin.
Can cikin dare ya fara, yasa hannu ya laluba, bai ji Suwaiba ba, yayi saurin murje idanun shi ,ya tashi zaune.
Canya hange ta zaune ta sauka daga kan gadon, tanata shar'bar kuka, tayi gaje-gaje.
ya sauko yazo inda take, ya ce "Suwaiba lafiya meke damunki ki?
Tayi saurin share fuskarta tare da cewa "Ba komai."
Ya tsugunna gaban ta sosai, ya ce "Ya zaki cemin ba komai? Hakanan zakita kuka ne? ko wani abu keyi maki ciwo?"
Ta ce "Don Allah kaje kayi barcin ka kawai, niba abinda keyimin ciwo!"
Ya kamo hannunta ya ce "To taso muje ki zauna kan gadon, tambayar ki zanyi."
Ta ce "Ko ka tambayeni babu amsar da zan iya baka".
Ya ce "Naji taso dai muje kiji."
Da kyar ya lallasheta ta taso suka zauna gefen gadon.
sannan ya kalleta ta
tare da 'kara tsaida hankalin shi a kanta, ya ce
"Kishi ko? Wai me yasa kike wahalar da kanki ne akan abinda ba kida maganin shi? Suwaiba inda ace idanna mayar maki da *KWANAKIN KI TALATIN* zamu samu zaman lafiya dake; to inaga da in mayar maki da sud'in kawai shi yafi alkairi."
Ta ce "To ai kaji inda matsalar take, zaka mayar min da kwanaki na ne kawai domin a samu zaman lafiya, ba don soyayya da d'oki na ba, ba kuma don son ran kaba, a'a sai don kawai a samu zaman lafiya, kaga kenan ya sha bam-ban da irin kwanakin da kayi a d'akin ta.
Nasser duk sanda na tuna lokacin dana baka kwanakin nan, ka amshe su cikin d'oki da jin dad'i, har kana yimin godiya; hankali na tashi yake, ko ba komai nasan yadda kake son ta ni baka so na haka, kaga kenan mayar min da kwanakin ma basuda amfani.
Nasser ya za'ayi in daina kuka? Al-halin ni na tabbatar son da kake yi mata ni baka yimin irin shi."
Yayi saurin cewa " Suwaiba waye ya gaya maki haka!? Ina son ki har bansan da wane yare kike so in sanar dake cewa ina son ki ba ki yarda, Suwaiba don Allah ki ba ni izinin in mayar maki da adadin kwanakin ki, ni dai ki daina yimin wannan kukan."
Ta ce "Bana so domin kuwa badon kana so zakayi su ba, sai don ya zame maka dole, ni na san cewa nayi asarar wad'an nan kwanakin har abada!Don haka babu yadda za'ayi ka rabani da kuka."
Ya ce "To kinsan abinda za'ayi? Tashi kiyi Al-wallah kiyi Sallah zai fiye maki wannan yin kukan, da zaman da kikayi kina kuka, dama Sallah kikayi kika samar ma kanki kwanciyar hankali, ki ro'ki Allah ya yayemaki wannan matsalar da take tare dake, tashi muje in raka ki kiyo Al-wallah kinji?"
Ta tashi suka shiga, gaba d'ayan su suka d'auro Al-wallah, sannan sukayi sallar nafila raka'a Hud'u, sukayi addu'o'in su.
Har zata kwanta ya tambaye ta, "Wace Addu'a kikayi? Kuma me kika ro'ka.?"
Ta ce "Na ro'ki Allah ya 'kara sanya maka soyayya ta a cikin zuciyar ka."
Yayi dariya tare da fad'in "Kai! kai!! kaih!!! Suwaiba, duk tarin soyayyar ki da take a cikin zuciya ta so kike a 'kara wata?Idan soyayyar ki tafi yadda take a cikin zuciya ta zata iya fasa ta, domin kuwa soyayyar ki ta riga ta gama mamaye dukkan ilahirin zuciya ta, ina son ki Suwaiba, kuma irin naki son da banne dana kowa, kece mace ta farko dana fara gani kika d'auki hankalina, tun a lokacin kika d'auki mafi yawa daga cikin 'bangaren zuciya ta kika mamaye, don haka ki kwantar da hankalin ki, duk wata mace ta daina baki tsoro, domin dai mujin ki kafin ya ganta ke ya fara gani, kafin ya fara son ta, ke ya fara so, don haka ba soyayyar kice zaki ro'ki Allah ya sanya mini ba, wannan ya riga ya sanya ta, ta kuma zauna cikin ikon shi, abu d'aya ne yake wahalar dake *Kishi,* to shine ya kamata ki ro'ki Allah ya sassauta maki shi, ya rage maki zafin kishin nan, ya sanya maki dangana, kinji Suwaiba ta."
