Chapter 9
by @khairatup01
***
GABA TAZO BAYA!
Ummulkhair S Panisau
(Khairatup)
009
"Amma yanzu shi kenan haka zan zauna na zuba ido na ga gidana yana neman gagarata?"
Sai da Amma ta taɓe baki sannan tace "Gaggawar ki ce ta janyo hakan, ban taɓa sanin ke mahaukaciya ba ce sai jiya uban waye ma ya baki wanann shawarar mu ɗauka Azlan ya mutu ribar me kika samu? Ba ɗa ba komai kin tashi a tutar babu da waye zaki yi kishin kin kashe shi?"
"Amma ban zaci ciwon na shi zai tashi ba nima idanuna ne suka rufe da kishi amma ban...."
"Rufe min baki shashasha ilimin ki bai miki komai ba saboda ke duk wani tsari na yana kan hanyar rushewa kuma baki isa ba Wallahi."
"To Amma yanzu me za ayi?"
"Ke kika sani ke za ki nema wa kan ki mafita tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke duka."
"Haba Amma taya zan iya wannan aikin kiyiwa Ammi magana mana kin ga dai ai ita tana jin maganar ki."
"Ki roƙi Allah Abbin ki kar ya ji wannan ta'asar kin sani sarai goyon bayan ya'yan ɗan'uwan shi zai yi."
"Amma don Allah kiyi wani abu Allah ina son Azlan sosai ke kin sani kina ganin fa ta yadda na samu ya aure ni amma duk da haka ban gama mallakar zuciyarsa ba tsawon shekaru goma."
"To ya za'ayi ki mallake shi kina shirmen? Kin haihu ne? Abinda zai sa ki mallake shi babu to ki gaya min ta yaya za ki mallake shi?"
Nafisa ta saka kuka ta sa hannayenta biyu ta rufe fuskar ta kullum in ta tuna wannan abu sai hankalinta ya tashi."
"Allah ne be kawo ba Amma."
"To Allah Ya kawo, san da ya kawo i wasa kika yi da damar ki kece silar da ya saka ya koma shi yasa Azlan yake ganin baƙin ki taurin kan ki dai shi ne yake rusa mana komai har kullum."
"Amma ban san haka zata faru ba ban sani ba."
"Aikin banza tashi ki bani wuri nayi tunanin me ya kamata muyi."
"Amma don Allah bana son na rasa Azlan ki taimaka min."
Tausayin Nafisa ya kamata ta saka hannunta ta shafa kanta ta lumshe mata idanu tace "Ke fa jinina ce ta yaya za ayi na bari ki zama bora? Auren ma an yi min bazata ne da ba za ayi shi ba Wallahi kuma ba zai zauna ba sai na san yadda nayi na datse masa numfashi sanann hankalina zai kwanta ita kuma Zainab ya zama dole ta ɗanɗane ni."
Nafisa ta rungume mahaifiyarta cike da samun wani sanyi a wani sashi na Zuciyarta.
Tana son Azlan kuma babu fashi bazata bar wa Nihila shi ba saboda ita ta sha gwagwarmaya da shi ba kowa ba yanzu kuma da suka kai wanann lokacin ai ba zata yi wasa da damar ta ba.
Amma tace "In kun san wata baku san wata ba."
*
"Bata dawo ba ne har yanzu Bilkisu."
"Bata dawo ba Alhaji."
"To me ya zaunar da ita haka? Ni fa surutai ne bana so."
"Haba Alhaji wane irin surutai sai dai na son rai yarinya da mijinta sai ace surutai ne ba a so?"
"Haka ne, amma dai ya kamata ta dawo haka."
Tayi dariya tana cigaba da zuge zolage sannan tace "Kwanaki kaɗan ya rage ma ta bar maka gidan gaba ɗaya sai na ga ƙulafucin."
