Chapter 3
by @khairatup01
GABA TAZO BAYA
Ummulkhair S Panisau
(Khairatup)
003
Da wani irin ciwon kai ya isa gida, kallo ɗaya tayi masa ta gane baya cikin hayyacinsa. Ɗan gayun nan mai aji yau ga shi ga kamarsa.
Yanayin gidan kawai ya kalla ya gane akwai matsala.
Umman ya gani a zaune tayi jigum tana hawaye hankalinsa ya tashi ya isa gabanta da sauri ya sunkuya yace "Ummanmu lafiya? Me ya faru?"
"Na shiga uku Abdullahi, asirina ya tonu ka ga yaron nan Jibril ya aiko an kwashe kayansa ya fasa auren Ramla. Gata can sai suma take yi,ga Saudat ma an koro ta yaya zan yi da rayuwata ni kam?"
"Innallillhi wa inna illahi rajii'un." Ya dinga maimaitawa. Ya kasa cewa komai kawai ya koma ya zauna dirshan auren da ya karɓo bashi a kan sa ga shi yanzu an fasa ta ina zai fara?
Aimana ta fito tace "Ai shi dama ramin ƙarya ƙurare ne Umma kuna ma tambayar me kuka yi bayan duk abinda kuka yi? Ai yanzu kuka fara ganin masifu."
"Don ubanki ni ce uwarki ba ita ba wai me yasa kike yin haka ne? Ke shi kenan baki da ramin kan ki a maimakon ki tausayawa yan'uwanki na ga ma daɗi kike ji ke."
"Ba daɗi nake ji ba Umma ina tuna muku ne abinda kuka shuka ne kuke girba kuka adabi Aunty Nihila, kin manta ke ma ya'yan naki duk mata ne ga shi nan ai tun a duniya kun fara gani izayar da kuka gana mata Wallahi sai ya mata sakkaya. Ku yiwa kan ku hisabi da kanku." Ta suri buta tayi banɗaki da sauri.
Umma jikinta ya sake yin sanyi sosai. Abdullahi bai iya cewa komai ba kawai ya tashi ya ja yan ƙafafunsa ya shiga cikin falon. Ihsan da Abul suka yo kansa suna masa Oyoyo.
Ya shafa kansu da hannunsa yana ƙaƙalo murmushi.
"Abba ina Aunty take yau ma baka ganta ba?"
"Na ganta tace na gaishe ku zata zo ta same ku."
"Abba don Allah ka kaimu wurin Aunty." Ihsan ta faɗa kamar zata yi kuka.
"Kar kiyi kuka zan kai ku gobe in kuka dawo daga school."
"Da gaske?"
"Eh,zan kai ku amma sai kun dawo daga makaranta tukunna."
"Yeah! Yeah!" Suka dinga ihun murna.
Ya lashi leɓɓensa ya shiga ɗakinsu Aimana nan ya ga Ramlat a kwance kan gado idanunta a rufe amma hawaye na zuba daga cikin idanunta ta rame a iya yini ɗaya saura kwana huɗu bikin nata fa amma ya zo ya yi musu haka. Wani abu ya tsaya masa a ƙirjinsa ya ji kamar numfashinsa zai ɗauke.
Daga bayansa ya ji maganar Aimana.
"Idon ta biyu so take ta kashe kanta saboda namiji ai don ya fasa auren ta ba rayuwarta ce ta ƙare ba na meye zata takurawa kanta. Ta manta irin iskancin da ta aikata."
"Wai ke Aimana me yasa kike haka ne bakin ki ya yi kaifi da yawa. Baki ga halin da take ciki ba."
"Na gani mana kun manta halin da kuka saka wata a gidan nan ne?"
Shi dai ba shi da bakin magana hasalima ransa a ɓace yake tunda ya samu labarin Nihila ta sake aure ta ƙubuta daga hannunsa ya rasa duk wani ɗanɗanon bakinsa.
***
Bayan sun tafi ta sake yin wanka ita fa dama can Allah ya yi ta mai ƙaunar wanka a kai a kai shi yasa bata rabo da mura.
