GABA TA ZO BAYA

Chapter 5

by @khairatup01

GABA TAZO BAYA
Ummulkhair S Panisau 
(Khairatup)
005

Bai sake kiranta ba ita ma bata a ka ba sai ta watsar da shi amma Barra ta gaya mata suna waya da Hafiz sosai har yaje ma gidansu sun sha hira. 

Kwana biyu tayi tana zazzaɓi bata zuwa tp ɗin amma da ta ga ta ji dama sai ta shirya Yaya Jamilu ya kai ta har bakin makaranta bata dari biyar a lokacin komai da sauƙi kuɗin mota ma daga unguwarsu zuwa Dakata Naira ɗari ce.
Bayan ta shiga ta sa hannu aka dinga mata ya jiki tana amsawa abu guda ne a lokacin ya takura mata wani ƙurji da ya fito mata a kan hanci ya tari ruwa ya yi girma sai zugi yake yi mata.
Bayan an fito tara ne suka fito don ganin yan makaranta. 
Wayar Barra tayi ƙara vivo ce ita kuma a lokacin wata ƙaramar Tecno ce a hannunta.
"Da gaske kana waje?" Taji tana faɗa.
"To gamu nan bari mu fito."
Ta kalle ta "Zo muje waje kin ga wai Hafiz ne ya zo zai wuce aiki yace bari mu gaisa."
"Kayya dama ke kaɗai kika je Wallahi hancina ciwo bana son a dinga ganina da shi."
"Don Allah muje." Ta ja hannunta suka fita tare.
Suna fita daga gate ɗin daga tsallake suka hangosu a jikin mota su biyu sai murmushi Hafiz Chiroma yake tayi.
Barra ta ja hannunta suka tsallaka.
Layin suka shiga suka tsaya.
A hankali Nihila tace "Ina kwana Chiroma?"
"Ina gajiya ƙawarmu."
"Ya kake?"
"Lafiya Lau,ya jikin naki,Masoyiya ta ce baki jidaɗin jikin ki ba kwana biyu?"
"Eh Wallahi da sauƙi amma." Ta kalli dogo ne ba shi da haske sosai amma ba za a kira shi da baƙi ba. 
"Ina kwana?" Ya juyo a hankali yace "Lafiya Lau." Sai ya juyar da kansa ya cigaba da game ɗinsa.
Muka cigaba da hira mu uku. Zugin nan ya ishe ni so nake na fasa shi amma Barra ta hanani tace na bari zai fashe da kansa kar na sa ya kuma tara wani ruwan kama ita kuwa ji take kamar tayi kuka saboda ciwo.
Chiroma ya kalli abokin nasa yace "Abdullahi ka ga yarinyar da nake gaya maka Sadik yace yana so ashe shegen ba haka bane."
Sai ya juyo da sauri ya kalle ta sannan ya ce "Hmm!" Kawai.
Chiroma yace "Kai dalla daɗina da kai baka da hali."
"To me zan ce ai na taya ta murna daman ina ita ina wannan mara mutuncin gara da kuka rabu ke ba mutumin kirki ba ne."
Duk da ta ji faduwar gaba amma haka ta daure ta kalli Barra tace "Na koma ciki sai kin taho."
"Ki jirani don Allah.'
"A'a." Bata kai ga juyawa ba hancinta ya fara jini alamun ya fashe jini sosai ke zuba zata sa hannu ta tare Abdullahi ya zaro tissue daga cikin mota ya bata ta goge.
Ya ga jinin dai bai tsaya ba kawai sai ya dauko kwallin gabaɗaya ya matsa kusa da ita kamar  zai taɓa hancin ya matse mata da kansa sai tayi baya cikin rashin sabo. Ya ɗage hannayensa biyu sama yace "Calm down babu abinda zan yi miki." Ya kuma warware mata tissue ya bata ta goge daga ƙarshe Barra ce ta matse mata har kuka sai da tayi ta manna wani a kai.
Chiroma yace "Ku koma ciki,ta huta, sannu ƙawarmu."
Kai kawai ta iya gyaɗa masa saboda azabar da take ji a tsakar kanta.
Wanda aka kira da Abdullahi yace "Sannu ki shafa robb."
