34
by @sheolly
💫KADDARAR SOYAYYA💫
By sheolly
🔥🔥
A wani ɓangaren kuma...
Muhammad da abokinsa na ƙut-da-ƙut, Fahad, suna zaune a wani ƙayataccen café bayan sun gama wani taro da suka halarta.
Fahad ya ɗauki cup ɗin coffee ya kurɓa kaɗan, sannan ya kalli Muhammad da murmushi.
"Bro, wallahi akwai wata tambaya da na daÉ—e ina son yi maka."
Muhammad ya É—an yi dariya."Ka tambaya mana."
Fahad ya girgiza kai.
"Me yasa duk lokacin da aka taɓo batun aure, sai ka canja fuska kamar an ambaci wani abu mai ban tsoro?"
Muhammad ya saki É—an murmushi, ya jingina bayansa da kujera.
"Marriage? No, bro... ba yanzu ba."
Fahad ya É—an turo baki."Ba yanzu ba? Kai fa shekaru na tafiya. Ka gama karatu, kana kula da business, komai yana tafiya daidai. Me kake jira?"
Muhammad ya yi shiru na É—an lokaci kafin ya ce,
"Ban taɓa jin zuciyata ta amince da kowace yarinya ba. Bana son in yi aure kawai saboda lokaci ya yi."
Fahad ya gyara zamansa.
"To idan iyayenka suka zaɓa maka fa?"Muhammad ya ɗan yi dariya.
"Ka san Daddy. Yana yawan maganar aure. Amma ni ban shirya ba."
Fahad ya girgiza kai cikin nuna damuwa.
"Wallahi, wani lokacin iyaye suna ganin abin da mu ba ma gani. Ba lallai ne zaɓinsu ya zama mara kyau ba."
Muhammad ya kalli abokinsa."Maybe... amma idan zan yi aure, ina son in yi shi da zuciyata ta amince. Ba wai don an matsa mini ba."
Fahad ya yi murmushi.
"Ina fatan ranar da za ka faÉ—i haka, Allah ya kawo maka wacce za ta sauya wannan tunanin naka."
Muhammad ya yi dariya.
"Let's see, bro."A dai-dai wannan lokacin wayarsa ta yi ƙara.
Ya É—auka ya duba sunan mai kira...
Daddy Calling...
Muhammad ya kalli Fahad, sannan ya É—aga wayar.
"Assalamu Alaikum Daddy..."
(Bai san cewa a ɗaya ɓangaren mahaifinsa yana ɗauke da wani babban al'amari da zai iya sauya rayuwarsa gaba ɗaya ba.)
Bayan Alhaji Umar Farouk da iyalansa suka tafi, gidan ya É—an yi shiru. Alhaji Bashir ya zauna a falon yana nazarin maganganun da suka yi da abokinsa.
Can sai ya É—aga murya ya kira,
"
Maryam... Amina... ku zo mana."
Ba da jimawa ba matarsa da sauran 'yan gidan suka fito suka zauna gabansa.
Ya yi murmushi sannan ya ce,"Alhamdulillah. Allah ya haɗa mu da abubuwan alkhairi. Ziyarar da abokina Alhaji Umar ya kawo mana ta yi mini daɗi ƙwarai. Allah ya ƙara ɗore mana wannan zumunci."
Matarsa ta amsa da,
"Ameen. Allah ya ƙara mana albarka."
Alhaji Bashir ya ci gaba da cewa"You know... wani lokaci Allah yana buɗe ƙofa ta alkhairi ta hanyar mutane ba tare da mun sani ba. Ina fatan duk abin da Allah ya ƙaddara mana zai kasance mafi alkhairi."
Maryam ta kalle shi cikin mamaki.
"Daddy, kana magana kamar akwai wani abu a ranka."
Alhaji Bashir ya yi murmushi kawai."Time will tell."Ya miƙe tsaye yana cewa,
"Allah ya sa duk abin da muke nema ya kasance alkhairi gare mu."
Duk suka amsa da,
"Ameen Ya Rabb."
A zuciyarsa kuwa addu'a É—aya ce kawai yake yi...
"Ya Allah, idan wannan tunanin nawa alkhairi ne ga Muhammadu na, Ka sauƙaƙa mana hanyarsa. Idan kuma ba alkhairi ba ne, Ka zaɓa mana abin da ya fi."
A ɓangaren gidan Alhaji Umar Farouk kuwa...
Bayan sun yi sallama da Alhaji Bashir, kowa ya shiga mota suka kama hanyar gida.
A cikin motar kuwa, Sadiq bai daina surutu ba.
"Daddy, wallahi abincin gidan Alhaji Bashir ya yi daÉ—i sosai."
Khadija ta yi dariya."Kai dai Sadiq, duk inda aka ba ka food mai daÉ—i, shi kaÉ—ai kake tunawa."
Sadiq ya yi dariya.
"Why not?Food is life."
Duk suka yi dariya, har Alhaji Umar ya ce,
"Wannan yaron ba zai taɓa canzawa ba."Sai dai duk da murmushin da ke fuskarsa, zuciyarsa cike take da tunanin maganar da Alhaji Bashir ya yi masa bayan sallar Magriba.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya.
"Ya Allah, Ka shiryar da ni zuwa mafi alkhairi."
...
Da suka isa gida, driver ya buɗe musu ƙofa, suka shiga cikin falon.Nan take Ammi ta taso daga kujerarta tana murmushi.
"Sannu da zuwa."
"Lafiya lau," suka amsa gaba É—aya.
Miemi ma ta fito daga ɗakinta, hannunta riƙe da wani littafi."Welcome back, Daddy... Welcome, Khadija... Sadiq."Sadiq ya yi saurin ƙarasa wajenta.
"Miemi! Wallahi kin yi missing."
Ta yi murmushi.
"Really?"
"Yes!.Da kin ga irin gidan da muka je."
Miemi ta É—an É—aga gira."How was the visit?Khadija ta amsa cikin natsuwa.
"Alhamdulillah, komai ya tafi lafiya. Sun yi mana tarba sosai."khadija ta kalli Miemi.
"Lessons É—inki fa?"Miemi ta yi murmushi.
"Alhamdulillah yaya khadija, na je. Har teacher ya yi mana revision saboda exams suna ƙaratowa.""Good girl. Allah ya ba ki sa'a."
"Ameen."
A gefe guda kuma, Alhaji Umar ya yi shiru yana kallon iyalansa É—aya bayan É—aya.A gefe guda kuma, Alhaji Umar ya yi shiru yana kallon iyalansa É—aya bayan É—aya.
Maganar da Alhaji Bashir ya yi masa tana yawo a cikin zuciyarsa.
Ya kalli Khadija na É—an lokaci, sannan ya kau da kansa ba tare da ya ce komai ba.
Ammi ta lura da hakan.
"Alhaji, lafiya kuwa? Tun da ka shigo kana kamar mai wani tunani."
Alhaji Umar ya yi murmushi kaÉ—an"Alhamdulillah... babu komai."
Amma a zuciyarsa ya san cewa akwai babban abu da zai tattauna da matarsa kafin ya yanke kowace irin shawara.A wannan dare, barci ba zai yi masa sauƙi ba...