GABA TA ZO BAYA

Chapter 10

by @khairatup01



Zaman shi ya gyara a kan kujerar falon Kaka bai samu ya rakata ba kamar yadda ya shirya saboda Granny da ta kira shi tsohuwa ce wadda in ka ganta zaka ɗauka ma bata gane komai don hatta gashin kanta sun koma frare tas da wani farin gilashi mai kwalba a kan fuskarta da igiya da aka rataya mata shi ta baya. A gefenta akwai sanda wadda take taimaka mata wurin zuwa duk inda take so.
Falon ɗan matsakaici ne amma cike da duk wani abin more rayuwa Hajiya.Nadiya Bint Sulaiman kenan tsohuwa mai ran ƙarfe mai ƙaunar zumunci asalinta yar Sudan ce don iyayenta a can suke sai dai aure ne ya dawo da ita ƙasar Najeriya.
A shekarar 1991 a ƙasar Sudan a Khartoum da yammaci ne a lokacin da iska ke kaɗawa a gefen kogin Nilu tana ratsawa ta bishiyoyin da ke gefen titin jami'ar inda ɗalibai ke kai-komo cikin harabar makarantar, wasu ɗauke da littafai,wasu kuma suna tattaunawa cikin larabci, Muhammad baya daga cikin ɗalibai da suke zaman banza ko ɓata lokaci wurin zirga-zirga da bai dace ba tunda ya san da yadda ya samu ya zo ƙasar karatu iliminsa da ƙwazonsa ne ya saka ya samu ya zo nan don kammala karatunsa ta hanyar wani babban mutum.
Tun yana ƙarami ya taso cikin gwagwarmaya har ya koyi nema tun bai san meye ma neman ba. Mahaifinsa ɗan kasuwa ne da yake jalauta rayuwarsa ta yau da gobe yana ɗan ƙarami Allah Ya yi masa cikawa. Saboda haka tun wuri ya san meye wahala tunda mahaifiyarsa bata da wani ƙarfi ita ma lallabawa take yi saboda su. A lokacin da talauci ya mata yawa kuma tana da buƙatar yadda zata kula da shi da ƙanwarsa dole ta auri wani Alhaji saboda da ƙuruciyarta a lokacin gata bafulatana kyaƙyawa son kowa ita ce amarya a tsakanin uwargidan da ta tsakiyar. Bai nuna mata bakin ciki ba ya bari ta tafi da yaranta biyu wanda dama don su tayi auren. Shi ya zame musu uba kuma garkuwa ba komai dai ya ɗauke musu ba amma ya ba su ilimi don shi ne ya yi sanadin tafiyar Muhammad Sudan karo karatu.
Kusan kowanne ƙarshen mako hana zuwa kasuwannin Omdurman da Khartoum sayen turare,yadudduka,kayan fara da wasu kayan gargajiyan. Daga nan sai ya tura su Nijeriya ta hannun wasu dilallai. Ba wani babban kasuwanci ba ne amma yana sa ran zai girma a hankali. Akwai ranakun da yake kwana da busassun gurasa da iya ruwa kawai a cikinsa saboda ya tara kuɗin da zai sayi kaya ya tura a siyar mai ,akwai kuma ranakun da zai yi tafiyar kilomita da ƙafa don ya rage kashe kuɗin mota.  Amma bai taɓa yin nadama ba ,saboda yana da buri,burin ma babba. 
Da wani yammaci ya je shagon Sulaiman Bin Ahmad karbar wasu tutar da yayi oda da sallama ya shiga shagon.
"Assalamu alaikum."
A maimakon muryar mai shagon sai ya ji murya ta daban muryar da ta saka zuciyarsa ta buga ya kalle ta a bazata kyakkyawar balarabiya ta amsa masa da "Wa'alaikum Salam."
Ba mace bace ita mai yawan magana ba kuma ba ta daga cikin mata masu jan hankalin maza tana zaune tana rubutu a wani littafi yayin da hasken rana ke saukowa ta gefen taga tana haskaka fuskarta.
Na ɗan lokaci Muhammad ya manta da dalilinsa na zuwa shagon ma saboda yadda kyawunta ya tafi da shi.
Ta lura da yadda yake mata wani irin kallo haka ya saka ta sunkuyar da kanta ƙasa da sauri shi kuwa ya ji zuciyarsa ta yi wani irin bugawar da bai taɓa ji ba. Haka dai yayi samu ya daure yayi abinda yake so ya tafi da tunanin ta fal.
