Chapter 4
by @khairatup01
GABA TAZO BAYA
Ummulkhair Sani Panisau
(Khairatup)
004
Amma ce ta fara shigowa cikin ɗakin. Sai Nafisa a bayanta jakarta saƙale a hannunta. Sai dai tana ganin Nihila tayi turus wani irin ɓacin rai ya ziyarce ta sai ta manta da ma wani Azlan ta zo dubawa.
Amma tace "Bayin Allah haka kuka cika asibitin nan kamar ku kaɗai ne masu jinya?"
Ammi ta murmusa yace "Ke na kya faɗa. Zauna mana." Ta matsa mata a kan sofa ɗin ta zauna.
Mama tace "Ina wuni Hajiya."
Bata waye ta ba kawai ta amsa "Lafiya lau. Wace ce wannan kuma?"
"Surukarmu ce maman Nihila ce."
"Wace ce haka kuma?"
Ammi taji ba dadi kafin ta bata amsa Nafisa ta rigata.
"Amma babbar wanan matsiyaciyar ce da ta aurar min miji ga ta can matsiyaciyar ma."
Amma tace "Au ho to ai shikenan Allah Ya wadaran naka ya lalace ko kunya ba kwa ji kun taho goɗai-goɗai da ku wai dubiya ba kunya ba tsoron Allah kai wannan abin kunya har ina."
Mama dai bata ce komai ba.
Nuwaira tace "Haba Amma don Allah me yasa kike yin haka don Allah?"
"Marin ki zanyi kika gaya min maganar banza, mara kunya dama na san ke kaɗai ce za ki sa baki ko uwarki bata isa ina magana tana yi ba sai ke yar yau."
Ammi tace "Nuwaira koma bana son haka fa kin sani."
Nihila dai ta soma wasa da yatsun hannunta.
Azlan kuwa ransa duk ya dagule ya so ya rufawa Nafisa asiri kuma sai ya fasa.
"Bani wayata Feenat."
Ta manta shafi da abinda ta aikata kishi ya rufe mata ido sai yanzu da yayi magana ta tuna.
Ta zare masa idanu alamar yayi haƙuri kar ya kawo maganar amma ina ya riga da ya shaƙa.
"Ki bani wayata da kika ɗauke min."
"Ban dauki wayar ka ba."
"Ammi ki gaya mata ma daga nan ta tafi gidansu don sai na hukunta ta akan abinda tayi mini."
Amma ta kama haɓa tace "To rasa kunya saboda an taɓa yar gwal da uwarta? To uban me tayi maka?"
"Ammi Nafisa bata da kunya bata da mutunci ta raina ni kuma kune kuka saka ta raina ni ba kwa son ku yi mata faɗa saboda ku kullum zancen ku na zumunci ne ita ce ƙarama shi yasa take min cin kashin da take so son ranta."
"Me tayi maka ne?"Ammi ta sake tambayar sa.
Komai ya kwashe ya gaya mata tas. Suka hau salati gabaɗayansu Sai jikin Amma ya yi la'asar ta kuwa zabga mata harara don bata gaya mata ta haɗa wannan gwaramar ba da ba zama ta yi wanann abin yanzu ba.
Sai ta ja bakin ta ta tsuke.
Nuwaira ce tace "Allah Ya sauwake." Haɗe da fuzge jakar hannunta wayarsa ta ɗauko mai ta kunna masa ta bashi. Ya ajiye a bedside drower gefen shi.
"Ai ban san za ka faɗi ba."
"Dama tunda baki da hankali ya za ayi ki sani tunda baki damu dani ba. Wallahi sai kin tafi gida kin ji ma na rantse."
Ta sa kuka "A gaban kishiya zaka ce min haka saboda baka sona."
Mama ta tashi ta kama hannun Nihila ta kalli Ammi tace "Hajiya mu zamu wuce Allah Ya ƙara sauƙi."
"A'a dawo Hajiya ki zauna ai duk an zama ɗaya."
"A'a don Allah dama da inda zamu je."
Haka dai suka fice.
Nafisa idanunta suka cika da hawaye.
"Babu inda zan je Wallahi ai nima gidana ne."
