JODAH

29

by @sadisakhna


 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

👑*WarÆ™a ta (29)*👑 

 

 

HaÉ—a magani nakeyi,amma harna gama bansan mai sassaka a cikin kwalbar ba,ajiyar zuciya nasake. GabaÉ—aya kwanannan nazama wata iri. Banda tunanin Hammar babu abinda nakeyi. Wai nayi masa hukunci ta hanyar Æ™aurace masa,amma kuma hadda tawa zuciyar nake hukuntawa.  

 

Bantaba sanin haka nayi zurfi cikin wautar sonsa ba sai yanzu,nayi zaton abinda yayimin zaisa naji haushi na tsaneshi ko kuma na fita a rayuwarsa,amma gabaÉ—aya na gagara tsanarsa,haushinma iya na kwana uku naji, tun a sannan nakeso naje naga halinda yake ciki,da kyar nake danna zuciyata na fasa zuwa. 

 

 

Maganin tsaida jini nake haÉ—awa, Na wani matashi Badakare da aka sareshi jiya bayan wasu barayi sun kawo hari. Ina cikin aikin wata baiwa tashigo inda nake. 

 

"Barka da aiki Joda" 

 

"Yawwa barka Rabi'atu ya aiki" 

 

"Alhamdulillah dama wani ne yazo wanda suka kwanta a É—akin gabas yana nemanki" 

 

Tana faÉ—a nasan Fasih take nufi,kamar bazanje ba sai kuma na ajiye abinda nakeyi na fita.  

 

A zaune na sameshi akan wani dakali ya juya bayansa,Æ™arisawa nayi na zauna a gefensa nima ina kallon inda yake,wasu bayine an sakashi É—ebe shara suna ta aiki. A raina nace Allah ya É—agani yamin sauyi da irin wajen. 

 

"Barkanki da wannan lokaci Joda,nasan zakiyi mamakin zuwana inda kike,duk da ba wannan ne karo na farko ba. Saidai wannan karon zuwan kaina nayi bada izinin mai gidana ba. Joda duk abubuwan daya faru tsakanin ki da yallabai Hammar nasani,tun sanda kika fara yimasa magani a farkon a haÉ—uwarku,lokacin da kika cigaba da kuladashi,sanda ya fansheki a hannun shugaban makarantar domin ceton rayuwarki, lokacin daya faÉ—a soyayyar ki har zuwa abinda yafaru tsakaninku satin daya wuce. Dukka yafarune bisa Æ™addara da kuma nufin Allah. Yallabai Hammar bai tabayin zaman awa samada uku waje É—aya da mace ba tun tashinsa,hasalima an saka hannu wajen haramta masa jin wani abu dangane da mace tun tashinsa. A ranar yadda cewar zuciyarsa tana matuÆ™ar sonki a lokacin wannan makullin na bangaren jin shauÆ™i ya buÉ—e masa,kuma tundaga ranar yake cikin matuÆ™ar wahala a duk lokacin da kuka haÉ—u kuma kuka rabu,yanzunma na tabbata Æ™arfinsa ne yagaxa wajen bawa zuciyarsa linzami har wannan abun ya faru. Dan Allah kiyi haÆ™uri Joda kada ki Æ™auracemasa. Kwana bakwai kenan yarasa nutsuwarsa da kuma lafiyarsa. Duk yanda wannan gasa take da muhimmanci a rayuwarsa amma yakasa maida hankali gashi wani satin za'a fara. Dan wannan nake roÆ™onki daki daure ki dubeshi Joda,koda ba'a matsayin mai gidanki ba ki dubeshi a matsayin masoyinki......" 

 

Wani abu naji ya tokaremin lokacin daya cigaba da bani labarin kalubalen daya samu na rayuwa a tasowarsa,nima dukkan abinda yake faÉ—a na zargesu a tattare dashi,idan ba haka ba maizaisa zuciyarsa tayi rauni a matsakaitan shekarunsa. 

 

"Naji abinda kace Fasih amma waÉ—annan uzurirrikan banajin sun shafeni da har zan sake MiÆ™awa rayuwata gareshi,masoyi bazaimin abinda yamin ba,duk da kuwa yasan halinda zan shiga bayan hakan. Da ma a matsayin baiwa da maigidanta ka buÆ™aci naje,wannan zan bashi dukkan abinda buÆ™ata matuÆ™ar rayuwata zata iya yimasa. Saboda hakan shine Æ™addarata kuma matsayina a yanzu,wato yin abinda maigidana yakeso koda kuwa ya kasance abinda ni banaso. Lokacin dana gano cewar ya mallakeni,nayi mamaki da bai nunamin wani sauyi ko nuna iko ba,hakan yasa na fara sakawa a raina cewar wataÆ™ila shiÉ—in dabanne da sauran Æ´aÆ´an manya,shi ba haka yakeba. Saida zuciyata ta aminta dashi tukunna ya nunamin kalarsa a fili. Yayimin yankan da bazai warke ba a raina. Babu ruwana da wahalar dayasha,tunda har yanzu banida matsayin dazai fayyacemin asalin wanene shi,domin a ganinsa bankai nasan hakan ba. Nasaka a raina cewa amfani kawai yake dani domin cimma muradinsa,amma ko kaÉ—an bai É—aukeni da daraja yanda yake nunawa ba" 

 

Tashi nayi zan bar wajen Ya tashi ya tare gabana da sauri,damuwa ce Æ™arara a fuskarsa kamar yanada mai lafiyar dazai mutu kuma an Æ™i kaimasa agaji. 

 

"Dan Allah karki É—auka haka,wlh yana matuÆ™ar sonki yana Æ™aunarki,halinda kika sakashi baki bazai iya furtawa ba,Jin girman zunubin daya aikata miki a zuciyarsa shine ya hanashi nemanki duk da kuwa shine abinda yake matuÆ™ar buri a yanzun,wato kasancewar ki a tareda shi. 