A wattanin da suka biyo baya ya cigaba da zuwa shagon kawai don Nadiya Bint Sulaiman wani lokacin kuma saboda kasuwanci, wani lokacin kuma saboda zuciyarsa. Sai dai har a lokacin babu abinda suke yi wanda ya wuce gaisuwa kawai da tambayar lafiyar juna.
A wancan shekarun ba irin wanann zamanin ba yarinya bata zama tayi hira mai tsayi da saurayi komai yana gudana ne cikin mutunci. Duk da haka akwai abubuwan da ido ne kadai ke isar da su ko da ba a furta su a fatar baki ba. 
Lokacin da Muhammad ya sanar da Alhaji Sulaiman cewa yana son Nadiya labarin ya girgiza shi sosai ba don ba ya son shi ba, sai don ya san Muhammad ba ɗan Sudan bane ɗan Nijeriya ne duk da ya san Muhammad yaron kirki ne mai gaskiya Kuma wanda ya san zafin nema, ga addini ga ƙwazo kawai matsalar ita ce Najeriya.
Koda ya kai wa matarsa Hajiya Safiya ta kafa ta tsare ba zata yarda a ɗaurawa ɗan Najeriya yarta ba.
"Hajiya...."
Tayi sauri ta dakatar da shi tace "A'a Sulaiman ka ƙyale ni don Najeriya ba kusa ba ce. Idan ta tafi,yaushe zamu sake ganinta?" Kalmomi ne da suke fitowa daga bakin uwa daga zuciyarta don soyayyarta ga babbar yar ta ba don ƙiyaya ba sai don tsoro.
An ja lokaci ana lallaɓa Hajiya Safiya bayan dogon bincike da tambayoyi da aka yiwa Alhaji akan Muhammad a nan Khartoum da ma Najeriya sai ya gamsu kuma ya yarda zai bawa Muhamamd auren Nadiya saboda kyakkyawar shaida da ya samu akan shi kowa zai ce mai biyayya ne kuma mai addini ga shi da gaskiya da neman na kansa, baya shaye-shaye,baya zaman banza,yana aiki tuƙuru kuma yana da buri." A hankali zuciyar Hajiyar ma ya soma sassautawa har ta haƙura ba wani dogon ɓata lokaci aka daura auren su aka yi duk wani cike-cike da ya dace na shari'a. A shekarar 1992 aka ɗaura auren su. Aure mai cike da albarka ba wai ƙarya ba. Muhammad bai mallaki komai ba sai mutuncinsa , iliminsa da burinsa.Nadiya kuma ta bar gidansu da zuciya mai cike da tsoro da fargaba amma cike da fatan alheri ga junansu da fatan Allah Ya zaunar da su lafiya.
Bayan shekara guda da aure Allah Ya albarkace su da samun ɗa namiji daga baya suka koma Najeriya. A lokacin ne kasuwancin Muhamamd ya fara bunƙasa sosai. Yana shigo da kaya daga Sudan,daga can zuwa Kano daga Kano zuwa Legas, daga Legas zuwa sauran sassan ƙasar.A hankali sunan Muhammad ya fara zama sananne tsakanin manyan yan kasuwa. Kowa yana ganin arziƙinsa sai dai ƙadan ne suka san tushen komai ya fara ne daga ɗakin ɗalibi a Sudan da kuma addu'ar uwa da mata kamar Nadiya. Shekaru suka ja ƴaƴansu suka girma su uku maza biyu mace daya sai dai macen tun a haihuwar fari ta rasu ita da abinda ta haifa sai ya rage sauran mazan biyu kawai jikoki suka zo duniya Alhaji Muhammad ya rasu ya bar Hajiya Nadiya da kewa. 
Duk lokacin da zasu zo ganin ta zata ba shi labarin Sudan da yadda suka haɗu da Kakansu har suka yi aure su ma suka haifa aka haifo su.
A lokuta da dama ya kan tsokane ta yace "Da gaske kika iya baro ƙasar ki saboda Kaka?"
Sai tayi murmushi ta shafa kansa ta kalli hoton mijinta marigayi Muhammad tace "Saboda wani lokacin ɗan adam ba ya zaɓar inda soyayya za ta same shi." A lokacin Azlan bai fahimci zurfin kalaman ba sai a yanzu da yake jin Nihila a matsayin duniyarsa.
Cikin larabci ta tambaye shi abinda ya haɗa shi da Nafisa har ya kora ta gida.
Da yake suna ji ba laifi saboda Granny bata bar yarenta ba su ma in sun je can ana yarawa da su tunda su ma su Ammi yan can ne Mustapha mahaifinsu abokin Muhammad ne ɗan asalin can ne kuma basu yada zumunci ba har sai da suka aurarwa da yaransu juna sannan suka huta.

