Chapter 6
by @khairatup01
GABA TAZO BAYA
Ummulkhair Sani Panisau
(Khairatup)
006
"Yanzu kana nufin komai ba za ayi ba?"
"A'a za ayi mana amma kada ki sake kice ba baki kwabo don ba zan bayar ba."
Tayi rau-rau da idanu sauran ƙiris hawayen su ƙarasa zubo mata.
"Amma ka san haka ake yi ko? Waye zai bani na lallen da ankon in ba kai ba? Komai sai kace ba za ayi ba to waye zai yi?"
Ya juya ya kalleta da gaske faɗa take yi masa ya cika da mamaki sosai.
"Innallillhi wai faɗa kike min akan bidi'a? To ba zan yi ba tunda na tambayi Umma tace min ba abinda zan bayar a gida za ayi miki mu sai dai a gayyace mu na sa a raina babu abinda zan yi yanzu kuma sai ki zo ki ce min ba haka ba na Umma zan bi ko naki?"
Takaici kamar ya kashe ta kawai sai ta juya zata bar wurin da sauri ya sha gabanta bakinsa a buɗe yace "Ni za ki juya ma baya ki tafi?"
"Idan na tsaya ne zamu yi faɗa gara na tafi."
"Rashin kunya kika koyo? Barra ce take kitsa miki wannan shirmen ko? Shikenan tunda hakan fitina zai zama an fasa yin komai a daura aure kawai a kawo ki ɗakin ki babu wani event da za ayi."
"Ai ba da kuɗin ka za ayi ba Abba Alhaji ya riga da ya biya inda Mama zata yi taron ta..."
Ya sa hannu ya rufe baki da mugun mamaki kamar wadda tayi saɓo yace "An canja ki Nihila ko kuma dai dama can haka kike munafurtata kike yi. Ni za ki yi wa rashin kunya ki ce min Abba ya biya gani matsiyaci ko?"
"Ni ban faɗa ba."
"Na gode! Kin yi ƙoƙari zan tafi."
"Sai Anjima." Ta ce da shi. Ya zaci hankalinta zai tashi saboda ya nuna ta ɓata masa rai sai ya ga ta juya da gaske zata tafi ta bar shi. Duk kuma sai ya ji babu daɗi ba wai ba shi da kudin ba ne abokinsa Galadanci ne ya gaya masa ya kula da aljihunsa ya san yadda zai kashe su don mata ba a sakar musu komai ko a nuna musu soyayya fiye da kima gara ka koyawa mace sonta ya fi naka ta yadda zaka juya ta son ran ka,sai yadda kace da ita haka zata yi.
Kuma su Ramlat ma sun ce ya basu dubu ɗari biyu su ma akwai abinda zasu yi. Yanzu kuma ya ga ranta ya ɓaci duk sai ya ji babu dadi. Har ta kusan shiga cikin ainihin gida ya dage ya kira sunan ta.
"Nihila."
Ta tsaya amma bata juyo ba haka ya taka ya isa gabanta yace "To me na fushin?"
"Ni ba fushi nake ba."
"To ga shi nan za ki tafi rai a ɓace salon ace ba ɓata miki rai?"
"Uhm ,ba komai."
"To nawa zan baki?"
Ta kalle shi da sauri tana son tabbatar da abinda ya faɗa ɗin gaske ne.
"Kina kallona ko ba kya so yar Abban?"
"Ina so mana. Duk yadda ka bani Allah sa albarka."
"To in na baki 300 ya miki?"
"Eh ya yi na gode."
"Shikenan in na je gida zan tura Miki ta account ɗinki."
"Allah saka da alheri Allah Ya ƙara buɗi."
"Amin. To ki saki ranki mana."
Bata san lokacin da ta yi dariya ba.
"Yauwa ko ke fa ita amarya ai ba a son ta da fushi. Kiyi lallen mai kyau kin ji?"
"To zan yi."
"Kitso za a yi miki kuma bana son ƙari."
"Ai bana ƙari dama da gashina kawai za ayi min."
"Yauwa. Na gaya miki za ayi taro a ɓangaren mu ko? Kuma zaku zo su Ramlat sun shirya zaman Ajo."
"To zan gayawa Mama."
"To sai da safe ."
"Allah Ya tashemu lafiya."
"Amin."