 

Joda bashida lafiya kuma kece maganinsa,dan Allah kada abinda zuciyarki yake rayamiki yasa ki kasa waiwayarsa. Batun rashin faÉ—amiki asalinsa,yanada babbar hujja akan hakan ga rayuwarki dakuma tasa,kisa ranki rashin sanin yafi alkhairi akan sanin shiyasa. " 

 

Duk da maganganunsa sun tabani amma naÆ™i nuna masa akan fuskata,batareda nasake cemasa komai ba na zaga ta gefensa nawuce. 

 

Bayan yabar wajen ina zaune babu abinda yake yawo a cikin kaina sai maganganun da Fasih yafaÉ—amin. 

 

Jiki babu kwari Fasih yakoma bangarensu,a kwance yasamu Hammar yarufe idonsa kaman mai bacci,fuskarsa harta rame,batareda ya buÉ—e idonsa ba yace. 

 

"TaÆ™i amincewa da maganganunka koh,nasan daga wajen kake a halin yanzu" 

 

Shuru Fasih yayi bashida bakin yimasa magana,a haka suka zauna kamar kurame har goshin magriba. 

 

Rike abincin daren nayi ina gaurayashi amma na saka kaiwa bakina,maganar Addah Rahilah naji kamar a sama,ashe duk abinda nake tana lura dani,watanta guda kenan muna kwana tare,dama idan mijinta bayanan nan take zuwa mu zauna har sai yadawo. 

 

"Duk wannan kewaye kewayen bazai kaiki ba,idan kina kewarsa yakamata kije ki ganshi kafin kiyi nadama" 

 

ÆŠaga kai nayi na kalleta,idona ya cicciko da hawaye kamar zanyi kuka. 

 

"Addah Rahilah nace ganshi fah kikace,bayan ketamin mutuncin dayayi,har yanzu na gagara gasgata hakan wai banida matsayin daza'a ce ni budurwace" 

 

"Hmmm Joda kenan,dan ma anan kika tashi kuma kinsan mai yake faruwa,sannan kinsan matsayinki a tsarin rayuwar wannan zamaninnamu,ballantana kice baki sani ba naÆ™ara miki Æ™arin haske. 

 

Mutuminnan kinasonsa kuma shina yana sonki,bayan wannan matsayin shi mai gidanki ne ke baiwarsa ce,amma kiga lokacin daya É—auka batareda ya taba sakaki wata bauta ba kokuma yabaki umarni,Æ™arshema burinsa shine baki Æ´an ci kafin ya tafi,kuma bayan yayi amfani da maÆ™udan dukiya wajen fansarki duk domin kar wancan azzalumin yasamu dama akanki. Dan wannan Æ™addarar ta gilma a tsakanin ku wadda bakomai bace a rayuwar bayi irinmu shine zaki Æ™ullaceshi. Kar abinda yake miki da kuma matsayin da Allah yabaki yasa kiji ke mai Æ´an ci ce,idan kishirwar samun babban matsayi ya rufemiki ido zai sakaki yin nadama maimakon É—aukaka Joda" 

 

Zuwa lokacin kukan danake riÆ™ewa yakubcemin,haka tajani tabani kafaÉ—ar kuka har nayi na gaji. 

 

Saida naji hankali na yadawo jikina kafin na debi ruwa nayi wanka,na shafe jikina da miski mai Æ™amshi sannan na É—auki kayana wankakku masu fasali na saka. Addah Rahilah taso nayi kwalliya amma naÆ™i,a haka na yafa mayafina na nufi sansaninsu, ina hango ranar danaje wancan satin da lokacin da zaren Æ™addara ya É—inke a tsakaninmu. Sai gashi a yau zan sake komawa da Æ™afata,saboda na farka daga mafarkin danakeyi wanda yake saka na ganni niÉ—in mai darajace. Na yarda cewar yagama mallakata,ba kuma iya gangar jikina ba harma da zuciyata gabaki É—aya sun sallama agareshi koda sona ko babu. 

 

 

Tari yakeyi wanda duk sanda yayi sai zuciyarsa ta motsa,yana kubar wani abu a kofi mai turiri da alama shayi ne na magani wanda nake haÉ—amasa,da alama Fasih ne yayimasa dan dama na koyamasa a lokacin ganin yana sonsa sosai. 

 

Dukkansu É—ago ido sukayi suna kallona,da alama basu tsammaci zan kawomusu ziyara ba a lokaci. 

 

"Sannu da zuwa Joda ki shiga ciki bari na kawo miki shayi" 

 

"Ahah karka damu fasih nagode a Æ™oshe nake,domin yanzu naci abinci" 

 

"To shikenan bari naje wajen karatu dama inason zuwa,banason barinsa shi kaÉ—aine shiyasa banje ba" 

 

Yayi maganar da yawon yafita ya barmu ni kaÉ—ai dashi,domin yasan shine abinda mai gidannasa yakeso. 

 

Da sanyin jiki na isa É—akin na zauna,tun haÉ—a idon da mukayi na farko naÆ™i yarda musake yin nabiyu,haka kurin naji kunyarsa ta mamayeni sosai. 

 

Hannunsa ya É—auka kamar mai tsoron tabani ya É—ora akan hannuna wanda suke kan cinyata,magana yafara cikin sanyin murya,wanda ko zuciyata da Æ™arfe akayita dole naji tausayinsa. 

 

"Nasan kina fushi dani kuma kin tsaneni ko Joda,amma banyi zaton zaki Æ™auracemin har na sati guda ba a sabon damuka bawa junanmu. Soyayyar kice da tsananin buÆ™atarki tasa na aikata miki haka,amma bawai dan na wulaÆ™antaki ba,dan Allah kiyi haÆ™uri kiyafemin,nayi miki alÆ™awarin bazan sake yimiki wani abuba batareda izininki ba" 

 

Saurin jijjiga kaina nayi tareda sheshsheÆ™ar kuka,dan ji nayi zuciyata tayimin rauni. 

