GABA TA ZO BAYA

Chapter 2

by @khairatup01

GABA TAZO BAYA
Ummulkhair S Panisau 
(Khairatup)
002

Ƙoƙarin zame hannunta take yi amma ya hana ta damar yin hakan ya sa idanunsa a cikin nata cikin sanyayyiyar murya tace "Ka cika ni don Allah."
"Sai kin gaya min haramcin hakan tukunna zan sake ki."
Ta cigaba da son janye hannunta amma ta kasa daga ƙarshe ya janyota gaba ɗaya ta faɗa kan faɗaɗen ƙirjinsa,zuciyarsu ta buga a tare, wani abu mai kama da shocking Azlan ya ji. Ya saki ruwan a ƙasa, ya sa hannunsa ɗaya ya taɓa bayanta. 
Wani yarrr ta ji a jikinta tuni jikin ta ya soma rawa.
Kawai sai ya cikata tayi baya da sauri ya kafa mata manyan idanunsa masu ladbtar da yan'mata.  Ta sunkuyar da kai.
"Da gaske fa jikin ki rawa yake Nihila."
Bata ce da shi komai ba amma tabbas ta ji wani abu wanda rabonta da jin sa tunda abubuwa suka sauya tsakaninta da Abdullahi.
"Me Nafisa tace miki Alhaji yake son na sake ki?"
"Tace kar na sake na shigo mata gida."
"To ke kin yarda gidanta ne?"
Ta kalle shi maganganunsa ma sun daina bata mamaki in kayi hagu sai ya yi dama in ka yi dama sai ya koma hagu ko ya nuna maka ma ba wanda ya iya sai shi.
"Ni dai ba zan iya hayaniya da matar ka ba kawai na yarda ka sahale min."
"Au haba!" Ya faɗa da gadara a maganar.
"Don Allah ka fahimce ni tun farko sai da na gaya maka ba irin ka ba ce ni bamu dace ba."
"Da wancan banzan kika dace kenan? Shi ne irin ku ko?"
Sai tayi shiru tuni hawaye suka cika mata idanu ta sa bayan hannu ta tare masu zubowa.
"A dake ni a hana ni kuka? Wato ni ne bani da bakin kuka sai ke sholisho ban da ma kin raina min hankali in zo zan gan ki da zumuɗina na gan ki da wani ƙato can a maimakon da kika gan ni ki ji wani iri ki taho sai kika yi biris dani kika bawa banza ajiyata ki ka cigaba da kula shi har sai da na zo da kaina na kora shi maimakon ki kira ni sai kika nunan iyakata saboda ba kya sona shi kike so shi ne yake burge ki shi ne irin ki." Ya faɗa da zafi-zafi ita kuma ta saki kukan da take dannewa gabaɗaya.
Sai kawai ya tashi ya yi hanyar fita sai ya tsaya kuma yace "Na rantse da Allah idan kika sake yi masa magana ban yafe ba."
Da sauri ta ɗaga kai ta kalle shi idanu jajir tace "A'a Dr kar ka manta uban ya'yana abu zai iya tasowa...."
"Na hutar da ke ni zan musu ni zai nema ba ke ba yanzu ni ne a saman ki."
"Kar ka rabani da su."
"Sai dai ki ce kar na raba ki da shi. Ko yanzu ya baki yaran nan amsarsu zan yi da gudu sai dai na san ba zai bayar ba saboda haka yanzu ni ne madadin ki."
Yayi ficewarsa ta sa tafin hannu ta rufe fuska ta rushe da wani irin kuka.
*

Tunda yayi parking motarsa samarin gidan suka taso suka tsaya cirko-cirko a gaban motar a lokuta da dama hakan na ba shi dariya sosai ya rasa yaushe zasu daina wannan ɗabi'ar ko Abbu ba sa yi masa haka amma da yake shi ana son a daki hancinsa ga shi nan sun taso.