Ya yi murmushi"Ba za ki gane yadda nake ji ba a raina Wallahi har yanzu tsoro nake ji kar uwata ta sake faɗawa wata rayuwar Wallahi ina son na ga kwanciyar hankalinta sama da komai ke ai kin san yadda ta gurzu ko?"
"To ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba wani hakan nan zai ji baya kaunar ka wani kuma duk duniya babu abinda yake so sama da kai yadda ka ga yatsun hannayenmu ba ɗaya ba to haka mu ma yan'adam muke kowa halinsa daban kuma ba duk aka taru aka zama ɗaya ba idan wannan mugu ne wancan na kirki ne ina ji a jikina yanzu Nihila ta samu surukai na gari saboda na hango dattako da mutuntaka a cikin ƙwayar idanunsu a kanta babu tsana babu ƙyama babu hantara ba ka ga yadda yan'uwansa suke nan-nan da ita ba Wallahi sai dai muyi musu fata na gari Alhaji."
Ya gyara zamansa yace "Haka ne, to Allah Ya sa albarka Ya sa hakan shi yafi alheri."
"Amin."
"Duk da haka dai ki kirata ki ji yaushe zata dawo."
"Gaskiya ba za a kira ta ba Alhaji ka daure ka saba."
"To shi kenan na ji ai ke dama haka kike so."
Tayi dariya kawai haɗe da miƙewa ta shiga kitchen miyar zogale zata yi sai ta bawa Uwani ta ƙirɓa mata zogalen ita kuma ta soma daka gyaɗa a cikin wani ɗan ƙaramin turmin ta na ƙarfe.
Cikin lokaci kaɗan suka tada kitchen ɗin da ƙamshi.
*
Azlan yace "Wallahi ba kwa kyautawa kawai mutum ya samu matar shi ta zo ganinsa sai ku wani zo ku hana mu sukuni me haka ne wai don Allah Ammi kina gani suka yi min haka waye ma ya ce musu ta zo ne?" Ya faɗa yana kallon Ammi kamar yaron da yake jiran ƙiris ya fashe da kuka.
Ammi tayi murmushi tace "Ban sani ba fa nima yadda ka gan su haka na gansu."
Nihila dai ta kasa sakewa da su.
Nuwaira tace "Sis-in-law zo na gaya miki mu. Kin ga wanann shi ne Rayyan,ga Ashraf,ga Nadir,ga Najla,ga Abeer sai Aunty Nadiya ita tana South Africa da mijinta da yaranta. Wannan small tiny ones ɗin kuma Nasreen,Mubeen da Munseef jikokin Ammi ne and Yaya Kabir babban Yayanmu ba nan yake ba gidansa na can Lamiɗo cresent sai Yaya Adeel na san kin san shi."
A hankali tace "Ma sha Allah! Allah Ya sa mu zauna lafiya dukan mu."
"Amin." Suka amsa.
Ammi tace "Ai kin ga Azlan ko ya girma ne a fuska da jiki amma har yanzu yana abin yara sai kina haƙuri."
"Innallillhi haba Ammi sai yarinya ta raina ni ai."
"Ai gaskiya ce duk wani sirrin Yaya da kike so ni za ki tambaya ni ce PA ɗinsa komai na sa na sani nice ta gaban goshinsa." Nuwaira ta faɗa tana nuna kanta.
Najla tace "Aunty Nihila, ni kuma yar'autan Ammi a mata daga yau ni ce PA ɗin ki nima."
"An gama."
Rayyan yace "By the way nima fa ɗan team ɗin ki ne Aunty amarya kiyi sauri ki tare na dawo gidanki da zama kawai."
"Ji ku, ji ku don Allah kato baligi da kai ne zaka dawo gidan waye?"
"Gidan Aunty Nihila."
"To baka isa ba ƙarya kake yi."
"Cewa fa nayi gidan Aunty Nihila ba gidan ka ba."
"Gidanta ne ma?"
"Eh mana ko Aunty."
Tana dariya tace "Eh gidana ne."