 

"Ahah nice yakamata na baka haÆ™uri,kayi haÆ™uri anan natashi ba'a koyamin baiwa tayiwa ubangidanta biyyaya ba,na tashi ne da koyon ilimi amma ba wanda yashafi sha'anin bauta ba,sai hakan yasakani ina manta matsayina da kuma naka gareni. Abinda kayimin haƙƙin mallakarka ka karba,ko a wajen Allah bakayi laifi ba,kawai abinda yasakani cikin zullumi shine ban taba tunanin hakan daga gareka ba Hammar,nayi zaton ka É—aukeni fiyeda baiwa a wajenka shiya........." 

 

"Wlh na É—aukeki joda,matsayinki a wajena yafi na mai Æ´an ci ma ballantana Baiwa,shin taya zan iya nunamiki zuciyata kiga cewar dominki take bugawa, wannan abinda yafaru Æ™addarace,amma ko kaÉ—an baya fassara matsayin da kike dashi a wajena,dan haka kar wannan yasake shiga tunaninki,ina sonki joda ina Æ™aunarki ban taba yiwa wata mace son danake miki ba,nima bansan mai yashiga kaina ba haka. Wasu abubuwan danakeyimiki harma dana boye matsayina nayine dominki,sannan kuma koda nafaÉ—amiki bazaki yarda,saboda ni kaina gani nake dana yanzu na dakuma na da gabaÉ—aya ba iri É—ayane. Dan Allah kidaina gudu na,ina tsoron kada zuciyata ta buga akan haka" 

 

Da kalamansa masu kama da asiri yashawo kaina na manta da ya tabamin laifi a rayuwata,yanda yake roÆ™on na kasance a rayuwarsa mutum bazai taba É—auka cewar shiÉ—in ubangida nane ba nikuma baiwarsa. Har mamakinsa nake,duk da nima inayi masa son dani kaÉ—ai nasan yawansa. A ranar biyeshi nayi muka baje duk wata soyayya da mukewa junanmu a aikace ba iya furucin kan fata ba. Nasha ruwan godiya da albarka a gareshi,yayimin alÆ™awarin Æ´an ci yafi sau a Æ™irga,saidai duk ban É—aukesu har rainaba saboda bai rubutamin a rubuce ba,saidai nasan a yanda yakemin lokaci kaÉ—anne yasaura yabani wannan abin danake mafarkin samu wato Ƴanci. A da nayi zaton yan cina yanaga Jajircewata da kuma Æ™warewata,bansani ba ashe yanaga adadin samun soyayya da kuma bada ita kanta soyayyar,sannan kuma da yarda da amana. 

 

Bacci mai nauyine ya É—aukemu,sai kusan asuba muka farka,har sannan babu fasih babu alamarsa,da alama yasan abinda zai wakana bai kwana a sashen ba,kuma gwara hakan domin daya ganewa idonsa abinda bazaiso gani ba. 

 

Tare mukayi wanka muna ta nishaÉ—i da raha,ji nake kaman mu dawwama a haka,karya koma Æ™asarsu nima kuma na daina mafarkin samun abinda yake fiyeda wanda na mallaka. 

 

 

**** 

 

 

Jifa yayi da ƘoÆ™on dake gefensa saida ya daki bango ya fashe,idonsa yayi jajir yana muzurai. Ita kanta Sunkia madina saida ta tsorita da yanayin da taga É—annata yashiga. 

 

"Ummah ki gayamin gaskiya idan ma boyeta kikayi, Har yanzu inaji a jikina kamar tana gidannan,kawai kin hanani ganinta ne. Wlh dagaske nakeyimiki inason yarinyar nan,kuma a yanda nakeji zan iya yiwa koma waye illah idan yace zai rabani da ita,dan haka kada ma ki dunga É—aukar furucina da wasa" 

 

Yau sati guda kenan kullum yana yawon neman Joda a cikin masarsutar,tun ranar dasuka haÉ—u ta zame ta gudu yarasa hayyacinsa. Baisan mai yake damunsa ba amma ya daina kallon kowacce mace a gabansa sai ita. Ita kanta Zaleekah tayi iya Æ™oÆ™arinta amma ya birkice mata,ko kanta tabashi babu sunan wacce yake Æ™ira saina Joda. Wannan abu ya bata mata rai sosai,shiyasa ta Æ™uduri niyyar itama nemanta domin ta É—aiÉ—aita rayuwarta. 

 

Gimbiya Asmah kuma tabi mahaifiyarta masarautar Ghana,saita warke kafin ta dawo,kuma kowa ya yarda da hakan,duk da a al'adarsu babu tafiya gida wanka to amma kowa yasan lalurinta yakai ayi mata wannan uzurin. Musamman da yanzu ita kanta ta daina yimasa wannan jahilin son,data kula cewar gogan baya ta ita,kota mutu ko tayi rai duk É—ayane a wajensa. 

 

A zuciye ya fita daga cikin turakar mahaifiyar tasa,wacce take kallonsa cikeda da takaici dama wasu abubuwan masu wuyar fassaruwa,wanda suka hanata ko magana tasake yimasa. Shi kansa daya ga haka yakama hanya ya fita. 

 

Bayan ya fita bin bayansa tayi da kallo tareda sauke ajiyar zuciya kana tace. 

 

"Allah kayi mana maganin wannan masifa,ko mai zayyi da baiwa yake wannan haukar akanta oho. Allah yasa Asmah da mahaifiyarta basanan daya jawomin abun kunya Æ™arara" 

 

Wata baiwa ce tashigo da saurinta jikinta yana rawa ta zube a gaban Sunkia Madeena. 

 

"Ranki ya daÉ—e da labari nazo Æ™unshe a bakina na abinda yake faruwa a masarauta yau" 

 

"Ko menene domin ke Saratu bakya rasa abin cewa,narasa a ina kike samo labarai,ko tsuntsu mai leÆ™e bai kaiki bayani ba" 

 

"Wannan hakane Ranki ya daÉ—e É—awisu kuma Bijimar wannan masarauta......labari nazo dashi na dawowar mai Girma Gimbiya Hareesah daga Birnin Jodan inda ta kammala karatunta" 

 

Dan dare ido Sunkia Madeena tayi kafin tace. 