Tana neman nail quter a drower ɗinta ta zaro wani hoto ,ɗauko hoton tayi ta ƙare masa kallo ta sa hannu ta shafa hoton haushin kanta take ji idan ta ji Zuciyarta na tausayin shi ko tana tuna wasu abubuwa da suka wuce na daga rayuwarsu. Ta lashi leɓɓenta na ƙasa. Su huɗu ne a hoton ita da Abdullahi da Barra da Hafiz a ranar da suka kammala NCE ɗinsu. Ranar da suka zo taya su murnar kammala karatu lafiya tare suka zo da wani abokin su Idris shi ya ɗauki hoton bayan an kwana biyu kuma Abdullahi ya wanko hoton duk ya raba musu wai na tarihi. Ta maida hoton tare da sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna a kan gado wayarta ta zaro daga ƙasan fillo ta soma neman layin Barra ta tuna bata gaya mata an daura aurenta da Dr ba.
Bugu biyu uku bata ɗauka ba har ta ajiye wayar sai kira ya shigo koda ta duba sai ta ga Barran ce.
"Afuwa Bestie ba laifina bane ina tare da Hafiz ne ya hana ni sakat shi da Imani duk sun gajiyar dani ya aka yi?"
Sai da tayi murmushi sannan tace "To ki gama da su sai muyi waya da safe."
"A'a gaya min ya aka yi me ya faru tunda kika kirani akwai wani abu hakan nan ba za ki kirani ƙarfe goman dare ba bayan na san ba ɗabi'ar ki ba ce ba hakan."
Tayi mamakin jin wai goman dare.
"Wallahi ban duba lokaci ba da ba zan kira ba kiyi haƙuri kin ji."
"Wallahi da zan iya sa hannu ta cikin wayar nan da na mummuka miki mari Allah. Kuma kar ki sake ki ce min wancan banzan kike tunani."
"A'a Wallahi shekaran jiya fa aka ɗaura aurena da Dr.Azlan."
Wani ihu ta saka tace Ke da gaske ?"
"Allah."
"Alhamdu lillah! Allah na gode maka Allah na gode maka Allah ka saka alheri da albarka a wannan aure Allah ka tsone idon maƙiya ke yau kin yi mini kyakyawan albishir."
"Dalla sai ka ce baki taɓa ganin aurena ba."
"Ai yanzu kika yi aure ƙawata wancan ai cin zarafi ne ke zan lallaɓa Hafiz ya bari na zo Kano ko kwana biyu ne nayi."
"A'a ki bari sai zan tare sai ki zo ayi komai da ke."
"Shikenan. Amma kina son shi ko?"
Sai da ta yi ɗan jim ta kasa cewa komai Barra ta sake cewa "Wallahi in dai baki cire son wancan wawan daga ranki ba to ba zaki ci gaba ba a rayuwa kina nan za a bar ki a baya ke har wani abu ya yi saura a tsakaninki da shi ne? To ki shiga taitayin ki na gaya miki."
"Ba fa haka bane." Ta faɗa a sanyayye kanta a ƙasa.
"Ai na san halin ki ne yadda kika nuna masa wannan banzan son ne ya saka ya raina ki har ya miki cin kashin da yake so."
Ta cikin wayar ta ji maganar Hafiz yana tambayar ta ita da waye.
"Bestie ce fa wai an ɗaura auren ta shekaran jiya ka ji abin murna ko?"
Ya amshi wayar ya sa a kunne yana murmushi yace "Kai Ma sha Allah na ji daɗi yau nauyin da ya tokare min ƙirji ya sauka saboda kullum ina zargin kaina da zama dalilin da ya sa kika san Abdullahi da ace ranar bamu zo tare ba da ba za ki san shi har ya shiga rayuwar ki ba kiyi haƙuri ki yafe min don Allah ƙanwata."
"Haba don Allah Hafiz kullum muka yi waya sai ka faɗa min haka ba laifin ka ba ne ba fa kai ma da ka san haka ne ba zaka bari ayi ba kuma kayi iya yin ka haka Allah Ya tsara sai ya faru ni bana zargin kowa Wallahi don Allah ka daina wannan batun kana saka ni ina jin nauyin ka."
"Ai magana ta ƙare ƙawarmu tunda har kin samu sauyi ina yi miki fatan alheri kuma ina roƙon Allah Ya sa ku zauna lafiya Ya kawo zuri'a ɗayyaba."
"Amin Baban Imani na gode sai da safe."
"Allah Ya tashe mu lafiya."
"Amin."
"Ga shi kuyi sallama ki kawo min tea ɗin ɗaki."
"To. Ke sai da safe zan sake kiran ki mu tattauna."
"To sai da safe ki shafa min kan Imani."
"To." Ta kashe wayar.
