Hs 18
by @legendspen
Page 18_
"Mu ta fi gida kuma?." Bhatool faɗa tana kallonsa, shi kuma ya gyaɗa ma ta kai. "Ni dai A'ah, yaushe mu ka zo haba."
"Ni zan tafi to." Tsaki ta ja ta dau jakarta ta fice, shikuma ya bi ta baya gwanda ta yi ta fushin amma bazai jure ganin yadda samarin wajen ke ta kallonta ba, a ƙafa ta fara tafiya. Motar ya shiga ya biyo bayanra, ta na ji yana mata hon amma ta yi banza kamar ba ta ji ba, sauka ya yi daga motar ya nufu ta yana faɗin. "Bhatool, ki tsaya mana."
"Me zan ma?."
"Ki tsaya mu tafi gida." Ci gaba ta yi da tafiyarta hankalinta kwance ba ta ko kula shi ba, sai da ta yi tafiya mai nisa sanan ta juyo, ga mamakinta sai ganin Senate ta yi zaune a kan wani tudu yana kallonta, fuskarshi kamar zai yi kuka. "Oh ni Bhatool, mai na kwasowa kai na haka?, shi da zai lallaɓani amma shike fushi." Ta faɗa a cikin ranta, a fili kam cewa tayi. "Idan bazaka tawo ba zan koma wajen bikina."
"To a ƙafa zamu tafi?." Harara ta maka mai sanan ta ce. "A me muka zo?."
"To ai kin ƙi shiga motar."
"Ɗakko mu tafi." Juyawa ya yi ya nufi motar ita kuma ta bishi da kallo. "Ga mutum har mutum amma sai shashanci kamar wani ƙaramin yaro." Motar yakawo inda take sanan ya buɗe ma ta ta shiga, haɗe rai ta yi ba ta ce ko ƙala ba dan haushin senete ne fal a ranta, dan wallahi gobe ma ba zata bashi katin dinner ba. "Oh wa ma ya aike ni." Ta faɗa a ranta. "Bazaki kulani ba?."
"Wai wane irin abu kakemun haka, kamar ƙaramin yaron, ni banajin yin magana."
"Ki yi hakuri." Ya faɗa yana cuno baki gaba. "Me ka yi mun?."
"Na baro ki daga wajen biki, Bhatool wallahi ina son ki, so mai tsananim gaske mai kuma nauyi, Bhatool bazan iya jure ganin maza na kallonki ba, Bhatool a kowanne dare kafin na kwwnta sai na yi kukan rashinki kusa da ni. Bhatool ban san so ba sai lokacin da na sanki, ban san zan iya tunkarar mace ba sai a kan ki, Bhatool ban san zan zama sakarai a kan mace ba sai a kan ki. Bhatool ban san zan iya kuka a kan mace ba sai a kan ki, Bhatool son ki ya shige ni a lokacin farko, ya mamaye rayuwata ta yadda banajin zan iya rayuwa ba tare da sautin bugun zuciyarki ba."
Shiru Bhatool ta yi, duk kalaman Senate suna shiga sassan jikinta, suna ratsa ƙashi da ɓargonta, wani irin san yi yana mamayw rayuwarta. Tabbas Senate abun a so ne, Senate mai son ta ne, ita kan ta ba ta tuna lokacin da son Senate ya shige ta, sai da tasan ya yi wa zuciyarta kamun da cire shi zai zama babbar wahala.
"Bhatool bana jin akwai abinda zai gagari sadaukarwa sabida ga soyayyarki." Kalaman da suka dawo da ita daga tunanin da take. "Bhatool nu dake haɗin Allah ne, ki yarda da ni, zan baki gata, zan baki kula, zan baki soyayya, zan zame miki bango da zaki jingina da shi a rayuwa, zan zame miki tsananin da zaki taka ki samu nasara a rayuwa, zan zame miki matattakalal da zaki taka ki samu al-jannah, Bhatool zan zame miki abokin rayuwa na har abada, Bhatool" ya kira sunata a ƙarshen maganar. Ɗagowa ta yi amma ta kasa kallonsa. "Ɗago ki kalli idona dan Allah." A hankali ta ɗaga idanunta ta sauke su a kan na sa. "Bhatool.."
"Na'aam."
"Bhatool ki so ni dan Allah, Bhatool na miki alƙwarin soyayya mai tsafa fa iganci, na miki alƙwarin sadaukar da komai nawa domin siya miki farin ciki Bhatool."
Ƙasa ta yi da kan ta, ta fara wasa da yatsunta. "Ina sonka Senate." Ta faɗa a cikik ranta, a fili kam shiru ta yi, amma kalaman senate suna amsa kuwa a cikin kunnuwanta, tabbas ta cika mai sa'a da samun senate.
"Kin yi shiru Bhatool."
"Na'am." Ta faɗa a ɗan tsorace. "Ba ki ce komai ba."
"Na ce mana."
"Banji ba sake faɗa."
"Allah ka ji." Dariya ya yi sanan ya ce. "Banji ba fa."
"Na ce Eyh."
"Eyh, me?." Shiru ta yi tare da yin ƙasa da kai. "Ba zaki ce komai ba?."
"Ina son ka nima." Wani sanyi Senate ya ji a cikin zucoyarsa, daman kuma amsar da yake sa ran ji kenan, godia ya yi wa Allah a fili sanan ya ce. "Bhatool na yi miki alƙwarin ba zan taɓa bari ki yi kuka ba, bazan ta ɓa bari ki ji babu daɗi ba, zan fara ta miki da komai nawa, in Allah ya yarda Bhatool."
(Uhm, ni kam na ce Team senate and Bhatool ku yi screemshot ɗin wanan alkwari na senate ku ajiye shi, dan wata rana ku dinga tuna mai😂😂)
~~~Red bricks.
Mom ce ta kalli Dad dake zaune yana danna waya, sanan ta ce. "Nifa bangane inda wanan zancen nala ya dosa ba, me kake nufi?."
"Wai mene baki gane ba, tun ɗazu muna ta maimaita zance ɗaya."
"Shi Justice audun mai ya ce, har da zaka ce baka amince da auren Senate ba, wane abu ya binciko a game da yarinyar?."
Miƙewa Dad ya yi sanan ya ce. "Nima ban san me ya gano ba, amma tun da ya ce mun akwai matsala to kin san dole akwai, dan haka ba zan taɓa yarda ɗana ɗaya tak ya yi aure waje mai matsala ba." Yana faɗin haka ya shige ciki, ta shi ta yi ta bi bayan sa ta na faɗin. "To mene yasa bazai faɗi matsalal ba sai dai ya ce akwai matsala, sanan justice Audu ai ba shi yake da ikon yin bincike a kan matar da Senate zai aura ba ko?."
"Ban san lokacin da kika fara mayar mun da magana irin haka ba, kin sani, na sani justice Audu abokin kwarai ne, tun kafin na sanki na san Audu kuma yakasance abokin shwara a kowanne lokaci, kuma kema a haka kika ta so."
ku yi hak'uri kuna ganin page din yan kadan, littafi na ne na farko, amma a gaba akwai masu yawa, pls karku manta da following dina, dan Allah.
Legendspen.