 

 

"Kina da tabbacin wannan maganar" 

 

"Saka wuka a wuyana ranki yadaÉ—e,amma wannan maganar bazata taba sauya ba,yanzu haka har masarauta an fara shirye shirye na tarbanta" 

 

"Tashi kije na sallameki toh kina iya tafiya" 

 

Kai yana rawa ta tashi tafita,jikinta a sanyaye ganin yau Sunkia Madeena bata yimata alherin komai ba. 

 

Magana take Æ™asa kasa tana cewa. 

 

"Kwananann nakula inna kawomiki labari bakya bani komai,idan hakane inkinsan wata ai baki san wata, nasan inda zan kai wani labari na tabbata zan samu babban alheri. Duk abinda kukayi da Yerima Kabeer naji, Magen dayake nema zanje na faÉ—amasa kalar kifin dazai jefa mata yakamata cikin sauÆ™i. Kowa ya mutu mu idan zamu samu ai" 

 

Tayi maganar tana Æ™iƙƙifta ido tareda yin dariyar mugunta.  Daga wajen kuwa batayi sanya ba ta nufi hanyar dataga Yerima Kabeer ya nufa. 

 

***** 

 

Yau kwana uku kenan tunda wata BaÆ™ar wasiÆ™a ta sameni daga hannun Yerima kabeer,boyewa kowa nakeyi kan babu abinda yake damuna,amma abun yana cina sosai. Ko Hammar yayimin tambaya sunfi a Æ™irga amma naÆ™i bashi amsa,saidai nace masa babu komai. Sa'a ta É—aya sun fara yin gwaji na gasarsu dan haka baya tani,nima kuma hakan yayimin daÉ—i sosai,domin nasan duk boye masan danakeyi watarana dole zai gane. Yanzuma É—auko wasiÆ™ar nayi a karo na babu adadi ina duba,É—aci da maÆ™aÆ™i suna É—arsuwa a cikin zuciyata.  

___Nasan zakiyi mamakin ganin wasiÆ™ata to kar hakan yabaki mamaki ko kaÉ—an,domin tun farko ma ban rabu dake ba ballantana kuma na haÆ™ura dake. Kema kuma nasan bazaki taba daina tunanin masarautar nan ba saboda GinshiÆ™inki kuma gudan jininki dayake ciki wato mahaifiyarki . Idan kinasonta da ranta da lafiyarta to daga yau duk abinda na aiko shine zakiyi,in kuma kina son shafewar rayuwarta daga doron duniya haÉ—e da baÆ™ar uÆ™uba shine ki butulcemin. Karkiyi tunanin aiki da Æ™wakwalwarki akaina,domin mutanena da suke wannan jami'a hannu bazai iya Æ™irgasu ba. GargaÉ—i na Æ™arshe karki taba bari yasan mai yake faruwa,idan ba haka ba kuma ........hhmmm. 

 

Ke mallakina ce ni kaÉ—ai,zan iya komai domin samunki. 

 

Daga Yerima kabeer mai shirin zama ubangidanki na har abada____ 

 

Hawayen dayake idona ne ya sauÆ™a akan takardar,shin wannan wacce irin masifa ce haka,wai ina baiwar ma mai yagani a jikina ne. DurÆ™ushewa nayi a wajen tareda Æ™iran sunan ummata cikin raunanniyar murya,Allah sarki ummata zan jure komai domin kubutar dai ta,kaman yanda suma itada Abaa suka bada rayuwarsu domin kubutar da tawa. Wannan karon nawa lokacin ne na kareta daga mugu azzalumin É—an sarkinnan. 

 

A zaune nake a bakin ruwa, wanda yake cikin lambun bayan sansaninmu, yamma ce babu kowa a wajen sai mu biyu,Hammar yana ciki yana wanka nikuma na tsurawa ruwan ido. A zahiri shi nake kallo amma a cikin zuciyata saÆ™on da aka bayar a bani yaune ya tsayamin a rai,wasiÆ™ace mai É—auke da cewar na fito bakin Æ™ofar Jami'a akwai daidai sa'a takwas na dare. Bulala hamsin ga mahaifiyata idan naÆ™i zuwa,sannan a bakin ranta idan na faÉ—awa wani. 

 

Irin waÉ—annan saÆ™on sune abinda nake karba akai akai kwannan,idan nayi niyyar bin diddigi kuma sai narasa wanene yabani saÆ™o,domin iya bayan nake gani bana ganin fuskarsa. 

 

Ruwan danaji akan fuskata ne yasakani saurin É—agowa na kalleshi cikeda alamar rashin gaskiya. ÆŠauke da kulawa yake kallona kafin yasaka hannunsa ya tallafo fuskata kana yace. 

 

"Joda Njusu(Zuciyata) menene yake damunki? Kwanannan kina nauyaya zuciyata da damuwarki wacce kika kasa faÉ—amin mecece ita" 

 

ÆŠagowa narkakkun idona nayi na zuba masa hawaye na zuba,inama zan iya faÉ—amasa. Domin kaman yanda yake cutuwa da ganina a damuwa shima banason sakashi a damuwar.  

 

Jijjiga masa kai nayi alamar babu komai,ina Æ™ara kwantar da fuskata akan hannunsa,bai sake cewa komai ba sannan bai É—auke hannunsa ba har muka É—au wasu lokuta a haka. 

 

"Allah yasa abinda kike boyemin bamai cutarwa vane a gareki ko kuma ni,idan hakane zuciyata bata iya yafewa hakan ba. Inason sanar dake nayi nasara a zagaye na farko dana biyu,sai mu jira na Æ™arshe makon sama. Naso muyi liyafar farinciki dagani saike amma kuma ganinki a wannan yanayin nima sai naji abinda bai sakani farinciki ba" 

 

Bansan mai zance masa ba dan haka kawai na faÉ—a Æ™irjinsa na rungumeshi inaso naji ko raÉ—aÉ—in danakeji a raina zai ragu. So nake nayi kuka amma bansan ya zai É—auki lamarin ba. Cikin raunanniyar murya na furta masa. 

