Chapter 7
by @khairatup01
GABA TAZO BAYA
Ummulkhair S Panisau
(Khairatup)
007
** ** ** ** ** ** ** ** **
Zaune take ita kaɗai a tsakiyar gadonta fuskar ta a lullube da mayafi. Ƙamshi ta ko ina ga ƙamshin sabon fenti. Tana wasa da yatsunta taji alamar an buɗe ƙofar fakon an shigo. Gabanta ya bada rass a tunaninta shi ne ya shigo sai dai taji wata Muryar daban ba tashi ba.
"Amarya ba kya laifi."
"Sai dai in bata yi laifin ba. Buɗe fuskar ki mu gani mu yayyen shi ne." Aunty Firdausi ta faɗa.
Bata iya buɗewa ba saboda kunya.
Ramlat ce tayi tsaki ta haye kan gadon tace "Lallaɓata kuke wai ? Bari na buɗe muku da kaina ku gan ta ba wani kyau ne da ita ba fa."
Suka bushe da dariya kuwa.
Aimana tace "Wai me haka don Allah Aunty Ramlat?"
"Ban sani ba uwar iya."
Sai taji wani banbarakwai anya kuwa yan'uwan na shi ne da gaske? Bata gama tunani ba ta ji an dage mata mayafin baya. Sai ta ga sun kalli juna su huɗu sun fashe da dariya sosai. Sai duk ta ji ta muzanta ma gaba ɗaya tuni idanunta suka cika da hawaye suna son zubowa tana ƙoƙarin danne su.
Aimana ta ji babu daɗi kawai sai ta hau saman ita ma ta rungume gefenta tace "Sannu da zuwa matar Yaya muna yi miki maraba da zuwa gidanmu. Fatan za ki karɓemu da hannu biyu-biyu?"
Hawayen da take ƙoƙarin riƙewa suka zubo mata ta sa hannu ta share su.
"Ina yininku." Ta ce a ɗarare.
Suka dinga yatsina da taɓe baki basu ƙara cewa komai ba suka juya suka bar ɗakin gabaɗaya.
Sai a lokacin ta ji tana shaƙar iska yadda ya dace ba kamar san da suna ciki ba. Tambayar kanta tayi "Anya suna maraba da ita kuwa?" Saboda ba yadda ya gaya mata suna sonta ta gani ba wata kalar tsana ta gani daban a cikin idanunsu. In har ba sa son ta yaya zata yi da ranta? Ga shi da su zata zauna a inuwa ɗaya.
Aimana tace "Ki kyale su, kin ji kar ki saka su a ranki a haka suke sunana Aimana ni ce ƙarama a gidan a hankali duk za ki san kowa."
Ta ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali tace "Na gode."
"Ba komai."
Aka sake buɗe ƙofa aka shigo ciki wannan karon ta ji ƙamshin turarensa ta jiyo har uwarɗaka.
"Kina nan?"
"Eh tare muka zo da su Yaya."
"Kin kyauta da kika tsaya da matata."
Tayi murmushi.
Ya samu gu ya zauna ya ajiye ledojin da ya shigo dasu yace "Sai ki tashi ai ko tunda na zo."
"Kai Yaya korata kake ma?"
"Eh na Kore ki."
Tayi dariya haɗe da miƙewa ta fice daga ɗakin.
Ya zare babbar rigarsa ya ajiye a gefe yana murmushi.
Hannunta ya kama duka biyu ya sumbata yace "Alhamdu lillah! Ina matuƙar godiya ga Allah da Ya mallaka min ke a matsayin matata in sha Allahu ba zan baki kunya ba."
Tana murmushi tace"In sha Allahu zan faranta maka nima."
"Sai kin yi haƙuri, bamu kaɗai ba ne, don Allah ki yi haƙuri da yan'uwana da mahaifiyata na san za ki tambayi kanki dalilin da ya sa na faɗi haka amma a hankali za ki gane komai. Dole sai kin daure dole sai kin yi haƙuri dasu suma suyi haƙuri da ke. Aunty Saudat da Aunty Firdausi sune suka yi aure, sauran duk suna nan gidan harda Umma. Na gaya miki kitchen ɗinmu zai zama tare da su Umma in kika yi abinci kina sakawa da su sannan ko fita za ki yi sai kin gayawa Umma in ta yarda ki je in bata yarda ba ki haƙura yadda kika ɗauki Mama haka nake so ki ɗauki Umma."
"In sha Allahu ba zaka yi kuka dani ba. Zanyi yadda kake so."
