GABA TA ZO BAYA

Chapter 1

by @khairatup01

GABA TAZO BAYA
Ummulkhair S Panisau 
(Khairatup)

001

"Don Allah ki sake bani dama na zamo mijinki a karo na biyu Nihila Wallahi na gane kurena,zan gyara abinda na ɓata."
Wani irin kallo na jefa masa irin kallon anya kuwa kana cikin hayyacin ka kuwa. Ban kai ga cewa komai ba ya sake tare mini numfashi.
"Ki tuna tun bamu gama sanin rayuwa ba muke tare kina ganin za ki iya rayuwa ba tare da ni ba?"
A wannan gaɓar na saki wani irin murmushin taƙaici na juya kamar zan tafi sai na kuma juyowa na kalle shi ido cikin ido.
"Wallahi Abdullahi baka da kunya." 
Yadda ya zaro idanunsa waje ne ya saka na gane cewa mamakin abinda na faɗa yake yi. Don na ba shi tabbaci na sake ce masa "Nace baka da kunya Abdullahi,kai yanzu ka yi wa kan ka adalci ba ma ni ba? Wai na tuna zaman mu to me kake so na tuna a zaman namu? Ne zan tsinta banda kayan takaici da baƙinciki ? Kar ka sake zuwa ƙofar gidanmu ka ce wai kana son na saurare ka don ka riga da ka ɓarar da soyayyar ka."
Ban yi aune ba kawai na ga ya yi ƙasa da guiwowinsa biyu ya haɗe hannayensa biyu a wuri guda kamar zai yi kuka yace "Nihal ki yafe min ki tuna da soyayyarmu....."
"Wallahi Allah Abdullahi ba zan yafe maka ba." Na faɗa hawaye sun ciciko min a idanuna.
Daidai lokacin motarsa ta danno cikin harabar gidanmu gabana ya faɗi don ban san zai zo ba ko da yake shi haka yake duk sanda ta raya mai sai na gan shi wataƙila ma ya kira ni ban ɗauka ba don wayar tana cikin gida. A hankali ya faka motar a inda ya saba sai dai bai fito ba na tsawon mintuna. Na juya na kalli Abdullahi da ke tsugunne cikin faɗa-faɗa nace "Ka tashi don Allah ka tafi bana son ganin ka Wallahi kallon kaɗai na fama min wasu ciwukan waɗanda na yi ƙoƙari na bar su a gidan ka don Allah ka shafa min lafiya babu wani abu da ya rage a tsaknina da kai."
"Saboda wancan mutumin ne kike wulaƙanta soyayya ta ko? To Wallahi ba za ki aure shi ba dole sai kin koma gidana."
Na saki baki ina kallon ikon Allah duk da hankalina ya kasu gida biyu ina jin a jikina yana kallon mu ne kuma ya cika ya yi fam ƙiris kawai yake jira ya fashe.
Murfin motar aka buɗe cikin sakan biyu ya fito daga ciki. Cikin kyakyawan shiga mai ɗaukar hankali idanunsa akwai baƙin space ba ka iya ganin ainihin idanunsa.
Yadda ya tsaya kawai zai nuna maka yana ciki ne. Dabi'arsa ce ya rungume hannu a ƙirji sai ya jingina da jikin motarsa yana kallon agogo. Sai a lokacin ma nake ganin rashin hankalina ma da tun shigowarsa ban je ba har sai da ya fito yanzu me zan ce masa na kare kaina? Bayan ya gaya min baya son ya dinga ganina da Abdullahi.
Miƙewa Abdullahi ya yi tsaye ya juya ya kalle shi. 
Cikin takun da bai wuce biyar ba ya iso gabanmu kamar walƙiya yayi mana sallama.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaikum Salam." Muka masa a tare.
Ya miƙawa Abdullahi hannu suka gaisa kowa ta ciki na ciki.
"In ba damuwa ina son ka bani aron matata." Ya faɗa da wani guntun murmushi a kan fuskarsa.