Dole ya gyara yanayinsa daga ɓacin rai zuwa walwala don baya son su gane baya cikin walwalarsa.
Da ɗaya da ɗaya suka dinga yin musabaha. Babu mai duhun fata a cikinsu kowa fari ne sai dai hasken wani ya fi na wani. Gashinsu kuwa asalin na larabawa ga su dogwaye ma sha Allah a lokacin da suke yara haka ake cewa gidansu gidan farare.
"Yaya Azlan sannu da zuwa."
"Yauwa Ashraf."
"Yaya Azlan yau ka daɗe."
"Eh na je na ga matata ne wani abu?"
Rayyan ya kama bakinsa yana dariya.
Nadir yace "Yaya Azlan yaushe zamu je mu gan ta?"
"Duk sanda kuka shirya zaku gan ta." 
Yana tafe suna biye da shi har babban falon Ammi. Ƙamshin turaren wuta ya cika falon wannan sabon Ammi ne ma'abociya son ƙamshi ce ba a raba falonta da ƙamshi.
Jikokin Ammin ya gani da Munseef da Mubeen sai Nasreen an mata two babies tayi kyau.
Tana ganin shi ta tashi tana haɗa hanya ta isa gabansa ya cafe ta yana dariya ta kama gemunsa yayi yar ƙara kaɗan irin wai ya ji zafin nan ta kuwa ƙyalkyale da dariya harda tafa yan ƙananan hannayenta an faranta mata rai.
A kan cinyarsa ya ɗorata sauran ma suka mamaye shi "Uncle, Uncle." Ya zaro sweets daga aljihunsa ya raba musu sannan suka bar shi.
"Nifa na ji ƙamshi ya gallabeni ashe ango ne ya shigo ah'ah mijin Nafisa mijin Nihila."
Ya saki murmushi ya dunƙule hannunsa ita ma haka suka haɗa knckles.
"Ina yin ki Nuwaira."
Suka tafa.
Ammi an saukowa daga bene a hankali fara tas kyakyawa a kallo ɗaya zaka gane ita ce ruhin gidan da kuma inda suka gado kyau.
Medicated glass ne a idonta.
Tana ƙarasa saukowa suka miƙe duka sai da ta zauna sannan suka zauna.
Tana zama Nasreen ta haye cinyarta tana son saka mata sweet a baki.
"Waya baki sweet."
"Akul Dakta."
Aka sa dariya.
Ammi tace "Ina ka tsaya ne ko ka je gun matar ta ka ku gana?"
Ya sosa kai ya sunkuyar da kansa yace "Ammi don Allah." Da Larabci ya faɗa ta yi murmushi kawai ta girgiza kai.
"To ai baka saba ba ne na zaci ma ka wuce ai."
"Ammi ba zan taba wucewa ban zo na gan ki ba."
Ta shafa kansa kamar wani ƙaramin yaro.
"Ammi ɗazu fa Nafisat ta je gidansu Nihila."
"Allah Ya sa ba wani abu aka ta musu a can ba?"
"Tayi fa zancen da nake miki ma Ammi yanzu haka Alhajinsu yace na bashi takardar ta baya son a sake maimaita baya."
Duk sai jikinsu ya yi sanyi fuskokinsu kaɗai idan ka kalla zaka ga damuwa a cikinsu.
"Karo na huɗu fa kenan Ammi gaskiya ya kamata kiyi wani abu a kai yanzu. Abin ya isa haka." Nuwaira ta faɗa muryarta na rawa.
"Zanyi magana mana ai abin ya isa haka na ga su basa duba zumuncin kar ka damu zan je da kaina gidansu ɗiyar tawa babu mai raba ku wannan karon, zanje da kaina ka ji?"
Ya gyaɗa mata kai.
Ammi mace ce mai son ya'yanta tun fil'azal tana son abinda suke so shi yasa gidansu abin sha'awa da burgewa basa ɓoye mata komai haka ma Abbunsu.