 

"Kayi haÆ™uri Hammar" 

 

Bai bani amsaba sai sake Æ™anÆ™ameni dayayi kawai. Allah ka kawo mana mafita nace a raina. 

 

A gaggauce muka rabu dashi kafin dare yayi saboda inason zuwa wajen da aka umarceni a wasiÆ™ar. Babu yanda baiso mu kasance a tare ba a daren,kasancewar zuciyarmu da gangar jikinmu sun saba da juna. Amma haka na sulale na tafi,saboda banajin sukunina a tattare dani. Idanuwana iya mahaifiyata suke hangowa a tattare dashi kaÉ—ai yana azabtar da ita. 

 

Inayin sallahr isha nasake lullube mayafina duk jikina na fita,kai tsaye hanyar bakin Æ™ofa na nufa,a raina nayi mamaki da naga dakarun Æ™ofar basu hanani fita ba,kenan suma wasune daga cikin mutanensa. Koda yake menene abin mamaki shine fah mai Æ™asar gabaÉ—aya. LelleÆ™awa na farayi amma banga kowa ba,saina tsaya na daÆ™iÆ™u kaÉ—an amma babu wanda ya bayyana,hakan yasa na juya domin komawa.  

Kicib naji nayi karo na mutum ina dab da shiga sansaninmu,gabana saida ya yanke ya faÉ—i,naji faÉ—uwar gaban da koda na fita wajen banji irin ta ba. Hammar na kalla a gabana da kayan shan iska a jikinsa a farare. Idonsa sun kaÉ—an sunyi ja kamar garwashi,sunan Allah na fara ambata a cikin kaina,inda na datseshi lokacin danaji muryasa. 

 

"Ina kikaje joda a cikin wannan lokacin,shin dama kinada wani wanda alaÆ™a take haÉ—aku dashi a wajen Jami'ar nan ne. Mai Yerima Kabeer yakeyi a cikin jami'ar nan a wannan lokacin. Karki gasgata min abinda zuciyata take rayamin,shin dama shine damuwar dakika shiga kwanannan,dan  kinason haÉ—uwa dashi ne. Tunda farko na tambayeki idan sonsa kikeyi zan barki gareshi amma meyasa sai bayan........ 

 

Saurin jijjiga kaina nayi,ganin yana magana cikin Æ™unan zuciya,Æ™irjinsa yana sama yana Æ™asa. 

 

Nayi mamaki mai yasa zaice naje waje kuma naje bayanan,sai a yanzu nagane duk wasan kwaikwayo ne na yaraba yardar da take tsakanina da Hammar,zan so na fahimtar dashi amma nasan babu damar hakan. 

 

"Shikenan tunda bakida abin cewa karki damu zuciyata ta daÉ—e da bani amsar data dace. shi bawa dama bawa ne,duk yanda kayi dashi kuwa" 

 

"Wlh ba haka bane Hammar dan Allah karka tafi ka tsaya ka saurareni dan Allah" 

 

A haka yatafi ya barni ina maimata kalmarsa ta Æ™arshe gareni cikin zafin rai. 

 

Mako guda ya shafe Hammr sun shiga zagaye na Æ™arshe a gasarsu amma har sannan bamu haÉ—uba. Gangar jikinmu na kewar juna,amma zuciyoyinmu sunÆ™i hucewa. 

 

Fitowata daga banÉ—akin kenan na ajiye butar dake hannuna,addah Rahilah ce ta kalleni da mamaki kana tace. 

 

"Jodah wai lafiyanki kuwa,bini bini saiki shiga banÉ—aki kuma da alamun ba bahayane yake kaiki ba sai fitsari,nima kaina fitsarin dakikayi yau idan Æ™irgashi zanyi yafi ashirin" 

 

Kallonta nakeyi amma banyi mamakin maganar tata ba,domin nima abinda nake tunanin kenan,shine lafiyata kalau kuwa,ga kasala danaji jikina yanayi ko kaÉ—an banason motsa jikina. Abinda yazo kaina ne yasakani zare ido  jikina kuma yayi sanyi Æ™alau,abinda yazo kaina nasan ita baizo mata kan ba,dan haka mayafina kawai na É—auka na fita daga sansanin namu. 

 

Tafiya nakeyi a hankali amma zuciyata cike take da sake saÆ™e,ga Æ™irjina yayimin nauyi sosai. Kai tsaye É—akin bincikenmu na shiga,sai a lokacin na kula ashe sati na guda rabona da wajen. Ko yaushe Ina sansaninmu tunda muka samu sabani da Hammar shima bana zuwa sansaninsu,kuma banida aiki sai Bacci,ga shuru shuru daya aureni da kuma zafin rai. 

 

Da Ummu hajar naci karo ta shigo ajiye wani abu da ban kula menene ba. 

 

"Joda lafiya kike kuwa kwana biyu bakya shigowa,ga aiki yayi mana yawa nida Subha" 

 

"Kiyi haÆ™uri Ummu hajar nasan banida uzurin Æ™in zuwa aiki amma naÉ—anyi rashin lafiya ne" 

 

"Ahhh karki damu koda akwai Æ™arancin rashin uzuri na aiki ga bayi ke bandake a ciki,amma dai ki dage sosai dan a kwanannan zaki bada bayanan Æ™arshen Jarabawarki ga Baba ina  fatan baki manta ba. Sanann yayi min maganar dama yanason ganinki" 

 

ÆŠan rusunawa nayi bayan na karbi saÆ™on zuciyata tana bugawa uku uku ina kuwa zan manta. Wanda akayi jarabawar a kansa shi ya warke amma kuma ni yasakani a matsala,na tabbata wannan jarabawar ma shine ya Æ™irÆ™ireta da kansa domin samun kusan ci dani. Bansan a wanne mizani zan ajiye haÉ—uwata dashi ba sam. Nakula a kullum amfani yakeyi da rashin sanina akansa yana min yadda yakeso,nayi zaton inada wayo,ashe akan soyayya ni wawuya ce marar ji da gani. Saidai duk da haka bazanga lafinsa ba,rashin bani damar nayi masa bayani ko kuma ko yaya ya fahimceni shine yasakani cikin damuwa.  