Ajiyar zuciya ta sauke na salama da sukuni iya yar maganar da tayi da Barra ta ji sanyi a ranta. Ta yi sallah tayi ta rokon Allah zaman lafiya da Azlan da danginsa.
Tayi addu'a ta bi lafiya gado ba tare da ta kira Azlan ba kuma bai kirata ba cikin lokaci ƙanƙani bacci ya ɗauke ta.
***
Tafiyar ƙasaita take yi har ta isa gabansa tana murmushi hannunta ɗauke da glass cup da ruwa a ciki ta ci ado kamar zata gidan biki.
A hankali ta iso gabansa ta sa bakinta a daf da kunnen shi tace "Barka da tashi masoyin Nih...." Bai yi aune ba ya ji saukar ruwa a kan fuskar sa shaaa a firgice ya tashi ya zauna yana sauke numfashi.
Ya sa hannu ya yarfe ruwan yana ƙoƙarin saita kansa yana ɗaga kai ya ga Feenat tsaye a kansa da roba a hannunta.
"Ruwa kika watsa min?"
"Na watsa maka kuma zan ci gaba da watsa maka muddin za ka dinga ambatar mini sunan waccar matsiyaciyar sauran dauɗa."
"Nafisa dama baki da hankali ban sani ba?"
"Ai ba zaka sani ba Azlan a haukana ai baka ga komai ba yadda na shirya maka tashin hankali a kan Waccar matar baka ga komai ba Wallahi."
Gashin kansa na gaba da ya kwanto masa saboda ruwa ya maida baya ya saki tsaki ya sauko daga kan gadon kayan bacci ne a jikin shi wandon iya guiwa.
"Ki tafi gida Nafisa kina buƙatar a koya miki tarbiyya."
Ta saki guɗa tana tafa hannaye tace "Uban kuturu ma ya yi kaɗan na je ina ? Wacce tarbiyyar za a koya min? Ai abinda ya yi ka shi ya yi ni duk.muje a koya mana dai."
Ya kama ƙugu yana jin yadda zuciyarsa ke angiza shi ya yi mata mugun duka amma sai ya daure ya danne ɓacin ransa ya juya ya yi hanyar banɗaki kawai. Ta bi bayansa da tsaki ta juya tana dariya kawai sai ta yanke shawarar rufe ɗakin ta baya saboda ma kar ya fita ta haɗa da wayarsa ta yi waje. Ta san yana jimawa a wanka saboda haka a gurguje ta shirya ya ɗauki mukullin motar ta ta fice daga gidan.
A cikin mota kuwa ta dinga surutai "Wallahi yanzu na fara maka rashin mutunci Azlan har sai ka saki Waccar yarinyar mai kama da kazar mayu."
Bayan ya fito daga wankan ya shirya duk ransa a jagule. Ya zuba tsaki yafi kuɗin a ƙirga zuciyar duk ba daɗi. Ya nemi wayarsa ya rasa ya kuma yin tsaki ya nufi ƙofa amma jan duniya ƙofa taƙi buɗuwa ya ja ya kuma ja amma ina kofa tace buɗe ni ya koma da baya ya kama ƙugunsa cike da ɓacin ran Nafisa ya sani babu haufi ita ce daga shi sai ita ne a gidan kuma ya ji tashin motar ta kenan ma ta fita ta rufe shi a ɗaki ta ɗauke masa waya ta manta shi likita ne ko yaushe za a buƙace shi a asibiti bai taɓa tsintar kansa cikin ɓacin rai ba irin na yau. Tsakin da ya jera kuwa babu adadi. Ga yunwa yana ji ya koma kan gado ya zauna ya dafe kai da hannuwa biyu yana auna irin abinda zai yiwa Feenat ya samu salama a zuciyarsa. Bai ga mai hana shi ɗaukar mataki ba.
A ranar bata je banki ba gidansu ta tafi ta kira banki ta sanar bata da lafiya ba zata samu zuwa ba.
Amma na kan dinning suna break. Ta fara kallon agogon da ke manne da bango sanann ta hadiyi chips ɗin da take ci tace "Ke lafiya da farar safiya haka?"
"Lafiya Lau Amma zuwa nayi na yini yau."
"Aikin kuma fa?"
"Wallahi na gaji ina buƙatar na huta Amma."
"Zauna ki ci abinci."