Sai da ta murmusa point ɗinta ya shige ciki sannan tace "To in na koma gida a nan bani da shi."
Daga haka suka tsallaka suka koma ciki. Barra duk ta damu da yanayin da ƙawarta ta shiga ciki.
Ba ayi minti ashirin ba Chiroma ya sake kiran Barra yace "Ki bawa Nihila wayar." Ta miƙa mata wayar ta amsa.
"Hafiz."
"Ba shi ba ne Abdullahi ne."
"Salamu alaikum."
"Wa'alaikum Salam, yaya jikin naki?"
"Ƙurji ne fa kawai."
"Kin raina shi ne?"
"A'a."
"To ya ƙurjin?"
"Da sauƙi."
"Sannu ,ki aiko ƙawarki ta zo ta amsar miki magani."
"To." Ta faɗa a mamankace ta bawa Barra waya.
"Ga shi."
Ta sa a kunne kawai dai taji tace "To gani nan."
Ta fita jim kaɗan ta dawo da leda a hannu tana buɗewa ta ga robb da wani magani da ruwan roba.
"Ke ko dai wannan son ki yake?"
"Ke komai so, tausayi na na ba shi kawai."
"Ke sun tafi fa suka dawo."
"Na sani."
"Shi kenan ma ji ma gani in tayi wari ma ji."
"Ke kika sani."
Da dadddare tana kwance a ɗaki saboda ciwon kai wayarta ta soma vibrating ta zarota daga ƙasan filo sai ta ga baƙuwar lamba ce haka ya saka tayi tsaki ta maida wayar amma ba a daina kira ba dole ƙanwar naƙi a fusace ta ɗaga kiran.
"Wai waye?"
"Abdullahi!"
Sai tayi shiru kamar anyi ruwa an shanye ta kasa cewa komai. 
"Yaya kike ya jikin naki ƙurjin ya daina ciwo ko?"
"Eh da sauki."
"Ƙawar ce ta bani lambar ki ba sata nayi ba." Ya faɗa yana murmushi har tana jin sautin murmushin nasa.
"Ba komai na gode fa da maganin ɗazu."
"Ba komai. Bari na kyale ki ki huta ko?"
"Eh na gode sosai."
"Ba damuwa sai da safe."
"Allah Ya tashe mu lafiya."
"Amin."
Daga ranar ne komai ya sauya wa Nihila da Abdullahi. A hankali suka fara shaƙuwa da juna kullum sai kirata safe rana dare abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba hatta Mama ta san da zaman Abdullahi.
Wani lokacin idan zai tafi aiki sai ya bi ta gidansu kawai don ya gan ta ko basu yi magana ba zai daga mata hannu a kan mashine ɗinsa sai ya wuce. 
Kowa ya san da zaman Abdullahi hatta Abba Alhaji.
Can ma tsakanin Hafiz da Barra suna soyayya don shi har ma iyaye sun shiga cikin maganar suna gama karatu za ayi biki.
Abdullahi su biyu ne maza a gidansu sauran duk mata ne sai dai shi Yayan na shi Faisal ba shi da lafiya irin autistic ɗin nan ne sai ya zamana komai na gidan shi ne yake yi tunda mahaifinsu ya rasu da jimawa. Mahaifiyarsa na son sa sosai a cikin ya'yanta kowa ma ya sani kuma yana da biyayya duk abinda take so yana ƙoƙarin ya kiyaye shi, bashi da yawan magana sosai amma yana da saurin fushi watakila shi yasa yake janye jikinsa daga cikin mutane ba kasafai zaka gan shi ko a cikin abokansa ba mafaɗaci ne abu kaɗan ke sa shi ya hau kuma duk girman ka sai ya wanke ka tas.
Gidansu ba wani babban gida bane sosai amma babu laifi. Mahaifiyarsa ta sha gaya masa a nan zai zauna tare da ita da yan'uwansa haka ya saka wani sashi na gidan ta ba shi aka gine masa shi dakuna biyu ne a ciki da banɗaki amma kitchen ɗin yana waje ne ainihin na gidan.