"Granny laifin ta ne bata gaya miki abinda tayi min ba?"
"Ta gaya min amma kai namiji ne kai babba ne sai kana ɗauke kai kar zuwan wata bare ya saka ka manta da ainihin jinin ka shi zumunci ai dangin ƙauna ne."
"Daɗina da ke son kai Granny ita ma yanzu ta zama jikar ki tunda na aureta kuma ba don ita na ce ta tafi gida ba duk da ban san me suka gaya miki ba amma zan gaya miki komai ki ji sai kiyi mana alƙalanci."

Ta ɗaga masa hannu tace "Bana son ana maimita magana ka sani na san halin kowa kuma na san abinda kowa zai iya aikatawa da wanda ba zai iya ba ina son don Allah ka yi haƙuri daga nan ka je ka ɗauki matar ka ku tafi gidanku tun kafin ma iyayen ku maza su sani azo ana ɓacin rai laifin iyayen ku mata ne ma da suka goya muku baya a wannan shirmen."

"Wallahi ke kin san ina son ki Granny ke ce fa masoyiyata ta farko ta ci darajar ki amma fa ki ja mata kunne ta sake sanin girmana da matsayinsa a wurin ta ni ba sa'ant bane ina duba zumuncin ne da darajar aure shi yasa nake ƙyale wasu abubuwan amma yanzu fa tura ta fara kaiwa bango bana so ta kai ni bangon."

"Na gode! Da ta ci darajar tawa. Muhammadu kafi sunan arna. Zan ja mata kunne da kyau ta daina yi wa maigidana rashin arziƙi."

"Yauwa to magana ta ƙare zata dawo gidanta."

Ta shafa kansa ta baza ya ɗan ɓata fuska "Ba ki san kuɗaɗe da lokacin da nake ɓatawa a kan gashin nan ba amma ke na ga burin ki ne kiyi ta ɓata min amma shi wancan Adeel ɗin ai ba kya yi masa."

Tayi dariya tace "wannan ƙyale shi bai zo ba tsoro yake kar ya bani kuɗin cefane kasan shi uban yan mammaƙo ne."

Yayi dariya ya tashi ya gyara links ɗin sa yace "Ya kika gan ni?"

"Kayi kyau. Sai ina?"
"Zance zanje gaskiya."
"A'a ka je ka ɗauko matar ka nace."
"Ki gane mana tsohuwar  zan dauko ta Allah ai na miki alƙawari zanyi yadda kika ce kawai dai sai na je na ga amaryata tukunna Wallahi."