Abdullahi yace "Matar ka ko matata?"
Hannu ya zura cikin aljihun wandonsa ya zare gilas ɗin fuskarsa yace "Baka san jiya an ɗaura mana aure ba? Saboda haka matata kake magana da ita a halin yanzu ba tare da izinina ba na san ka san hukuncin hakan a musulunci , ko da yake ba laifin ka ba ne laifin ta ne da ta fito wurin ka."
Kaina a ƙasa na kasa haɗa idanu da shi amma ina jin kaifin idanunsa a kaina.
Abdullahi yace "Innallillhi wa inna illahi rajii'un." A lokaci guda ya dafe kai ya juya ya kasa cewa komai yana haɗa hanya ya yi hanyar waje amma baya ganin gabansa sosai.
"Yallaɓai zan iya yi maka bayani."
Sai da yayi wannan murmushin nasa sannan yace "Ki yarda ba za ki iya ba." Yana kaiwa nan ya juya da sauri ya nufi motarsa kamar an dasa ni na kasa tsaida shi har ya shiga ciki yayi reverse ya fita daga gate ɗin gidan ban motsa daga inda nake ba. Da gaske na ɓata masa rai kenan. Tambayar da na yiwa kaina kenan.
A saluɓe na ja nauyayun ƙafafuna na shiga cikin gida gabana faɗuwa kawai yake yi duk da ba wai ina jinsa a raina sosai ba ne sai dai ban ji daɗi da ya gan ni da Abdullahi ba.
Muryar Mama na ji tana tambayata.
"Tunanin me kike yi ne?"
"Na'am Mama?"
Sai ta kalle ni ta ce sani "Zo nan ? Ba dai wani abin ya miki ba?"
Nayi saurin girgiza kaina da sauri sai dai hawayen da suka sauko min a kumatu ne suka rusa ƙarfin halin da nake ta ƙoƙarin dannewa.
Mama ta tashi ta kama hannuna tayi cikin falonta dani babu kowa a falon.
Na kuma kallon falon cike da jerin akwatunan lefena da aka kawo min a karo na biyu. Na sa bayan hannuna na share hawayena.
"Wani abin yayi miki ne?"
"A'a bai min komai ba."
"To mene ne? Kin fa san ba a son kina shiga ɓacin rai kar ki sake tsugunnar damu Nihal."
"Ba komai Dr ne ya zo."
"Kuma ya ga Abdullahi?"
"Eh."
"Yanzu yana ina Daktan?"
"Ya tafi."
"Ya tafi bai tsaya ba."
"Kai wannan abu beyi daɗi ba ki kira shi to a waya."
Na girgiza mata kaina "Ba zai ɗaga ba."
"Ko ni na kira shi?"
"A'a ki kyale shi."
"Kai wannan yaro baya kyautawa sai ya yi kamar ya haƙura sai ya dawo Allah dai ya sanyayya wannan rigima.laifina ne da nace kije yanzu ko Alhaji ya ji wannan abin ai na kaɗe har ganye na."
"Ba zai gaya masa ba. Bari na shiga na kwanta kaina ciwo yake yi mini."
"To shi kenan ki sha magani zan saka Abula ta dama miki furar akwai ragowar a fridge."
Ban ce mata komai ba na miƙe na shige cikin uwarɗaka. Da wayata na fara cin karo a kan gado na ɗauko na duba na ga kiran Dr sau biyar kuwa a fili nace "Turƙashi lallai dole ya yi fushi."
Na shafa screen ɗin wayar na maida ta na ajiye hijab ɗin jikina na zare na cire hulata gashina ya zubo ya kwanta a bayana. Babu wuta sai na tashi na buɗe tagar ɗakin don ba a kunna mana solar ba.
Wata zuciyar na gaya min na kira Dr tunda ni na masa laifi sai dai ɓangaren taurin kai da kfiyata ya saka na ƙi kiran nasa. Kawai sai na bude wardrope na ɗauko riga mara hannu na saka na bi lafiyar gado.