"To Amma." Ta faɗa tana zama mai aikin Amma ta fito ta haɗa mata tea ta zuba mata chips da ƙwai da souce ɗin hanta. Tare suka yi break ɗin har Daddy ya sauko shi ma ya yi mamakin ganinta a wannan lokacin saboda ya san a ka'ida tana wurin aiki ne ba nan ba.
"Daddy kai ma tuhuma ta zaka yi dalilin zuwana?"
"Aikin fa?"
"Hutu ba karba Daddy ina son na huta."
"To.Ina doctor kwana biyu bai zo mun gaisa ba."
Ta taɓe baki sannan tace "Daddy ai ba zaka gan shi ba tunda ya auro dangin asiri sun tsafe shi."
"Har yanzu baki russuna ba kenan? Ke auran nan ni ne na daura shi ma ki haɗa dani mana na ga alama so kike yi ki raba mana zumunci."
Ta kyaɓe fuska tana son tayi kuka.
Amma tayi caraf tace "Kun kasa gane yarinyar nan duk laifinta kuke gani banda na Azlan ai an cuce ta da ƙuruciyarta aka mata kishiya kishiyar ma bazawara yar talakawa a nemo daidai standard ɗin ta mana."
"Wallahi kina bani mamaki a lokuta da dama Kina babba amma kullum cin ƙasa kike yi a maimakon ki nuna mata abinda take yi ba daidai bane sai kike sake hure mata kunne akan an mata ba daidai ba ko kunya ba kya ji ai abinda ya yi Azlan shi ya yi Nafisa jini ɗaya suke ba wai a banza aka ɗauko yan'uwantaka aka saka ba."
"A cikin ku waye ya yi aure sai shi ne zai zo mana da sabon salo."
"Don ba a muku ba sai aka ce ba za a yiwa ya'yan ku ba bana son son kai fa da rashin son gaskiya."
Ta zumɓuri baki tace "Hummm ayi dai mu gani."
"Allah Ya kyauta gaskiya ce ba kya so ke da yar ki. Amma ku sani in ma kuna shirin tada wata fitinar ne to ba a gidana ba saidai ku tafi can wani wurin kuyi don ba zan ɗauki kowanne irin Iskanci ba. "
Ƙaryawar da bai yi ba kenan ya tashi ya fice.
"Amma Wallahi ba zan yarda a cuce ni ba."
"Babu mai cutar ki kwantar da hankalin ki yadda na zauna ni kaɗai a gidana babu yata da zata fuskanci uƙuba can su ji da zumuncinsu."
"Ai baki ga yarinyar ba ma."
"Kin ji ko maza da kwashe-kwashe kuma Allah Ya rufa asiri."
"Amin Amma."
Cikin ƙanƙanin lokaci Azlan ya fita daga cikin hayyacinsa saboda yunwa da kuma bukatar shan maganinsa jininsa ya yi ƙasa baya gani sosai maƙogwaronsa ya bushe bai taɓa sanin kishi zai iya rufe mata idanu ta aikata masa wannan muguntar ba sai yau.
Jikinsa har rawa yake yi ya fara sarewa da lamarin sake rayuwa ma a yau ga shi ta tafi da wayar shi bare ya kira Rayyan ko Adil wata ƙila ma yau ce ranar shi ta ƙarshe a doron ƙasa.
Drawers ɗinsa ya dinga buɗewa ko zai ga chocolate ya sha ya samu suger level ɗinsa ya sauka amma babu ya manta a wancan ɗakin suke har magungunan sa. Ya dafa kai da hannu biyu ko ina na juya mai ya gama galaɓaita kawai jiri ya ɗebe shi ya faɗi ƙasa a hankali idanunsa suka soma lumshewa har suka rufe ruff.
***
Tun ƙarfe goma da ta ga ta kira shi bata samu ba ta shiga wasi-wasin ko lafiyarsa ƙalau saboda bai saba kaiwa wanann lokacin bai zo gaishe su ba. Har asibitin ta kira aka ce bai je ba kuma yana da wani case ana ta kiran wayarsa bata shiga nan fa hankalinta ya tashi saboda ba ya wasa da aikinsa yana ba shi muhimmanci sosai.
Adeel ta yanke shawarar kira a waya. Bai ɗaga wayar ba sai managarsa ta ji yana cewa "Ammi na iso."
Ta juya da sauri ta gyara zaman glasses ɗinta ta miƙe tace "Kira min Azlan a waya mana."
