GABA TA ZO BAYA

Chapter 8

by @khairatup01

GABA TAZO BAYA
Ummulkhair S Panisau 
(Khairatup)
008

Tsawar da aka yi ce ta firgita ta har ta dawo cikin hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke iya tuna wancan rayuwar kamar a majigi.
Numfashi ta shaƙa ta fesar ta koma da baya wani murmushi ne ya ƙuɓuce mata a laɓɓanta in ta tuna wasu abubuwan sai ta ɗauka ba zata sake yin rayuwa ba, in ta tuna baya ta auna da yanzu sai ta sake godewa Allah wani abin kuma idan ta tuna sai ta ji haushin kanta ya kamata na yin saken da suka yi mata wasu abubuwan. 
Wata zuciyar ta ce da ita "Ya kamata ki kira shi ki ji yanayin jikin na shi ko na komai ai mijin ki ne."
Shawarar da Zuciyarta ta gaya mata ta ɗauka ta kira layin sa, bata san ya aka yi ya ɗaga ba kawai ta jiyo muryarsa kamar yana faɗa.
"Sai yanzu za ki kira ni?"
Ta zare wayar daga kunnenta ta sa haƙoranta na sama da na kasa ta datse harshenta ta rintse idanu. Sai kuma ta mai da wayar kunnenta tace "Ina wuni?"
"Ban gan shi ba!"
"Ya jikin naka?"
"Kin damu ki sani ne?"
"Na damu mana?"
"Mtsw!" Ya yi tsaki. Bata ji komai ba saboda a ɗan tarrayar da suka yi tare ta gane shi mafaɗaci ne kuma baya iya ɓoye ɓacin ransa in ka masa zai gaya maka kai-tsaye sai dai ka daina kula ki ko ka ji haushinsa baya ɓoye abu a ransa ko zaka ji daɗi ko ba zaka ji daɗi ba.
"To kayi haƙuri."
"Ba zan haƙura ba."
"To ka rama."
"Zan rama ai ba sai kin faɗa ba."
Tayi dariya.
"Dariya ma kike yi min?"
"A'a ban yi dariya ba kunnen ka ne."
"Hauka na fara ko?"
"A'a ban ce ba."
"Kin ga bacci zanyi mene ya faru kika kirani da dadaddare?"
"So nake na ji ya jikin na ka."
"Da sauki kamar yadda kika ji murya ta raɗau."
"To Alhamdu lillah sannu."
"Yauwa."
Sai suka yi shiru duka su biyun sai saukar numfashin junansu ke tashi kawai. Da ya gaji da shirun yace da ita "Gobe zaki zo ko?"
"Ina kenan?"
"Ban sani ba."
Tayi murmushi tace "Me yasa kake saurin hasala ne?"
"Marin ki zan yi."
Tayi dariya kawai. Bata san me yasa ba bata san ya aka yi ba yau tana jin zata iya Tsokanar sa son ranta ta riga ta gama gane laggonsa.
"Nace za ki zo?"
"To."
"Ba to ba za ki zo?"
"Zan zo."
"Ke kaɗai za ki zo."
"To ai Mama ba zata bari na fita ba."
"Mama ba zata hana ki zuwa gun mijin ki ba."
"Kawai sai na ce mata zan je gun ka?"
"Ni sai na kirata na gaya mata za ki zo ki gan ni."
"Kuma zaka iya ɗin?"
"Wallahi zan iya."
"Na yarda."
"Kiyi min kunu kin ji?"
"To zan yi maka."
"Amma fa gidana zaki zo an sallame ni."
"Gidan ka kuma?"
"Eh na ji kin ja harda gunna."
"Gida fa?"
"Kika kuma maimaitawa sai na buge bakin ki."
Tayi shiru ta zame ta kwanta a kan gadon tana da na sanin ma me yasa ta kira shi. 
"Ba zaki zo ba ko?" Tayi masa banza.
Ya ƙulu kuwa.
"Shi kenan tunda haka ne umarni na baki ba shawara ba sai kin zo in baki zo ba ai kin san abinda Allah Ya tanadar miki ko?"
Tayi rau-rau da idanu waje tace "Haba mana."
"Na gama magana ki yi min abinci kin ji?"
Bata ba shi amsa ba shi kuma ya kashe wayar ta bi waya da kallo a hannu.