*
Ji yayi kamar zuciyarsa tayi bindiga hayaƙi ya ji kansa yana yi mai kawai.
Tsaki kuwa ya jerasu sun fi a ƙirga kawai hoton Nihal yake hangowa da wancan wawan a tsugunne. Ya daki sitiyrin motar.
"Uban me yake ce mata da zai tsugunna mata waye ya ba shi damar kula masa mata ma?" Tambayar da ba shi da amsar ta.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya isa asibitin. Ƙawarta ce ta addabe shi haka ya saka ya tashi ya tafi don ya gan ta ga tarin aiki d ya bari amma haka ya tsallake su ya tafi kuma sai ya yi kyakyawan gani.
Kamar ya fasa ihu haka yake ji amma babu halin yin hakan.Yatsan sa ya saka a baki ya soma raine farcensa wannan wata ɗabi'a ce ta shi da yake yi idan yana cikin ɓacin rai.
Ya zaro wayarsa ya duba ko ta kira shi ko ta ajiye mai saƙon ban haƙuri amma ina bai ga komai ba, ya san dama ba zata yi masa ba. Ya ƙudurta shi ma ba zai kirata ba har sai ta neme shi saboda shi ta yiwa laifi baya jin ma zai iya bari ayi tariyar nan da sati biyu hankalinsa ba zai taɓa kwantawa ba yadda ya san labarin soyayyar Abdullahi da Nihal zai iya hure mata kunne ta koma masa duk da faman da suka sha kan ta dawo daidai. Cukurkuɗaɗen gashin kansa ya shafa da sauri kamar yana son ya kamo wani abu a cikin gashin nan ko tsabar kishi ne ke cin sa a jikinsa.
Ya rasa irin son da yake yiwa Nihal tunda ta shiga cikin rayuwarsa ya kasa komawa asalinsa. Ko Hidaya da suka yi shekara goma sha ɗaya da aure bai taɓa jin irin wannan feelings ɗin a kan ta ba sai a kan Nihal abu kamar asiri daga patient ta maida shi mara lafiyan ƙarfi da yaji.
"Dr.Azlan." aka kira shi. Juyawa ya yi da sauri. 
"Dr.Shattema." ya miƙa masa hannu suka gaisa.
"Na zo ai ɗazu ban gan ka ba ashe baka nan ma?"
"Wallahi na ɗan fita wani uzuri ne ya akai?"
"Ka manta da wannan mara lafiyar da nace maka ina son ka duba ta?"
Ya dafa goshinsa yace"Oh! Na sha'afa Dr. Tana ina?"
"Tana ofis ɗina bari na turo maka ita."
"To sai ta zo."
Ya ja ƙafafunsa da suka yi masa nauyi kamar dutse ya shiga ciki. Ƙananun kaya ne a jikinsa wandon irin me kamawar nan ne sai rigar mai longsleeve agogon hannunsa Gucci ne haka ma takalmin ƙafarsa.
Ofis ɗinsa ya buɗe ya shiga wani ƙamshi ya doki hancinsa da hotonsa da na Hidaya ya ci karo a kan teburin da ɗan ƙaramin frame size picture haka suna kallon juna suna dariya hannunsa ya kewaye bayanta dimple ɗinsa ya shiga ciki sosai hoton dai ya yi matuƙar kyau kamar su suka yi kansu cike da zallar farinciki.
Yana zama aka yi knocking matar ta shigo ciki bayan ya mata izinin shiga ciki.
Nihila tana zaune a tsakar gida tana yankan allayahu. Uwani ta shigo tace da Mama "Maman Jamilu akwai baki fa a waje."
Ta kalle ta tace "Kuma kika bar su a wajen ? Ki ce su shigo mana."
Nihila bata daina yankan allayahu ba saboda maganar bata shafe ta ba. 