"Yaya Nuwaira Ki je Yaya Ammar ya zo."
"Tashi ki wuce Nuwaira ai dama dare ya yi kar yara suyi bacci daman."
Ba tare da musu ba ta miƙe ta kalli yayan nata tace "Yayana ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai faru in sha Allahu, wanann ba zata ƙubuce maka ba don duk tayi mana muna sonta."
Ya lumshe idanunsa ya gyaɗa mata kai kawai Sannan yace "Rayyan ka je ka kai su Nasreen mota." 
Ya tashi ya ɗauki Nasreen ya kama hannun Mubeen shi kuma Munseef Nuwaira ta riƙe shi.
"Wallahi Azlan ba zaka kwanta ba sai ka saki yarinyar nan."
Ta cikin ɗakin ya ce mata "Wai Nafisat na gina gidan nan da kudin ki ne? In dai ba da kuɗin ki na gani ba to tabbas zan iya kora ki gidanku darajar Ammi kika ce har kike iya gaya min yadda kike so amma idan kika kai ni bango sai na shata layi a tsakanina da ke Wallahi."
Ɗif tayi shiru kamar anyi ruwa an ɗauke abin ya bata mamaki yana nufin ta tafi ta bar masa gida kenan.
Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ta bar ƙofar ɗakin.
Ba tare da ɓata lokaci ba ya yi wanka ya yi sallah sannan ya ci abincin da ya taho da shi ya saka kayan baccina ya bi lafiyar gado. Akwai consultant ɗin da zai yi da safe.
Sai dai ya kasa baccin sai juye-juye yake yi fuskarta ke masa yawo yadda take ta kuka kishinta ne ya masa yawa sosai baya son ya ga Abdullahi in ya tuna ya ma taba aurenta haushi yake ji ya tsani mutumin tsaki ya saki ya ɗauko wayar sa don ba zai iya jura ba.
Layinta ya kira bugu biyu uku har ta katse bata ɗauka ba ya dinga jera tsaki sai ya tura mata da saƙo.
"Ki ɗauki wayata na san idon ki biyu kina jin tsoron Allah kuwa Nihila?"
Tana karanta saƙon ta ji jikinta ya yi sanyi ta sa hannu ta share hawayen ta. Yana kira ta ɗaga wayar.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce da ita.
"Me ya hana ki bacci?"
"Ba komai."
"Har yanzu ba ki daina kukan ba."
"Uhm." Ta faɗa tana shan majina.
"Saboda wancan abin kike ta kuka?"
"A'a."
"Shi ne mana."
"Ba haka bane."
Ya taɓe bakinsa sannan yace "In ma don shi ne kin yi a banza ba lada, ki samu ki sha maganin ki sannan ki kwanta ki huta da safe su Ammi zasu zo bana son su gan ki wani iri yadda kika ci kukan nan zaki iya cewa baccin ma ba za ki yi ba an taɓa Miki Majnoon to sai kuyi haƙuri na riga na ɗaga tutar yanzu Azlan n mijinki ba saki ba yaji a tsakanin mu."
Bai bata damar sake magana ba ya kashe wayar dama so yake ya ji muryarta ya kuma tabbatar da cewa ta daina kukan.
******

Cikin shirin fita aiki ya fito fes da shi sai ƙamshi yake yi. Shadda ya saka amma ɗinkin irin armless ɗin nan da singlet a ciki sai wando ya saka wata hula yar karama. 
Wayarsa a hannu yake saukowa daga benen.
"Ammi Allah idan ta sake yi min irin wannan abun sai na mare ta kin sani saboda ke ne na kyale ta fa."
"Na sani Azlan ka ƙara haƙuri ka san dai kai namiji ne, yanzu mata biyu ne da kai sai ka koyi haƙuri."
"To Ammi amma dai..."
"Ka ga."