"Wallahi Ammi tun safe nake gwada layinsa amma baya shiga a kashe wayar na zaci ma ko yana nan ne"
"Bai zo ba kuma bai kirani ba na kira Shettima shi ma yace nemansa suka yi anya kuwa lafiyarsa ƙalau kuwa abin ya min wani banbarakwai."
"Gaskiya to akwai wani abu in har ba ya asibitin ma bari na kira Feenat na ji."
"Kirata ni na ma manta da ita hankalina baya nan."
Yana dariya yace "Kai Ammi Azlan fa ya zama babba ki dinga saukakawa kan ki da tunaninsa."
"Kune kuke ganin kamar kun girma amma mu a wurin mu har yau kune dai yaran da muka ɗauka a tsumma."
"To zauna bari na kirata."
Ta koma kan kujera ta zauna.
Ya kira layin Nafeesat sau uku amma bata ɗaga ba kuma tana gani tana Harara wayar.
"Yaya?"
"Bata ɗauka ba kuma tana shiga."
"Anya lafiyarsu ƙalau kuwa?"
"Ai shi ne."
"A'a muje gidan gaskiya ba lafiya na tun safe ban ji shi ba ga shi yanzu har azahar ta wuce kuma ita ma ta ƙi daga waya gaskiya ba lafiya ba."
"In fa tana aiki ne ? Kin san wannan aikin nata."
"Duk da haka."
"To bari na kira Nihila mu ji ko ta san inda mijinta yake."
"Kai kana da son jan magana."
"A gwada mana Ammi."
"Naji kirata."
Nihila ya soma kira bugu biyu ta daga wayar.
"Ina wuni Yaya Adeel."
"Ina gajiya amarya yaya kuke?"
"Lafiya ƙalau."
"Yayi kyau. Yau kuwa ina mijinki ina ta kiransa wayara ta ƙi shiga."
"Nima ban sani ba na kira shi nima ban same shi ba."
"To Shikenan bari na je asibiti ƙila ayyuka ne suka sha kansa nan ma Ammi ke nemansa."
"To ka gwada zuwa can ɗin."
"To shi kenan sai Anjima."
Ya ajiye waya. Da yake a handsfree ya saka Ammi ta ji komai tace "Kai ba lafiya ba muje gidan ko ba shi da lafiya bamu sani ba."
"To Ammi muje."
Suka tafi.
Suna fakin suka ga motar Azlan a fake a farfajiyar gidan.
"Na gaya maka bai fita ba don ba ɗabi'arsa ba ce ba.Ga motarsa nan."
"Haka ne Ammi akwai abinda ba daidai ba ne."
Ya taba ƙofa amma a kulle ya dinga zagaya har ya samu taga a bude ya shiga ta ciki.Dama ya san inda suke ajiye spare keys ɗin gidan ya budewa Ammi.
Ammi na shiga taga jakar aikinsa ta ɗauka tace "Ka ga jakarsa yana nan."
Tsoro ya fara mamaye su suka hau sama a tare.
Ita ma ƙofar ɗakin a kulle ya dinga bugu amma ba a buɗe ba. Ya ce da Ammi tayi baya ya saka iya ƙarfinsa wurin ɓalla ƙofar ɗakin.
Suna shiga suka tsaya cak ganin Azlan a yashe a ƙasa baya cikin hayyacinsa.Ammi ta saki kuka hannu a ƙirjinta.
Adeel ya sa hannu a kan ƙirjinsa ya kama hannunsa ya duba yace "Suma ya yi."
"Mu tafi asibiti Adeel."
Likitan ya cire stethoscope ɗinsa daga wuyan mara lafiyan tare da duba waɗanɗa suke kawo shi. Fuskokinsu cike da damuwa.
"Kada ku ji komai,babu wata matsala. Bp ɗinsa ne yayi love wanda yunwa da rashin cin abinci ta haddasa masa."
"Yunwa kuma?"Ammi ta tambaya tana kallon likitan.
Ya gyaɗa kai yace "Eh
.Jikinsa yayi week sosai. Amma yanzu ba wata matsala na saka masa ruwa da magunguna da suka dace ."
"To mun gode likita."
"Za ku iya jira a waje shaida yana buƙatar Hutu."
A hankali idanunsa suka fara motsi har ya buɗesu a hankali cike da kasala yace "Ammi."
Da sauri ta juya tace "Alhamdu lillah ya farka."
Likitan ya sake duba shi ya kuma mai tambayoyi ya amsa masa.