Munseef yace "Nima can zan koma Aunty."
Ta shafa kumatunsa tace "Ina maraba da ku duka."
"Yeah! Yeah! Suka yi ta tsalle suna zagaye har manyan. A cikinsu ma Ashraf ne mara magana sai aukin murmushi da game a waya tunda suka shigo take lura da shi.
Ranar dai a gidansu Azlan ta yini don har girki tare suka yi da yamma a gidan saida suka gama sannan tace zata tafi duk sai suka ji kamar kar ta tafi.
Azlan ya shirya cikin shadda ya sauko sai wani irin murmushi yake yi kana ganinsa ka ga yana cikin walwala da farinciki kamar ba mara lafiyan jiya ba.
Ya karɓi mukullin motar Rayyan yace "Bani aro na kai matata gida."
Rayyan ya ba shi yana dariya yace "Yaya Wallahi kun dace ka ga yadda kuka yi kyau kamar irin amarya da ango zasu gaida iyayen amarya too much Perfect."
"Abinda nake faɗa a raina kenan." Nadir ya faɗa.
Najla ta jerasu guri guda tayi musu hoto kuma hoton ya fita yadda ake so.
"Oya ya isa ku kyale min yarinya ta tafi gida haka ki gaishe da Maman taki da Alhajin mun gode da ziyara."
"Zasu ji in sha Allah."
Nutsuwarta da biyayyarta na daya daga cikin abinda yake burge Ammi da Nihila yarinyar yanayin ta ya yi mata ɗari bisa ɗari saboda bata son mace mara kamun kai ko mai yawan rawar kai.
**
Ta tuna ranar farko da tayi ƙoƙarin yin girki don ƙawayen ta sai da ta sha disgin da har yau bata manta ba.
Lokacin da Aimana ta dawo da ledar cefane tayi ta mata godiya.Ba tare da ɓata lokaci ba ta soma sabgoginta tana girki tana gyara wuri. Gida ya sake ɗaukar haske ga ƙamshi ta ko ina.
Ta ɗauko sababbin fulas ta zuba abincin a ciki ta kai ɗaki ta adana.
Yana tashi daga bacci ya shiga yayi wanka ya sauya kaya.
Lokacin ta dawo daga ɓarin su Umma ta daka Sakwara tayi miyar ganye.
Ya kalli fulas ɗin hannunta yace "Wannan fa?"
"Umma ce tace na kawo maka sakwara nayi."
"Kai amma na ji daɗi bani na ci dama fita zan yi."
Ta ajiye ta ɗauko plate ta zuba masa dama guda biyu ce ba manya malmala ba yan daidai ya ce ta juye masa duka . Bai tambaye ta ta ci ko bata ci ba shi dai kawai cikinsa ya sani. Ya gama ya wanke hannu a bakin famfo tana biye da shi da wani ƙaramin towel. Ya karba ya goge hannunsa.
"Yanzu na ji ni daidai zan fita sai anjima zan dawo akwai abinda zan taho miki da shi ne?"
"A'a ba komai sai ka dawo Allah Ya bada sa'a."
"Amin na gode." Ta raka shi har bakin ƙofa sannan ta koma wanka tayi ita ma ta saka wata atampa super Abba Alhaji ne ya ɗinka mata ita.
Tayi mata kyau kuwa. Sai duba waya take ko Barra ta kirata ba su suka zo ba sai wajen ƙarfe uku na yamma tayi ta mita kuwa.
"Ke waya ke zuwa gidan ma'aurata da wuri sai da muka gama sabgoginmu sannan muka fito ya garin."
"Lafiya Ƙalau Wallahi ya gajiya?"
"Ba gajiya kin gan ki kuwa shegiya kin murmure kin yi shar da ke."
I"Allah ko?" Suka tafa. Nan suka yi ta hira ta kawo musu lemon da ta haɗa ta saka ƙanƙara dama ragowar ta juye ta kai musu suka fara da shi har suka yi sallar la'asar sannan ta kawo musu abincin.