"Dama ina za ki je faɗe yake yi shi ma." Amma ta faɗa.
"Idan akwai kuɗin ki a cikin ginin gidan kar ki tafi ki ga yadda zan yi."
Ammi tace "Ka yi min shiru kai! Babu inda zata je in ita bata da hankali kaima baka da shi?"
"Ammi don Allah ki daina goyon bayanta da baku zo ba fa kila yanzu anyi shimfiɗa ana zaman makokina muguwar yarinya mai baƙin hali haka ake soyayar? Wallahi sai Nafisa ta tafi gida zan ma zauna nayi nazarin zamana da ita na gaji da fitsararta."
Amma tace "Kai ya ishe ni haka an gaya maka bata da gidan uba ne? Sai wani yen yen kake faɗe sai ta tafi sai ta tafi to sai meye waye kai ne ma ? Yarinya matar manya ta rufa maka asiri ta aure ka...."
"To ai sai na sakar miki ita ta auri manya." Ya faɗa a ƙufule.
"An zo wurin." Nuwaira ta faɗa.
Sai Amma ta ƙame tayi tsit ta san halinsa sarai zai iya sakin a gabanta.
Nafisa ta sa kuka "To kayi haƙuri don Allah ba zan sake ba wanann ba kishi ne ya rufe min ido."
"Na yi haƙurin amma sai kin tafi."
Ammi tace "Yanzu ban isa da kai ba Azlan?"
"Duk duniya ba sama da ke Ammi amma yau ɗaya ina son ki bari na yi aikina na miji."
Adeel ne yace"Haka ne Ammi kuyi haƙuri don Allah ya ɗauki mataki don Nafisa bata da hankali ya kamata ta gane abinda ta aikata ba daidai bane Azlan zai iya rasa ransa da bamu je ba."
Ta san gaskiya suke faɗe amma bata son ta saɓawa yar'uwarta.
Amma ta tashi a fusace ta kalli Ammi tace "Safiya kina ganin yadda ya'yanki suke min rashin kunya amma kin zaɓi kiyi shiru to baku isa ba Nafisa zata tafi kuma ba zata dawo ba har sai ka dawo da kan ka ka neme ta mara kunya mara mutunci kawai."
Ta kalli Nafisa tace "Ke wuce mu tafi."
Nafisa tayi sakare ta kasa motsi bata son tafiya ta kalle shi irin kallon roƙo amma ya ɗauke kai.Baƙinciki kamar ya kashe Amma ta daka mata tsawar da hatta Nasreen sai da ta firgita ta sa kuka.
"Zaki fita ko sai na ci miki?"
Dole ba yadda ta iya haka ta juya suka tafi.
Ammi ta kalle shi tace "Me yasa baka ji ne?"
"Ammi dole ne ta san muhimmancina wannan karon bata ganin girmana ku kan ku bata gani saboda Aunty Amma da take yi miki yadda take so saboda tana yayar ki."
"Bana son fitina Azlan."
"Don Allah Adeel ka bi Nihila ka bawa Mama hakuri don Allah duk na muzanta da abinda aka musu."
"A'a kyale su ai ba zan gansu ba kuma na san zasu fahimta ka kwantar da hankalin ka ita ma Feenat ɗin kishi ne ya rufe mata ido amma gaskiya yau abinda tayi ba abin a ɗuke kai bane."
Ɗakin yayi tsit.
Sai dare aka ba shi sallama ya so ya tafi gidansa amma Ammi tace sam a gidanta zai zauna sai ta ga ya warke sossai zai tafi tunda ya kori matar.
Aka saka dariya.Ita Nadiya ba anan take aure ba tana can South Africa can mijinta yake aiki so zuwanta sai shekara-shekara.
***
Kafin su isa gida ma an soma yayyafi lokaci ne na damuna dama. Basu yi zancen da Mama ba kowa ɗakinsa ya wuce daga nan.
A bakin taga ta tsaya tana kallon yadda ruwan sama ke sauka ta jikin tagar. Wasu abubuwa basa mutuwa a zuciya...sai dai kawai su jira lokacin da za su dawo.A hankali tunanin ta ya koma shekarun baya, ranar da komai na ta ya sauya.
