Dokin ƙarfe

Page 2

by @fatimakabir588

‎Zainab ta share mata hawayen da takeyi sannan ta lallashe ta kuma ta jaddada mata cewa lallai kar ta damu baba shi zai zame mata matsayin uba wanda takeh san sa albarkar shi, Zahra ta dauki shawarar ta sosai daga nan kuma suka fara wani zancen,sai wurin karfe tara zahra ta tafi don tasan yanzu uncle A ya isa dawowa,a hankali take tafiya har ta iso cikin part din su,har zata wuce tajii muryar uncle A yaceh Fatima daga ina kike, uncle daga wurin zainab,kika yo mii, gurin zainab koh gurin wancen matsiyacin watch man din.jin zagin da yayima baba yasa ranta yayi masifar baci koba kimai ai mahaifin bestyn tane a harzike taceh uncle wai me wannan mutumin yayi maka ne dan Allah,dakai da shi baku da wani banbanchi a gurin ubangiji wllh duk daya kuke, uncle idan yanzu ka mutu cikin farin yadi za'a nade ka sannan kuma a saka cikin kasa kamar yadda za'a yi ma wancen wanda ka kira da matsiyaci ba dadin jii,kuma wllh daddy (haka duk wani da' dake cikin family yake kiran shi) kana da tabbacin cewa da dukiyar ka zaka ray........tass.. kakeji,wani irin wawan mari ya kafa mata wanda yake waje ma saida yaji,dai -dai lokacin da yaya mas'ud ya ajiye mota a parking lot 
‎Ya fito yana nufo main parlour din na part dinsu ya jiyo karar marin, a gigice ya shigo dai dai lokacin da daddy yake safke hannu shi daga fuskar ta,yana fadin Fatima wato wuyanki ya isa yanka yanzu ni kike kallon idona kike fadama san ranki sbd tsabar rashin kunya,shikin shashekar kuka ta chigaba da fadin: wllh daddy ko yanzu ka zagi baba musa saina fada maka rashin dacewar hakan,kuma daddy kasani ita duniya fararra ce kuma karewa takeyi amma ita ranar lahira itace ranar tonan asiri ranar da kowa zai tsaya a kotun da babu lawyer sannan kuma babu dukiya kuma babu wanda zaka ce ma ga kudi ya baka abunda kake so Allah kana gani ka fidda ma duk wanda aka zalunta hakkinsa. Ke... Jin anrike hannunsa ta baya yasa ya jinkirta da fadin abunda yayi niyya,a fusace ya jiyo dan ganin wane marar kunyar ne,ido hudu sukayi da yaya mas'ud sannan ya juya ya kara kallon Fatima da take kuka babu kakkautawa, cikin bacin rai da zafin rai yaya mas'ud ya fara mgn, waikai wane irin mutum ne mai san kanshi wanda baya la'akari da halin da wasu suke ciki sai naka,shi wanda kake zagi ai baima san kanayi bah kuma wllh bari kaji abunda baka sani ba ita Gakiya dokin ƙarfe ce kuma Allah ba azzalumin kowa bane kuma baya hukunci da zalunci baya tauye hakki a ko yaushe ka rinka tuna wannan sannan ita duniya budurwar wawa wanda baizo ba ma jiranshi takeh, mtswwww ya kama hannun zahra har zasu wuce suka tsinkayo muryar shi yana fadin:kuma wllh auren Fatima babu fashi sai anyi shi ko kuna so ko bakwa so sai anyi shi😠
‎Oho dai Allah yasa haka shine alkairi yaya mas'ud ya fada yana shigewa ta hanyar part din yaran gidan,sai da ya kai zahra har dakin ta sannan ya juya ya koma nashi part din.
‎.....................
‎Washe gari da safe bayan sun gama breakfast uncle A ya keh sanar da fatima cewa ta zama cikin shiri yau basai an kwana ba wanda zai aura ma ita zai zo su gana,ba musu ta amsa da toh,daki ta shiga ta fada toilet wanka tayo tare da turarirrikan wanka wanda ta saba amfani dasu sannan ta fito lotion din ta tashafa mai dadin kamshi wanda ko bata sa turare ba kamshin shi kadai ya isa,colecture ta shafa a duk illahirin jikin ta sannan ta shafa madarar turare mai mix sai kamshin ya hadu ya bada wani irin daddadan kamshi, Fatima tun tana karama yarinya ceh mai mutukar san kamshi,bayan ta kammala shafar,clotheset ta shiga ta sako wata atampa mix and match mai navy blue da sky blue riga da straight sket ce sai tayi masifar kyau dama gata fara, irin matan nan ne masu silver& oily skin dan ko bata shafa mai ba ba'a ganewa,gata irin matan nan da Allah yayi ma baiwara tsayi hadi da fadi sannan ga diri,jikin nan ta yana ta faman glowing kamar kankara,bata daura kallabin kayan ba sai tayi rolling din gele sky blue sai tayi wani irin kyau baza ka taba cewa itace bah flat shoe blue feshe jikin ta tayi perfume kala uku ba masu karfi bah tana kama handle din kofar zata fita sai ga zainab ta shigo. Besty yazo faj ke ake jira, awwwwn wannan irin kyau haka besty karfa kisa ya kasa maida kanshi gida 😂ita dai Zahra murmushi kawai ta iya yimata don ita kadai tasan abunda takeji a zuciyar ta ga wata iriyar fargaba dake ziyartarta tunda uncle A yaceh da ita wanda suka zaba mata yana nan zuwa su gana,cikin kamilalliyar murya mai ciki da amoh ta shiga dakin bakin da sallama kamar yadda kawarta ce ta rako ta shima haka tare yake abokin sa......
‎Ina wunin ku zahra ta fada cikin ladabi 
‎Lafiya......matashin saurayin dake zaune akan kujera yayi kafa daya bisa daya yana dannar waya Samsung Galaxy S10 sanye yake da brown din suit ta salim fit suit kafarsa sanye da leather shoe black color ga Rolex makale a hannunsa ya amsa ta gefen ido ta dan saci kallom sa ba laifi gayen ya hadu ita sai take ganin kamar tasan fuskar bata gama tunanin inda tasan fuskar ba ta sinkayi muryar sa yana fadin sunana UMAR FAROOQ HASHIM 😎