"Allah Ya sa amaryar nan ta iya girki."
"Hello! Kina ci zaki haɗa da yan yatsun ki Granny hattara dai."
"Kai fice min kai ka san kuwa zaƙin hannuna? Ka tambayi wanda suka yi zamani da ni yaro."
"Ai matsalar duk sun tafi ke kaɗai fa kika rage."
Bai ma tsaya bata lokaci ba ya shiga gidan kaitsaye. A lokacin Nihila ta gama cin abinci tana wanke hannu a tsakar gida wando ne da riga a jikinta sai hula bata taɓa tunanin ma za a shigo ba. Bata lura da shi ba sai da ta ga hasken farin wata ya nuna mata inuwar mutum sannan ta ɗaga kai ta kalli wurin da yake.
Da sauri tayi baya a tsorace.
Yayi dariya yace "Calm down! Ni ne fa."
Cike da kunya ta sunkuyar da kanta ƙasa har yau ta kasa sabawa da shi. 
Daga falo Mama tace "Yaya dai kuma kina ina? Daga wankin hannu?"
"Mama ina zuwa kin ga Dakta ne ya zo."
Daga ciki tace "Dakta kuma wani abu ya manta ne?"
"A'a." Ta faɗa da sauri murya na rawa.
Dr. Azlan ya yi dariya yace "Mama zuwa nayi na mata bangajiyar girki."
Sai a lokacin Mama ta yarda da shi ne sai kuma ta ji kunya ta kamata.
"Sannu da zuwa."
"Yauwa Mama."
"Ki buɗe masa sitting room ɗin mana ya shiga sai ki kai masa abinci ya ci."
"A'a Mama Wallahi a ƙoshe nake." Ya riga ta magana.
"To Shikenan,ki tashi ki je mana kin yi zaune."
Miƙewa tayi tsam ta tashi ta koma ciki ta janyo mayafi ta saka sannan ta shiga falon Abba Alhaji ta ɗauko mukuli ta buɗe sitting room Sannan ta masa iso.
Ta dauko masa ruwa mai sanyi da zoɓo mai sanyi a fridge kuma cikin ikon Allah dazu an bar wuta yayi sanyi.
Tana kai-komo yana bin ta da kallo.
Ya haɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta.
Saida ta gama komai sanan ta zauna ba tare da ta kalle shi ba tace "Barka da dare."
Yayi murmushi sannan yace "Barkanmu. Ya kika zo gida kiyi haƙuri na so ɗazu na dawo da ke amma Granny tayi kirana."
"Ai ba komai."
"A haka kike zama wai a tsakar gidan in wani ya shigo fa?"
"Ai ba wanda zai shigo saboda ba a shigowa iyakar mutum haraba sai yayi sallama matan gidan su kimtsa."
"To dai duk da haka,bana so."
"To."
"Yawwa. Yanzu ya kike ganin za ayi da tariyar?"
"Ai ban sani ba su Mama basu faɗa ba."
"To ki tambaye ta."
Da sauri ta kalle shi, ya ɗaga mata gira.
"Ba zan iya tambayar ta ba gaskiya, ai maganar ta iyaye ce."
"Don Allah ni a bari ki tare wani satin."
"Don Allah ka bari ka ƙyale su in suka gama tsarin zasu faɗa."
"Gaskiya ba zan iya ba, zan yiwa Yaya Jameelu magana sai ya gaya musu ni na gaji."
"Kuma faɗe zaka yi?"
"Kina wasa."
"Don Allah ka bari ka ji?"
"Ba kya son mu kasance tare?"
"Ba haka bane."
"Har yau kina tunaninsa kenan,na ga kin kasa bani lokacin ki da hankalin ki har yanzu , Wallahi ina da kishi,ina son ki,bana son yadda kike nuna min halin ko in kula ba laifina bane Allah ne ya ɗarsa min son ki da ƙaunar ki ban shirya ba ban ma taɓa zaton zan iya aure wata mace ba saboda babu auren mata biyu a tsarina don Allah ki ɗan sassauta mini."
Zuwa sannan hawaye take yi, ta sa bayan hannunta ta share hawayen ta. Jikinsa yayi sanyi ya tashi tsaye yace "Zan tafi ki daina kukan ba sai kin yi kuka ba na san ba kya sona kuma na san an miki kutse da ba a baki dama yadda ta dace ba."
Da sauri tace "Ba haka bane." Ganin yadda ran shi ya ɓaci. 
"Ba laifi kika yi min ba fa zan je na ɗauko matata mu tafi sai da safe."
Bai tsaya sake sauraronta ba ya fice daga sittingroom ɗin tana jin yana yiwa Mama sallama. Sai da ta ɗan ɓata lokaci kafin ta tashi ta koma ciki taji babu daɗi.
A hanya ransa duk a dagule haka ya je gidansu Nafisa. Bai ma yi kyakkyawan parking ba, ya shiga ciki suna parlour a zaune da Amma da Nafisa suna shan fruits suna kallo. Wando da riga ne a jikin Nafisa wandon bage ne rigar kuma yar karama har cibiyarta ana gani tayi parking gashinta baƙi siɗik ta saka masa headband baƙi.
"Salamu alaikum!" 
A tare suka juya ganinsu ga bakin ƙofa. Ammi ce ta amsa ciki-ciki "Wa'alaikum Salam."
Nafisa kuwa ta ɗan yi murmushi ta miƙe ba kunya ta isa gaban shi ta rungume shi. Ammi ta ɗauke kai duk da ba wani abu bane hakan a wurinsu.
Bai hanata ba shi ma ya yi kewarta sosai ya ɗan sumbaci goshinta yace da ita
"Ana mishtāg leyki" (Na yi kewarki.)
Ta kankame hannunsa tace "Ana kaman mishtaga leyk" (Nima nayi kewar ka) 
Ya sake kallonta yace 
"Amma bit'aklik shinu? Shuftik baqeiti ahla wa samīna. Ashe ana bas al-waḥīd al-mishtāg leyki?"  (Me Amma take baki? Na ga kin ƙara kyau kuma kin yi kiba. Ashe ni kaɗai ne nake kewarki?)
Ta ɗan daki ƙirjinsa ta kwanta a kai. 
Hannunsa ta kama suka shiga ciki tare.
Ya samu gu ya zauna.
Amma ta taɓe baki ta ɗauke kai. Yana lura da ita ya yi murmushin gefen baki sannan yace "Amma masa al-kheir.Inti kwayyisa?" (Ammi Barka da dare,yaya kike)
Ta kalle shi a yakwane sannan tace"Tamam,Alhamdu lillahi (ina lafiya,Alhamdu Lillahi)
Yayi murmushi sannan yace "'Alhamdu Lillahi.Allah yikhaliki,Ammi. (Alhamdu Lillahi, Allah Ya bar ki , Amma."
"Ameen."

"Amma na san kina fushi dani ina bada haƙuri komai ya wuce na zo na tafi da matata."

"Ga ka ga ta ai me zance? Tun kan nace ta nuna min ta ajiye makaman nata. Allah Ya kyauta."

Nafisa ta ɗan sosa kai ta zumɓuri bakinta tace "Haba, Ammaaaaa" ta ja sunan.