Lafiyayiyar Party jellof rice tayi musu ga nama a ciki.
Barra tace "Uwargida mai capacity ah kina sha'anin ki matar Abdullahi."
Murmushi kawai tayi.
Umaima ce ta fito daga ɗakinsu ta ce da Umma "Wai ba kya jin kamar ana ta shewa a gidan Yaya ko dai baƙi tayi bata gaya miki ba?"
Umma ta ɓantari goro tace "Ya aka yi kika ji ke?"
"Ai kin san ɗakinmu na jikin gininsu gidan bulo yana da sirri ne?"
"Bantan uban can a gidana?"
"Tashi muje mu gani."
Aimana tace "A gaskiya wanann ba halin kirki bane tunda aka kawo yarinya kun hana ta wala ,haba Umma ya za ayi ki biye musu kina uwa? Mu ma fa duk mata ne Allah Ya baki yaya za ki ji idan ana mana irin wannan abin da suke saka ki kina yi."
"Ke na ci uwar ki Aimana don uban ki mugun bakin ki baya tashi sai akan ya'yana a bani wadda nake so mana ba wannan da bana so ba."
"Wallahi Umma ina jiye miki ranar da GABA ZATA ZO BAYA"
"Allah dai Ya yafe miki Aimana amma kamar ba jinin Umma ba wani lokacin in kina bacci har sake duba ki nake yi na gani ko babu wani abu da zai nuna ke ba jininmu bace sai na ga kamar canje aka yiwa Umma a asibiti kuma dai Umman tace ita kaɗai ta haihu a ɗakin ranar ba a mata musanye ba kuma kina kama da Abbanmu."
Aimana ta zabga mata harara tayi tsaki. Bata son su je saboda zasu ga abincin da Nihila tayi duk da ba laifi bane amma a gun Umma da ya'yanta laifi ne babba.
"Don Allah ku kyale ta ƙawayen ta ne suka zo in suka tafi sai kuje."
"Kin ji ko Umma wai ƙawayenta kenan an musu wani abun ƙwalam ko?"
"Yar nan haka ne aiko yau za ayi bala'i a gidan nan in har anyi girki a ɓarin Abdullahi an karya min doka."
"Muje, muje, Umm muje kar a kwashe."
Ta ja Umma tana yiwa Aimana gwallo.
Aimana tace"Allah Ya shirye ku don dai kun samu Nihilar bata da fitina ne kuma ta fito daga gidan tarbiya bata saba ganin irin wannan abin ba amma ina fatan yau da gobe ta koya mata halin ku tana ramawa."
Suna tsaka da cin abincin aka bankaɗo ƙofa aka shigo.
Umma idan ta bai sauka a ko ina ba sai a kan tray ɗin abinci ga lemuka ga nama ga meatpie.
Umaima ta soma tafa hannaye tana salati.
"Umma kalli?"
Da ƙyar Nihila ta haɗiyi yawu saboda tashin hankali har wani gumi ne ya tsatsako mata a goshinta. Da sauri ta miƙe tsaye tace "Umma sannu da zuwa."
Umma ta ɗaga mata hannu da sauri idanunta sun ƙanƙance.
Barra da ta ji ance Umma ita da Ummi suka haɗa baki a tare suka ce "Umma Barka da Yamma."
"Ke! Waye ya baki iznin taka mini dokar gida?"
Nihila tayi tsilli-tsilli da idanu tuni hawaye sun cika fam ƙiris suke jira kawai su fara aikinsu.
"Baki ji tambaya bane waye ya baki izinin taka mini doka? Oh na gane saboda ba ni ce uwar ki ba ko shi yasa kika taka min doka kika yi abinda na haramta miki yin shi."
"Don Allah kiyi haƙuri Umma." Ta faɗa tana hade hannayen ta biyu tana yarfe su kamar wadda za a zane an kamata da laifin sata.