Ya fad'a cikin sigar lallashi.
Ta d'aga kanta alamar E.
Ya ce " To tashi mu kwanta, ki daina damuwa kinji."
Aiko duk yadda ya so ya fita wurin aiki da wuri, saida ya makara, don haka da safe cikin sauri yayi break, yana shiryawa ko sallama baije yayima Hauwau ba ya fita .
Bayan kwana biyu, misalin 'karfe biyar na yamma, ya dawo gida, kai tsaye d'akin Hauwau ya wuce, bayan ya zauna, ta kawo mai Abincin sa tare da fad'in.
"Sannu da dawowa, yau dai naga ka dad'e."
Ya ce "Hakane na dad'e, wani aiki ne ya tsayar dani, mekika dafa min?"
Ta ce "Abinda nasan kafi so, ina so yau kaci abinci sosai."
sannan ta fara zuba mai, yana kallon ta sosai, bayan ta gama ya ce "Sannu da aiki."
Tayi dariya ta ce "Na gode mujina, ina jin dad'in yadda kake yaba min akan komai."
Shidai ya kafe ta da idanu, sannan yace "Zauna ina son zamuyi magana."
Ta zauna tare da fadin, "Amma da ka bari ka gama cin abincin."
Ya ce "A'a ba komai, maganar tanada muhimmanci sosai."
Hauwa'u ina son ki, ina kuma 'kaunar d'orewar zaman lafiya tsakani na dake, da kuma abokiyar zaman ki, to don Allah ki duba darajar soyayyar da ke tsakani na da ke, kiyi min wata al-farma guda d'aya.
Hauwau ba ki san halin da nake ciki ba, ina 'boye maki ne saboda bana son tashin hankalin ki, tabbas!! na lura ke mace ce wadda take farin ciki a lokacin da ta samu mujinta cikin farin ciki, kuma kike 'bacin rai a lokacin da kika ga wata damuwa a idon mujin ki, da yawan maza irin matar da suke so su samu kenan, ni kuma Allah ya azurtani da ita. Hauwau ko kinsan cewa ina cikin tashin hankalin daya hanani walwala? sai dai inaga da taimakon ki za'a samu sau'kin shi, koma maganceshi baki d'aya, Hauwa'u , Suwaiba ta tada mani hankali, idan na shiga d'akin ta, babu abinda take yimin sai aikin kuka, ni kuma bana son inga tana kuka, ta tada hankalinta duk iya yadda baki zato, nima kuma ta tadamin nawa hankalin, kuma duk hakan baya rasa nasaba da *KWANAKIN NAN TALATIN DATA BAMU NA AMARCI, shine daga baya take danasani, ta kuma kasa ha'kura ta dangana ."
Dai-dai nan ya sauko daga kan kujerar, ya dur'kusa gabanta, ya ce
"Hauwa'u ki taimaka ki bani *KWANAKINKI TALATIN* in mayar mata, kona samu zaman lafiya, don Allah Hauwau."