"Na gode."
Ya sumbaci goshin ta ya zare mayafinta daga kanta.
Yana ƙoƙarin saka bakina a cikin nata kawai ya ji muryar Umma a kansu.
"Har ka saka ta a loko?"
Suka daburburce da sauri ya cikata. Nihila ta ga abin wani iri a ranta tace "Su kuma haka suke?"
"Na ga ka shigo baka min saida safe ba an kawo amarya ka manta dani?"
Ya sauka ƙasa yace "A'a Umma ba haka ba ne."
Umma ta kalle ta tace "Ke baki iya gaisuwa ba?"
Ta sauko daga kan gado jiki na rawa tace "Barka da dare Umma."
Sai da ta taɓe baki sannan tace"Barkanmu."
Ta sake taɓe baki ta ƙarewa ɗakin kallon tsab. Ta hangi leda ta sa hannu ta dauka ta duba nan ta ga kaza da yogurt.
"Lallai Abdullahi! Ka samo mata ka manta da uwa to ina nawa kason? Kar dai ka ce min baka kawo min ba?"
Ya dabarbrce ya rasa ma me zai faɗa kunyar duniya ta ishe shi kan abinda take yi a gaban Nihila.
"Baka da amsa daman ai to na tafi zan ɗibar mana abinda ya yi saura zan aiko maka da shi don sai mun ci mu ma ai duk mun sha hidiman biki mun gaji muna da buƙatar ta."
Ta sa kai ta juya ta fice.
Ya koma ya zauna kansa na sara masa.
Koƙarin danne mamaki ta take yi ganin yadda duk ya rikice ya ma kasa magana don ta kwantar mai da hankali ta tashi tace "Bara nayi wanka don duk na gaji."
Yana ganin ta tashi tsaye ya kama hannunta. Juyawa tayi da murmushin yaƙe.
Miƙewa yayi shi ma tsaye ya tsaya daf da ita numfashi su na dukan juna. Ya sa hannayensa biyu ya tallafi fuskarta ya ɗora goshinsa a kan nata. A hankali ta lumshe idanunta biyu tana jin saukar ɗumin numfashinsa a kan fuskar ta.
"Am sorry!"
"Uhm!"
"Ba Uhm ba ki buɗe baki kiyi magana."
"Me zan ce maka to?"
"Komai ma kawai dai kar kiyi shiru."
Ta samu ya juya da sauri ya kamota ya dawo da ita da baya ya sa hannayensa biyu ya rungumo cikinta. Bakinsa ya saka a gefen wuyanta. Wani irin shocking ta ji a jikinta bata saba ba bata ma taɓa haɗa jikinta da na wani ba sai yau.
"Habib...biiii wan.."
"Shhhh! Ya isa kar ki hana ni abinda Allah Ya hallata mini,kar ki ɓata mana wanann daren mai cike da tarin albarka da ɗimin tarihi."
"Ba zan hana ka ba amma ya kamata muyi abinda Annabi ya umarce mu da muyi. Muyi sallah mu nuna godiyar mu ga Allah."
"Oh! Haka ne fa to muje
" Suka tafi hannayensu saƙale da na juna. Yana tsaye tayi alwala shi ma ya yi alwalar ya saka mukulli a ƙofa ya kulle ko ina sannan suka shiga ciki suka yi sallah raka'a biyu kamar yadda addini ya tanadar.
Ya kama kanta yayi addu'oi sannan yayi mata tambayoyi ta ba shi amsa bai yi mamakin yadda ya san abubuwa ba saboda ya san yar wane gida ce.
Daga nan ne fa wasan ya sauya ya rufe idanu tsab ya yi abinda ruhi da gangar jikinsa suke ta kwaɗaita masa bai sarara mata ba kuma bai raga mata ba har sai da ya samu ya je inda yake son zuwa.
Ta galaɓaita amma bata nuna raki ba tunda an gaya mata ba a son raki dole ne tayi haƙuri don wannan ɗin shi ne ginshiƙin auren kuma ba a raba maza da son shi.
Da kansa ya dafa mata ruwan zafi a kitchen ɗin Umma da sassafe ya kai mata banɗaki ta kimtsa ya kuma kai mata wani tayi wanka ta kwanta bayan ta sha tea da wainar kwai ya bata paracetamol ta sha. Ba a ɗauki dogon lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita.
Ya ƙare mata kallo tsaf don ta burge shi fes ta zo ba yadda ya dinga tsoro ba kasancewarta yar boko. Har zai kwanta sai kuma ya ga gara dai ya je ya gaishe da Umma kar a kuma samun matsala.