Ta ina ma sata soma cewa Mama zata je gidan sa? To me zata yi a gidansa. Ta haɗiyi yawu da ƙyar ta juya ɗaya ɓarin ta kasa sukuni sai juyi take yi kawai a kan gadon. A haka har bacci ya ɗauke ta sai kiran assalatu ta ji. Miƙa tayi ta tashi zaune tayi addu'a sanan ta sauke ƙafafunta ta shiga banɗaki tayi brush tayi alwala sannan yayi raka'atul fijir ta jira jam'i suna jin sallah sosai saboda a jikin massalacin gidansu yake. Da suka idar bata tashi ba sai da tayi azkar ɗinta sannan ta tashi. 
Falon Mama ta isa ta gaishe su sannan ta koma ɗakinta ta kwanta ba ita ta tashi ba sai wajen tara na safe. 
Shi ma Uwani ce ta shigo ta taɓa ta.
"Uwanin Mama."
"Tashi ɗiyar albarka ki zo ki ɗora tukunya mijinki yayi neman alfarma abincin matarsa yake son ci kuma Abba Alhaji ya ba shi izini."
Wani irin wuntsulowa tayi daga gado sai jin ta tayi daɓas a ƙasa ta zube ta sa hannu tana murza idanu ko bacci ne bai sake ta ba.
Uwani ta yi dariya tace "Ke kam anyi mara ƙwari."
"Uwani me kike ce?"
"Cewa nayi ki zo ki yiwa mijinki girki. Zai aiko mota. Tashi ki shirya da kyau."
Miƙewa tayi da sauri tace "Me kike cewa ne?"
"Allah da gaske nake Miki."
"Waye ya kira Abba?"
"Wannan mijin naki mai sunan yan gayu bana iya fadar ɗaya sunan Muhammad dai."
Kan gadon ta koma ta zauna tana zumburar baki. Tunani ya faɗa. "wato ya san ba zata je ɗin ba shi ne ya biyo mata ta haka? Shi ne ya kira Abba Alhaji tunda ya san Abban mutum ne mai girmama matsayin miji da aure gaskiya ya yi mata aika-aika kuma ba don yayi hakan ba tabbas ba zata je ba sai ta nemo wani abun ta laƙawa kanta."
Tana wanann tunanin taji ihun Mama na kiran sunan ta "Wai ba zaki fito ba don ubanki sai na zo?"
Tashi tayi da sauri ta saka sliffers ɗinta a waje ta fita.
"Wani daren za a sake yi miki ne tun ɗazu na aika a kira ki kin kwanta ko ba ki san ba a barin mara lafiya da yunwa ba ko sai motar ta zo baki shirya ba wane irin abu ne wannan fisabilillahi."
Ta sunkuyar da kai kamar zata yi kuka amma sai ta danne tace "Mama me za a dafa amma don Allah duk jama'ar gidansu a rasa mai kai masa girki sai ni?"
Mama ta kama haɓa ta ajiye tsitsiyar hannunta tace "Ba shakka! Eh kin haɗu to ke ya ce saboda ke ce ya fi iko da ita ke ce a ƙasan sa ke ce matarsa ke yake so ki kai masa in ba za ki iya ba kuma ya rage naki ki kira shi ki sanar mai ba za ki yi ba kin ga shi kenan ya san tarbiyyar gidan Alhaji Abdurrahman."
"Kai Mama me ya kawo Abba kuma ciki?"
"Uwarki!" Ta faɗa kai-tsaye tana kallonta.
Don ta kawo ƙarshen mujadalar ta da Mama ya saka ta juya tayi hanyar kitchen tana ƙunkunai haka har ta soma yin komai bata bar kitchen ba sai da ta haɗa light abinci har tea sai da ta dafa mai kayan ƙamshi jaysar foods tea spices(***) kayan ƙamshinta gangariya ne masu sanyin ƙamshi da daɗi ga tashin kan mai gida da ma baƙi.
A gurguje ta je tayi wanka ta saka wata Abaya baƙa an mata ado da wasu duwatsu kana ganin abayar ka san tsadaddiya ce ta ɗaura mayafin abayar gashinta ya bada wani cukus a baya saboda a tsefe yake, ta fesa turare kaɗan ba da yawa ba, ko kwalli bata saka ba ta lakaci vasline ta shafa a leɓɓenta. Jearsy veil ɗin nan ta samu mai ruwan kasa ta yafa ta saka agogo sannan ta dauko glasses ɗinta ta saka fes ta fito da ita. Yar ƙaramar jaka ta ɗauko ta saƙala a hannu tuni ta fito a matar manyanta.