Daga haka suka yi sallama. Yana fita ya hau babur ɗin shi ya tafi.
***
"Ke Saudatu kalli uban kuɗin da yaron nan ya kashe a haɗa lefen nan."
"Wallahi Umma ki kwashe rabi dama na gayawa Ramlat sai an kwashe rabi baki ga yarinyar ba baƙa kamar bebin roba wannan dimple ɗin ne kaɗai ya cece ta shi ma sai tayi dariya take kyau."
"Hum! Baki san abinda nake ji ba a raina Saudat yaro ya kafe ya dage sai ya auri shegiyar yarinyar nan. Jiya fa ya saka aka sake gyara ɓarin da zasu zauna har yana ce min an auna bayan biki za ayi musu kitchen a can."
"Kin ji ko? Tun kan ta shigo ma ta fara sauya masa ra'ayi. Kar fa ki zuba ido zagewa za ki yi fa ki ƙwato ɗan ki da ƙyar fa ya yarda zai bamu dubu ɗari biyun da mita wai bai sallami mayar shi ba."
"Aiko sai na ci ubansa.Zai zo ya same ni da shi da alfiruwar matar ta shi."
Saudat ta gyada kai ta zari wani turare wanda yafi kowanne tsada tace "Wannan zan ɗauka kin san tsadarsa kuwa Umma?"
Umma dama uwar son kuɗi tace "Gaya min nawa ne?"
"Dubu talatin fa da ɗoriya."
Umma ta kama ƙirji ta hau salati tana kyarma "Dubu talatin ɗin lafiya?"
"Wallahi Allah Umma."
"Amma sai na kwashewa yaron nan albarka. Haka fa Ramlat ta faɗa min hadda atmapar dubu hamsin a ciki da ta tamanin."
"Ai tankaɗe za ki yi da rairaya ki kwashe na arziƙin ki bayar a kai mata shirmen haka kawai in kika ba ayi wasa bama sai ki ga an baiwa wata tsohuwa babbar atmapar ke kina nan ke da kika sunkuya kika haife shi ba ki mori komai ba."
"Ba shakka! To ba zai yiwu ba bari ya zo ya same ni ai duk kuna nan a zo a kwashe a kai mata akwati guda ma da wancan kit ɗin ya ishe ta."
"Shikenan ma Umma hakan ya kamata ayi."
Nan fa suka yi ta zuga Umma akan kayan lefen da Abdullahi ya haɗawa Nihila.
Tunda ya shiga cikin gidan ya ga sun zura masa idanu ya yi turus ya kasa ma ƙarasawa ciki musamman ma fuskar Umma da ya ga tamau kamar an sanar mata da wani babban saƙo marar daɗi.
"Lafiya na gan ku a haka waye ya rasu?"
Umma tace "Uban ka ne ya rasu shege bawan mace mara mutunci."
Shi da bai san me yayi ba yarinyar nan ma ba komai yake yi mata ba amma ance masa bawan mace sai dai ya juya ya ga kannensa da yayunsa duk rai a dagule ga kuma akwatunan lefe a tsakiya an cire kaso da yawa daga ciki.
Ya haɗiyi yawu ya ƙanƙance idanu ya haɗiyi yawu da ƙyar yace "Me kayan nan suke yi a nan a haka a barbaje ba an gama ganinsu ba ne?"
Umma ta sa hannu ta jefa masa daƙuwa da hannu tace "Ungo naka nace. Nace maka Ungo naka shege fitsararre dan keson uwa! Wallahi ba za a kai mata kayan nan duka ba kai in takaice maka ma akwati ɗaya za a kai da wannan ɗan kit ɗin in basa so su dawo da shi."
"Haba Umma ya za ayi haka ai wanann ni za a zubarwa da mutunci kamar ni ace na kai wanann ɗan kayan me za ayi dasu in an kwashe?"
"Siyarwar za ayi ko a rabawa yan'uwanka."
"Gaskiya Umma ba zan siyar ba kuma ba zan bayar ba haba sai na gama abu sai su zo su zuga ki ke kuma ki hau ki zauna ba kya duba nawa mutuncin gaskiya ban yarda ba." Ya faɗa kamar ƙaramin yaro sai a lokacin Aimana tace "Wallahi Ummanmu wannan ba daidai bane ita Aunty Saudatu ai ba a rage mata ba aka kawo mata kowa yadda yake so ake yi masa amma sai a takurawa Yaya gaskiya ba adalci a nan Wallahi."