Wani irin ƙamshi ne ya fara yin sallama a tsakar gidan kafin takun takalmi irin mai tsinin nan ƙwas-ƙwas dalilin da ya saka Nihila ɗaga kai ma kenan don ganin su waye wannan suka zo.
Kyakkyawar mace ce mai matsakaicin shekaru fara tas sai dai fuskarta a ɗaure kamar ta shanu a bayanta mata biyu ne suma kyawawa da su. 
Mama tace "Bismilla sannunku da zuwa."
Ɗayar ta ɗagawa Mama hannu tana yatsina fuska tace "Dakata Hajiya ba wurin ki muka zo ba wurin yar ki muka zo."
Sai dai kafin Mama ta bada amsa ɗayar ta dinga bin gidan da kallo tana yatsina baki sai kuma ta ja tsaki tace "Wallahi ya ji kunya dai shi kam."
"Kun yi shiru nace wace ce ke?
"Sunana Feenat ni ce matar Dr.Azlan da yar ki ta aura ba tare da amincewata ba."
Sai da gaban Nihila ya buga da ƙarfi ta ajiye wuƙar da ganyen hannunta. 
Mama tace "Matar Azlan ce?"
"Eh,ita ce uwargidansa."
Nihila ta ji duniyar ta tsaya mata cak tunanin da ya fara faɗo mata shi ne kar dai abin jiya ne ya dawo mata yau?
Mama tace "To maraba da ke ku shigo ciki ai ba ayi ta tsayuwa ba."
Sai da ta ja wani dogon tsaki sannan tace "Ba zama na zo yi ba na zo na sanar muku da cewa Azlan mijina ne ni kaɗai babu hurumin wata a rayuwarmu, kar ku sake ku bari ƙafafun yar ku ya taka gidana da sunan kishiya don kuwa zata gwammaci kiɗa da rawa."
Mama tace"Subahanallahi! Abin duk bai kai haka ba Nafisa. Kuyi haƙuri dai ku zo ku zauna."
Nihila ta miƙe tsaye da nufin barin wurin. Nafisa tace "ke ce kike shirin ƙwace min miji kenan?"
Nihila ta daure ta juyo tace mata "Ba ƙwace miki miji zanyi ba auren ki ya yi aurena ya yi. Dukanmu sunan mu matan Azlan."
Nafisa ta daka mata wani irin tsara "Dr.Azlan mijina ne ni kaɗai shekarun mu goma da aure akan me zai aure ki kamar bani da rai?"
"A'a baiwar Allah ki yi a hankali, ba yadda za ayi ki zo har cikin gidana ki ce za ki ci min mutuncin ɗiyata a gabana ki juya yadda kika shigo ki kama hanya ki tafi don ina guje miki ɓattaciyya."
"Har wannan gida ne? Ke ce gida a wurin ki kuma kece take ɗiya a wurin ki amma ni a wurina da ita da bola ɗaya suke Wallahi."
Mama ta ji wani ɗau a kanta ta rasa kuma ne zata ce.
Nafisa ta cigaba "Ko an gaya muku wadda ta auri mijin wata tana da mutunci ne a idon duniya sunan ta dai second wife. An gaya muku bamu san yar taku ragowar wani bace shi ma ya gaji da mugun halinta ya saki shi ne kuka rasa wa zaku ɗorawa sai mijina. To kun yi ƙarya."
"Haba Nafisa, bai kamata ki zo har gidanmu ki dinga wannan abun ba ina ganin Dr ya kamata ki yiwa ba ni ba, ai ko da ya auri ne a sauran wanin bani na kai masa tallan kaina ba shi ya dage har ya samu ya aure ni ba ni ce na ce zan aure shi ba."
"Azlan ba zai taɓa son ki ba kuma baki isa ba raba mijina da ke ba ina son na karanta miki wannan karatun kar ki sake ki ce za ki shigo min gida don daga ranar da kika shigo min gida daga ranar za ki yi bankwana da farin ciki da kwanciyar hankali, tashin hankali zaki yi ta karo da su iri-iri a hanya don Wallahi sai ki bar min mijina."