"Salamu alaikum" yayi sallama yana ɗage labulen falon umma.
A gabanta da fulas ɗin kosai da jug mai cike da kunu. Yaranta sun zagaye ta kowacce da kofi da kwano a gabanta.
"Wa'alaikum Salam. Salammanme ta bar ka ka fito kenan?"
Ya zauna a ƙasa yace "Barka da safiya Umma fatan kin tashi lafiya?"
"Da ban tashi ba ai ba ka gan ni ba."
Bai ce komai ba ya gushe da Aunty.Saudat da Auntyn Firdausi shi kuma su Ramlah suka gaishe shi.
"Jiya kuma muka yi ta bugun ƙofa an maido maka naku rabon kazar ka ƙi buɗe ƙofa"
"Mun kwanta ne Umma."
"Amma ake jiyo yan koke-koken ku."
Kunya kamar zai nutse ya rasa ma mai zai ce mata ya rasa me yasa take mantawa shi ɗin ɗanta ne babu irin wannan zantukan a tsakaninsu kunyarta yake ji sosai.
"A zuba maka kokon ko kuwa ka zama yaron tea and bread?"
Yayi murmushi yana gyaɗa kai kawai ya miƙa mata kofi yace "Ai ni kin san ɗan koko ne Umma."
Ta karɓa ta zuba masa ya sha ya ci ƙosai. Bai bar falon Umma ba sai azahar yana son fita amma baya son ta yi mita ko ta ce wani abun. Amma zuciyarsa na gun matarsa.
Ita kuwa ta ci baccinta da ta tashi kuma sai ta ji ta nemi duk wanann gajiyar ya rasa sai abinda ba'a rasa ba. Ta sake yin wanka ta sauya kaya wata atampa ta saka da Abba ya ɗinka mata na fitar biki tayi kwalliya tayi kyau ras amarya da ita sai annuri take fitarwa daga fuskarta.
Ta duba bata gan shi ba haka ya saka ta yanke shawarar zuwa ta gaishe da Umma. Ta ɗauki mayafinta mai tsada ta saka wani flat ɗin takalmi ta fita sai ƙamshi take yi.
Tun kan ta shiga falon saƙon isarta ya iske su saboda wani azababen ƙamshi da ke fita daga jikinta.
Tana yin sallama ta ɗaga labulen ta shiga duk suka zura mata idanu har sai da ta tsargu. Baƙar fatarta luwai-luwai na ɗaukar ido saboda ya sha gyara.
Ku san tuntuɓe tayi ta samo ta daidaita nutsuwarta.
Gaban Umma ta isa ta sunkuya ta gaishe ta "Barka da rana Umma."
"Barkanmu."
Sai kuma tayi shiru.
Aunty Saudat tace "Ina wuni amarya?" Mu mun gaishe ki ai.
Ta ɗan ji kunya ta juya ta gaishe su ɗayan bayan ɗaya harda su Lamrat ma. Aimana ce tai dariya tace "Kayya! Aunty Nihila ai duk wanann ƙannan Yaya ne sune zasu gaishe ki ba ke ce za ki gaishe mu ba."
Umaima ta zabga mata wata uwar Harara kamar idanunta zasu faɗo ƙasa sanann taca "A wannan ai ko Isha ta girmeta."
Nan dai ta zauna bata sake magana ba sai dai Aimana ta dinga jifanta da tambayoyi har ta sake da ita suka yi ta hira.
Da rana tayi sosai Umma ta kira ta.
"Ke Khadija tashi ki ɗora mana abincin rana ko? Lada ya isa kin zauna sai zuba kike yi ko kunya ta ba kya ji."
Ba girkin ne ya bata mamaki ba yadda ta ambaci Khadijan ne ya ɗan sanyayya mata guiwa bata saba jin ana kiran sunan haka gatsal ba sai duk ta ji ba daɗi a yadda ma ta lura daga jiya zuwa yau akwai matsala a ahalin Abdullahi kamar basu karɓeta ba... Muryar Umman ce ta sake shiga kunnuwanta.
"Ko ba za ki yi ba ne kike kallona?"
Da sauri tace "A'a zan yi Umma. Me za a girka?"
"Tuwo ne za ki tuƙa shi yanzu ma kuwa ki tuƙa na dawa miyar kuka kuma kowa sai ya ci."
"To." Kawai ta faɗa ta tashi ta kalli Aimana tace "Ina ne kitchen ɗin?"