Umma tace "Eh ku gaya min ƙasusuwanku sun kai. Zama ku iya haɗa ƙwanji da ni."
"Gaskiya ce ba kya so Umma."
"Eh gaya min gaskiya yar da na haifa a cikina jiya. Ku haɗu ku zane ni ko."
Suka yi shiru ana tsaka da wanann takadamar Kawunsu ya shigo.
"Salamu alaikum! Wai ba za a fito da kayan ba ne Abdullahi?" Sai shi ma yayi turus ganin kaya a barbaje.
"Ya haka kuma ba a shirya su ba aka kirawo mu?"
Umma ta soma harare-harare a ranta tace "Ga uban iya ya zo sarkin Allah yace Annabi ya ce." Ta tsuke baki ta zunɓuro shi gaba sosai.
Aimana ta tashi tace "Gara da kazo Kawu Wallahi su Aunty Saudat ne suka zuga Umma wai sai an rage kayan nan akwati ɗaya kawai za a kai wai sun yi yawa."
Ya zare idanunsa yace "Wannan ko ya'yan banza ɗan'uwan naku ma baku bari ba saboda mugun hali?"
"A'a bari Isma'ila,kamar yaya mugun hali ka daina jifan su da wanann kalmar Yan albarka ne yarana."
"Wallahi mugwaye ne don Iskanci uban waye ya rage nata in ba hassada da ƙyashi ba ma ne na cewa a rage kaya ke kuma aimaka Sarkin son ya'ya kin hau kin dire kin biye musu. To tun kan raina ya ɓaci ku maida duk abinda kuka ɗauka duka za a kai." Ya juya ya kalli Abdullahi yace "Kai kuma in ka ga dama ka zama namiji."
Ba don sun so ba suka dinga cusa kayan suna sakawa a haka Aimana na gyarawa ba a jima ba aka maida komai yadda yake. Wasu samari suka dinga fita da kayan. Akwatuna shidda ne da kit sai wani adudu da wata ƙaramar Ghana must go aka fita da su. Umma ta dinga bin kowa da harara Aimana dai ta dinga godewa Allah a ranta da Allah Ya saka Kawu ya shigo gidan a daidai da Wallahi sai an kwashe su an siyar.
Shi kan shi Abdullahi abin ya masa daɗi amma bai nuna ba kawai ya sa kai ya fice daga gidan shi ma.
A ɓoye ya bada dubu ɗari yace a bayar na dinki da cefane ya kuma kira Hafiz yace masa kai wannan geron da man da buhun shinkafar da ya suka siya don kai wa da lefe da jarkar mai. Ya shiga gidansu abokinsa Musa da yake jikin gidansu shi ma ya karɓo carpet ya bayar .
Kawo Isma'il ya ce "Ka kyauta kayi ta addu'a Allah Ya rabaku lafiya." Shi dai bai ce komai ba yana gani suka tafi kai kayan. Ya ji wani sanyi da aka wuce da kayan ma a yau don tunda suka ce sai sun siyar da sai dai ya tarar sun siyar ɗin har baya son Aunty Saudat ta zo gidan don in ta zo sai yadda Allah Ya yi da su a gidan dama ranar dole sai ta haɗa wata masifar.
Juyawar da zai yi suka yi ido huɗu da Sameera.
"Sameeran Maminta daga ina ."
"Unguwa na je."
"Sannu da zuwa." Ya faɗa yana murmushi.
Ta kalle shi da kyau sanann tace "Ka rantse dai ba ka sona."
Ya yi mata wani kallo sai kuma ya murmusa yace "Ya za ayi nace bana son ki."
"Ga zahiri kuwa. Ai ka san ina son ka amma ka tsallake ni ka je ka zaɓo wata alhalin na san ka san ina son ka."
"Haba Sameera bai dace ki ce haka ba. Ai wancan da aka yi na ƙuruciya ne ba na komai ba da na kika ƙara hankali cewa kika yi ba soyayya muke ba kin ga ai da dake za ayi ni kuma san da kika dawo na riga na samu Nihila."
Ta taɓe bakinta sanann tace da shi "Ai a hakan ma ban cire tsammani ba na san zaka aure ni ko kana so ko baka so dole ne wannan."