"Wallahi Umma kar ki yarda ko da yake laifin Yaya ne yana nan ya tare a gidin mace kin ga fa kuɗin da aka kashe a wannan girkin."
"Ba shakka Abdullahi ya yi aure wuyansa ya isa yanka da zai yanke hukunci ba tare da ya sanar min ba. Ya baki wannan uban kuɗin kika yi wannan girkin wa ƙartai baligai."
Hankalin Barra da Ummi ya tashi basu taɓa ganin irin wanann masifar ba ya za ace mata da gidanta da mijinta ba zata yi girki ba sai an bata umarni? A ina ake yin hakan? Ba zata iya ba tabbas Nihila na cikin masifa.
Barra tayi ƙarfin halin cewa "Kiyi haƙuri Umma ...."
"Ke yi min shiru bana magana ana magana ,Wallahi sai na fasa miki baki yarinya."
Umaima ta gyaɗa kai.
"Kwaso min abincin nan ke ki kai min can in ga uban da zai amsa. Ai kuɗin ɗana ne wato baki san ciwonsu ba baki san da yadda ya samo su ba shi ne ke kika zo kike burge wasu shi ma munafiki zai zo ya same ni sai ya gaya min nawa ya asarar a nan."
Ba tare da ɓata lokaci ba Umaima ta kwashe komai ta fita lemon da ke cikin jug kuma Umma ta ɗauke tana tsaki.
Suna fita ta saki kukan da bata shirya ba ta sa hannaye biyu ta rufe fuska.
Barra ta sa kukan ita ma tace "Nihila meye haka wanne irin zama ne wannan?"
Tana kuka tana gyaɗa kai ta kasa yin magana jikinta sai rawa yake yi.
Tana shafa bayanta tana lallashinta.
"Ya isa kiyi haƙuri ban san zuwan mu zai zame miki matsala ba da ba zamu zo ba ki daina kuka don Allah."
"Kuyi haƙuri Barra, ban san...." Ta kasa ƙarasawa saboda yadda take shiɗewa.
Tausayinta ya kamata ta rungume ta. Ummi ma jikinta yayi sanyi sosai.
Data daidaita nutsuwarta kukan ya tsaya ta kama hannun Barra da na Ummi tace "Don Allah, kar ku gayawa kowa abinda kuka gani ko kuka ji musanmman ma Mama da Alhaji kun ga suna fama da Aunty Karima ma bare su san nawa hankalin su ya sake tashi sun girma yanzu bana son na rasa su."
"Baki da hankali so kike yi mu bar ki a nan ki mutu?"
"Iya su ne suma zan samu matsayi a wurinsu a gaba babu ruwan Abdullahi yana sona baya bari a ɓata min Umma mahaifiyarsa ce babu yadda zai yi da ita dole ne muyi mata biyayya laifina ne tun farko da ban sanar mata ba tunda ta gaya mini dokokin gidanta."
"Da wacce Iriyar zuciya aka hallice ki Nihila? Ke ba zan iya wanann rayuwar rashin yancin ba ina ilimin naki? Kin manta wace ke ba wanan ce Nihilar da muka sani ba gaskiya ba zai yiwu ba."
Tana kuka ta sake kama hannunta tana roƙonta tace "Yadda Allah Ya rufa muku asiri nima ku rufa min kar ku gayawa kowa faɗar da zaku yi sai yafi karya ni a kan wanann ina son mijina bana son rabuwa da shi."
Haushi ya tiƙe Barra kawai sai ita ma ta zauna ta saki kukan tana faɗin "Innallillhi wa inna illahir rajiun." Suka yi ta maimaitawa a tare har Ummi da ita na kukan take yi. Sai aka rasa mai rarrashin wani a ɗakin. Sai da suka gaji don kan su sannan suka tafi ko sallar magariba basu tsaya sun yi ba.