***
Tana aji tana koyar da darasin turanci ɗaliba ce a lokacin a kwllijin ilimi ta jihar Kano wato Cas. Tana karantar fannin turanci da Hausa wato (Eng/Hau) a lokacin tana yin Teaching practice ɗin ta ne a nan GSSSKawaji ne ta mata a jikin babban massalacin dakata.
Su biyar aka tura makarantar daga mabanbanta departments wani na daukar Hausa ,wani na daukar Soscial studies ,wani na ɗaukar Arabic wani na daukar English. Wasu kuma ma yamma aka basu wato ɓarin Junior Secondry school su uku ne suke zuwa da safe da ita da Barra aminiyarta shaƙiƙiyarta abokiyar kuka da dariyar ta sai wani dan islamic ana kiransa da Habib. Cikin ƙanƙanin lokaci suka saba da malaman makarantar da ɗaliban saboda yadda suka iya sakin fuska.
Bayan ta gama period ɗinta sai ta ji tana jin yunwa ta kalli Barra tace"Taso muje mu samo abinci ko a kasuwa ne yau yunwa nake ji ban karya ba kuma ban shigo gidanku ba na san da zan sha ko tea ne."
Barran ta kalle ta tace "Ba zaki siya awara ba ko a gun masu tallan nan ba kasuwa fa sai mun ɗan yi yar tafiya kar muje a zo bama nan."
Ta kalle ta tace "Kuma fa haka ne don na ji sauran suna cewa an jajje duba su."
"Eh."
"Tashi muje to mu siyi awarar."
Suna fita suka haɗu da wani malami Malam Yahaya yace "Ina zuwa malamai?"
"Awara zamu siyo."
"Da kan ku ba zaku aika yara ba?"
"A'a ai duk suna karyawa ne nan da nan ai ba sai mun kira wani ba."
"A'a ku kawo zan siyo na kawo muku staff room ku koma."
"Ayi haka kuwa Malam."
"An ma yi." Ya amsa ya juya su ma suka koma.
Suna shan kwanar da zata maida su can Staff room ɗin kamar an jefo Malam Isiyaku kawai yace "Menene ma'anar barkonon tsohuwa da turanci."
Aka koma kallon-kallo tsakanin Barra da Nihila.
Sai kuwa ya saka dariya ganin duk sun zama serious suna son tunawa.
"Wasa nake muku."
Barra tace"Allah Ya kyauta maka." Haɗe da jan hannun Nihila suka koma staff room suna dariyar Malam. Ba a jima ba aka kawo musu awara da yawa harda kunun aya.
Barra tayi dariya tace Kamar fa malamin nan son ki yake wai harda kunun aya."
Haka suka gama aka tashi suna hanya takalmin Nihila ya tsinke.
Barra tace"Ji don Allah wani iskanci tuni bai tsinke ba sai yanzu da aka tashi don wulaƙancin takalmi?"
Nihila tace "Wallahi Allah kuwa ,yanzu ina zan samu mai gyaran takalmi?"
Suka soma hahangawa.
Nihila ta ɗaka mata duka a baya "Ke yanzu baki ji kunya ba ke da unguwarku amma ba ki san inda ake gyaran takalmi ba."
"In na nuna miki in zama ƙuli-ƙuli."
"Ai kin san ba zaki zama ba."
Suka shiga wani layi na jikin katangar makarantar daga hannun hagunsu.
Basu yi nisa ba wata mota na bin su fara ce motar da farko sun zaci sun tare hanya ne sai suka yi gefe sosai suka tsaya don ya wuce ga mamakinsu sai ya tsaya ya suke gilashin motar su biyu ne a ciki.
Ɗayan ya leƙo da kan shi yace "Ina zaku je haka yan'mata?"
Barra ce ta zumɓuri baki da yake tana da masifa sukan ce mata Aunty ma a wasu lokutan ma'anan Aunty Masifa akwai wani abokin karatun su da ya saka mata sunan.
"Ina ruwan ka kai dai ka wuce malam."
Dayan yace "Haba ke kuwa ko dai sunan ki Fatima?"
"Ban sani ba."tace masa.