Nihila dai ta kasa ce mata komai kawai ta sa mata idanu ko a da bata da hayaniya bata iya faɗa ba watakila shi yasa ta sha wuya a gidansu Abdullahi bata da zafi sam-sam. Tuni hawaye sun soma zubo mata tare da shiga tashin hankali a karo na biyu a maimakon cigaba da take hangowa kanta sai ta ga ashe ma tsugunne bata ƙare mata ba wani sabon babi zata kuma shiga anya kuwa ma bata yi gangancin auren Dr ba kuwa?
Haka suka zauna jigum a falo miyar da bata iya yi ba kenan.
Uwani ce ta ƙarasa tuwon tayi miyar.
Haka Abba ya dawo da Jamilu da Shu'aibu suka dawo daga kasuwa suka same su a zaune jigum.
"Salamu alaikum."
"Wa'alaikum Salam,sannu da zuwa Alhaji." Mama ta faɗa.
Bai amsa mata ba yace "Lafiya na gan ku haka , wani abin ya faru ne?"
Nihila ta saki kukan da take ya ƙoƙarin dannewa kar su zubo.
Ya shiga tashin hankali yace "Subahanallahi! Nihila yaya aka yi me ya faru ne wai?"
Mama tace "Hmm! Wallahi abin ne babu daɗi Alhaji, ai ɗazu muka yi baƙuwa ashe abiyar zaman ta ce ta zo ta yi mana tijara a gidan nan."
Alhaji yace "Ban gane ba wace ce haka?"
"Matar Dr mana."
Nihila tace "Don Allah Abba ka raba auren nan ba zan iya ba, zuciyata ta riga da ta gama yin sanyi ba zan iya hayaniya ba Abba matar nan masifaffiya ce kar a maimaita baya ku rufa min asiri ku rabani da shi."
Abba ya ja numfashi sai kuma ya ajiye ledar hannunsa ya zaro wayarsa daga cikin aljihun wandonsa.
"karɓi Jamilu kira min Dakta yanzu ya zo ya same ni a gida."
"Tam Abba."
***

Azlan ya gama duba patients dinsa na ranar shirin tafiya gida yake yi ma sai kiran Aunty Binta ya shigo masa. Ya koma ya zauna kamar yana ganinta ya gaishe ta cikin ladabi.
"Aunty Mama Barka da yanzun."
"Rufe min bakin ka a nan. Abinda ka aikata mun samu labari sai dai ina mai tabbatar maka da cewa sai dai ka zaɓa ko ita ko Nafisat."
Ya san dama za a buga sai dai a shirye yake tsab don nuna musu yanzu ya shirya ɗaukar duk wani wulaƙanci ya daina tsoro suna ɓata masa aure dole ya nuna musu shi namiji ne.
"Aunty Mama ina neman afuwarki amma a cikinsu babu wacce zan zaɓa duka ina son su kuma na shirya tunkarar kowanne ƙalubale a kan wannan auren."
"Ka ce min haka mana fitsararre mara kunya ba da kai zanyi ba ma yaro da uwarka zan yi."
Sai da ya rintse idanunsa jin yadda ta zagi Amminsa sai dai bai isa ya tanka ba tare ya gansu uwa ɗaya uba ɗaya shi waye da zai rama.
A hankali ya ce "Ayi mini Afuwa Aunty Mama...." Ta katse kiran ya bi wayar da kallo dama ga haushin.Nihila da yake ji ga wannan bare kuma a kai ga rigimar Feenat.
Bai gama tunani ba wayar ta sake neman agaji , yana dubawa ya ga lambar sirikinsa Alhaji Abdurrahman Maifata.
Cike da girmamawa ya ɗaga kiran.
A maimakon muryar Abba sai ya ji ta wani daban.
"Jamilu ne Dakta ne ko?"