Suna zaune a falo suna shan fruit wayar Amma tayi ƙara ta dauka ta ga Ammi ce.
"Hello."
"Yaya Azlan ne jikinsa ya tashi muna asibiti amma ya farfaɗo ma."
Sai da ta ɗan taɓe baki sannan tace "Subahanallahi! Wanne asibitin?"
"Muna nan rijiyar Zaki."
"To bari na taho."
"Eh gaskiya."
Suka ajiye waya. Ta kalli Nafisa tace "Don ubanki dama Azlan ba shi da lafiya kika taho nan?"
Saida taji gabanta ya buga mata da ƙarfi sosai tayi kasake ta firgita wani irin tsoro ya kamata ba wai tsoron rufe shin da ta yi yayi sanadiyar kwantar da shi a asibiti ba a'a tsoro ta ɗaya kar ya tona mata asiri a ɗauki mataki a kanta musanmman ma Abbinsu. Wani gumi ta keto mata a goshi.
"Me zai faru idan aka gane ita ce ta kulle shi bai ci abinci ba bare ya sha maganinsa ba? Me zai faru idan ya faɗi gaskiya?"
Har ta hango kanta tsamo-tsamo a gaban hukuma ana tuhumar ta,ga iyayensa da wannan yan'uwan nasa da suke mugun son junansu ai reɗe ta zasu yi tas su ci mata uwa da uba.
"Ke ina magana kin tafi wani tunanin."
"Amma yaya jikin na shi?"
"Ance ya farfaɗo tashi mu tafi."
Ta sauke numfashi ba don samu ragin wani abu ko sassauci ba.
Cikin rawar murya tace "Ya Allah ka rufa mini asiri."
***
"Mama kin ji wai ashe Dakta ba lafiya yana asibiti ma a kwance."
Mama ta ajiye ledar hannunta na spices da take zubawa na order da za'a karba.
"Subahanallahi yaya jikin na sa ba dai wani abu ne sosai ba ko?"
"Eh da sauki tunda Yaya Adeel ya ce ya farka."
"To Alhamdu Lillahi sai ki shirya mu tafi ai."
"A'a Mama ki je dai." Ta faɗa tana kallon ƙasa
Maman tace "To mijina ne Nihila?"
Ta girgiza mata kai ta juya sai da ta sake kaya ta saka hijab ɗinta har ƙasa ta ɗauki jaka ta saka slifas ta fito.
Suna fita suka samu adaidaita sahu suka tafi.
Dakin cike yake da yan'gidansu kai kace wata shahararriyar ciwo yake yi. Yana sanye da singilet da canula a hannunsa ruwa na tafiya.
Ammi zaune a gefensa a kan kujera su Nuwaira duk sun cika ɗakin yayi yayi su fita sun ƙi.
A hankali ƙofar ɗakin ta buɗe lokacin Ammi na ba shi Ayaba a baki kamar wani ƙaramin yaro , ya ɗaga kai zuciyarsa ta buga kawai yana jin a jikinsa ita ce ilai kuwa bayan shigowar Mama ya hango ta cikin kyakkyawar shiga ya sauke ajiyar zuciya na salama.
Ammi ta gyara zamanta tace "Sannu da Zuwa Mama kune tafe?"
"Wallahi sannun mu Hajiya yaya mai jikin?"
"Da sauki Wallahi sosai ma kin gan shi."
"Mama Barka da yamma."
"Barkanmu ɗan nan yaya jikin naka?"
"Jiki da sauƙi sosai Mama."
Nihila tace "Ammi ina wuni,ya mai jikin?"
"Da sauki Nihila ya kike ? An taso ki ko?"
Bata ce komai ba.
Nuwaira ta bata wuri tace ta zauna.
Su Rayyan kuwa baibayeta suka yi sun manta da wani mara lafiya abin har kunya ya bata.
Azlan yace "Wannan ba halin kirki ba ne ku sake hali."
Suka yi dariya.
Mubeen yace "Wannan ce matar uncle tana da kyau kun ga wani abu a kumatun ta she puts on glasses like Ammi."
Aka sa dariya Ita dai ta kasa sakewa.
Mama kuwa zuciyarta kal ganin yadda ake nan-nan da ita sosai abin ya mata daɗi tana ji a jikinta sauki da walwala sun zo Nihila ita ma.
Shi dai kallonta yake yi a faƙaice ta burge shi musanmman da ta sako hijab ko ƙafarta ba a gani saboda tsayin hijab ɗin.