Nihila kuwa tayi murmushi tace "Kuyi haƙuri yunwa take ji daga makaranta muke."
"Allah Ya isana Nihila." Ta faɗa tana dukan bayanta gaba daya sai suka saka dariya.
Mai tuƙin yace "Kuyi haƙuri mun tsaida ku a titi mu ma shigewa zamu yi kuma sai na ga ya dace na san su waye ku saboda ɗaya daga cikin ku tayi min sata."
Hankalinsu ya tashi suka soma rantse-ransten basu ma san su ba bare su musu sata.
Nihila uwar tsoro tace "Don Allah kuyi haƙuru bamu ma san ku ba me muka sace muku?"
Yayi dariya yace "Ke ce ma kika yi min satar tunda ga baya na hange ki sai na ji kin burge ni har mun wuce na ga ba zan bari ki ƙubuce min ba sai na yo you-turn na biyo ku sunana Sadik wannan kuma Abokina ne sunan shi Chiroma na ga iri kuma ina so ko nace a dawo min da zuciyata."
Barra tace "Amma gaskiya ya shiga hakkin mu bawan Allah da gaske mun zaci satar muka yi maka."
Wanda aka kira da Chiroma yayi dariya yace "Ku shigo ciki sai mu sauke ku na ga kamar takalmin ku ya tsinke sai a siyi wani a hanya."
Suka kalli juna kamar ba sa son su shiga.
Sadik yace "Don Allah ku shiga Wallahi ba zamu cutar da ku ba ina zaku je?"
"Makaranta zamu koma cas."
"To shi kenan ku shigo ku yarda da mu."
Cikin motar suka shiga gidan bayan yayi reverse ya juya suka fita daga layin.
"Ya sunan ki?"
A hankali tace "Nihila."
"Kai nice name sunan yayi daɗi amma mene ainihin sunan?"
"Khadija."
"Ma sha Allah! Ni kuma suna na Sadik."
"Ya yi kyau." Ta faɗa cikin rashin sabo.
Abokin nasa yace "Ni kuma sunana Aminu na ga ba wanda ya tambayi suna na ke kuma Fatima ya sunan ki?" Sai da ta zabga masa harara sannan tace"Barra'a ana ce min. Barra."
"Kai an iya saka sunaye kai Ma sha Allah amma dai da an sani Fati aka saka miki." Da alamu dai shi matsokani ne don har suka sauke su tsokanar Barra yake tun tana kula shi har ta haƙura ta rabu da shi. Da suka sauka Sadik yace "Ki bani lambar taki mana." Ya faɗa yana langwaɓar da kai.
Babu yadda ta iya haka ta ba shi lambar wayar.
"Kema ki bani taki mana kin ga anyi tuwona Maina."
"Bani da waya." Ta faɗa tana yin gaba. Nihila tayi dariya tace "Zan baka lambar ta."
Ta bashi lambar yayi godiya sai da suka tafi ta juya zata koma ciki sai ta tuna da takalminta ya lalace. Sanyin mota da hira ta saka ta manta da wannan matsalar ga shi Barra tayi shigowar ta kawai sai ta yanke hukuncin ɗaukar takalmin a hannun ta kawai sai ta ga wani dan ajin su Abubakar da sauri tace "Zo! Zo! Zo nan , zo don Allah ka bani aron takalmin ka kafin mu shiga na bawa Baba ya gyara min."
"Toh ai ke tawa ce muje." Ya zare takalmansa ya bata ya shiga ta ɓarin maza ita kuma ta bi ta ɓarin mata.
"Ai na zata a can za ki kwana."
"Ke dai ki rage fushi dalla."
"Zage ni saboda kin yi saurayi."
"Hhh ke kam Allah Ya shirye ki muje a gyara min takalmin."
Suna zuwa gun Baba ba tare da ɓata lokaci ba ya gyara mata takalmin.
"Ke kam wannan Sadik ɗin ba shi da hayaniya kin huta amma wannan abokin nasa kamar ya ari bakin aku."
"Ke dai bari ai na bashi lambar wayar ki."
Ta saki salati tana tafa hannaye har ana juyowa ana kallonmu.