"Eh shi ne."
"To , ka zo gida yanzu Abba na son ganin ka da gaggawa ba lafiya ba."
Ya miƙe tsaye yace "Subahanallahi me ya faru Yaya Jamilu?"
Sai ka zo ɗin dai tukuna za ka ji."
"Shikenan yanzu zan taho."
Ya ajiye wayarsa. Farcensa ya sa a baki ya ɓalla ya tofar ya ja mulkin motarsa ya yi waje da sauri.
Yana ƙokarin buɗe motar wayarsa ta sake ƙara yana dubawa ya ga sunan "Mi Amor." 
"Hello Mi..."
"Ka bani kunya Azlan Wallahi ka yi abin kunya kai ba ka ji kunyar kwaso bazawara ba sauran wani? Ba ka ji kunyar kwaso yar talakawa ba wadda status ɗin ta bai kai namu ba ka rasa da wa zaka haɗani sai waccar yarinyar a rame a jeme kamar matsattsiyar rama? To da sake sai dai family ya rushe amma sai ka sake ni don ba zan taba yarda ka haɗani kishi da waccar ƙazamar ba sam baka isa ba Wallahi never Azlan ka sake sabon karatu na gaya maka."
A daidai wannan lokacin ba ƙaramin danne zuciyarsa yake yi ba da ace a gabansa take masa wannan rashin kunyar da wataƙila ya sauke mata aljanun da suka hau kanta sai ya ji muryarta na ci gaba da gaya masa baƙaƙen maganganu. Daga ƙarshe da ya fusata sai cewa yayi "Nafi kuka bulukiyar ma na ci uwarta."
"Hehe! Wallahi da ni kake zancen Azlan ba dai kun haɗa baki anyi munafurci ka yi min kishiya ba? To da sake na rantse da Allah duk sai kun yi da na sani sai kun san kun taɓo ni."
Ya yi tsaki yace "Kiyi duk abinda za ki iya zamu iya ɗauka daidai nake da dattin kan ki Nafisa duk masu hure miki kunne kike min raini ba son ki suke ba kai ki zasu yi su baro ki."
"Mtsw." Ta ja tsaki ta kashe wayar.
Wani irin abu ya ji ya saukar mai wani irin ɓacin rai ya ziyarce shi bai san rainin da Nafisa tayi masa ya kai har haka ba abin ya wuce gona da iri ya yi shiru ya yi dum ƙirjinsa na bugawa da sauri da sauri tuni wani ciwon kai ya saukar masa ya sa hannu ya dafe kansa yace "Is okay Azlan ka kwantar da hankalin ka ka yi haƙuri su mata haka suke basu da kai." Da kansa ya yi consoling kansa sannan ya shiga cikin motar bayan wayar Nafisa kawai ya san cewa ta aikata wata tsiyar ne.
Yana isa ya faka a harbar gidan ya ƙarewa gidan kallo saboda tuna maganar Nafisa da ya yi wai yar talakawa gida ne fa da girmansa daidai rufin asiri ga wurin parking ga gate, ga babban tsakar gida banda ɗakunan ciki da madafi komai dai a wadace shi ne don raini za ta ce yar talakawa bata san yadda yake jin Nihila a ransa bane wataƙila shi yasa take aibata masa ita.
"Salamu alaikum." Ya yi sallama daga ƙofar da zata sada shi da cikin ainihin tsakar gidan.
"Amin wa'alaikum Salam." Uwani ta amsa masa.
"Maraba lale Bismillah shigo ciki mana shigo."
Ya zare takalminsa ya shigo ciki da baƙar safa a ƙafarsa.Bai zauna akan kujera ba a ƙasa ya yi zaunensa kawai ya yi shiru.
Ba a jima ba Uwani ta dawo da ruwa da zoɓo mai sanyi sai cincin ta ajiye masa sanann tace "Bari na kirawo Mama tana ciki."