"To Ammi yaushe za ku je?"
"Anjima zamu je wurin sha ɗaya Abbu yace zamu tafi tare da shi ina jiran Nuwaira ta ƙaraso."
"Yauwa in kun je don Allah Ammi ku tsaida ranar tariya."
"Kai Azlan yaushe ka zama mara kunya?"
"Ammi kunyar ki zan ji? Ke fa kika haife ni ke ce abokiyata ta farko."
"Allah Ya shirye ka. Ka wuce ka tafi aikin ka zan aiko Rayyan ya kawo maka abinci na san bata girka maka ba."
"Yauwa Ammi sai ya zo ɗin."
A kan kujera ya gan ta gashi a baje kamar wata aljanna mascara ta zazzago saboda kuka.
"Ni kake wulaƙantawa saboda ka auri wata banza ko?"
"Sunan ta Nihila."
"Banza ce mana me aurar mijin wata."
"Nihila sunan ta."
"Allah sai ka zaɓa ko ni ko ita."
Murmushin gefen baki ya yi kawai ya yi taku ɗaya sai kuma ya tsaya yace "Nafisa,kar kishi ya rufe Miki ido kiyi ta min rashin kunya ba zan saki Khadija ba saboda ban aure ta don na sake ta ba sai don na zauna da ita na har abada. Da za ki kwantar da hankalin ki da ya fi saboda wanann abubuwan da kike yi fa ba zai saka na saki Nihila ba."
Ta saki kuka mai tsuma rai ta soma ihu ya sa kai ya fice kawai yana girgiza kai wannan karon bazai saki kowa don farincikin Nafisa ba.
Yana fita ta kira wayar Ammanta.
"Amma na shiga uku na lalace yace ba zai sake ta ba."
"Ki kwantar da hankalin ki ke ba abinda zai faru dole sai ta tafi ki daina wannan banzan kukan haba ai sai ya raina ki."
"Amma ba zan jura ba yana son ta fa sosai ya fi son ta da matan da ya aura a baya baki ga yadda yake gayan maganganu ba."
"Zai daina ai sai na shayar da shi ruwan rashin mutunci da ni yake zancen ai ko mu iyayenku bamu zauna da kishiyoyi ba shi ma bai isa ba."
"To Amma."
"Ki yi shiru ki shirya ki tafi aikin ki."
"To Amma."
"Na gaya miki kar ki ƙara masa maganar banza."
"To Amma."
***

"Muhammad Adil" ya gani a screen ɗin wayarsa murmushi yayi sannan ya daga kiran.
"Bro for life ya aka yi ne?"
"Baka ga lambar ba da kyau?"
Sai ya cire wayar daga kunnensa ya maida.
"Wai ka dawo?"
"Eh mana"
"Yaushe don Allah?"
"Jiya da dadddare."
"Amma baka kirani ba?"
"Kayi haƙuri na ga dare yayi ne."
"Kana ina yanzu?"
"Ina gidana"
"Ka zo mana asibiti ka same ni."
"Da zanje gun Ammi ne tukunna."
"A'a Ammi bata nan fita zasu yi anjima."
"Shi kenan bari na taho."
"Sai ka zo akwai Magana fa."
"Munafuki ai na san me ka aikata Wallahi sai ka san ka sake aure ban sani ba."
"Tuba nake takwara."
"Za ka yi bayani."
***

Sanye take da doguwar riga ta atampa tayi daura ɗankwalin atmapar da Safa a ƙafarta.
Falon Alhaji ta shiga nan ta tarar da su duka a zaune.
Sai da suka gaisa sannan tace "Mama wai ya ce Ammin shi zasu zo Anjima."
"To sai da ya taso ta?"
Bata ce da ita komai ba.
"Alhaji ka ji fa yanzu ya za ayi?"