Ko Mama sai da tace "Tabarakallah?!" Lokacin da ta fito ta jima bata ga ta yi kyau irin na yau ba tana dariya tace "Yauwa ko ke fa? Yanzu kika yi fes da ke ai."
"Mama." Ta faɗa tana murnushi.
Yaron Abba Biliya ne ya shigo da sallama yace "Aunty Nihila ya iso wai."
"Ka saka komai a mota?"
"Komai an saka."
"To je ka gani nan."
"An gama Autar Mama."
"Mama zan tafi amma tsoro nake ji."
"Ba abinda zai faru ke dai Allah Ya sauke ku lafiya."
"Amin. Sai na dawo."
"A dawo lafiya ki gaishe da Hajiyar shi kuma kice masa ina masa ya jiki Allah Ya sa kaffara."
"To zan gaya masa sai Anjima."
Ta fice Mama ta bi bayanta da kallon murna.
Motar da ta ɗauko Nihila ta dinga ratsawa ta kan titi tana shiga layuka. Tun daga nesa take hango manyan gidaje masu katanga irin na alfarma,amma bata ga wanda ya ɗaga mata hankali ba irin ƙofar gidansu Azlan tun daga gate ma hankalinta ya tashi bare ta kai ga shiga ciki.
Ɗaga kanta tayi sosai tana ganin yadda ƙaton gate ɗin aka rubuta sunan gidan da manyan harufan masu ƙyalli. A gefen gate ɗin kuwa wani ɗaku ne na masu gadi.
Mai gadin ya buɗe gare ɗin cikin girmamawa bayan ya gane motar. A lokacin da motar ta shiga cikin harabar gidan,idanuwan Nihila suka sake girma a fili kuwa ta furta "Subahanallahi.." Doguwar hanya ce da aka yi da tayal mai sheƙi har cikin ainihin ginin gidan. A gefen hanyar akwai korayen ciyayi da aka gyara cikin tsari irin na gidajen sarauta. Furanni masu launuka daban-daban da suka ƙarawa wurin kyau yayin da dogayen bishiyun dabino ke jere a gefe wanda suka ƙarawa wurin martaba.
A tsakiyar harabar kuwa akwai wata babbar maɓuɓɓugar ruwa mai fasalin zamani. Ruwa yana walƙiya kamar lu'ulu'u a ƙarƙashin hasken rana.Nihila ta ji kamar tana cikin wani fim.Tun tana yarinya take jin labari kuma take karanta irin wanann arziƙin sai dai bata taɓa gasgantawa ba sai a yau da ta shigo da kanta. Motar ta tsaya a ƙofar shiga. Babban ginin gidan ya kasance bene mai hawa biyu,an yi masa zanen fari da ash. Tagogin manya-manya ne masu gilashi na musanmman da ke nuna alfarmar ginin. A saman gidan kuma akwai fitilu na ado da suka ƙara kawata gidan.
A hankali ta fito daga cikin motar,ta tsaya na dan lokaci tana kallon ginin. "Wai mutane ne zaune a irin wanann gidan yanzu?" Ta tambayi kanta. Ta taka a hankali zuwa ƙofar shiga.Ƙofar kanta ta isa a ce an yi ta ne don a fade ta. Katako ne mai tsada da aka sassaƙa da zane-zane masu ƙayatarwa.
Mai aikin gidan ce ta buɗe mata ƙofar.
Tayi mamakin yadda aka yi ta gan ta ita dai ta samu ƙarfin halin yin sallama.
"Salamu alaikum"
"Wa'alaikum Salam. Sannu da zuwa Hajiya." 
"Na gode." Kawai ta iya faɗa. Ta shigar da ita ciki. Tana shiga fakon farko taji kamar numfahsinta zai ɗauke. Falon babba ne ƙwarai da gaske an shimfiɗa carpet mai kauri da taushi wanda in ka taka kamar kana taka auduga. Kujerun falon kuwa ba irin wanda ake gani a ko ina ba ne. An yi su da fata masu laushi launin cream da zinariya. Tsakaninsu akwai manyan tebura na gilashi masu sheƙi. A jikin bango kuwa an rataye Manyan hotuna masu tsada da kuma wasu zane-zanen zamani masu ɗaukar hankali.
A sama akwai wata chandelier mai walƙiya a rataye daga saman rufin falon,tana haskaka ko ina da wani irin haske.