 

Bayan ta fita É—agowa nayi kafin na nufi yin abinda yakawoni,akwai hanyoyi dayawa dana karanta na gwada abinda yake damu na,amma banda lokaci dan haka zan gwada hanya mafi sauri daga ciki. 

 

Wata Æ™aramar tukunya na É—auko ta Æ™arfe na É—ora akan inda rura wuta. Garwashi na zuba na haÉ—a wuta akai,kafin ya ruru na shiga makewayin dake wajen na iyo fitsari. 

 

Kawowa nayi na zuba a tukunyar na zuba gishiri kafin na É—ora bisa wutar data faraci. 

 

Idanuwana na zuba akan fitsarin dake cikin tukunyar,kaman ance idan na É—auke kai zai bacewa ganina. 

 

Bayan kaman daÆ™iÆ™u masu yawa fitsarin yafara tafasa a cikin Æ´ar tukunyar. Runtse ido na nayi ina jin kamar jiri yana É—ibana sakamakon yanda naga fitsarin ya fara curewa yana tara kumfa mai kauri a samansa. Alamace wacce na riga nagani kuma bazan taba musawa ba. Wato ina É—auke da juna biyu. 

 

Hannuna yana rawa nakai na shafa cikin a hankali,duk da nasan babu abinda zanji a lokacin. ÆŠauke tukunyar nayi jiki a sanyaye naje na zuba kana na gyara wajen tass. 

 

Fitowa nayi daga wajen,ban tsaya ko ina ba sai sansanin su Hammar. Duk yanda nakejin jikina ya karaya amma hakan bai sakani sarewa ba,na riga na shaidawa zuciyata bazai karbi abinda mahaifata ta Æ™unsa ba,amma soyayya ta dana gani a cikin idonsa shine É—an karfin gwiwar dayasaka zuciyata take É—ore akan Æ™afarta. 

 

Har na saka Æ™afata zan shiga sai kuma naja na tsaya,shin mai zan fara cemasa kenan,tunda wannan akasin yafaru ko hanya baya yarda mu haÉ—a,an sha faÉ—amin masu matsayi bazasu taba ganin darajarmu ba koyi mana uzuri,shin mai yasa duk ban yarda ba,gashi ba'a je ko ina in abu yashiga tsakaninmu sai ya tabbatarmin da matsayina a gareshi.  

 

Musa ne kaÉ—ai a farfajiyar wajen yana shara cikin hanzari da alama bayaso rana ta faÉ—i bai gamaba. 

Sallama nayi hakan yasa ya É—ago ido ya kalleni babu yabo babu fallasa. Tun kafin nakai ga tambayarsa ina Hammar yace. 

 

"Bayanan yana majalisi a can zasu kwana ana tantace wanda yayi nasara tsakanin shida Yeriman Masar,kije  saiki sameshi a wajen karbar sakamako gobe da safe,ko kuma ki bari idan angama taron ya dawo" 

 

Toh na amsa dashi kafin na juya zan tafi,maganar musa ce a karo na biyu tasakani tsayawa. 

 

"Abinda kikayi ya bata masa rai sosai,kiyi addu'ar yazama wanda ya lashe kambun gasar ko murnar hakan zaisa ya sakko daga fushinsa gareki" 

 

Ban bashi amsa ba sai share guntun hawayen idona danayi nabar wajen,a raina nace Allah yakaimu goben ayi duk wacce za'a yi. 

 

Kasancewar yanda bacci na yaÆ™ara nauyi yanxu saboda yaron cikin dana É—auke dashi yasa tunda nayi sallahr asuba wanda itama daÆ™yar nayi na kwanta kamar gawa. 

 

BuÉ—e idona kenan kunnenan suka jiyomin busa da sarewa daga can tsakiyar jami'ar, wato har anfara gudanar da shagalin Karrama gwanin kenan,wanda nasan bakowa bane illah Hammar,sai na shiga tuno yanda nake tayashi bincike dakuma taimaka masa da dukkan abinda Allah ya mallakamin na ilimi,domin ganin masoyina kuma sanyin idaniyata yayi nasara.  

 

Tashi nayi jiki babu Æ™arfi na shirya,domin gani nake kaman idan naÆ™ara jinkirin ko daÆ™iÆ™a É—ayane zai bacewa ganina ya tafi batareda na gana dashi ba. 

 

Lokacin dana isa wajen maÆ™il yake da mutane daga wurare da dama,masu mulki da kuÉ—i sunfi yawa,an Æ™awata wajen da abubuwan saka nishaÉ—i da É—aukar ido,bayi sai kai kawo suke wajen ganin sun biyawa buÆ™atar duk abinda baÆ™in sukeso. Kayan masu kulada marasa lafiya nasaka saboda kar a sakani aiki idan anganni,domin jikina bashida Æ™arfin dazan iya hada hadar da akeyi,ni macece mai kuzari da rashin son jiki,amma wannan duk ya kau a kwannan. 

 

Kutsa kai nakeyi inaso nakai gayin tozali tashi,ana tureni ina turewa a haka idanuwana suka sauÆ™a akansa ana daidai miÆ™a masa kambun zakara daya lashe kyautar na É—aya a gasar ilimin a kaff nahiyar africa,abinda nake mafarki kuma nake burin zama,amma shigowarsa rayuwata haka ya katsemin wannan burin ya shiga gabana batareda na ankara ba.  Hannuna na saka na rufe bakina saboda kukan dayazomin,banyi masa baÆ™in cikin samun wannan nasarar ba saboda ni kaina shaida ce yayi amfani da  kaifin tunaninsa dakuma lokacinsa ya tsaya yacancanta da karbar wannan kambun. Abinda yasakani kuka shine yanda ni tawa rayuwar ta sauya a shekarar ne yabani mamaki da takaici,gabaÉ—aya na nemi wannan jodar mai Æ™wazo da Æ™oÆ™arin cimma buri a rayuwa na rasa.  