"Ina kan bakana Balki in har ba zasu iya hana tashin fitina ba dole ne mai babban suna ya saki uwata saboda ba zan iya manta wahalar da yarinyar nan ta sha ba in dai dangin mijinta basa son ta fa gaskiya dole ne a haƙura ai kin san komai ke me bamu gani ba?"
"Haka ne Alhaji ai shi Dakta na ga da hankalinsa yana son ta a tsaye yake."
"Ba a gane mutum ta haka duk da ina kyautata masa zato mai kyau."
"Allah Ya sa mu dace. Sai ki tashi muje ki haɗa musu wani abu mai ɗan sauƙi ai ba sa zo su tafi a haka ba."
Tare suka fita daga falon kitchen suka nufa yan abun da suke da shi suka soma haɗawa mai sauƙi daidai na marmari. 
Alhajin ma bai fita ba a ranar yana jiran in sun zo sun tafi sai ya wuce shi da Jamilu.
Da misalin ƙarfe sha biyu daidai na rana suka ji diri-dirin motoci a gidan. Uwani ta yi musu iso ainihin babban falon gidan wanda yake a share ƙal-ƙal sai ƙamshi turaren wuta yake yi.
Nuwaira da Ammi da Abbu da Yaya Kabiru ne suka zo sai Nasreen.
Suna zama Uwani ta shigo da tray a hannunta dauke da ruwa mai sanyi ta shigo ta ajiye musu ta kuma komawa ta ɗauko cincin da meatpie da cake ta ajiye musu sai wani flask ɗin mai jellof ɗin shinkafa da kaza.
Ammi tayi ta mamakin koƙarinsu lallai da karamci a tare dasu.
"Maraba sannun ku da zuwa sannunku Hajiya."
Ammi na murmuhsi tace "Sannunmu.Mun same ku lafiya?"
"Alhamdu lillah."
"Madalla."
"Bismilla kun ɗauko hanya." Mama ta faɗa tana nuna musu kayan gabansu.
Nasreen ta tashi tana haɗa hanya ta hau kan Mama.
Mama tace "A'a wannan kisiyar ko kinibibi ba zai saka na bar miki gidana ba ehe ba ɗaki yarinya."
Duk aka saka dariya .
Alhaji yace "Kar ki ari bakina ki ci mini albasa ina so ga amarya ma sha Allah ga gashi ga idanu ai kawai ki koma daga gefe Hajiya."
Nuwaira tayi dariya sannan tace "Ina Auntyn tamu take?"
Mama tace "Tana cikin ɗaki bari Uwanin ta raka ki." 
"To."
"Uwani! Uwani!"
"Na'am Mama."
"Ki rakata ɗakin Nihila"
"To an gama ta so Hajiya."
Tana gaba Nuwaira na biye da ita.
A hankali Uwani ta buɗe kofar ɗakin ta shiga.Nihila da ke kan sallay ta juya da sauri don har yau ba ta daina firgita da wasu abubuwan ba.
Da ta ga Uwani ce da baƙuwa sai ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe da sauri.
Uwani tace "Uwar masu gida kina da baƙuwa Hajiya Mama tace na rakota gun ki."
"Sannu da zuwa." Ta faɗa a hankali tana murmushi.
Nuwaira ta yi tasbihi ga Allah ba fara bace Nihila amma baƙinta mai kyau ne fuskar ta ba wasu ƙuraje ko hayaniyar mai.
"Zauna mana."
Nuwaira tayi dariya dimple ɗinta ya koma ciki sosai ta tafa hannu ta tsaya in surprise.
Nihila ta ɗan ware ido tana mamakin wacce ce wannan kamar wata dishyu.
"Baki san ni ba ko?"
Ta gyada mata kai sannan tace "Ban gane ki ba."
"Don Allah baki ga kammanina da wanda kika sani ba?"
Ta sake kallonta sai kuma ta murmusa tace "Allah ban gane ba wace ce ?"
"Kai don Allah amma ba laifin ki bane laifin bro ne da bai nuna miki mu ba."