Dayan bayan ɗaya Nihila ke kallon komai. A ranta kuwa cewa tayi "Lallai Azlan ɗan gata ne ya tashi a irin wannan wurin dole kuwa ɗabi'ar sa da mu'amalarsa da tarbiyyar sa su kasance na daban."
Wani sashin daban aka wuce da ita a hanya ta dinga ganin ƙanan falaye daban-daban da kujeru kala-kala har hakan ya so ya rikita ta. Ga wani ƙaton dinning area da zai iya cin mutane sama da ashirin. Kitchen ɗin cike da kayan aiki na zamani da suka fi samuwa a kitchen ɗin otel.
Duk inda idonta ya sauka sai ta ga komai a tsare cike da ƙawa da burgewa babu hayaniya, babu cunkoso babu abinda bai dace da wurinsa ba komai yana da nasa matsayin.
Da suka ƙarasa gaban falon Ammi,zuciyar Nihila take ta dokawa. Fakon ya fi wanda ta gani da farko girma da komai.
Kujeru ne na alfarma,labulai masu tsada,fitilu masu ƙayatarwa da ƙamshin turare mai daɗi. A tsakiyar kujerun kuwa Ammi ce a zaune cikin doguwar rigar atampa da ɗaurin nan na baya Turai Yar'adua.
Fuskarta cike da annuri da walwala. 
"Assalamu alaikum Ya Nihila." Ammi ta faɗa tana murmushin da ya kai har ƙasan ranta.
Nihila tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa ta zube a ƙasa tsakiyar falon.
"Wa'alaikum Salam Ammi."
"Tashi! Tashi ki zo nan."
Ta ƙaraso cikin girmamawa.Ammi ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita.
"Yaya kike?"
"Lafiya Lau." Ta faɗa muryarta na rawa.
"Ki saki jikin ki Nihila kema ɗiyata ce kamar su Nuwaira."
"In sha Allahu Ammi."
Nihila ta ji daɗin yadda Ammi ta ƙarbeta saɓanin lokacin da Umma ta tarbeta da ta auri Abdullahi. Ammi mace ce mara iko da girman kai ko nuna isa ga dai arzikin amma babu girman kai.
"Yana ɗakinsa yau ya bore sai ke ce za ki ba shi abinci."
Bata iya cewa komai ba.
Ammi tayi murmuhsi ta miƙe tace "Fita zanyi daman. Ki hau sama daki na biyu daga gefen dama nan ne ɗakin mijinki."
Ta sake kallon fuskar Ammi. Fuskar nan ta uwa mai cike da tausayi da karamci. Sai ta ji ta fi kowa dace da samun uwar miji.
Ta nufi matakalar benen  mai sheƙi yayin da take hawa,Zuciyarta na bugawa da sauri. Ba wai saboda girman gidan ba,ba wai saboda alfarma ba, sai saboda mutumin da take shirin gani Dr.Muhammad Azlan.Mutumin da yake ƙoƙarin sauya mata akalar rayuwa gaba ɗaya.
Ta tsaya a gaban ƙofar ɗakin da Ammi ta kwatanta mata hannunta na rawa yayin da take koƙarin buɗe ƙofar a hankali ta ja numfashi sanann ta buɗe ƙofar kai ka ce jarabawa zata zana ko kuma interview ɗin aiki zata.
Da farko ƙamshin turaren Azlan ne ya bugi hancinta,wani ƙamshi mai sanyi da nutsuwa. Idonta ya fara yawo cikin ɗakin. Ta sake tsayawa cak tana ƙara yiwa Allah tasbihi.Ɗakin na da girma kai ka ce wani ƙaramin gida ne mai ɗaki ɗaya kamar dai gidan ba a ƙasarmu ba kai kace ƙasar waje ne. Bangon ɗakin fari ne mai ɗan ratsin ruwan toka,yayin da manyan tagogin gilashi ke barin hasken rana na ratsowa ta ciki.
A gefe kuma wani ɗan falo ne da aka tsara da kujeru masu tsada,da kuma wani book shelf cike da litattafai.
Idanunta suka sake sauka a kan faɗeɗen gadon da Azlan yake kai sanye da gajeren wando mai launin baƙi da farar rigar bacci marar hannu. Saboda rashin lafiyar da ya yi ta kwana ɗaya har fuskar sa sai da ta yi yar rama,amma hakan bai rage masa kwarjini ba. Kansa kwance a kan matashi yayin da idanunsa ke a lumshe.