Kansa kawai ya iya gyaɗa mata ya dauki ruwan sanyin ya kafa bai sauke ba sai da ya shanye tas sannan ya sauke bottle ɗin kuma da za a ƙara masa ma shanyewa zai yi saboda yadda yake jin zafi a ransa.
Sai wulga idanu yake yi don ya ga ta ina zata fito duk da ya san ba zata yarda da fito ɗin ba in har ta ji zuwansa bare kuma ɗazu ta mai laifi.
Alhaji ne da Mama suka shigo falon a tare da sauri ya gayra zamansa yana ƙoƙarin tsugunnawa Alhaji ya ɗaga masa hannu.
"A'a zauna! Zauna Dakta."
"A'a Alhaji ba ayi haka ba Barka da dare."
"Barkanmu,zauna na yafe ni na ce ai."
"Allah ƙara girma Alhaji."
"Amin."
"Barka da dare Mama mun same ku lafiya?"
"Lafiya Alhamdu lillah. Ya aikin ?"
"Alhamdu lillah."
"To madalla ya wajensu Maman taka?"
"Tana lafiya lau du da yau ban ganta ba amma daga nan can zan tafi."
"Ka gaishe ta kam."
"In sha Allahu."
"Erm....Malam Muhammad magana ce nake so muyi da kai mai muhimmanci Musanmman akan auren ka da Nihila."
Ambatar sunan Nihila kaɗai da Alhaji ya yi sai da ya ji gabansa ya faɗi.
Ya gyara zamansa yana kallon ƙasa saboda ya bawa zancen Alhaji muhimmanci.
"Ɗazu bana nan an gaya mini matar ka ta zo ta tada min hankalin gida." 
Gabansa ya ba da ras...kamar fashewar tangaran haka ya ji. Ya maida kansa ƙasa cike da kunya.
Alhaji bai tsaya ba.
"Magana ta ɗaya ce Muhammad ka sauwaƙawa Nihila. Saboda na samu dawo cikin hayyacinta da ƙyar ba zan so ta kuma samun kanta a cikin halin da ta samu kanta a baya ba, ina son ya ta. Bana son tashin hankali ni kam, tunda dai matar ka bata murna da wannan aure ka je ka rubutowa Uwata takardar ta Allah Ya haɗa kowa da daidai shi dama ba mu muka ce ba kai ne ka dage har aka yi saboda girman iyayenka amma tunda matar ka bata so ba zan kai Nihila inda zata yi rayuwar bora ba."
Sau biyu yana ƙoƙarin buɗe bakinsa don ya yi magana amma ya kasa, nauyi harshensa yayi masa a ransa kuwa fade yake "Ta yaya ma za a ce za a raba shi da Nihila sun san  irin son da yake mata kuwa? Barazana da haukar Nafisa basu isa su saka ya kuma aikata saki ga yar kowa ba. Saboda haka ya daga kai a hankali yace "Allah Ya huci zuciyar ka Alhaji, ban san abinda Feenat ta zo tayi ba amma ina mai tabbatar maka da ba da yawun wani ta zo ba sai don raddin kanta, da yardar Allah zan ɗauki mataki don Allah Alhaji ka daina ambaton saki ban auri Nihila don ina son na sake ta ba sai don ina son mu ƙare rayuwarmu cikin walwala da farin ciki da kuma ibadar aure in dai da raina da numfashina ba zan barta ba Alhaji ayi haƙuri a bani dama."
Mama ta cafe. "Da dai ka haƙura Dakta baka ga irin abinda matar ka ta zo ta mana ba Nihila bata iya faɗa ba bata san hayaniya ba ka duba dai ka warware saƙar nan."
"Mama hakan ba zata sake faruwa ba in sha Allahu ita ma kishi ne na sani."
"A'a wannan da gaske take yi mu muka ga abinda muka gani tunda ta shiga ciki ma bata sake fitowa ba tana can tana aikin kuka."
Yana son ya ce a bashi dama ya ganta yana kunya ya rasa yadda zai yi.