 

Yayi shiga ta alfarma,fuskarsa na nuna zatin haiba da kuma Jini na kwarjini,manyan mutane sai kallonsa suke da idon cewar ya zarcesu,inama ko magana dasu zai samu damar yi. Na sake yarda shiÉ—in ba tsarana bane sam,burin yerima kabeer akaina nasan shine yarabani dashi,amma ko bai rabani dashi ba nima inaga yakamata na raba kaina dashi,zamana cikin rayuwarsa bakomai zan tsinta ba sai Æ™alubale. Jijjiga kaina nayi a raina nace kai inaaa komin lalacewar kura tafi kare,Hammar ba tsarana bane,shin mai yasa bangane hakan ba sai yanzu. Kodan da lullube yake da fatar akuya,saida ya yayeta nagane ashe zakine a ciki wanda barewar zuciyata bazata iya zama a kusada shi ba. 

 

Fita nayi daga cikin taron na koma gefe ina haki,saboda rashin numfashin dayake wajen da kuma yawan mutane yasa na farajin jiri yana É—ibana. 

 

Ƙafafuna nauyi sukayimin,ina shirin durÆ™usawa naji anyi sama dani kamar wata an kama kaza,Wani Æ™aton namijine baÆ™iƙƙirin dashi,ya jefani Æ™asan Æ™afar wani. Kallon takalminsa nayi kawai nagane wanene,kuma dama nasan babu maimin hakan saishi É—in. Ban É—ago na kalleshi ba saboda banda Æ™arfin yin hakan,abu kaÉ—an nakeyi naji na galabaita.  

 

"ÆŠagomin kanta ta kalleni dakyau sannan ta kalli girman matsayina" 

 

Bai rufe baki ba naji an DaÆ™umi tsaÆ™iyar kaina An É—ago fuskata tana kallansa,wani kallo nakeyi masa da yawuce ma a fassarashi da tsana,da alama kuma hakan yanayi masa daÉ—i,domin shu'umin murmushi yake aikamin tareda nuna wani waje da hannunsa. 

 

A hankali na waiwaya zan kalli wajen,Æ™irjina yana bugawa domin bansan mai zan gani ba. 

 

Zaro idona nayi ina jijjiga kai da Æ™arfi ganin ummata durÆ™ushe a filin Allah mutanen sunata kai kawo, alamu Æ™arara sun nuna anyi mata dukan tsiya sannan aka tuleta da Æ™asa,ga kayanta duk a furfuje. Wani nauyi naji zuciyata tayimin,walaÆ™ancin dayayi mata kuma nagani da idona ya zarce duk wanda yayi a raina. Shi mai tayi masa sai maidata tamkar mahaukaciya haka, dan kawai ta haifeni ta kawoni duniya shine laifinta? Wacece ni,mai nake dashi da har na tsole masa ido yazamana bashida tunani ko abinyi sai azabtar dani. 

 

Juyowa nayi na kallleshi daidai lokacin da Hammar ya fito daga wajen taron mutane duk sun fara raguwa. Matan da suka shiga gasar ne kewaye dashi kowa tana faÉ—in ya tura takardar neman aurenta garinsu,yawancin su Æ´aÆ´an sarakuna ne da alama. Tun da yafito daga wajen nake kallonsa,ko kaÉ—an nasan banida ikon faÉ—awa kafaÉ—arsa domin yaceceni saboda banida tabbacin a yanzu hammar É—in danasani ne kokuma sabo wanda ya bayyana bayan ya cimma burinsa.  

 

Karaff idanuwanmu sukayi karafkiya da juna daidai lokacin dayake yiwa wata fara a cikinsu magana,fuskarsa É—auke da murmushi. Kallona yakeyi na yanayin dana gagara fahimta,maida kallonsa yasakeyi kan yerima Kabeer wanda yasake masa É—an iskan murmushi. Mayi zaton tunda ya kalleni zai kawomin agaji,ya ajiye haushina dayake ji sai bayan ya ceceni tukunna,saboda ganina a tsugunne kam ai yasan bada san raina nazo gareshi ba. Amma sabanin fahimtata sai naga ya É—auke kansa tamkar baisan da wata halitta wai ita Joda ba.  

 

Jina,ganina,tunanina dukka a lokaci É—aya sukayi wata É—aukewa ta wucin gadi,na fara tunanin anya kuwa ba mafarki nakeyi ba. Hammar ne? .....mai kuka akan soyayyata,mai nunamin rauninsa,mai nunamin kulawarsa,shine ya É—auke kansa ganin yasamu abinda yakeso daga gareni,ya gama da mangwaron ya jefar da Æ™wallon,idan yagama dani yazanyi da jininsa dayake jikina kenan ni Joda. 

 

Kaina na sauÆ™e Æ™asa,ko É—igon hawaye babu a cikin idona gabaÉ—aya ya bushe. A lokacin dayake neman taimako na tsaya akansa,amma yanzu dani ke neman agajinsa ya nuna tamkar bai sanni ba. 

 

Tsugunnawa naji Yerima kabeer yayi a gabana yana kallon cikin idanuwana,ransa yanayin fari daya hango karaya da Æ™unan zuci a cikin idona. Sanann cikeda farinciki yasaki wani murmushi kafin yace. 

 

"Ai dama na faÉ—amiki cewar bana taba rasa duk abinda zuciyata keso,kuma gashi kinga zahiri. Nayi tunanin zan cigaba da buga wasan ashema abin da sauÆ™i zaizomin tunda gashi shida kansa yaÆ™arisa karyamin zuciyarki. Ashe ma shiba Jarumin namiji bane,ko kuma dama ba Æ™aunarki yakeyi da gaske ba tunda har Æ™aramin wasa irin haka zai saka yaja da baya ya sallamaki. Saiki koyi darasi daga haka ki gane ni kaÉ—aine mai sonki da gaskiya,da har na iya yin wannan gwagwarmayar duk domin samunki.  