Nihila ta ji zuciyarta ta yi wata irin bugawa.
A karon farko take ganinsa a cikin yanayi haka.
Ba cikin shiga ta aiki ba,ba cikin ƙasaita da kwarjininsa irin na kullum ba. Sai don matsayin mutum mai buƙatar kulawa.
A hankali ta taka zuwa kusa da gadon. Ta tsaya tana kallonsa. Ta kasa Musa cewa Azlan kyakyawan namiji ne ko a cikin halin rashin lafiya yana nan da wani irin kwarjini da ke saka mutum kasa ɗauke idanuwansa daga kansa. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali daidai da lokacin da Azlan ya buɗe idanunsa. Da farko bai gane wa yake gani ba sai kuma da idanunsa suka buɗe sosai ya saki murmushi yace "Nihila." Muryarsa a raunane. Nihila ta ji wani abu ya doki zuciyar ta.
"Yaya jikin na ka?"
Azlan bai yi kuskure ɗauke idanunsa daga kan fuskar ta ba.
"Yanzu da na gan ki sai na ji na warke duka."
"Wanann ai ba amsa ba ce."
Ya ɗan yi dariya ,dariyar ma a raunane.
"Alhamdu lillah. Ina samun sauƙi."
Ta ja kujera ta zauna kusa da shi.
"Wai da gaske ka kira Abba Alhaji ka ce ya bari na zo na kawo maka abinci."
Ya gyaɗa mata kai yace "Ni ne."
"Amma baka ji kunya ba?"
"Abbana ne fa kuma ke matata ce."
"Gaskiya baka ji."
Ya ƙyata mata ido yace "Na sani."
"Ina girkin kin yi min ma kuwa?"
Ta sauke kanta ƙasa tana wasa da zaren mayafinta a hankali tace "Nayi."
Azlan ya motsa kai kaɗan kuma ya ji dadin amsar yace "Da gaske?"
"Eh."
"To ina basket ɗin?"
Nihila kuwa ji take yi kamar tana cikin wani yanayi da zuciyarta ke ƙoƙarin guda,amma jikinta ya kasa bata haɗin kai. 
"To yana ina yunwa nake ji da kika gan ni nan ko tea ban sha ba ina ta jiran ki." Ya faɗa yana shafa cikinsa.
Tayi sunkuyi da kai ƙasa tace "Na manta a cikin mota."
"Haba don Allah waye ya kawo ki?"
"Ban san shi ba."
"To ina zuwa." Ya faɗa yana saukowa daga kan gadon kan ya kai tagar ɗakin ya zare rigar jikinsa ta kulle idanu da sauri cike da kunya ba don wai bata saba ganin namiji a haka ba sai don tana kallon wanann rayuwar a matsayin sabuwar rayuwa wadda bata hanga ba wadda bata taɓa zata ba wai ta ga wani bayan Abdullahi.
Ya isa jikin taga a gefensa da akwai wata yar ƙaramar landline ya yi dialing sai ji tayi yana tambayar waye ya kawo matarsa yanzu.
Abin dariya ma ya bata har sai da ta kasa hana murmushin fitowa. Kawai dai taji yace "Ok" ya ajiye waya.
Ya koma ya zauna a kan gadon ya soma lalube a cikin duvet tace "Me kake nema?"
"Wani abu ne ya ɓace min a ciki ko za ki taya ni dubawa abin na da muhimmaci sosai."
Ta miƙe innocently ba tare da wani tunani ba ta hau kan gadon ta yaye duvet ɗin sai dai bata ga komai ba a ciki tana juyawa ta ga ya ma daina laluben kawai ya zauna yana kallonta kamar bai taɓa ganinta ba.
"Ban ga komai ba."
Ba zato ba tsammani kawai ya sa hannunsa ya janyota jikinsa gabaɗaya ta faɗa kan sa suka zube a kan katifar gabaɗayansu su biyun. Ita ce a samansa amma bata yarda ta buɗe idanunta ba ruf ta kulle su saboda tsananin kunya da kuma tsoron da ya ziyarce ta a lokaci guda. Shi kuwa ya kafa mata na mujiyarsa yana kallo cike da admiration baya son wannan yanayin ya wuce yana son su kasance a haka kawai ba tare da wani damuwa ko tsaiko ba saukar numfashinta na ƙara masa wani irin abu a gangar jikinsa da ruhinsa.