Hankalinta bai tashi ba sai da yace mata ya samu wadda yake so ita ta so ya auri wata yarinya nan bayan layinsu sunanta Sameera mahaifinta mai kuɗi ne mahaifiyarta ƙawarta ce sosai sai dai ta ga yana masifar son ita Nihilar kuma ya gaya mata shi ita zai aura. Wannan lissafin bat taɓa kawo shi kusa ba tayi zaton yadda yake son abinda take so ba zai mata jayayya da auren Sameera ba.
"Yanzu so kake na zama dattijuwar banza ko me? Na riga na amsawa uwar yar nan zaka aure ta sai kawai yanzu su ji wai ka tafi ka auro wata?"
"Umma don Allah ki daina maganar nan ina son ta ne da bana son ta ba zan ce ina son na aure ta ba. Kiyi hakuri daga baya idan hali ya bani dama sai na auri Sameerar."
Sai da ta watsa masa harara sannan tace "Ana maganar yar mai kuɗi kai kana maganar yar yaku bayi irin mu masu rufin asiri. Ka ga tun wuri ma na gaya maka bana son yarinyar nan da kake son jajiɓo mana."
"Wallahi Umma yarinyar kwarai ce kuma na san za ki sota idan arziƙi ne in Allah zai iya bani a haka ina nema."
"Mtsw! Ka kalli yan'uwanka kuwa duk mata? Wa zai musu in ba kai ɗin ba? Shi wancan ga shi nan dai shi ne babba amma ba shi da amfani ba shi da lafiyar da zai ɗauki nauyin mu yadda kake nuna son yarinyar nan tsab zaka iya zubar damu ka kama ta mu kuma ban da kai waye gatanmu?"
"Haba Umma, taya za ayi ki ce zan zubar daku saboda mace ai kema kin san bani da kamar ku ina son ku."
"Tunda ka dage shi kenan zan yiwa Kawun na ku magana sai aji yaya za ayi."
"Yauwa Ummata ko ke fa."
Bata ce masa komai ba dai ta bi shi da ido. Hakan nan yarinyar bata yi mata ba kuma bata taɓa ganinta ba bata san ta ba amma ba ta son tarayyarta da Abdullahi ba don komai ba sai don bata san yar talakawa tana son ya'yanta duk su auri mau kuɗi mace ce mai dogon buri a rayuwarta gata da masifa waɗanda suka yi kishi da ita ma sun bar mata gidan ita kaɗai ta mulki gidan har mijinta ya rasu duk wadda ta shigo sai ta fita saboda makirci da iya tsarinta. Idan baka san Umma ba tsab zata kai ka ta baro ka.
A cikin kar ya'yanta babu mai mata biyayya sama da Abdullahi komai ya samo ita yake kaiwa ko yake fara sanarwa tsoron da take yi kar ya je ya tare a gindin mace yadda taga yana son yarinyar har tsoro take ji kar a ƙwace mata ɗa shi yasa take son ta aura masa wadda ta sani wadda zata iya juyawa. So take yi ta ci gaba da riƙe shi kamar yanzu.
***

"Yaushe kika je kika yi lalle?"
"Dazu na je."
"Amma lallen na meye?"
"Ka manta biki zamu yi?"
Ya ɓata rai ya sosa hancinsa yace "Ba ma ni kika yiwa ba kenan?"
"Hadda kai mana."
"A'a biki zaku yi shi yasa kika yi dai."
"To zan yi maka naka in ya fita."
"Ke kika sani dai. Bani wayar ki."
Ba musu ta ɗauki wayar ta ba shi ya soma bincikensa yadda ya saba da ya gama ya saka game yana bugawa. Sai cicin magani yake yi yaki sakewa suyi hira yadda suka saba wanann halin nasa ne bata so sam.
Yana buga game aka kirata a waya bai miƙa mata ba sai ya ɗaga kiran Muryar namiji ya ji. A fusace ya miƙa mata wayar "Wani ƙato yana kiran ki."
Jiki a sanyayye ta karɓi wayar ta saka a kunne ita ɗin ma bata gane lambar ba ga shi a tsorace take kar ta ɓata masa rai shi yasa ma bata ɗauki murya ba.
"Hello."
"Nihila ki fito ki amshi ankon na ki an gama ɗinkin." Sai a lokacin ta sauke ajiyar zuciya ta kashe wayar tace "Ina zuwa bari na amso kayana na biki."