Sai a lokacin ta dau haske ta manta ma da zuwansu bata zaci suna da sauƙin kai haka ba saboda yadda ta ji ana faɗin kuɗinsu.
"Lah! Nuwaira ko?"
Ta saki ajiyar zuciya ta zauna a gefen gadon tace "Gaskiya yanzu na samu wani relief a raina da na ji kin ambaci sunana har zan tadawa bro hankali yanzu a waya ace baki san fav ba ai an samu matsala."
"Kiyi haƙuri ban gane da wuri ba kin san bamu taɓa haɗuwa ba."
"Na haƙura matar yaya."
"Nagode. Bara na kawo miki ruwa da abinci."
"A'a don Allah zauna na cigaba da ganin ki saboda na kai wa Bro rahoton ya iya zaɓe Ma sha Allah!"
Murmushi tayi tace "To zauna na je na gaishe da Ammi na san tare kuke ko? Jiya ya ce min zaku zo ai da kun zauna ma."
"A'a bamu ga ta zama ba kam ana son a raba Bro da numfashinsa, kin san ko yadda yake jin ki a ransa kuwa?"
Bata ce da ita komai ba kawai ta juya ta fice da yake da hijab a jikinta.
Nuwaira kuwa bakinta ya kasa rufuwa hakan nan Nihila ta sake shiga mata rai nutsuwata ta kai har godewa Allah tayi da mijinta ya sake ta ta zama rabon yayansu.
Launin fatar ta na daga cikin irin chocolate colour da ke da dumi d sheƙi mai kyan gani,kyakyawar fuskarta da yanayin hallitar ta sun sa ta zama mai jan hankalin mai kallonta.
Hancinta siriri ne kuma dogo,yayin da gilashin ya ƙarawa fuskarta wani irin kamala da kwarjini.Gilashin bai rage mata kyau ba sai ma wani salo na Musanmman da ya ƙara mata.
"Yayana ya yi sa'ar mata." Ta faɗa a hankali.
Ba wai iya kyawunta ne ya ja hankalinta ba, akwai nutsuwa a tare da ita."Na gamsu da dalilin da ya saka Yaya ya zaɓe ki ,kin dace da shi sosai." Ta fadi kamar tana gabanta.


Nihila na isa falonsu ta gyara hijab ɗinta. Da sallama ta shiga.
"Salamu alaikum."
"Wa'alaikum Salam" suka amsa.
Da ta shiga ta hangi wata mata na murmushi ko ba a faɗa mata ba ita ce Ammi mahaifiyar Azlan shi kuma dattijon Abbu mahaifin Azlan.
Ammi tace "Nihila ko."
Kanta a ƙasa tace "Eh."
"Sannu ku da zuwa."
Suka amsa mata a tare.
Abbu yace " lallai na gane dalilin da ya saka Azlan daina gane komai Allah Ya baku zaman lafiya a gidanku."
"Kalmomin da Abbu ya faɗa suka bata kunya tsoron da ta shigo da shi ta nema ta rasa sai ma wani sauƙi da ta ji ya ratsa ta.
Ta juya ba tare da ta kalli Ammi ba tace "Ammi Barka da rana an zo lafiya?"
"Lafiya lau ɗiyata yaya kike?"
"Lafiya lau."
"To ma sha Allah! Kin gan mu mijin ki ya taso mu da farko dai kuyi haƙuri bamu san ma Nafisat ta zo ba amma mun samu labarin irin rashin kunyar da ta zo t aikata muku muna bada haƙuri haka ba zata sake faruwa ba in sha Allahu. Alhaji ka yi hakuri ka janye batun ka mu kam mun ga ya ba mai rabamu da ita kuma." Ammi ta faɗa tana murmushi har ranta Nihila tayi mata duk a matan ma da ya aura ita ce ta kwanta mata sosai saboda nutsuwarta da sanyin ta.