Umarnin da gangar jikinsa ke ba shi yake bi kawai ya sa hannayensa biyu ya tallafi fuskarta jikin ta shi yana jin kamar ya sumbaci leɓɓenta sai dai kafin ya kai ga cimma burinsa ta buɗe idanunta da sauri suka yi ido huɗu da juna ta daburburce bata ma san lokacin da tayi tsalle ta dire ƙasa ba.
Yace "Ufff! Wannan matar zata wahalar da mijinta da yawa ashe."
Bata ce komai ba jikinta sai rawa yake yi kawai.
Ya jingina da matashin fillo yana kallonta hannayensa sarƙe da ƙirjinsa.
Aka ƙwankwasa ƙofa ya kalleta  a inda take kawai yace "Shigo." Mai aikin gidan ne ya shigo a hannunsa ɗaya da basket ɗin abinci ɗayan kuma kwalin magani ne.
"Yallaɓai ga shi Ammi tace kayi wanka tukunna sai ka ci abincin ka sha magani."
Azlan ya ɗaga masa gira kawai ya juya ya fita.
"Kin ji abinda Ammi tace ko?"
"Na ji ka tashi kayi wankan."
Azlan ya miƙe daga kan gadon a hankali ko da yake ga samu sauƙi,sai dai akwai gajiya a tare da shi.
Wani sashi na ɗakin ya nufa da wani babban walk in closet a gefe sannan ka hangi ƙofar banɗakin ta alfarma.
Kafin ya shiga ya waiwaya ya kalle ta.
"Ban ce ki tafi ba fa."
Ta harare shi.
Yace "Kin iya wanann abin ashe."
Tayi dariya ya juya ya shiga.
Yana shiga ta sauke ajiyar zuciya ta yiwa ɗakin kallon nutsuwa sai a lokacin ta lura da abubuwa da dama a ciki.
Babban hoton su ta gani akan shelf da Abbi da Ammi da ƙannensa mata da maza da yayanshi da jikokin gidan harda Nafisa a jiki hoton yayi kyau gabaɗayansu farare ne tas babu mai duhu sai dai na wani yafi na wani.
Da ta gaji da kalle-kallen sai ta zauna tana duba wani littafi kusan mintuna talatin kafin ya fito.
Cikin wata shadda fara an mata aiki na gaske a jiki.Gashin kansa a jiƙe turaren jikinsa ya gauraya da ƙamshin sabulun da yayi amfani da shi. Suna haɗa idanu ta ɗauke kai.
Yace "Wai kunya kike ji?"
"Eh."
"Baki isa ba Wallahi."
"Ka samu ka ci abincin ka sha maganin ka."
"Likita ce ke ne?"
Kafin ta bashi amsa aka tura ƙofar ɗakin.
Rayyan ya fara gani sanann Nadir sai little Nasreen da ɗaya da ɗaya suka dinga shiga cikin ɗakin.
"Yaya Azlan!"
"Amma baku da mutunci uban me ya kawo ku ina ganawa da matata?"
Rayyan yace "Shi yasa ashe tun safe Yaya yake tambayar mu ko kin zo ashe-ashe."
Suka sa dariya "Nuwaira ta rungume ta."
"Kai ku fitar min daga ɗaki."
"Haba ɗakin gidan Abbi dai kai ba ga gidan ka can ba."
Nuwaira ta sake mannewa Nihila tace "Kin san me?"
"Me?"
"Yau Yaya Azlan ba zai iya bacci ba don murnar ganin ki."
"Nuwairaaaa." Ta ja sunan cike da kunya.
"Ai gaskiya ta faɗa." Mubeen ya faɗa.
Nan fa suka yi ta hira har sai da Ammi ta shigo da kanta tace "Ku kyale min ya haka haba."
"Ammi wasa fa muke yi mata."
Azlan ya zauna a kan kujera.Nuwaira ta zuba amsa abinci yana ci yana santi duk suka yi kan shi ya basu ya ƙi da ƙyar ya basu spoon ɗai-ɗai suna ta santi Ammi ma sai da ta ci cokali biyu da ƙyar.
Wani sanyi mai daɗi ya ratsa Nihila ƙwalla ta sauko mata na farin ciki da gamsuwa wataƙila gidan take tsoron shigar sa a farko shi ne wurin da ƙaddara take son ta samu natsuwa a ciki. Ko ba a faɗa ba tayi dacen dangin miji.
Azlan da yake kallonta suka haɗ ido ya ɗaga mata gira alamar mene ne ta girgiza masa kai.