Bai ce mata uffan ba sai gayɗa kai kawai yake yi kamar wani ƙadangare. Ta tashi ta fita wajen a kan babur ta ga Hamisu ƙanin mijin Aunty Karima ne shi yake yi mata ɗinki dama.
"Hamisu sai yanzu?"
"Kiyi haƙuri makaranta ce ta saka ni a gaba da ƙyar nayi miki ma fa."
"Na gode hakan ma ai ka fitar dani kunya tunda ka ɗinkan har ka kawo min."
Tana karɓar ledar Abdullahi ya fito daga gidan rai a haɗe kallo bata ishe shi ba kawai yayi gaba har Hamisu na masa sallama bai amsa ba. Dariyar yaƙe tayi tace "Bai ji ka ba."
Ba don ya karɓi zancen ba yace "To ni sai Anjima."
"Shikenan."
Ciki ta koma jiki a salube haushi ya ji don ta fita kuma ai ya san shi kadai take kulawa amma kullum kishinsa sake yin gaba yake yi. Wayarta ta fito da ita daga cikin skirt ɗin da ta soke wayar ta kira shi amma fafur ya ki ɗaga wayar. Duniyar Allah bata son ɓacin ran Abdullahi sam-sam bata son abinda zai saka ya yi fushi da ita wani irin so take yi masa wanda kowa ma ya san tana shakkar  ɓata masa rai abu kamar asiri ko hanata abu ya yi bata yi saboda tsoronsa da take yi da wannan yayi amfani yake yin yadda yake so da al'amuranta har ta kai idan zata unguwa sai ta kira sa ta gaya masa in kuma ya hanata ta hanu ko da waye kuwa. 
Kafin wayewar gari ta jera masa kira ya kai sau ashirin har sai da ya dinga yankewa it Kuma bata haƙura ba sai da wayarta ta gargaɗeta da low battery shutdown tayi sauri ta saka wayar a caji tana tauna farce a nan gaban wayar tayi zamanta jiki na rawa tana gadin waya tayi caji har bacci yayi awon gaba da ita.
Bata farka ba sai da ta ji kiran assalatu. In dai ibada ce bata wasa da ita sallar asuba bata wuce ta kwata-kwata sai dai idan da ciwo,shi ma a ɗaɗafe take yi.  Yanzun ma da ta idar da Sallah sai ta samu kanta da rokon Allah Ya saka Abdullahi ya kirata kuma ya yafe mata daga ƙarshe Kuma ta saki kuka a cikin tafukan hannunta. 
Ta kan tambayi kanta me yasa take son sa sosai haka? Me yasa bata iya yi masa musu? Me yasa bata iya bijire masa ko duk son ne ta kan zagi so ta kuma yi Allah wadai da irin son da take yi masa amma ta kasa dainawa ta kasa haƙura da shi. Son sa take yi da zuciya ɗaya kuma bata ƙaunar ta ga ta ɓata masa rai.
Yinin ranar dai kamar mara lafiya haka ta yini har sai da Mama ta gane akwai matsala kuma ba zai wuce ita da Abdullahi bane.
"Rayuwar da kika zaɓa wa kan ki kenan ke Nihila?"
"Mama me ya faru?"
"Ke Shikenan akan saurayi duk sai ki fita daga hayyacin ki kiyi ta ciwo saboda shi ?"
"Kai Mama me kika gani?"
"Tunda kika shigo jiya na lura da yanayin ki ai kuma na san shi ne yazo faɗan kuka sake yi kenan?"
Ta girgiza mata kai tace "A'a Mama ba faɗa muka yi ba kawai bana jindaɗin jikina ne."
"Ai shi kenan koma dai menene dai ki shiga hankalin ki bana son asara saboda namiji."
"To Mama."
"Ki tashi ki je ki sako hijabin ki na aike ki gidan Yaya Uwa."
Saida gabanta ya faɗi jin aike ta za ayi ga shi ya hana ta fita ko nan da can.
"Ko ba za ki ba ne?" Ta ji muryar Mama na tambayar ta. 
"A'a bari na ɗauko."