Abbu ya ɗora. "Alhaji Abdurrahman ina mai bada haƙuri kuma na yi maka alƙawarin Nihila ba zata yi kukan shigowa ahalinmu na , a matsayin ka na uba na gane dalilin tsoron ka Musanmman bayan abinda ya faru a baya sai dai ina son ka saka a ranka daga yau daga yanzu Nihila ta zama yata tana ƙarƙashin kulawata ba zan bari a zalince ta ba da yardar Allah in dai da raina da lafiyata."
Hankalin Alhaji ya kwanta ya ji wani sanyi a ransa zuciyarsa ta gamsu da dattako da mutunci na wannan ahalin masu karamci da  mutuntaka, yanzu ya gamsu da auren Azlan babu da na sani a cikinsa. Ya sa hannun ya kama na Abbu ya jijiga shi ma Abbun y jijjiga suka yi dariya tare .
Mama dai bakinta ya kasa rufuwa Nihila ta samu gidan da ya dace da ita.
Ammi tace "Ance tana da yara ko ya ban gan su ba?"
Mama tace "Ai suna can wurin uban ya ki ya bata su."
"To Allah Ya raya su cikin aminci."
Suka amsa da "Amin" duka.
"Matar yaya nan kika yi zamanki kika bar ni?"
Da sauri tace "Kiyi haƙuri." 
Ammi ta lura da Nihila na da saurin tsorata koda yake Azlan ya gaya mata a baya patient ɗin sa ce tayi fama da depression har abin ya so ya taɓa mata ƙwaƙwalwa. Kuma yanayin azabar da ta sha a gun Abdullahi da danginsa ba zai bar ta da wuri ba. Tausayi ta ya sake kamata.
"Na haƙuta matar fav. Ammi Wallahi kin gan ta she is so pretty."
Ammi ta ɗan harareta tace "Ki kyale min ya fa to."
"Ammi Allah da gaske nake."
"To mun ji."
Basu jima ba suka tafi.Bayaj tafiyarsu Mama tace da Alhaji "Na samu wani sauƙi a zuciyata yanzu Nihila ta samu surukai masu sonta kuma in sha Allahu ba zata yi kuka ba."
"Bi'izinillah kuka ya ƙare mata kam."
Nihila dai ta tashi ta bar falon.
Tana shiga ɗakin ta taji wayarta na ruri koda ta dauki wayar shi ne yake kiranta ta ɗaga wayar.
"Salamu alaikum."
"Wa'alaikum Salam matata."
"Uhm."
"An daina kukan?"
"Eh."
"Kin karya ko?"
"Eh."
"Magani fa?"
"Na sha."
"Ba abinda kike so?"
"Eh."
"Ko ni ba kya son na zo?"
"A'a."
Adil ya yi dariya daga can taji dariyar.
"Kin saka Adil yana min dariya ko. Ke Wallahi ƙauyis ce ba a gwale ango fa."
"Kayi haƙuri."
"To zan haƙura amma sai kin yi mini wani abu."
"Mene ne?"
"Kice min I love you!"
Sai tayi shiru ta kasa magana.
Abdil yace "Rabu da shi jeki yi harkar ki."
"A'a bani na baki umarni ba."
"To ai aiki zanyi."
"Lala zan gayawa Mama gaskiya ba kya bani lokaci."
"Yanzu su Aunty Nuwaira suka tafi."
Sai da ya saki dariya sosai har sai da ta tsargu sanann yace "Nuwaira ce Aunty? Kar in kuma ji kar in sake ji ai kece a samanta in ma ta girme ki kece Auntyn ta yanzu baki san shekaru biyar na bata ba?"
"To ai ta girme ni."
"In ma ta girme ki ni na baki girman yanzu."
"To."
"Anjima zan zo fa."
"Me zaka yi?"
"Ganin ki zan yi mu gaisa kin ga jiya ai faɗa muka yi da ke."