Yayi mata kallon baki da hankali amma sai ya wayance ya zura hannayen shi a cikin aljihun wandonsa biyu ya yi murmushi yace "Ban san me Allah Ya rubuta ba amma ni a karon kaina ita kaɗai ce jal matata a duniya da lahira."
Sai da tayi dariyar gefen baki sannan tace "Ma ji ma gani in dai ranmu da lafiyarmu ai zamu gani. Kai ne dai sai na mallake ka ko baka so kuwa."
"Shikenan ina taya ki addu'a. Sai Anjima zan yi waya da matata."
Ta shaƙa kuwa ta cije leɓɓe tayi gaba. Ta gama cin alwashin shiga rayuwar shi a karo na biyu.
Sun yi soyayya a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba daga Allah sai su sanda ya nuna mata aurenta yake so yayi sai ta nuna masa ai ta wasa ce ba gaske bata shirya ba ya kyale ta ba a jima ba ya haɗu da Nihila kuma sai Allah Ya haɗa jininsu suka daidaita shi ne yanzu take son ta haɗa masa fitina wai tana son shi kuma sai ta aure shi.
***
"Ai Umma ki kwantar da hankalin ki ba dai gidanmu zata shigo ba kar ki damu sai mun saka ta gwammaci zaman gidansu akan auren Abdullahi don ba zamu bari muna ji muna gani arziki ya wuce mu ba kin ga dai alƙawarin da Hajiya Mami tayi mana in an auri Sameerar kin ga kuwa ba zamu yi sanya ba."
Umma na tunar goro ta dakata tace "Ku kyale ni da ita dani take zancen shi ma ya gama rawar kafar zai dawo hannuna ne."
"Yauwa kar ku raga mata duk wani aikin gidan nan ku loda mata shi duk wani abu ku maka mata shi har sai ta fita da ƙafafunta."
"Ai shi yasa na ce ba zai Kaita ko ina ba tana nan gidan tare da mu."
"Yauwa Umma na san zaku iya dama a cikinmu wannan Aimanar ce mara zuciya ."
"Can ta yo mugun gado a dangin ubanku wata rana sai na zaune ta a gidan nan ta daina numfashi zan ji sanyi a raina."
Aunty Saudat tayi dariya sosai har tana kama ciki.
Aisha da Umaima suka shigo cikin uniform ɗin hygiene.
"Wash! Umma Wallahi yau mun gaji sosai. Da ƙyar muka samu abin hawa.'"
"Sannunku da zuwa."
"Yauwa." Umaima ta faɗa.
Aisha ta ciro leda daga cikin jakarta. Tana buɗewa ƙamshi ya ɗume ɗakin gabaɗaya tsire ne lafiyaye ya sha kayan lambu sai tururi yake yi kamar a lokacin aka siyo. Umaima kuma ta zaro wata ledar a ciki kuma shawarma ce da lemo mai sanyi.
Umma tace "Daga ina wannan kayan kuma ya'yan nan?"
"Wallahi Umma wani ne ya gan mu a bakin titi a gajiye ya rage mana hanya har nan fa ya kawo mu shi ne ya siya mana."
Umma ta washe haƙoran ta jajir saboda cin goro sannan tace "Ba dai haka ya tafi baku samo lambar sa ba?"
Umaima na tauna nama tace "Haba waye shi? Ai ya bamu lambar waya kuma zai dawo. Aisha yake so."
"Yauwa,yanzu na ji batu yaran albarka arziki na bin ku ko ina. Ki kama shi ram ki samu ki huta muma mu huta ato."
Aisha na dariya ta miƙa mata shawarmar tace "ki ci Umma."
"A'a bana son wanann naman nake so."
Ta tura mata ledar gabanta suka zauna suka haɗu suna ci suna santi ba ƙarya naman akwai daɗi sosai.
Aimana ta shigo ta gan su suna ci.
Umma ta zabga mata harara tace "Zo nan ki dangwala tunda ke Allah beyi ki da farinjini ba kullum kina ɗaka daga makaranta sai gida ke ta Allah."
Maganar ta doki Aimana amma sai bata nuna komai ba ta ce "A'a na ƙoshi bana ci."
"Oho miki ke kika sani mu muna ci."
Ta saka wayar ta a kunne ta kunna karatun Al'ƙurani mai girma tana saurara.