Ta tashi ta shiga cikin ɗakinta ta ɗauko hijabinta har ƙasa ta saka wata baƙar safa ta ɗauko face mask ta saka.
Mama ta kare mata kallo sannan tace "Kai ,Allah Ya sauwake miki."
Bata ce komai ba dai ta amshi saƙon ta fita. Mama ta bita da kallon taƙaici. 
Tana tafe tana sake kiran layinsa amma bai daga ba daga baya ma sai ta ji haushi ta ƙyale shi ta shiga adaidaita sahu tayi tafiyar ta daga  can ma sai ta yi zamanta suka yi ta hira sai la'asar lis ta koma gida.
 Har aka gama bikin bai kirata ba kuma bai je ba ita ma bata sake kiransa ba saboda ta ji haushi abinda ya mata.
Wasa-wasa sai da suka yi sati biyu basu yi magana da juna ba har ma Nihila ta shiga Sabgar gabanta ta daina ma tunainsa duk da Zuciyarta na sako mata shi amma tana yakice shi.
    Anyi sallar isha'i Abba Alhaji ya shigo cikin gida da babbar rigarsa yana kiran sunan Nihila.
Mama ce ta fara fitowa tace "Lafiya dai Alhaji?"
"Ina Nihila take?"
"Tana ɗaki me ya faru tayi wani abun ne?"
"Ki kirawo ta mana Bilkisu."
"To bari na kirata." Tana juyawa ma sai ga Nihila na fitowa daga ɗakin da sauri hannunta ɗauke da ɗankwali tana son daurawa saboda Abba Alhaji baya son a zauna ba a ɗaura ɗankwali ba.
"Na'am Abba ,sannu da zuwa gani."
"Zauna nan." Ta samu gu ta zauna ta lankwashe ƙafarta.
"Kina da labarin wannan yaron Abdullahi zai aiko manyan sa tambayar aure yau?"
Da sauri ta ɗaga kai ta soma jijiga kai "A'a Abba Wallahi ban sani ba." Ta faɗa da murya na rawa kamar zata yi kuka an kama ta da wani laifi mai girma.
Mama tace "Ya za ayi ta ɓoye mana wannan maganar?"
"Allah Mama ban sani ba ku yarda da ni."
Abba yace "A'a shi ma ya faɗa min dama ina son na tabbatar ne. Yanzu ke kina son shi ?"
Tayi sunkuyi da kai tana son ta ce masa a'a kuma bakin yayi nauyi.
Ya sake tambayar ta "Kin yarda a karɓi kuɗin su? Don in na karɓa fa ki sani ba gudu ba ja da baya."
Bata yi magana ba amma Zuciyarta na dukan uku-uku tunani take yi anya kuwa tana da future da Abdullahi kuwa? 
Mama ce tace "Tunda ka ji tayi shiru tana so mana fatanmu Allah Ya sa albarka a auren."
"To to, Amin."
Ya juya ya fita daga gidan. Mama tace "Kar dai ki cuci kan ki in kin san ba kya so ki gaya min tun yanzu na kira shi a warware maganar don kin san daga baya ba zai ɗauki uzurinki ba."
"Ina son shi Mama."
"Shikenan. Allah Ya sa albarka Ya sanya alheri Ya kaɗe fitina."
Ciki-ciki ta amsa da "Amin."
Ɗaki ta shiga ta ɗauko wayar ta nan ta ga message ɗin shi ya mata sakon ban haƙuri.
"Tuba nake Hayatina na san na ɓata miki rai amma ina son ki sani ban manta da ke ba kuma ba zan iya jure rashin ki ba ina can ina neman yadda zan mallake ki ni kaɗai. Yau Kawuna sun je gidan ku neman min auren ki kuma an bani ina taya mu murya."
Tana gama karantawa ta saki murmushin da bata shirya ba, haɗe da sunkuyar da kai ta cusa kai cikin fillo.
Sako ya sake shigar mata.
"Ba zaki kula ni ba Gimbiya?"
Hannunta na rawa ta tura masa da saƙo.
"Bana kula ka kaima ka daina kulani."
"In daina kula ki in kai raina ina? Ke ce fa ran?"
Tayi dariya kamar yana ganinta sai kuma ta tura masa da amsa.