Amma tace "Me nace?"
Bata sake magana ba. Can suka yi shiru da Amma taga dare nayi tace "Ku tashi ku tafi dare na yi zaman na meye? Ku dai ku ji tsoron Allah, ku riƙe auren ku kar na uku ya shiga tsakanin ku."
Yayi dariya kawai ya miƙe yace "Amma babu abinda zai sake faruwa in sha Allah wannan ma Feenat ce ta janyo da ba za a ji kan mu ba."
"Ni dai ina gaya maka kar ka cutar min da ɗiya saboda ka auro wata can don idan ka saka min ya hawaye saboda wata can bare Wallahi ba Kano ba kuma ba Sudan ba babu inda za a ƙwatar maka Nafisa sai dai son ka ya yi ajalinta. Saboda mu ba bora bane ki ka sani tunda ka gani a gidan ku ƙanwata bata da abiyar zama nima bani da abiyar zama ita kanta Granny ba ayi mata abiyar zama ba mu kaɗai muka yi mulkinmu muka yi zumunci mu amma kai kam da maitar mace sai da ka samo wata ka kawo mana watan ma bare ka kiyaye ni to."
Yana murmushi yace "Ayi haƙuri Amma in sha Allah sai alheri babu wani abu da zai faru ki daina damuwa zan riƙe alkawari da amana Amma ina Son Feenat waye bai san ina sonta ba? Shekarar mu goma fa muna ta sha ɗaya muna tare tun ƙuruciya har Allah Ya ƙulla muka zama abokan zama don Nihila ta zama cikinmu ba zai saka na daina ganin girman Feenat ba."

"Babu ruwana da duk wannan soki burutsun kai can ka sani ni dai gaskiya na gaya maka bana son wai-wai ko ance." 
"In sha Allah, Amma babu abinda zai faru Nihila bata da matsala zasu zauna lafiya bare ma kowacce da gidanta."
Amma na jin haka hankalinta ya tashi ba haka take so ba so take su zauna a gida ɗaya saboda ayyukan da zasu yi su tafi daidai bata so ayi nesa haka ya saka tace da Nafisa "Zo muje."
"To Amma."
Ya koma ya zauna da kyau ya zaro wayarsa ko zai ga kiran Nihila irin ta ɗan lallashe shi haka sai ya ga ba kiranta. Ya saki siririn tsaki,ya maida wayar ya ajiye ya ɗan kulle idanunsa fararen idanunta suka masa wani flash suka wuce hatta beuty point ɗinta sai da ya gani wanda yake matuƙar burge shi yake sukar masa da nutsuwa bai san lokcin da ya saki murmushin ba shi ma. A fili ya motsa leɓɓensa yace "Ina son ki yar mitsilata."

Can daki kuwa Amma ta kama hannun Nafisat tace "Kar ki saki ki yarda a raba muku gida?" Ta faɗa tana kama kunnenta daya irin yadda ake wa ɗa kashedi.

"Me yasa Amma? Bana son ganinta fa bana so komai ya haɗani da wanann yarinyar me yasa zance ya bar mu a wuri ɗaya?"

Amma tayi tsaki tace "Idan aka raba ku taya ya zaki koreta daga gidan ki gabaɗaya?"

Tayi shiru tana nazarin maganar Amman.

"Dole ne sai ta zauna a inda kike sannan ne za ki san irin matakan da za ki ɗauka a kan ta da irin makaman yaƙin da za ki shirya mata yadda ta shigo ta fita da kanta ta san cewa ba mijin irin mu ake aura ba."

"To Amma yaya zan yi Wallahi bana son ta a rayuwar Azlan."

"To so nake ki wasa ƙwaƙwalwrki, so nake ki  kifafa tunanin ki, so nake yi ki nuna min nonona kila tsotsa don ba a haifi macen da zamu yi kishi da ita ba saboda haka ina son ki sa a ranki yadda ta zo haka zata koma nan kusa ba da jimawa ba."

"Duk abinda kika ce Amma zan yi dole ne na koya mata hankalin aurar min miji da ta yi ba tare da na yarje mata ba Azlan nawa ne ni ɗaya ba zan raba shi da kowa ba."

"Haka nake son ji. Sannan ina son ki saka a ranki ba zaki sake maimaita wanann shirmen da kika yiwa Azlan ba wannan zuwan ma da kika ga ya yi ni na yiwa Grannyn shi magana da kaina ta saka ya sauko har kika ga ya zo, saboda haka ki sauya taku wanann kishin haukan na fili na soke shi ayi yaƙin ta bayan fage don ya fi riba."

"Tam Amma zanyi Wallahi."

"Yauwa haka nake son na ji ki saki jikin ki me zata nuna miki wannan abar? Baki ganta bane baki gan ki ba ke fa jinin larabawa ce me zata nuna miki na kyau ko farin fata ko gashi ga ki da ilimi ga kuɗi."

"Wallahi Amma haka ne zan kiyaye in sha Allahu kuwa."