Humff!! Tayi ajiyar numfashi, ta ce "Babu abinda zaka nema a wurina ka rasa, babu wani taimako da zaka nema a wurina banyi maka shi ba, zan iya baka duk wani abu dana mallaka a rayuwa ta, indai baifi 'karfi na ba,*AMMA BANDA KWANAN AURE NA!!*
Bari in 'kara jaddada maka Nasser!wad'an nan kwanaki *TALATIN* tayi asararsu har Abada!bazan iya bata suba!kuka kuma taitayi! Duk ranar data gaji ko kuma ruwan jikin ta ya 'kare saita bari! kada ka 'kara yin tunanin
cewar don ka mayar mata da wad'annan kwanakin za'a samu zaman lafiya, ka d'auka tamkar ka 'kara bankad'o wani tashin hankali ne a cikin gidan ka! Kuma koda wasa kada ka 'kara kawo mani wannan zancen! Dai-dai da kwana na d'aya bazan iya bata ba!! Ku 'karata can kai da ita! In kunga dama ku kwana kuna kuka tare, ni ina nan ina barci na!!! "
Ya ce " Amma kuma.......... "
Ta ce "Kaga dakata Naseer! Inna samma wannan maganar ce tasa ka tsaida ni wallahi bazan saurare ka ba, kuma wannan maganar na kashe ta daga yau! Duk ranar daka 'kara kawo min ita zanyi fito-na-fito da Suwaiba! Domin bata isa ta hargitsa min rayuwar aure na ba! Shikenan ta tada maka hankalin da zaka kasa sakewa dani ko? To ka barni da ita ni zan iya yi maka maganin ta! "
Yayi saurin cewa " A'a bana son irin wannan Hauwa'u, tunda muke rigimar mu da ita kin taba jin ta sako ki a ciki? Tsakani na da ita ne kawai, ban taba jin tace ga abinda kikayi mata ba, don haka bana son rigimar nan ta koma tsakanin ke da ita, maganar ma ni a barta."
Ta ce " Ah toh! Ai gara inyi maganin abin tunda wuri, don karka d'auka cewama ko wata rana zan yarda. "
Ya sa hannu ya ture abincin data zuba mai, cikin fushi ya tashi ya bar d'akin.
Ta ce "Haka kawai! Mata ta tada maka hankali don in ka dawo d'aki na ka kasa sakewa! Don neman ta had'ani da kai, nasan maganin ta, 'kila nima saina fito na nuna mata inada 'yanci, kuma gidan muji na ne!"
Haka taita fad'a ita kadai tana tattara kayan Abincin data ajiye.
" Wannan ma ai mugun abu ne! Gashi ko abincin ma tasa ya kasa ci, to dani take magana.
Bai dawo gida ba sai misalin 'karfe goma na dare, tana zaune tana jiran shi, sannan sai gashi ya shigo, babu dai wata fara'a a tare da shi, wuri ya samu ya zauna tare da ce mata
"Had'o min ruwan zafi zansha."
Ta tashi ta had'a mai, ta kawo mai, sannan ta zauna daf! Dashi, ta ce "Yau shine abincin naka? Naga ko da rana baka ci abinci ba, yanzun kuma ka dawo banga alamar zaka ci ba."
Ya ce "Shi kad'ai zan iya sha yanzun."
Ta ta'be bakin ta tare da fad'in "To ai shikenan."
Tasa hannu zata zuba mai, ya tare ta, ya ce "Bash shi kawai zan hada."
Ta cire hannun ta ta rabu dashi, ya gama iyakar fushin da yake da ita, bata 'kara yi mashi magana ba har ya gama sha, sannan ba tare da yace komai ba ya tashi ya shigewar shi d'aki.
Ta kau bishi da kallo, ta ce "Yau naga ikon Allah, wannan fushi kuma na menene?"
Ta tashi ta kawar da kayan Tea d'in daya gama sha, sannan ta shiga d'akin.
Kwance ta same shi, yana shirin yin barci, ta ta'ba wuyan shi ta ce "Love bakada lafiya ne?"
Yayi banza da ita ya juya mata baya, ta zauna gefen gadon ta ce "Me kake nufi?"
Ya ce "Hauwa'u ki rabu dani, tunda har inada wata Al-farma da zannema a wurin ki, ki kasa yimin, to gaba dayan ku zan tattara ku in 'kyale ku, randa kuka dai-dai ta kanku aci gaba da zaman auren."
"Wai Naseer kana nufin In d'auki kwanakina in baka? Har don nace bazan bayar ba kake fushi! To shikenan na yarda, amma saidai inka amince in tafi gidan mu, inyi wata guda acan, lokacin daka gama kwanakin a d'akin ta saika dawo dani."
Ya tashi zaune tare da cewa "ita gidan su ta tafi lokacin data baki nata kwanakin?
Wata hanya ce dai kawai zaki 'bullo min da ita don ki bani wahala, kuma kinsan abinda ba zai yuwuba kenan........