Da Aunty Firdausi da Aunty Saudat sune yayun Abdullahi, duk suna da aure ne , Ramlat,Aisha da Umaima da Aimana duk ƙanensa ne. Babban wan su ba shi da lafiya yana da matsalar ƙwaƙwalwa tun yana yaro ya taso a haka yana gidan amma a can wani ɓari shi kaɗai sai dai a kai masa abinci da ruwa in an samu kuma Umman ta gyara shi ko Abdullahi. Gidansu irin gidan nan ne na kowa tasa ta fishe shi ba ruwan kowa da harkar kowa duk yadda ka dama ka sha uwa ba ƙwaba in dai zaka kawo mata abin duniya gata da faɗan masifa da son abin duniya. Ga kishin ya'ya kuma in baka bata a ya'yan ma dole ne sai ka ga bambanci da mai bata.
**
An kai kaya lafiya. Abba ya bada tukuici kuwa da yawa saboda yaba kyauta. Abdullahi yayi kokari sosai Wallahi shi kan shi yana namiji ya yaba masa bare su Mama a cikin gida.
Bakin Nihila ya kasa rufuwa daga ɗaki tana jin yadda ake yaba ƙoƙarin da gwaninta ya yi.
Ta kira shi kuwa.
Yana ganin kiran ta ya ɗauka.
"Amaryata."
"Angona."
"To ya aka yi amarya."
"Kira nayi na miƙa godiyata gaskiya kayi ƙoƙari sosai Allah Ya saka maka da alheri Ya ƙara maka buɗi."
"Amin amaryata ai tunda ke nayiwa komai ma zan yi sun miki dai ko?"
"Sun yi."
"Haka nake son ji. Allah-Allah nake yi ranar da za a shaida ta zo."
Tayi dariya tana kallon ƙasa kawai.
"To me kike tanadar mini?"
"Me kake son na tanadar maka?"
"Ke kaɗai ma kin wadatar."
"To ai taka ce."
"Inye! Bakin ya buɗe?"
Tayi murmushi kawai.
Nan suka ci gaba da hira tare da tsara yadda rayuwarsu zata kaya da alƙawarin kasancewa tare har abada da yadda zasu ririta juna. Sun jima a waya kafin suka gaji suka ajiye wayar.
Rai da buri! Wasu burukan fa ba a haifesu a ciki suke mutuwa. Kaddara kan sauya komai cikin lokaci ƙanƙani Musanmman lokacin da baka tsanmmata ba.
*****
"Ayiriri amarya! Ke kika ce kina so da baki ce kina so ba da ba a baki shi ba." Waƙar da ke tashi kenanan a ɗakin yan matan amarya.
Ba zata iya biye musu ba saboda yadda gabanta ke faɗuwa saboda fargaba hakan nan take jin wasu irin abubuwa na mata yawo a ciki.
Bata kuma shiga tashin hankali ba sai da Aunty Rahila ƙanwar Abba ta shigo tana dariya ba tace "An ɗaura alkawarin Allah Ya cika kin zama amaryar Abdullahi. Allah Ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitina Ya kawo zuri'a ɗayyaba."
Sai da ta ji wani abu "Gif'" a tsakar kanta kamar an maka mata wani abu gabanta ya sake bada sautin "Ɗum" da gaske yau zata fara sabuwar rayuwa ba irin wadda ta saba da ita ba ,yau an bude mata sabon babin rayuwa tare da wasu ahalin ba wanda ta taso ta ganta a cikinsu ba, yau ta zama matar wane ba iya yar Abba Alhaji kaɗai ba.
Siraran hawaye suka dinga zubo mata a fuska. Barra na dariya tana ɗauke mata su.
Shafa'atu ta kama haɓa tace "Ke banza wa yake kuka ran auren sa?"
Barra tayi dariya tace "Kukan farin ciki ne ke kar ki damu matar Abdullahi."
Suka kuma saka mata dariya.
A haka dai aka dinga shigowa ana mata Allah sanya alheri masu nasiha na faɗa nayi ita dai zugum ba wani ganewa take yi ba abinda ya ishe ta ma ya ishe ta.