"Da kyau! Muje kar ya zargi wani abun. "

Ba tare da ɓata lokaci ba ta shiga ɗakin ta abaya ta ɗora a kan kayan jikinta ta fesa turare ta ɗan shafa powder ta sa lip balm ta fita da jakarta a hannu.
Yana ganinta ya tashi tsaye yana murmushi ya miƙa hannunsa don amsar jakarta. Ta noƙe kafaɗarta don ya san bata son ta ga ya ɗaukar mata jaka shi kuma sabon shi ne yana son ya dinga ɗauka a ganinsa ba wani abu bane babu laifi yin hakan duk a cikin so ne. 
Amma dake bayansu ta ɗan saki fuska ganin yadda yar ta ke ta walwala hakan ya mata daɗi sosai.

"Amma mun tafi."
"To Allah Ya kai ku lafiya."
"Amin."
Ya buɗe mata motar ta shiga ya zagaya shi ma suka tafi a hanya suka yi yan siye-siyen da zasu yi sannan suka dauki hanyar gida.

Suna isa ya kulle ko ina bayan ya buɗe ƙofar ya sunkuce ta sama har tayi yar ƙara saboda ya mata bazata. 

"Zan ga ranar da za ki yi nauyi Feenat kin yi sirranta da yawa."

"Kai don Allah duk wannan ƙibar da nayi kaima fa ka faɗa ɗazu."

"Oh! Yeah ,haka ne fa ashe. Ya goga hancinsa da nata suka saka dariya.

Wanka suka yi tare sanann suka hau kan gado da kan shi ya zuba musu naman a cikin plate ya saka musu straw cikin cup ɗin smotthie ɗin.

"Am sorry for what i did ba laifin bane son ka ne ya min yawa shi sa kishin ka ya hana mini sakat ban san abinda nayi zai iya taɓa lafiyar ka ba idanuna sun rufe."

Ya tallafi ƙeyarta ya haɗa goshinsa da nata yana murmushi yace " Na yafe miki kawai kar ki sake maimaita abinda kika aikata min. Kuma ina so ki sa a ranki Nihila yar'uwar ki ce ba kishiya ba bata da matsala tana da ilimi tana da tarbiyya she's gone through alot, tana buƙatar sauyin rayuwa bata da matsala in kika kama girman ki za ku zauna lafiya Wallahi ni nake gaya miki haka."

Tayi murmushin yaƙe haɗe da sumbatar lips ɗinsa sannan tace "In sha Allah! Ba zaka samu matsala daga ni ba, na ji ma kana cewa zaka raba mu ne me yasa?"

"Saboda ba kya son ta."
"A'a ban ce bana son ta ba Allah! Ka bar mu a nan mu saba ko don ya'yan da zamu haifa a gaba. Ta ɗauki ƙasan ni in ɗauki nan sama ya ishe mu kowacce two bedrooms ga kitchen zamu zauna lafiya ai."

Ya ja kumatun ta yace "Ma sha Allah! Don Allah kina yin yaji ko sau ɗaya ne a wata saboda kina hankali in kika dawo gaskiya Amma ta cancanci yabo."

"Me kake nufi to yanzu?"
"Ina nufin kin yi hankali."
"Yanzu da bani da shi hankalin?"
"No ba haka nake nufi ba,amma ba lokacin wannan bane yanzu i need you kwana nawa ban ji ɗumin ki ba kina can kina kwanciya da fushin Allah kin bar mijin ki yana tara-tara a hanya dai, lalube yake yi bara a kufai."

"Kai fa ka ce na tafi."
"Da gangan nake ke baki san wasa ba ko irin ma ki ɗan cije kice aa ba zan tafi ba ɗin ai kai mijina ne ba zan bar ka ba."
Tayi dariya ta rungume shi.Ya san halin kayarsa shi yasa ya iya da ita sau da dama zasu yi hakan kuma zai nuna fushin amma idan suka tashi komawa sai ya manta da wancan laifin ita ma ya mantar da ita shi yasa tun asali ta su ta zo ɗaya a family saboda sahu mutum ne wanda ya san yadda zai yi da kowa a saukaƙe.
*

Tunda ya tafi zuciyarta ke fuzgarta kan ta kira sa ta ba shi haƙuri yana ta haƙilo da ƙoƙari kan ganin ya bata farinciki amma zuciyarta ta kasa buɗewa don ba shi wani gurbin, bata sani ba ko zata iya sake bawa wani ɗa namiji zuciya da yardar ta ba saboda a baya tayi ta ji ba kyau ba daɗi bata so ta sake shiga wata ckwakiyar musanman ma da ta san wacce matar shi ba zata iya haniya ba, ba zata iya jurewa ba zuciyarta zata fashe wannan karon bat jin komai yanzu bata da wani feelings na soyayya. Ta saki tsaki ta kalli agogon bangon ɗakinta ta dare yayi da ta kira Bestien ta Barra ita kaɗai take iya Sharing damuwarta da shi daga ita bata iyawa da kowa hatta Aunty Karima bare kuma Mama da bata son ta ɗaga mata hankali.
Ta kwanta ta cure wuri guda kamar mai jin sanyi kamar wata mage . 
Tunani fal cikin ranta har bata ma san wanne ya kamata tayi ba yaranta take kewa tana ji tana gani an raba ta da su saboda rashin imani da rashin kirki kuma ba son su ake ba musguna musu ake yi saboda kawai ita ta haife su ta sa hannu ta share hawaye da suka zubo mata a lokaci guda kuwa ta furta "Ya rabbil-alamin Allah ka kawo min mafita Ya Allah ka nuna min hanyar da ta fi zama alheri a gare ni." 
A haka bacci ya ɗauke ta. 