Kanta har ya soma yin ciwo saboda kuka idanunta kuwa sun kumbura sun yi jajir da su saboda kuka da murza da suka sha.
Sanda ya dawo anyi isha bai shiga ɓarinsa ba ɓarin Umma ya fara shiga .
Suna jin sallamar sa Umma ta fashe da kuka harda ƙara da ihu. Hankalinsa ya tashi ya isa gabanta da sauri ya sunkuya yace "Umma meya faru waye ya taɓaki"
Ramlah tace "Wa kuwa ban da matar ka."
"Nihila kuma?"
"Ita mana. Yarinyar nan don bata da kunya bata da mutunci wai tayi wa Umma tsawa saboda ta mata magana akan abinda tayi ba daidai ba."
Umma ta sake sake saka kuka wanda inda ya lura babu ko ɗigon hawaye a cikin idanunta sai ihun kawai.
"Rashin kunya ta yiwa Umma Nihilar?"
"Sai nanatawa kake yi ƙarya za ayi mata ne? Ko kana ganin ba zata iya ba?"
Tashi ya yi tsaye a fusace ya juya ya fice.
Yana fita suka saka dariya harda tafawa.
Umma tace "Wallahi na saka ta tafi da ƙafafun ta."
"Ai Wallahi Umma sai ta bar mana gidanmu don nan wurin Sameera ne ga inda zamu dangwali arziƙi."
"Faɗi ki ƙara ai bana son yarinyar nan ko kadan kina ganinta kin ga munafuka mai fuska biyu a haka sumi-sumi da ita kamar ta Allah amma zuciyarta baƙa-ƙirin."
"Ai yau zata san waye Yaya sai ma ya kifa mata mari ma tukunna zai sani."
Ko kan sallayar bata bari ba taji ya kira sunanta da wani irin karajin da sai da ta firgita ta zabura ta ji kamar an ja ta daga kan sallayar tayi baya jikinta na rawa.
Yana zuwa ya sa hannayensa biyu ya cakumota ya tayar da ita sama yana matse mata damtsen hannu wanda zafin kamun sai da ya saka kanta sake sarawa tana haɗe haƙora tace "Da zafi Hubby! Ka cika ni me nayi maka don Allah?"
Wata hankaɗa yayi mata da sai da tayi baya ta doki kai da bedside drower ta sa hannu ta tallafe gun da sauri tace "Argh!"
"Umma sa'ar ki ce da za ki mata rashin kunya? Idan Mama ce za ki iya ma maida mata martani ne bare Umma? Kina sona amma ba kya son mahaifiyata dama ana gaya min kina yi mata rashin kunya sama-sama dama kallon ki nake yi so nake yi na kama ki da kaina tukunna sannan na yanke miki hukunci na rantse miki da Allah a kan Umma sai dai ki bar gidan nan ke sai dai ayi uwar watsi kowa ya rasa ashe baki da hankali?"
Saboda ta riga da ta tsorata da shi ma kasa cewa komai tayi kawai sai ta haɗe kai da guiwa ta fashe da kuka tace "Kuyi haƙuri don Allah ban san haka abin zai janyo ba kuyi haƙuri."
"Yaya ƙarya take cewa tayi fa ma tayi girkin ai da ƙudin mijinta ne kuma nan gidan ta ne babu wanda ya isa ya hana ta ko ya saka ta ko kai ne ."
Idanunsa suka sake ƙanƙancewa ya matsa kusa da ita da sauri tayi baya a tsorace kar ya sake kamata don inda ta buge ma jini ya soma fitowa ya tashi kaɗan.
"Don Allah kar ka dake ni ban faɗi haka ba."
"Umma ƙarya zata miki kenan ko kuma Ramlat ce zata yi miki ƙarya?"