Aunty Saudat tace "A'a yar boko mu nan da icce muke amfani cewa zaki yi ina murhun yake."
Aimana ta tashi ita ma tare suka haɗa komai hayaƙi na tashi haka ta zauna tayi girkin nan. Tunda ya shigo ya isa wurinsu bai ganta ba ya san tana wurin Umma ko da ya shiga sai ya tarar tana aikin girki duk sai hawaye take yi saboda hayƙin itacen ya ji ruwa. Ya san kuma akwai gas akwai gawayi amma Umma ta zaɓi ta bata wannan mattaccen itacen.
Don ma Aimana na taya ta haka suka gama ta zuba ta kaiwa Umma.
Umma na cakalar tuwon ta taɓe baki da fuska ta kalle ta.
"Ke yanzu girikn ma baki iya ba?"
Ta kalle ta jiki a sanyayye.
Umma ta sake cewa "Wanann kike kira girki? Ji miya tsululu ba wani Kyan gani?"
Nihila ta kalli faratin gabanta bata ga inda ta kuskure ba amma sai ta maze tace "Kiyi haƙuri Umma...zan sake ƙoƙari." Ta faɗa cike da sanyin murya.
A lokacin ta gane cewa ba kowanne kuka ne yake fitowa da hawaye ba,wasu kukan suna dannewa ne a zuciya. Ta tashi daga zaunen tana ƙoƙarin danne rauninta ta fita daga falon. Ɓarinta ta koma ta shiga ta kulle ƙofar ɗaki ta jingina bayanta da jikin ƙofa hawayen da take dannewa suka samo nasarar zubowa.
"Ya Allah na shigo da niyyar zama 'ya a wurinta ,amma zata karɓe ni a matsayin 'ya kuwa?' ta tambayi kanta tana goge hawayen da ke zubo mata ta tashi tare da sakawa a ranta zata cinye komai don Abdullahi ta kuma yi alƙawarin danne komai saboda ta gina aurenta sai dai tana fatan kar ta manta kanta garin neman matsuguni a zuciyar Umma.
A hankali ya kwankwnsa ƙofar dakin yana magana kamar munafuki.
"Open the door Habityna ni ne."
Tashi tayi da sauri ta sa hannu tana share hawayen don kar ya gani sai dai abinda bata sani ba shi ne ya riga da ya san abinda ya farun.
Buɗe masa tayi tana ƙaƙalo murmushi tace "sannu da dawowa ina ka je ne?"
Rungumeta yayi a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya a jejere iya wanann abinda ya yi mata ya saka ta manta da wancan takaicin har ta saki murmushin gaske da ya kai mata zuci.
"Me ya faru?"
"Ba komai i love you."
"I love you to."
Ya kama hannayenta biyu ya sumbata yace "Lemme kiss them kin ga tuwon nan sai da na shanye miyar tas kunnuana na motsi Aimana tace min kece kika yi nace amarya guda aka saka girki zan fara yaki tace min ai ke kika ce za ki yiwa Umma don ki faranta mata." Shi kan shi ya san abinda yake faɗa bai zauna ba amma bai san ya zai yi ba ne kawai yana son ya ga tana cikin walwala ne.
Dariya tayi sosai ta gyara tsayuwarsa tace "Na gode! Amma ba sai ka yi haka ba Umma mahaifiyata ce nima su iyaye ba sa yin laifi a gun ya'yansu ban ji haushi ba. Zan ƙara himma don na ga na zama yadda take so ba laifinta ba ne so take yi na zama surukar da take son ta samawa ɗanta."
Ya sumbaci goshinta yace "Idan ban godewa Allah ba me zanyi? Na ƙara son ki kuma nayi miki alƙawarin zame miki abin alfahari har ƙarshen rayuwarmu kuma ba zan taɓa barin ki ba duk tsanani duk wuya.",
Tayi dariya tace "Iya hakan ma ya ishe ni kar ka manta alƙawarin ka."
"Ba zan manta ba wanann alƙawarin maza ne."
Tayi dariya ta juya ta ce "Au akwai alƙawarin maza dama?"
"Sosai ma baki san ni namiji bane?"
"Ah na sani fa Man." Ta faɗa tana dariya. Sai ya ji sanyi a ransa da ta manta da wancan damuwar.
"Me zaki dafa mana to mu?"
"Da ka bar shi sai na je na ɗebo mana tuwon a fulas mu ci."
"A'a ni fa bana son wani tuwo."
"To ka yo cefanen abinda kake so sai na girka mana angona."