Washegari da ta tashi da yake bata sallah da sauri ya haɗa abin kari bayan ta ɗumamawa su Abba Alhaji tuwo ta juye musu a fulas sanann kuma ta soya chips da plantain da kwai ta dafa tea mai kayan ƙamshi.

Kafin Mama ta fito ta kammala komai.Hatta ruwan wankan Abba Alhaji ta ɗora a heater saboda ta san nan da awa ɗaya Yaya Jameel zai shigo don su tafi kasuwa tunda gidansa na a jikin gidansu daga bayan layinsu kuma Yaya Shu'aibu. Ku san ma layin duk sune da ahalinsu.

Wanka tayi ta saka kaya marasa nauyi ta fito. 
Tare suka karya da su Mama sannan Abban yayi wanka. Yana fitowa Yaya Jameelu na shigowa da sallama.
Suka amsa da fara'a ya samu gu ya zauna sai nishi yake kamar wanda ya ci gudu da yake yana da ƙiba shi a cikinsu ƙato ne tabrakallah ya ɗauko jikin Abban gasu nan gaint ga tsayi ga jiki dama kamanninsu ɗaya da juna.

Da suka gama komai zasu tafi tayi tsalam tace "Don Allah ku sauke ni a hanya sai na ƙarasa gidan Aunty Karima."

Mama ta gyara zama tace "Ka ga iskanci sabon salo tun jiya baki faɗa ba sai yanzu?"

"Ba ma wai sai yanzu ba, ta gayawa Mijinta?"

"Ato kai ma dai ka faɗa ,don an raina ni ne ma amma ban da haka kina son zuwa amma baki gaya mai jiya ba kuma fa nan ya zo da daddare."

Kawai sai ta samu bakinta da cewa "Yaya na gaya masa fa jiyan kuma yace naje."

"To ke kin ji ta nemi izinin tashi ki ɗauko kallabinki mu tafi."

"Ban yarda ba Wallahi Alhaji."

"Ya haka ne Bilkisa? Shikenan sai ki uzurra wa yarinya ki daina tausayin ta wai."

"Nayi shiru Alhaji , amma ban yarda ba."

"To na ji..Tashi muje ina makara."

Da sauri ta tashi ta shiga ciki bata jima ba ta shirya ƙaton hijabi ma ta saka da face mask ɗinta a hannu ta fita.
Aunty Karima na wanki a tsakar gida ta ji Muryar yar'uwarta na sallama ta ajiye kayan tace "Kai wana ke gani kamar amarya?"
"Kai Aunty nice mana."
"Ah lallai yau na ciri tuta shigo,zauna."
"Sai wata baƙuwa kike maida ni."
"Ai rabon da ki zo gidan nan an jima Nihilar Abba. Ya gida ya kika baro su?"
"Lafiya lau Wallahi, suna gaishe ki a nan suka suke ni ma sanann suka tafi kasuwa tun ranar nan nake son zuwa Allah beyi ba sai yau."
"Kin kyauta." Ta faɗa tana miƙewa ta fita kitchen ta shiga ta kawo mata abin kari ta ci.
Suna hira suna aiki nan da nan suka gama komai yara na makaranta. 
"Yaya Sunusi baya nan kenan?"
"Eh ai yau yana Dakata kwanan amarya ne."
"Lah mantawa nake yi ai kina da amarya."
"Hh. Kalli hannun ki don Allah kamar na maza har yau ba kya son saka  lalle a hannun ki."
"Wallahi Aunty cin rai."
"Ai kuwa ba inda za ki sai an miki. Bari na kira Atika ta yi miki ja da baƙi sannan a yarfa miki kitso."
"Kai Aunty bana so ba daɗew zan yi ba fa, ana azahar zan tafi."
"Ai na rantse sai an miki."
Mai lalle ta zo aka fara lalle da jan aka soma. Aunty na sabgoginta kan a gama ta gama girki ma. Lallen kuma ya mata kyau sosai ya fito da hannun nata ras. Duk da tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta tana jin wani iri saboda yau Dr bai kirata a waya ba. 
Kitson ne ma ba a yi mata ba saboda yamma tayi hankalinta yayi gida. Aunty ta haɗa mata kaya a leda na magunguna da na turaruka da kayan kaɗi na miya na Mama. Ta rakata farfajiyar gidanta a lokacin ma yara sun kusan dawowa saboda tun safe in suka tafi sai yamma lis suke dawowa.
Ta saka mask ɗinta ta saka glass ɗin ta da ya jakarta a  rataye a hannunta ɓarin dama. Bata sake bi ta kan wayarta ba tunda ta duba bata g kiransa ba dama shi ne mai kiran ita bata yi bayan shi sai su Barra sai Aimana da take haɗata da su Abul a waya suna gaisawa.