 

Ziyarata ta kare daga nan,kiji daÉ—inki dama domin ke nazo bawai dan zuwa kallon lusarin gwaninnaki ba. Zan tafi da tsohuwarki amma ki sani idan kika wuce kwana uku baki shigo masarsutar daular songhay a matsayin baiwa ta ba,to sunan waccar abar matacciya a hannuna,kuma mutuwar walaÆ™anci,domin saina saka an keta mutuncinta sau ba'a adadi har sai ta fuskanci mutuwarta a haka,sannan na bada namanta a namun daji. Dan haka saiki zaba. Sannan ki tabbatar kunyi salle walle dashi,domin idan yace zai biyoki kokuma yabani ciwon kai to kuwa kinsan sauran........duk da nasan tunda yasamu abinda yakeso to barin Æ™asar zayyi,a yanda nakalli babu soyayyar ki a ransa to kuwa ba lallai yasake waiwayo nahiyar nan ba" 

 

Runtse idona nayi inajin gudumar kalamansa tana dukan zuciyata,ji nakeyi inama inada damar toshe kunnuwana a lokacin ta yanda bazanji abinda yake faÉ—i ba,amma babu damar hakan faÉ—insu yakeyi kuma dole naji. MiÆ™ewa yayi yabar wajen,ganin ya doshi mahaifiyata yasa na tashi da sauri nabi bayansa,banaso ta ganni tasan kuma na ganta a halinda take ciki,duk yanda zuciyata take dankwafata akan karnayi komai kuma karnace komai a lamarin amma nakasa, da na kalli ya nufi inda take kuma da wuÆ™a a hannunsa gani nakeyi kaman na fusatashi ne,kuma yana zuwa kasheta zayyi ko ya illatata,duk da yace bazai kashe ta ba sainaÆ™i zuwa amma kwata kwata shiÉ—in ba abin yarda bane.  

 

Cikin rawar jiki na shiga tsakaninsu shida ita tareda zubewa a gabansa ina jijjiga kai,abinda naÆ™in wato magana,shina buÉ—i bakina na fara yi.  

 

Dan Allah kayi haÆ™uri kada ka cutar da ita,wlh zanyi duk abinda kace dan Allah karka kashemin ita,ita kaÉ—ai taragemin zanzo na sameka kafin kwana ukun dan Allah kada ka cutar min da ummata" 

 

Maimatawa nake tayi tamkar mahaukaciya,ganin hakan yasa ta É—aga idonta daga kallon Æ™asan da takeyi itama tana kallona da mamakin mai nakeyi a wajen. Da alama yace zai taho da baiwa ne ya zabeta,suna fitowa yayi mata haka.  

 

Amma ga mamakina ashe tasan yana biÉ—ata ne shiyasa yamata haka. 

 

"Joda....ahah karki faÉ—i haka,idan dan tanice ban yarda ki lalata rayuwarki dominni ba,bamu ceto rayuwarki domin ki zama baiwar kan gado akaina ba. Ance rayuwarki tana cikin aminci anan wajen,to ki cigaba da zamanki,ko ganinki ana biyu ma banyi tsammanin zanyi ba, samun Tabbacin kina raye kuma cikin aminci yafimin komai,idan na mutu kiyi addu'a kinji,kisa a ranki nabi mahaifinki muna tare" 

 

"Ahah umma karkice haka zaki rayu,zamu rayu tare duk tsanani dan haka ki daina faÉ—in haka. Insha'allahu sainayi rayuwar dazakiyi alfahari da ita" 

 

"Banzo da ita domin na baku damar zantawa ba,nazo da itane domin na nunamiki iyakarki da kuma abinda yake jiranki idan kika Æ™iyin biyayya, batun jin daÉ—in rayuwa wannan ke kikaÆ™i. Idan kika so a yau in kika bani haÉ—in kai sannan kika miÆ™amin dukkan yardarki da rayuwarki to kuwa bake kaÉ—ai ba,itama sai ta san akwai jin daÉ—i a wannan duniyar.  Kai Mangi jata ka É—aureta a bayan doki yana janta da kafarta mu tafi,Æ´ar ta ce ta jawo mata,data bani haÉ—in kai da har gaisheta zan dungayi tamkar surukata" 

 

Kaman yanda ya faÉ—a inaji ina gani suka É—aure hannayenta ta igiya suka ratayawa doki yajata tamkar wacce  Tayi kisan kai......  Gudu nakeyi ina neman su kunceta cikin magiya da alhini.  

Fincikoni yayi tareda Jefani gefe yana Dariyar mugunta. Su ummu Asma'u ne da ummu hajar sukazo wucewa,ganin alamar samun dama nayi,hakan yasa na Æ™wallawa ummu hajar Æ™ira akan ta taimakeni,amma sabanin fahimtata sai na kalli sun rusuna sun gaidashi alamar girmamawa sannan suka wuce,ko kallona basuyi ba nida nayi Æ™iran agaji karesu. 

 

Kallon takardar daya wullamin nayi,wacce idan nasaka nasaka hannu yana nuna na zama baiwarsa. Tsit nayi kamar ruwa ya cinyeni. Bawanda zai taimakeni,dagani sai mahaliccina babu wanda zai dubeni a mutane kam babu..nasaka hakan a raina. Dukkansu kowa kansa yasani,babu wanda zai iya saka kansa a haÉ—ari dominni. To amma mai yasa zanga laifinsu rayuwarsu suke karewa suma. 

 

Ina kallo kowa yamin kallon fanko marar amfani yabar wajen,daga ƙarshe shima bayan an gyara masa keken dokinsa ya hau ya tafi cikin izza da mulki da kuma kwanciyar hankali,tamkar bai ɗaiɗaita rayuwar baiwa Allah ba kuma baiwar mutane.