"Shikenan in na fita yanzu zan yo cefanen. Ke kuma ki sake min wata kwalliyar so nake ki tashi kaina."
Hancinsa ta ja sosai da ƙarfi cikin wasa tana dariya ya kama hannun yace "Muguwa sakar min hanci."
"A'a ba zan saki ba."
"Allah da zafi ki sakar min kar na Miki kuka."
"Haba Man wanne irin kuka kuma yanzu fa ka gama min bragging kai Man ne."
"Eh ai ke ma kin sani ko har wurin ya warke ne?"
Ta cika shi tana jijjiga kai tayi gaba.
Ya sha gabanta da sauri yace "Gaya min ya warke ne wurin yau na kawo ziyara na bada sakon a inbox ɗina."
"Baka ji."
Sosai ta bashi dariya ya shiga banɗaki a gurguje yayi wanka ya fito ya sauya kaya ya saka ƙananun kaya.
"Ka yi kyau." Ta faɗa masa lokacin yana taje gashinsa a gaban mudubi.
"Allah ko matas?"
Ta daga masa yatsu uku tana gyada kai alamar ya yi kyau.
"Na gode sai na dawo."
"Ah ka manta."
Ya juyo yace "Me?"
"Baka yi hugging ɗina ba."
"Awww! Shi yasa nake son ki zo nan come ne take a cuddle."
Suka rungume juna ta raka shi har bakin ƙofa ta masa addu'a ya fita.
Ta sake share ko ina ta kunna turaren ƙamshi ta sake wanka ta sauya wasu kayan tayi sallar la'asar lokacin anyi sallah. Nan tayi zamanta tana danne-danne a wayarta. Daga ƙarshe ta kira Mama ta kira Abba Alhaji sanann ta kira Barra ta kira Aunty Karima har sai da katin wayar ya kare tas sannan ta haƙura. Har karfe biyar da rabi bai dawo ba ta fara jin yunwa gashi babu abincin a ciki sai ta ɗebo dubulan da gereba ta haɗa shayi ta ci.
Tana zaune ta ji ana buga ƙofa ta tashi ta ja mayafinta ta yafa ta fita.
"Waye?"
"Ke dalla can buɗe masu gidan ne."
Ta rasa me ta musu da suke mata irin haka ƙiri-ƙiri suke nuna mata ƙiyaya.
Ta buɗe ƙofar a hankali sai ta ga Umaima ce ma amma sai ta maze tace "Umaima kece ashe shigo mana?"
"A'a ba shigowa na zo yi ba zuwa nayi na gaya miki Umma na kiran ki." Tana gama faɗa ta fice.
Ita kuma ta hau tunanin me yasa Umma ke kiranta Allah ba wani laifin ta mata ba.
Ta shuri takalmanta tayi waje.
"Gani Umma."
"Na gan ki."
Sai tayi shiru dai to me zata ce?
"Kin min tsaye mara kunya ke kuma taki kalar tarbiyyar kenan?"
Da sauri ta sunkuya ƙasa tana jijiga mata kai tace "A'a ba haka bane kiyi haƙuri don Allah."
"Sai aukin bayar da haƙuri bayan kina sane kike iskancin." Aunty Firdausi ta faɗa.
"Kin wani tafi can kin zauna ni ba a haka a gidana fitowa za ki yi kiyi shara kiyi min wanke-wanke ko ina ki gyara shi tsab bana son ƙazanta kuma gwanda ma ki sani wannan ayyukan kece za ki na yin su daga yau girki, shara, wanke-wanke wanki ban ɗauke miki komai ba don ba zuwa kika yi ki miƙe ƙafa ba kawai ba maganar raba tukunya idan kin girka ki ɗibar muku ki kai can amma ban yarda ki dafa ko ruwan zafi ba ne a gidan nan."
Gaba ɗaya kanta ya ɗauki caji bata saba ba bata taɓa jin wannan abun ba tana amarya guda a ranar ta na farko ta soma cin karo da wasu salo iri-iri na daban. Anya kuwa....
Wata tsawa ta daka mata tace "Tashi mana." Jikinta ya soma rawa har sai da ta faɗi a ƙasa a nan inda take.
"Ji munafurci Umma salon wani ya ce dukanta kika yi."
"A faɗa mana ni akwai shegen da nake shayi ne?"
"Babu fa Umma ba wani shege ai kin isa girman ki ne matar ɗan ki ce ya hallata."