Nan Barra ta saka ta sake wasu kayan saboda Abba Alhaji ya kirata kuma ta san nasiha ne dai za ayi mata. A sitting room ɗin ta tarar dasu da yawa mazan iyaye da kakanni a tsakiya ta hango Abdullahi a zaune cikin farar shadda wadda tayi masa mugun kyau ya yi mata wani kyau sosai. Ta sunkuyar da kanta ƙasa ta zauna a inda aka nuna mata.
Ba tare da ɓata lokaci ba ƙanin Abba Alhaji ƙarami yayi gyaran murya ya soma jawabi ya karanta musu hakkokin aure da sharuɗɗai ya kuma jaddada musu da amfanin haƙuri da juna da kiyaye ɓatawa juna rai. Ya gaya musu da su koyi girmama ra'ayin juna idan kuma ɗaya ya hau ɗaya ya saki ya zama babba ba sai ana jin kansu ba. Sosai yayi musu nasiha mai ratsa jiki aka kuma damƙawa Abdullahi amanar Nihila yace ya karba kuma zai yi iya yinsa don ganin ya cimma alƙawarin da ya ɗauka.
Aka tambayi Abba Alhaji ko da sauran magana yana murmushi yace "Kun faɗi komai ni dai fatana shi ne Uwata kiyi biyayya ga mijinki irin yadda kika ga Bilkisa ta tana yi kin ga dai ba a taɓa jin kan mu ba kuma ba wai ɓatawa juna bane kawai ta san ni ne na san ta kuma ta fini haƙuri da juriya a aure sai ana haƙuri za ki ji wata rana kamar ya fi ki ko kin fi shi sai dai ki sani shi ne a gaba da ke kuma ya isa dake ya zama uba yanzu a wurin ki ban da rashin kunya ko kawo ƙara ki riƙe mana mutuncin gida ga Karima nan da Jamilu da Shu'aibu babu wanda aka taɓa yin kuka da su a fanin aure ina son kema ki zama mai koyi da su ko ma ki fi su. Kuyi haƙuri da junanku kuyi haƙuri da junanku kuyi haƙuri da junanku kun ga na maimaita sau uku ko?" Suka gyaɗa kai jiki a sanyayye.
"To ku ƙara haƙuri ku kiyaye dokokin ubangiji banda cutar juna in abu ya shige muku gaba ku zauna ku tattauna ku samo mafita sai dai idan ya fi ƙarfin ku ne zaku iya samun mu don mu nuna muku hanya in ba dole ba ma bama son mu san komai na rayuwarku."
A tare kamar haɗin baki suka ce "In sha Allahu Abba."
"Allah Ya yi muku albarka."
"Amin." Suka amsa a tare.
Bayan sun fita aka yi ta hotuna. Suna tsaka da hotuna ya ja hannun matarsa gefe aka saka ihu abokan ango da ƙawayen amarya.
Ba ruwan shi da mutane a farfajiyar gidan ana ta musu dariya ya samu wani gu ya ƙeɓe da matarsa ya sa hannunsa ya ɗago haɓarta.
"Matata!"
Ta kuma sunkuyar da kanta ƙasa. Ya yi murmushi ba tare da ta yi aune ba ya sa bakinsa akan goshinta ya sumbata.
A tsorace ta ɗaga kai tana kalle-kallen ko ba a ganinsu.
Yace "Me wai kina duba ko an gan ni ne?"
Ta gyaɗa masa kai.
"To sai me ai yau ko me zan miki Allah Ya yarje min nayi don kin zama muharammata,matata abar alfaharina."
"Gaskiya ka bari kunya kake bani."
Yayi dariya sannan yace "Ke rungume ki ma zanyi Wallahi."
Ta yi yar ƙara "A'a Wallahi."
"Yanzu fa aka gama mana faɗa har kin manta?"
"Gaskiya aa ana kallonmu fa."
"Waya ce su kalli mata da miji maganin yan tsarku za ayi kawai."
Tayi dariya.
"Yunwa nake ji."
"Me zan samo miki? Gara na fara dutyna tun yanzu."
"Akwai ai a ciki."
"Na sani."
"Ka tafi mana to."
"Kai wai korata kike yi?"
"Eh ɗin."
"Allah ba zan bar ki ba ina nan da ke."
Ta zare masa idanu sanann tace "A ina ake yin haka don Allah gaskiya ka tafi a daina kallonmu."
"Gaskiya ba zan tafi ba sai dai mu tafi tare ni da ke."
"Kam!"
"Eh."