"La'ilahaillallahu-Muhammadar-rasulillahi Sallallahu alaihi Wasallama na shiga uku ni jikar mutum huɗu ki ka ba shi lambar wayata?"
"Ke dalla me haka kin sa ana kallonmu."
"Da gaske kike kin bashi lamba ta?"
"Wallahi na ba shi.Tausayi ya bani na ga yana son ki ne."
Kafin ta sake magana kuwa wayarta tayi ƙara ta ɗauka.
"Salamu alaikum."
"Kece likitar zuciya da ke dubata..."
"Na bani kin cuce ni Nihila kin ga ni ko Wallahi shi ne."
Ta cikin wayar ta ji yana dariya sosai kawai sai ta katse wayar ta dage ta sa hannu ta rankwashar mata tsakiyar kai.
"Wayyo Allahna! Da zafi fa Barrat."
"Kullum sai na miki ɗaya duk ran da ya sake kirana a kan ki zan huce."
Yankan farce take yi a tsakar gidansu. Mama na kitchen tana dafawa Alhaji shayi baya shan shayin kowa sai na Mama. A lokacin magariba tayi wayata na ƙara a ɗaki yar gidan Uwani Hafiza ta kawo mata wayar.
"Aunty Nihila ana kiran ki tun ɗazu."
Ta amshi wayar tace "Na gode ina jin ta amma gandar tashi nake yi shi yasa ban ɗauko ba" bata sake cewa komai ba kiran ya sake shigowa. Ta ɗaga da sauri ganin baƙuwar lamba ce.
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaikum Salam Gimbiyar mata ai na ɗauka ba za a ɗaga wayata ba har na fara jin kamar zan yi kuka."
Ta kalli wayar ta maida kunnen ta cike da rashin sanin mai magana tace da shi "Waye don Allah anya ni kake nema sunan Nihila Abdurrahman ba Gimbiya ba."
Ta bashi dariya kwarai kuma sai da ya dara sosai har ya saka ta tsargu ta tsani dariya kawai sai tayi tsaki ta yanke shawarar yanke kiran.
"Kar ki katse don Allah maganar ki ce ta bani dariya Wallahi ai na san ba sunan ki bane ni ne nan na baki sunan."
"To waye ne?"
"Sunan Sadik ɗazu muka haɗu dake a Dakata kin tuna?" Ya ja kalmar kin tuna ɗin sosai.
"Lah! Kai ne? Ya kaje gida ina abokin ka?"
"Ni ne. Abokina yana gida ya shiga cin abinci ni kuma ina bakin massalaci nace bari na kira ki na ji."
"Ka kyauta kuwa. Mun gode fa ɗazu."
"Me abin godiya ai duk yiwa kai ne."
"Haka ne."
Sai suka yi shiru ku san sakan biyar sai kuma yace "Ki min kwatancen gidanku zan zo in anyi isha'i."
"Kai! Ba za a bari na fito bayan isha'i ba Abbanmu baya bari gaskiya."
"Wayyo! Ban sani ba kin da tun ɗazu na zo na gan ki ba zan iya bacci ban gan ki ba."
"Kai haba dai da fa taya kake baccin in baka gan ni ba."
"Da ai ban san ki ba yanzu kuwa na san ki."
"Sai dai ka bari sai gobe ka zo tunda yau ta ƙure in aka yi magariba sai ka zo ko?"
"To Allah Ya kaimu goben bari na bar ki haka zan kira ki anjima."
"To na gode mu jima lafiya."
Suka ajiye waya.
Cike da farinciki ta tashi daga kan kujerar ta shiga ɗakinsu. Nan ta tarar da kaya a kan gado ko ba a faɗa ba Aunty Karima ta zo in dai zata zo to fa za ta hargigsa ɗakin kuma ba wani abu ta ajiye a ciki ba fa kawai neman magana ne.
Ana idar da sallar isha ta kira Barra a waya.
"Ƙawata mutumin nan ya kira ni fa ɗazu ina ta son na gaya miki."
"Shi ne kike ta wanann tsallen?"
"Ke banziya ba a rana news da ke."
"Ai ke ce kun zaƙe baki san shi ba kawai sai rawar kai kike yi kuma dai na san baki da rawar kai."