"Kina kallona kamar baki san Umma ba zata bari kiyi abinci daban ba, sannan akan ki ko ƙawar ki ai ba zan saɓawa mahaifiyata ba ko?"
A sanyayye tace "Haka ne kayi haƙuri ni idan ka min izini zan dafa ba tare da ta sani ba ina da ƙaramar electric kuma ana samun wuta sai na girka a uwarɗaka ba zata san nayi ba."
"Wannan kuma ke kika sani. Kawai dai babu wani cefane da zan miki wurin ki zasu zo ki san yadda za kiyi dasu don ban gayyaci kowa ba."
"Barra ce fa?" Ta faɗa cike da mamaki.
"Barran!"
Daga haka bata sake cewa komai ba har ya gama sabgoginsa ya fice. Ita kuma ta koma barin Umma tayi duk wani abu da ya dace sannan ta koma ɓarinta in har ayyukan gidan ne ma har ta saba ta daina damuwa.
Bayan anyi sallar magariba ta rasa yadda zata yi ta samu kuɗin da zata yiwa su Barra abin arziƙi kawai sai ta yanke shawarar kiran Yaya Jamilu a waya.
"Hello Yaya."
"Amarya ce yaya gida yaya kike?"
"Lafiya ƙalau Yaya. Ya su Mama da Auntyn?"
"Kowa lafiya ƙalau ina fatan ba wata matsala ko?"
"Eh komai lafiya Yaya."
"To hakan yayi. Ya aka yi?"
"Yaya don Allah kuɗi nake son ka tura min zan yi baƙi ne kuma bana son na takura masa da bani-bani."
"Ba matsala zan tura miki amma ina fatan babu wata matsala ko?"
"Eh Yaya babu wata matsala."
"To! To shi kenan."
Ya kashe wayar. Ba ayi minti biyar ba alert ya shigar mata ta banki dubu ashirin ya tura mata tayi ta murna ta kira shi tana masa godiya yace ba komai. Ta gama lissafin abubuwan da zata yi kuma me zata siya sai jiran safiya kawai sai dai tana ta nazarin taje da kanta ne ko kuma ta aika Aimana amma kuma ai bata son Umma ta sani kawai ta yanke da kanta zata yi siyayyar kawai. Bata gaya masa ta samu kuɗi ba.
Da ya dawo ya ci abinci ya kwanta cikin dare ya lalube ta son ransa kafin ya ƙyale ta inda sabo ta saba ta ma daina damuwa. Yana gamawa ta tashi taje tayi wanka ta kwanta.
*
Da safe ta dama kunu tayi ƙosai kowa ta zuba masa yadda ake yi. Tana shirin tashi Umma tace mata "Zauna nan." Ba musu ta zauna.
"Wai ni yanzu watan ki nawa a gidan nan ne?"
"Wata biyu ne da rabi an kusa uku."
"Amma na ji shiru har yanzu babu wani labari?"
Bata gane nufinta ba haka ya saka tace "Umma ban gane ba.'"
"Yo ya za ayi ki gane dama tunda munafuka ce ke. To da gwari-gwari ina batun ciki ko juya ce? In juya ce tun wuri na san inda dare ya min na watsa ki na auro masa wata don ni ban son harkar hau. Kin gan ni nan ina da wata ɗaya na fara laulayin yayansu ke kuma na ga tsit ba fa zan ɗauka ba."
Shiru tayi kamar anyi ruwa an ɗauk ta rasa me ma zata ce mata jikinta duk ya yi la'asar. To me zata ce mata duka-duka yaushe aka yi auren ma da za a soma maganar ta ƙi haihuwa lamarin matar ya fara takura mata Wallahi.
Ta nuna ta da yatsa "Wallahi in ma wani abin kike sha ki daina tun wuri don idan na kama ki kina shan ƙwayoyin hana ɗaukar ciki sai na kora ki gidan uba da uwa."
Ta haɗiyi yawu cike da taƙaicin Umma na son dinga sako iyayenta a maganar ta anyhow.
"To." Kawai ta faɗa a takaice.
Tashi tayi ta fita tana jin ƙirjinta na mata wani irin suya. A kwance yake a kan gado sai sauke numfashi yake yi yana baccinsa haiƙan. Babu ruwan shi da wata damuwa saboda shi namiji ne kuma ɗanta komai ma ya yi daidai ne.
Jira take yi ya fita taje tayi siyayayarta amma kamar baya son fita ma a ranar da ta ga sha biyu ta kusa kawai sai ta kira Aimana suka keɓe a soron gidan ta gaya mata yadda take so ayi.