Numfashinta ya soma sama da ƙasa saboda fargaba ita fa bata saba da wannan rayuwar ba, ko da Abba Alhaji yake da tsanani bai taɓa sa hannu a jikinsu ba kai ko Mama bai taɓa yi mata irin wanann tsawar ba bare ya kai hannu jikinta in ma laifi kayi masa a nasihace zai yi maka faɗa kamar yana lallaɓaka yau kuma ta ga wani sabon namijin daban dole ne ta shiga cikin tashin hankali fiye da koyaushe.
Tashi yayi a fusace ya fice daga ɗakin. Ramlah tayi shewa tayi tafi harda girgiza sannan ta fice daga ɗakin.
A nan ta zame ta kwanta ta dunƙule a wuri guda tana jin jikinta na rawa ta ko ina.
A fili cewa take "Me yasa rayuwa ta juya min baya? Ina tarin alƙawarurukan soyayyar da ya yi mata? Ya san mahaifiyarsa da yan'uwansa ba sa son ta ya kawo ta cikinsu don su kashe ta? Innallillhi wa inna illahir rajiun Allah ka shiga cikin lamurana ka kawo min sauki."
"Umma don Allah kiyi haƙuri ki yafe mata ɓata mikin da tayi zan tabbatar da hakan ba ta sake faruwa ba Umma."
Sai da ta ja tsaki sannan tace "Ai ɗan kuka shi ke ja wa uwarsa jifa tun usuli da ka yi yadda nace ai ba zaka kawo mai ranani ba amma ga shi nan mai ka janyo min ,ba don sun kai zuciyoyinsu nesa ba ai ba za ayi da kyau ba sai ace sun kashe maka aure."
"Haba Umma wanne irin abu ne wannan don Allah kiyi haƙuri zan yiwa tufkar hanci."
Ya tashi ya fita. A inda ya barta a nan ya koma ya same ta a kwance a dunƙule tana kuka. Duk da ya ji wani iri amma haka ya ɗauke kai ya shige banɗaki a lallai an ɓata masa rai ya bar ta a gun.Yana gama shiryawa ya saka jallabiyarsa yayi ficewarsa.
Ta jima a gurin kafin ta tashi ta hau kan gado ta kwanta wani abu ya tsaya mata a maƙoshi ƙishi take ji amma ba zata iya ɗarawa daga inda take ba.
A haka har bacci ya ɗauke ta.
Shi kuwa bai samu dawowa ba sai wajen daya yana can majalisa suna shan shayi suna yan gulmamakinsu.
Ya shigo ya yi duk abinda zai yi ya haye kan gado gashi babu Nepa dama ya cire rigarsa daga shi sai gajeren wando ya kunna fitilar wayarsa ya gan ta nan da nan ya ji sha'awarta ta kama shi bai damu da yanayin da take ciki ba kuma bai damu da tana so ko bata so ba kawai a lokacin buƙatar kansa yake so ya biya a karo na farko ba tare da lalami ko lallashi ba ya murjeta son ransa bai damu da halin da take ciki ba jikinta duk yayi tsami bata da ma ƙarfin hana shi ko ƙwatar kan ta karatu ɗaya ke faɗo mata "Ba a juyawa miji baya idan ka hana shi hakkinsa Mala'iku dubu ke kwana suna tsine maka. Dolen ta ne dole ne tayi masa biyayya." Tana ji tana gani ya gama sauke mata wahala ya koma ya baje sai tashin munshari ta ji kawai .
Tana hawaye ta sauka jikinta yayi tsami ta ɗebi ruwa ta zuba a tukunya ta kunna gas ta zuba.
Sai da ya tafasa sanann tayi wanka ta yi alwala ta dinga jera salla ko zuciyarta tayi mata daɗi. A nan bacci ya ɗauketa.
Daidai lokacin da dereba ya tsaida motar ya juya ganin sun yi minti biyar bata motsa ba hankalinta baya nan yace "Hajiya mun ƙaraso."
Tayi firgit ta kalle shi idanun ta jajir tace"Na gode." In dai zata tuna da baya sai ta manta yanzu. A hankali ta fita ta shiga cikin gida.