Alhaji ne ya lura da hakan shi yasa ya tashi tsaye yace da Mama.
"Balki ki buɗe wancan sitting room ɗin ta zo ta same shi."
Bata musa masa ba ta tashi tayi ciki. 
Zuciyarsa zafi yake masa bai san ɗanyan kan Nafisa ya kai haka ba sai yau ta ya ma aka yi ta san gidan har ta zo? Sai yanzu ma ya gane inda maganganu ta suka dosa ɗazu a waya.
Ya lashe leɓɓensa da suka bushe ruwa yake son ya ƙara sha don shi ma'abocin shan ruwa ne a kai a kai baya wasa da shi zai iya yini bai ci ba amma ba zai iya yini bai sha ruwa ba koda na awa guda ne.
Ya saka farin hannunsa ya shafi maƙogwaronsa .
Zara-zaran yatsunta ya fara hangowa da yake kansa a ƙasa yake. Har ta iso kusa da shi ta tsaya bai ɗaga kansa ba haushinta yake ji saboda ta tsaya da Abdullahi ɗazu a waje bayan ta san baya son ko sunan shi ta ambata ya tasani mutumin nan kamar ransa.
Bata ce masa komai ba ita ma ta juya ta fita sitting room ɗin ta buɗe ta koma ta leƙa tace da shi "Na buɗe."
"Zo ki bani ruwa mai sanyi." 
Ba musu ta dawo ta shiga kitchen ta dauko a fridge kafin ta dawo ya isa bakin ƙofar sitting room ɗin. 
Tana shiga ta ajiye masa a gabansa ta koma ta zauna. Sai ya ki ɗauka ya tsaya kallon yadda idanunta suka kumbura saboda kuka.
"Kuka Nihila?"
Ta girgiza masa kai da sauri duk da ta san ba yarda zai yi ba.
"Kuka kika yi mana saboda Nafisa wa yake wa kishiya kuka in ba ke ba shagwaɓaɓiya? Sai ki saka ta raina ki ai."
A hankali ta ɗaga kai ta kalli cikin idanunsa da sauri ta sauke ganinta daga na shi ta juyar da kanta gefe.
"Dawo da ganin nan kaina."
Duk abinda bata so Dr yana so duk abinda ya san yana mata wahala Dr shi yake so ya sani sarai bata iya haɗa idanu da shi matsananciyar kunyarsa take ji.
"Sau ɗaya zan sake maimaitawa ki kalle ni."
Babu yadda ta iya haka ta ɗaga kai ta kalle shi.
''Good! Me ya kawo wancan yaron ɗazu?"
Tana wasa da yatsun hannunta tace"Wannan yaro kenan?"
"Tambaya ta ma kike yi?"
"Ji nayi kace yaro."
"Ba yaron bane?"
"Uhm." Kawai ta faɗa.
"Uhm? Saboda na taɓa miki masoyi ko?"
"Ba kyau fa."
"Ashe kin san ba kyau amma kika je inda yake ba da izinina ba?"
"Ai bani na je ba shi ne ya zo."
"Me yasa zai zo wurin ki kina matata?"
"Zuwa ya yi ya bani haƙuri wai na koma gidansa shi ne na ce masa ai an ɗaura aurena jiya."
Ya kulle ido ya sa haƙoransa na sama ya datsa leɓɓensa na ƙasa har yana jin zafin sosai amma bai saki ba.
Wai ta koma gidansa.
Ya ja wani dogon numfashi ya saki ya ce "Zo ki bani ruwan nan kin zo kin ajiye min a ƙasa ni ne ma zan ɗauks Nihila?"
Bata yi gardama ba ta miƙe ta isa ta sunkuya ƙamshinta ya doki hancinsa hijabi ne a jikinta iya guiwa. 
Ta ɗauko ruwan ta miƙa masa ya sa lallausan hannunsa ya kama robar ruwan da hannunta idanunta ta zare ta kalle shi da sauri.