"Sau nawa na kira ka amma ka ƙi ɗaga wata sati nawa rabon da ka gan ni?"
Daga can ya murmusa sannan ya rubuta mata.
"Ina nan a kwance ina jinyar rashin ku a kusa dani Habibty. Wallahi bana son na ga wani yana kallon ki ko yana kula ki ranar ji nayi kamar zuciyata ta ƙone saboda ganin ki da shi don Allah ki dinga haƙuri kina kiyaye kishina."
Sai kuma ta ji tausayin sa ya kama ta.
"To kayi haƙuri amma kaima kana sassauta mini ka san kai kaɗai nake so da kuma kai kaɗai na saba."
"Na haƙura! Na kira ki?"
"Eh."
Ko minti ɗaya ba ayi ba kiransa ya shigo.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sanann yace "Sai yau numfashina ya dawo daidai don Allah ki daina yin fushi dani."
"Ai kai ne kayi fushi dani."
"A bar wanann zancen ya riga da ya wuce. Kin yi kewata?"
"Sosai."
"Kamar yaya?"
"Ba zai misaltu ba."
"Yanzu ya kike ji da na kusan zaman angon ki?"
"Farinciki na gaske."
"Kin gan ni sai kyauta nake yi a ƙofar gida."
"Haba?"
"Da gaske."
Tayi dariya kawai.
Haka suka cigaba da hirar su ta masoya kamar basu yi faɗa ba. Daga ranar walwalarsu duk biyun ta koma kamar da.
"Barra an kawo kuɗi fa."
"Ke haba da gaske kike kin wai?"
"Allah kuwa."
"Kai amma na taya ku murna."
Suka rungume juna suna dariya.
A gidansu Barra ta wuni ranar sai da aka yi magariba Hafiz ya zo ya ɗauketa  ta raka ta waje suna hira shi ma Hafiz suka yi da shi yake tsokanarta ashe ba rabon Sadik bace rabon na Abdullahi ne.
Tayi dariya kawai.
Barra tace"Wallahi kayi kurum kar sarkin kishin duniya ya zane ka."
"Kai Barra don Allah wai me yasa kike yi masa haka ne?"
Suka sa mata dariya.
"Ai Wallahi na ma gaya miki gaskiya sai kin yi da gaske. Kin san yanzu da Sadik da Abdullahi ba sa magana? Tunda Abdullahi ya ji Sadik ya taɓa kula ki ya daina kula shi kwata-kwata."
Ta kama haɓa sannan tace "Ai yana da rigima Habibina sona yake yi sosai."
"Allah masoya." Barra ta faɗa.
Nan dai suka gaji da Tsokanar ta suka tafi.
Ta shiga ciki ta tarar Mama na lissafin kuɗin spices don ta fara shirin biki. Wata biyu aka saka   bikin duka. 
"Zo nan."
Ta isa gabanta ta zauna a ƙasa tace "Mama."
"Yauwa gobe zamu kasuwa da ke a fara siyayayr nan Karima tayi nauyi."
"To Mama."
Nan ta zauna tayi ta gaya mata abubuwan da take son ta siya mata tana dariya Ita dai.
"Ɗakuna nawa ne a gidan?"
"Mama kar ki sai abubuwa da yawa, ki sai muhimman kawai a gidansu ne fa ɗaki biyu ne ko kitchen babu a ciki sai a tsakar gidan na su tare da Umman shi. Kin san shi kaɗai ne bata son tayi nesa da shi ne."
Mama tayi ɗan dum tayi shiru tana kallonta.
"Anya kuwa Nihila wannan zaman zai yiwu kuwa? Ba fa na san fitina irin ta uwar miji."
"Mama ba komai a hankali yace zai lallaɓa ta mu bar gidan."
Ba don ta so ko ta gamsu ba tace "To Shikenan, Allah Ya sa hakan shi yafi alheri amma dai gara ace komai na ki daban ne saboda bana son ana samun matsala."
"Kiyi ta yi mana addu'a kawai Mama."
"Shikenan Allah Ya sa alheri."
"Kin ga yanzu sai kina siyan dan daidai in a gaba mun tashi sai ki siya min."
"To hakan ma ya yi. Zan gayawa Alhaji duk da haka."
"To Mama."