"To sai ka zo."
"Ki yi min girki kin ji? Ina son na ci abincin ki."
"Me zan dafa maka?"
"Duk abinda kika dafa zan ci."
"To. Amma da ina son naje gidan Aunty Karima."
"A'a ba yau ba ki bari zan kai ki da kaina."
"To shi kenan."
"Ga Adil nan wannan ƙanin nawa."
Adil ya amshi wayar.
"Yaya kike amarya?"
"Lafiya lau."
"Ya fama da ƙanina?"
Tayi murmushi kawai.
"Tare zamu zo fa."
"To sai kun zo."
"In mun zo za ki gane mu?"
"Eh."
"Shi kenan zan gani ko za ki gane mu."
Azlan ya amshi wayar yace "Ke na ba shi minti goma fa shi ne ƙanina kar ki zo kiyi tunanin da gaske yake."
Ita dai ta gaji da wayar ko don bata son dogon hira ne oho.
Tana ajiye wayar ta yi sallah aza
***
Sai da suka koma gida suka sake shiri amma gidan Adil suka tafi. 
Matarsa ta yi musu girki amma suka ce sun riga sun yi wa amarya alƙawari babu yadda ta iya haka tana gani suka shirya suka tafi. Azlan da Adil ba sa girma kamar yara suke abubuwansu gara ma Azlan bai haihu ba amma shi Adil yaronsa ɗaya Imam in suna abu ka ce su ma yaran ne.
Ya so su je gun Ammi amma sai yace in sun dawo sa je suna zuwa unguwarsu Nihila aka kira sallar magariba sai da suka tsaya a massalaci suka yi sallah sannan suka shiga gidan.
Kiranta ya yi a waya yace da ita "Na zo ko nace mun zo."
"To ina zuwa."
Sai da ta buɗe sitting room Sannan ta ajiye fulasan ta fita ta musu iso.
Saida suka shiga suka gaisa da Mama sannan suka koma can.
Mama tace da Nihila "Dama su biyu ne?"
Dariya tayi tace da ita "Eh su biyu ne baya nan ne ɗayan a Turai yake aiki shi yasa ba ku san shi ba."
"Ikon Allah aikuwa kamaninsu kwabo da kwabo ke yanzu kin gane su?"
"Eh mana."
"Tayaya kayan su ma ɗaya fa."
"Baki lura bane ɗaya yafi ɗaya haske da tsayi kuma ɗaya gashinsa ba yawa ɗaya kuma ba shi da dimple."
"Ke yar nan kice kin san Dakta haka?"
Bata ce mata komai ba kawai ta fice.
Ita kanta sai da ta lura sosai ta gane ko da zata shigo dasu Adil ne yayi magana ba Azlan ba.
Zaunawa tayi a ƙasa.
"Sannunku da zuwa ya hanya ya aiki?"
"Alhamdu Lillahi. Ya kike ?"
"Lafiya ƙalau."
"To madallah."
Sai suka yi shiru.
"Baki gane mu ba ko?"
Sai da ta yi murmushi sannan tace "Na gane ku mana."
"A'a baki gane ba ke da baki taɓa ganin mu tare ba."
"Allah na gane ku."
Suka yi ta mamaki Adil yace to bambance mu.
"Kai ne Yaya Adil, kai ne Dakta." Ta faɗa tana nuna su daidai.
Azlan yace "Ke ya aka yi kika sani?"
"Ya fika tsayi da haske kuma shi ba shi da dimples irin naka ,gashin ka ma yafi nasa yawa."
Adil yace "Smart."
"Ke dama kina kallona amma ban sani ba?"
Tayi dariya har nata beauty point ɗin ya shige ciki.
"Wallahi ana shan wuya kafin a ganemu amma ke a kallo ɗaya kika gane mu lallai kin cancanci kyauta."
"Gaskiya dai ya kamata ka bata kam."