Sai ta ji jikinta ya yi sanyi tayi shiru kawai.
Barra ta gane kamar bata ji daɗin abinda ta mata ba sai ta ce da ita"Haushi kika ji wai? Ba gwale ki nayi ba kawai bai min ba ne ban yarda da shi ba amma dai ki kula koma dai menene."
"Shi kenan na gode. Ya goben zamu je?"
"Wallahi na gaji amma in za a bar ki sai na shirya muje."
To Allah Ya kaimu. Ni fa sai dai ma nace gidan Aunty Karima zan je don gobe Abba Alhaji yana nan ba zai bari na fita ba da baya nan ne ma da sauƙi Mama ba zata hana ba."
"To shi kenan. Ki gaishe da Mama."
"Zata ji kice wa Ummi ina gaida ta."
"In Allah Ya yarda za ta ji ɗazu take zancen ki daman."
"Allah sarki Umminmu."
Basu sake yin waya ba sai washegari ,a washegarin ma da yamma kawai ya ce mata ta fito yana ƙofar gidansu daidai inda ta faɗa a nan ya tsaya da farko ta zaci wasa yake yi sai tace da shi "Haba dai wani irin ka zo?"
"Da gaske nake miki ga gate ɗin ku baƙi a ƙofar gidan akwai tuƙa-tuƙa ga massalaci ma a gefe, ga wani shago na caji."
Ta saki baki da gaske ya zo kuwa a hankali tace da shi "Ina zuwa gani nan."
"To."
Sumi-sumi ta samu Mama tana wasa da hannu cike da fargaba tace da Maman.
"Uhm erm Mama dama... daman."
Mama na ɗinki tace "Ya aka yi kike kame-kame?"
"Baƙo nayi a waje ina zuwa."
Mama ta dakata da ɗinkin ta juya ta kalle ta ba don ta aikata laifi ba sai don bata saba ba, bata saba jin hakan daga gare ta ba.
"Me kika ce?"
"Ina zuwa nayi baƙo a waje."
"To shi kenan ku shigo haraba ban san tsayuwa a waje."
"Tam Mama."
Ta koma ta saka hijabinta ta ɗan fesa turarenta mai sanyin ƙamahi ta shafa vasline a bakinta sannan ta fito. Kalar ta ba mai haske bane amma tayi kyau.
"Ki kula dai."
"To Mama."
Ta fita da kanta ta buɗe ƙofar gate ta fita farar motarsa ta ci karo da ita yana cikin motar amma ya zuge glass ɗin motar. Tun kan ta ƙaraso yake murmushi na gefensa a hankali yace "Kai kuma usatzziya ka kwaso."
Sadik ɗin yayi dariya suka tafa daidai lokacin ta ƙarasa wurinsu tana murmushi tace da shi "Sannu da zuwa, ban zata da gaske kake ba fa."
"Gani nan ai zato ya ƙare."
"Sannunku. Ku shigo ciki mana."
"A'a ai nan ma ya isa kema shigowa za ki yi."
Ta ware idanu tace "Ina?"
"Cikin motar mana baki ga akwai rana ba?"
"Hhh! Ba wani rana ai yamma tayi ba zan shiga ba gaskiya."
"Amma jiya kika shiga?"
"Jiya ai muna da yawa bani kaɗai bace."
"Yanzu ma ni da ke ne da abokina."
"A'a gaskiya yanzu ma sai da Mama ta min kashedi ku shigo harbar gidanmu."
Sai ta ga sun kalli junansu sun yi dariya.
Abokin nasa yace "Kai maza anya kuwa zamu kuwa?"
"Gaskiya dai dole a sake duba harkar."
"Ai tunda na ga yanayin na san ba hannunka bace."
"Babu wai."
"Kun yi shiru?"
"Aa ki bari kawai ai na ga gidan zan dawo akwai inda zan kai shi."
Sai guiwarta tayi sanyi amma sai ta dake tace "Shikenan na gode sosai."
"Muke da godiya."
Ya ja mota suka tafi.
Kamar wadda kaza ta fashewa a ciki haka ta koma cikin gida da annurin da ta fita ba da shi ta dawo ba.