HASASHEN SOYAYYA

Hs 17

by @legendspen

_Page 17_

*Bayan kwana biyu*

~~~~Red bricks

"Tom yanzu Hajiya daga ganin yarinya sai ku yankw hukuncin gidan da ta fito?." Dad dake zaune kan kujera ya faɗa yana kallon Mom dake yan ka masa fruit. "Yarinyar fa ƙanwar matar barrister ce, kuma kasan matar barrister ai." 

"Duk da haka fa Hajiya, kawai dan dai kina son yarinyar ne shi yasa haka."

"Tabbas kam, yarinyar ta na da shiga rai kuma ɗan lalena ne ya kawo ta." Dariya Dad ya yi sanan ya ce. "Shikenan zan sa a yi binciken da ya ka ma ta."

"Amma fa ni cikin ƙan-ƙanin lokaci nake so ayi komai a gama." Mom ta faɗa sabida ta fuskanci kamar bai shirya aurar da Senate ba, wata dariyar ya sake yi saman ya ce. "Komai saurin ki dai, sai kin jira lokaci ko?."

"Eeyh!." Ta faɗa kawai tare da ci gaba da haɗa masa fruit ɗin. Senate ne ya fito cikin shiri, ya sha ado cikin milk clour na shadda wacca ta yi matuƙar amsar jikinsa, fuskarsa mai kama da ta larabawa ta fio fes cikin browm clour ɗin hulal da ya saka, tsintsiyar hannunsa ɗaure da golden clour Rolex watch, turaren jikinshi ya ƙarade gidan baki ɗaya, a hankali ya tako zuwa falon.

Da kallon soyayya Mom ta bi shi, a ranta tana yi masa addu'ar kariya da neman sa'a an kan komai. "Dad barka da hutawa."

"Barka dai Amgo, sai ina?." Murmushi ya yi, tare da yin ƙasa da kan sa. "Zanje dinner ne." 

"Tom Allah ya tsare."
"Amin Dad." Ya faɗa tare da miƙewa xuwa inda Mom take, bai ƙarasa ba Dad ya ce. "Akwai kuɗi a wajen ka ko?." 

"Eyh Dad akwai." Gyaɗa kai Dad ya yi, ya ci gaba da shan fruit ɗin sa, shi kuma ya ƙarasa inda Mom take.

"Mom zan huce." shafa kan shi ta yi sanan ta ce. "Allah yatsare, a kula mun da Bhatool." 
"In sha Allah Mom." Daga haka ya fice, motarshi ya hau ya nufi address ɗin da ta ba shi na wajen kwalliya.



~~~~~~Bhatool.

"Amrah, banga gold ɗina ba." Bhatool ta faɗa tana bincike jakarta. "Innullahi wa'inna illahir raji'un, Bhatool sake dubawa dai." Amrah ra faɗa ana ci gaba da mata kwalliayar. "Wallahi Amrah banganshi ba; Allah yasa gida na bar shi." 

"Amin dai kam." Amrah ta faɗa dai-dai lokacin sa Jannah ta shigo,wacce daman angama yi mata ta kwalliyar ita da Bhatool. "Suhaima ke ce mun wai sun kusa ƙarasawa." jannah da ta shigo ta faɗa. "Chaii, Amrah ayi a gama miki ɗaurin nan." 

"Bhatool ya baki sa ɗan kunne ba?." Jannah ra tambaye Bhatool. "Na bar shi gida wallahi." 

"Ya salam!, yansu ya za'ayi?."

"Ɗaurin na wa za a sakko mun da shi har kunne."

"Eyh kam hakan zai yi ma." Mai kwalliayar ta faɗa bayan ta gama yiwa Amrah ɗauri, dai-dai lokacin da kiran Senate ya shigo wayar Bhatool. "Laa kunga yazo." 

"Waye?." Amrah ta tambayeta. "Senate." Ta bata amsa. "To mu yi sauri kar mu ɓata mai lokaci, kun san manyan mutane ba sa son jira." Amrah ta faɗa tana haɗe kayanta. "To ko mu fara fita ne." Amrah dan ta ƙara faɗa. "Ke matsalata da ke hutar ciki." Jannah ta bawa Amrah amsa. "Duk hutar cikin ta dai nima angama mun." Bhatool ta faɗa tana sauka daga kujerar kwalliyan, daga nan suka ka ɗai su ka fice. 

Haka kwai Senate ya ji kwalliyar Bhatool ta yi yawa, gaba ɗaya ya ji shi wani kala duk ya damu, "Dama ba ta yi ba." Ya faɗa a zuciyarsa, a fili kuma ya sakar ma ta murmushi. "Ina yini." Amrah ta faɗa tare da Jannah. "Lafiya kalau, ya taro?." 

"Taro gashi ana ta sha, ya gajiyar jiya?."Amrah ta ba shi amsa, ita dai Jannah tana ƙoƙarin shiga mota. "Alhmdlh." Ya faɗa a daƙile tare da shigewa mota, su ka huce hall ɗin.

Ko a hall ɗin Senate ya hana Bhatool sakewa, ko ina suna tare yana binta a baya, yan maza na ta kallonta haka shima yan mata na ta kallonsa, zallan kishi kawau ke ɗawainiya da shi, ya yu kicin-kicin ya haɗe rai, Bhatool kam da ta fuskancin haka sai ta yi banza da shi, ko ina ya yi ta bin na ta. 



~~~~~~Hausari


"Toh Isiyaku bari ka ji mun isa har mun yi yawa mu aurar da 'ya'yan Ahmad, ko da ran Ahmad ko babu ran sa; domin ni ce babba cikin ku." Goggo larai da ke zaune kan kujera yar tsugunno ta faɗa, kawu Isiyaku ne ya ce. "To ai Larai wanan zancen banza ne zancen wofi, idan ba mu aurar da ita ga na gida ba wa zamu bawa? duk lalacewa Saddiku ɗan mu ne, kuma shi da kan sa ya ce idan an aurar mai Bhatool yar gidan Yaya Ahmad zai nutsu, zai daina shaye-shaye, da wanan yawon tafiya legas ɗin." 

"To ko ba zai daina ba tun da ya ce yana son aurenta ai sai an ba shi;dan haka na gama magana, kawai ku haɗa kayan nagani ina so ku kaiwa uwarta." Goggo larai ta faɗa tare da mikewa tana dafa bango.

Furai ce ta kalli Habi su ka kwashe da wata shegiyar dariya, sanan Habi ta ce. "Ina baƙin cikin ganin su Bhatool sun ci gaba." 

"Wallahi Habi nima haka, ke da ina da dama Karimar ma sai na kaso na ta auren." 

"Bari muje fa Bhatool gidan Yaya Sadik, ita ma sai ta fito." 

"Ai wallahi nasan da zarar an aurar da Bhatool ga Yaya Sadik, ta ta taƙare, sai ta hulaƙanta ta sha wahala, ta gane Allah ɗaya ne." Dariyar su ka ƙara fashwewa da ita.




~~~~~Senate & Bhatool.

"Wai bazaka zauna ka ci Abinci ba?." Bhatool ta faɗa, dan ta fara gajiya da wanan bin bayanta da Senate ke yi. "Naƙoshi." Ya faɗa murya kamar zai yi kuka, kujera ta samu ta zauna shima ya zauna kusa da ita, sanan ta ce. "Senate mene matsalal wai?." Turo baki ya yi gaba sanan ya ce. "Duk kin yi wani kyau, yan mazan sai kallonki su ke." 

"To ai kai ma ka yi kyau ko?; kuma 'yan mata sai kallonka suke."

"Mu ta fi gida." 

Legendspen
***