Ta jima a bakin titi tana jiran abin hawa duk ta ƙosa ta tafi gida saboda magariba ta kawo kai.
Ta jera tsaki ya kai sau goma saboda taƙaicin abin hawa ƙunƙunai take yi "Ita Aunty ba ka zo gidan ta ba ka rasa abin hawa in yamma tayi." 

Tunda ga nesa ya gane wacece zuciyarsa ta harba masa har yana sa hannu yana dafe saitin ƙirjinsa na ɓarin dama. A maimakon ya wuce saboda ya san abinda yake ƙoƙarin yin ba daidai bane sai ya zaɓi da ya aikata laifin ko zai samu wani sassauci a ransa don shi hakan a gunsa ma ba komai bane don shi ne ma aka cuta aka take masa gona. Ya haɗiyi yawu ya ƙara gudun mashin ɗinsa yana horn ya tsaya a gabanta da confidence.
Bata daga kai ta kalli waye ba amma ta gane ƙamshin mai mashin ɗin hankalinta ya tashi gabanta ya faɗi ta ɗan yi baya a tsorace tace "Meye haka Abdullahi?"
Yayi murmushi yace "Alhamdu Lillahi ashe baki manta ni ba."
"Ba haka bane me yasa zaka zo ka min tsaye a nan ko baka san me kake yi ba?"
"Na sani kuma ba gona zan wuce da iri ba na ga kamar kin gaji ne ki zo na sauke ki a gida."
A fili tace "Innallillhi wa inna illahir rajiun kamar yaya na zo ka sauke ni da kai ne ka kawo ni?"
"A'a wai don ki huta da ganin ki na san kin gaji ai na san ke matar aure ce kina ganin zan yi miki wani abu ne?"
"Ai ko zaka yi Allah ba zai baka iko ba. Don Allah ka tafi kar wani ma ya gan ni da kai."
"Don Allah fa nace ki hau na kai ki na san ke matar aure ce yanzu ai rage miki hanya zanyi ko don darajar su Abulkhair."

Hanya ce ta biyo da shi ta nan bayan ya ɗauke Dr Shattima. Yana danns waya yana tuƙi so yake ya kirata ko zata ɗauka saboda ɗazu ya kirata sau huɗu bata ɗaga ba sai ya yi mata uzurin bata gani ba. Bai ma san nan unguwar Aunty Karima take ba saboda basu taɓa zancen ba to yaushe ma suke hira da zai sani. 
Zuciyarsa ce ta buga da sauri ya ji wani irin abu ya tsarga masa, ya haɗiyi yawu haɗe da jawo robar ruwa ya ƙwanƙwaɗa.  Kamar ance ya ɗaga kai ya gansu a kusa da juna bai san dalili ba amma zuciyarsa na raya masa ita ce a tsaya koda ya sake yin gaba sai da ya ji hantar cikinsa ta kaɗa ganin Abdullahi yana yi mata magana a kan mashin tunanin da yake yi me ya kawo ta nan? Daman sun yi da shi zata fita ne bai sani ba. Wani irin kishi ya kama shi, zuciyarsa ta soma azalzala kawai ya ci burki ba tare da ya shirya ba har mai adaidaita sahu ya daki bayan motar amma bai damu ba mai adaidaita na ihu "Haba don Allah malam ya zaka zo ka yi wannan cin burkin a tsakar titi ka jawo mana asara ba zan yarda ba...." Amma shi ba ta shi yake ba so yake kawai ya isa ya sa hannu ya gaura mata mari shi kuma ya masa bugun burodi.

Tana ganinsa tayi baya da sauri har ta kusan faɗuwa salati take tana ƙara sanar da Ubangiji jikinta ya soma rawa abu biyu ne ya ɗaga mata hankali na farko bata gaya masa zata fita ba na biyu ya sake ganin ta da Abdullahi babu abinda zata faɗa da zata kare kanta a wurin shi kuma Mama ko Abba Alhaji duk wanda ya ji wannan abin kashin ta ya buɗe.

Ta baya ya janyo wuyan Abdullahi ya masa riƙon gam wanda hakan ya zo wa Abdullahi a bazata.

"Dr...."

"Wallahi kika sake kika ce tak sai na manta wace ce ke ,fasa miki baki zanyi da hannuna sai yayi jini."

Last free pages domin samun cigaba ku tuntubi lamar nan a sama.

Littafin GABA TAZO BAYA na kuɗi ne ₦500 kacal.